← Book details Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 114

Sashe 61

Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin yanayin tashin hankali Moddibo ya tsugunna agefenta na dama yayin da M Jameel ya durƙusa agefenta na hagu kana suka haɗa baki tare da cewa.
“Innayi ya dai me yasame ki?”.
Kallonsu tayi hawaye na cigaba da kwaranya daga idanunta ta sauƙe numfashi kana tace.
“Wa'azinku na jiya ya ratsa jikin mutane wa'azin yasa mutane acikin ɗimuwa wa'azinku na jiya ya tunatar sannan yasa tashin hankali kuma wannan zamanin muna fama da Masifa Allah dai ya yaye mana jiya hankalina atashe yake domin ire-iren abubuwan akeyi!”.
Jinjina kai M Jameel yayi tare da sauƙe numfashi kana yace.
“Hakane sosai ma Innayi amma mu cigaba da addu'a babu abinda ya gagari Ubangiji ga dama yazo watan Ramadan muyita addu'a Allah ya yaye ya taƙaita ya sauƙaƙa mana”.
Atare Modibbo da Innayi suka amsa da.
“Ameeen”.
Miƙewa M Jameel da Moddibo suka atare kana M Jameel ya Kalli Innayi tare da cewa.
“Toh Innayi zamu tafi Tafseer A masallacin makarantar mu”.
Jinjina kai Innayi tayi kana tace.
“Ubangiji Allah ya tsare ku ya kuma sake ɗaukaku”.
Ameeen suka amsa tare da juyawa zasu fita har sun kai ƙofa Innayi ta ɗan ɗaga sautin Muryanta tare da cewa.
“Yauwa wai niko ya batun tafiyar mu ne?”.
M Jameel ya juya tare da cewa.
“Komai ya kammala na tafiyar mu Insha Allah ranan sha biyar ga wata zamu tashi misalin sha biyu da rabi na dare jirginmu zai tashi jibi kenan ba in sha Allah, kuma sai munyi tafsir ɗin ranan ma zamu tafi Taraba”.

Kai ta gyaɗa kana tace.
“Allah ya nuna mana Ubangiji Allah ya kaimu lokacin lafiya amman kuma kace sai kunyi tafsirin ranar?”.
Kai ya jinjina tare da cewa.
“Eh kinga Tara na dare zamu fara, goma zamu tashi, dama kuma kafin mu tafi zamu gama shirin mu duka, tsananin mu Gembulan da taraba kuma tafiyar awa ɗaya da rabine, kinga kenan sha ɗaya da rabi zamu isa, zamu samu awa ɗaya ma acan kafin mu tafi, Abba na kuma su gobe nema zasu tashi”.
Cike da gamsuwa Innayi ta jinjina kai tare da amsawa.
“Allah ya kaimu lfy”.
Ameeen suka amsa a tare kana suka fice mota suka shiga M Jameel ke Driving cikin nutsuwa har suka isa masallacin.

Suna shiga suka fars gabatar da tafsirin kamar yanda suka saba ƙarfe ɗaya da rabi dai-dai suka gabatar da sallah Moddibo yayi limanci bayan sun idar suka cigaba kiran sallar La'asar yasa suka dakata da karatun tare da miƙewa suka gabatar da sallah bayan sun idar suka fito suka shiga mota awannan lokacin ma M Jameel ke Driving har suka iso gida.
Hong M Jameel Yayi Modibbo ne ya fita ya buɗe musu.
Anutse suka fito tare da furta Bismillahi,
Ahankali Moddibo ya gyara tsayuwarsa tare da fesar da sassayan numfashi.
Ido ya tsirawa bishiyar Ayaba da iska ke kaɗawa har na tsawon sakonni goma, sai kuma ya maida kallonsa kan Bishiyar mangoro Idanunsa ya lumshe domin Allah ya sani ganin sirrai ya fiye mishi ganin komai daɗi. sannu ahankali ya riƙa tuna lokacin da yarinyar tashigo gidan har tayi nasaran hawa reshen bishiyar mangoro mai girma da tsawo, da kuma sanda ta faɗo akan yatsun ƙafarsa.
Da sauri ya buɗe idanunsa
Tare da jan dogon tsaki mai cike da tsanar lamuran yarinyar. Idanunsa ya juya jin M Jameel na cewa.
“A.J tunanin mai kakeyi haka ka tsiwara Bishiya ido?”.
Sanyayyar Ajiyar zuciya Moddibo ya sauƙe tare da furzar da iska mai sanyi daga bakinsa kana yasa hannu ya shafa kwantaccen Sajen fuskarsa ya maida kallonsa kan M Jameel da har zuwa lokacin shiyake kallo,Ya mutse fuska yayi kana yace.
“Babu komai”.
Daga haka ya wuce gaba Kai M Jameel ya Girgiza tare da bin bayansa suka shiga Babban falon Moddibo da komai ke kimtse sai tashin ƙamshi yake.

Zama M Jameel Yayi akan 3sitter tare da faɗin.
“Wash' Allah!”.
Kallonsa Moddibo yayi amma bai ce komai ba Bedroom ya nufa tare da janye Hiramin kansa kana ya cire jallabiyar dake jikinsa ya buɗe ƙofar toilet da addu'a
Kana yashiga shawer ya sakarwa kansa yashiga cuɗe jikinsa ya ɗauki kusan minti ashirin kafin ya fito zama yayi agaban Dressing mirrow ya shafa Mai sama-sama kana ya miƙe ya sanya Jallabiya Maroon colour da farin hirami. Feshe jikin sa da turarukansa masu daɗin ƙamshi yayi. shima M Jameel wanka yayi tare da sauya kan jikinsa zuwa Jallabiya fari kana ya ɗaure kansa da Maroon Hirami Sosai sukayi kyau atare suka fito zuwa farfajiyar gidan anan suka samu Innayi da Asma'u na aikin abin buɗa baki kallon Innayi dake soya ƙosai yayi sai kuma ya maida kallonsa kan Asma'u dake dama kunun sadaka na masallaci har ta gama ta rufe sai kuma suka bita da ido.
Kallon Asma'u dake kwaɓa fulawa, kuka, da kanwa M Jameel Yayi yace.
“Yau kuma ɗan wake ake mana ne Asmeey?”.
Kai ta jinjina kana tace.
“Eh dan naji jiya Yaya Moddibo nacewa ɗan wake mukayi ne shiyasa yau nace bari ayi”.
Murmushi Moddibo yayi ya mai binta da wani irin amintaccen yace.
“Kai kin kyauta mun kuwa, kwana biyu bamuci ba inaga tunda azumi ya kama kamar baku yimana shiba”.

Kallonsa Asma'u tare da ce wa.
“A'a munyi amma ranan baka ciba agidan Ummi kuka sha ruwa ranan”.
Jinjina kai yayi yace.
“Toh yau kam Insha Allah zamu dawo muci ɗanwaken nan”.
Murmushi tayi ta na jefa ɗan waken da cokali tace.
“Allah ya dawo daku lafiya”.
Ameeen suka amsa kana suka mayar da Kallonsu kan Innayi dake musu gashin Zabbi sai tashin ƙamshi yake.
Idanu M Jameel ya lumshe yace.
“Innayi zamu wuce”.
Da murmushi afuskarta ta kallesu tace.
“Ubangiji Allah ya tsare”.
“Ameen”,Suka amsa sannan suka fice atare kai tsaye masallacin Juma'ar da suke limancin suka nufa cike da nutsuwa da kuma kamala suka gabatar da tafsirin Alkur'ani acikin Suratul Zariyat yayin da Moddibo ke jan baƙi M Jameel na tafsiri ƙarfe shida dai-dai suka tashi.

Anutse suka fito daga cikin masallacin suka shiga mota akuma dai-dai lokacin wayar M Jameel ya hau ruri cike da nutsuwa ya gyara zamansa tare da ciro wayar daga aljihun sa Sunan Abban sa ke yawo a screen ɗin kallon Moddibo da idanunsa ke lumshe yayi yace.
“Kaga Abba ke kira”.
Ya ƙara sa maganar tare da Amsa kiran yakai kunnensa tare da cewa.
“Assalamu Alaikum”.
Daga ɓangare Abba yace.
“Wa'alaikum Salam Babana”.
M Jameel Yayi murmushi tare da cewa.
“Na'am Abba na”.
Gyaran murya Abba yayi kana yace.
“Nikam laifin me mukayu mukune da kai da Moddibo da baza kuzo mu samu ladan baku buɗa baki agidan nan ba”.
Murmushi M Jameel Yayi yace.
“Ayyah Abba na laifin me zaku mana mukam a duniyar nan gama A.J ɗin yana jinka”.
Ɗan Matsawa kusa da M Jameel ɗin Moddibo yayi kana yace.
“Abbah mai zaku mana A duniya ko kun yi mana abu baza muyi fushi da kuba waye zaiyi fushi da iyayensa?”.

Murmushi Abba yayi yace.
“Toh tun da akayi azumi baku zo kunsha ruwa a gidan nan bafa, abin yana damuna yau fa kwana goma sha uku kenan da baku zo kunsha ruwa agidan nan ba fa”.

Dariya M Jameel Yayi yace.
“Abba ka dai manta mun zo ranan da akayi azumi biyar agidan muka sha ruwa fa”.
Gyara zaman wayar Abba yayi akunnensa kana yace.
“To ai bana nan ba asha ruwan dani ba yau dai so nake kuzo musha ruwa tare”.

Gyara zama Moddibo yayi yace.
“Abba baza mu bari sai gobe ba?”.
“A'a yau nakeson ganinku kuzo musha ruwa anan”.
Cewar Abba.
Jingina kai Moddibo yayi tare da lumshe idanunsa kana yace.
“Toh shikenan Abba zamu zo insha Allah amma bari mu fara zuwa gida”.
Cikin sauri Abba ya Girgiza kai tare da cewa.
“A'a karfa ku makara kuzo komai ya kammala ku kawai ake jira ga kun lokacin ya ƙarato”.
Atare suka haɗa baki wajen cewa.
“Toh shikenan Abba ga munan zuwa”.
Kallon Moddibo M Jameel dake Driving Yayi kana yace.
“Muje?”.
Moddibo kuwa Idanunsa dake lunshe ya buɗe yace.
“Eh muje mana J”.
Kai M Jameel ya gyaɗa kana ya juya akalar motar zuwa Unguwar su Abba ba abinda ke tashi acikin motar face ƙira'ar Alkur'ani acikin Suratu Yusuf tare da Sanyayyar ƙamshin tularensu, Wayar Moddibo dake gaban aljihu ne ya hau ruri Anutse yasanya lallausan tafin hannunsa mai zagaye da gashi ya ciro wayar tare da kallon sunan mai Kiran Malam Arɗo amsa kiran yayi tare da kai wa kunnensa.
Daga ɗaya ɓangaren Malam Arɗo yayi gyaran murya kana yace.
“Wai kai baza kazo kasha ruwa agidana ba ko sau ɗaya ne Moddibo?”.
Murmushin gefen baki Moddibo yayi tare da shafa kwantaccen Sajensa kana yace.
“To Malam ka gayyace mune ai baka gayyace mu shan ruwa ba”.
Da sauri Malam Arɗo yace.
“To na gayyace ku xo yanzu”.
Girgiza kai Moddibo yayi tare da lumshe idanunsa kana yace.
“Toh ba yau ba dai sai gobe”.
Da sauri Malam Arɗo ya zare Ido tare da cewa.
“To duk abubuwan da nasa aka dafa muku kuma fa?”.
Murmushin gefen baki Moddibo ya kuma yana imagine fuskarta malam Arɗo kana yace.
“Ka bawa mutanen gida suci ba rabon mu bane
gobe kuma Idan Allah ya kaimu kama na namu kuma ayi da mutanen gida duka”.
Cikin sauri Malam Arɗo yace.
“Wato dai kai ko yaushe sai ka kawo min sabon tsari acikin al'amari na ko”.
Murmushi M Jameel yayi shaƙuwar dake tsakanin Moddibo da malam Arɗo ya wuce zaton mutane.
Moddibo kuwa ɗan Murmushin dake ƙarawa fuskarsa kyau yayi kana yace.
“Ai dole dai kam”.
Dariya Malam Arɗo yayi yace.
“Dama gobe ka tabbatar lokacin shan ruwa yana yi na ganka, ba sai na kira ba ka gaishe da Jamilu kar ku cinye min kati na”.
Ya ida maganar tare da katse kiran.
Murmushi M Jameel Yayi kana yace.
“Malam Arɗo ko?”.
Murmushi kawai Moddibo yayi yana motsa laɓɓansa alamar tasbihi yake.
Chapter 61 · 0% Book details