← Book details Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 98 OF 114

Sashe 98

Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Cikin sauri tace.
“Bafa za'a kashe Jameel ba, kawai Alhj idan zaka nemi ragi ka nemi ragi, sai kace baka sha zafin neman kuɗin ba zaka ɗauka agabtale ka basu kamar ba kasan darajar suba, amma babu yanda zaka ɗauki wannan maƙudan kuɗin ka bayar akan Jameelu!”.

Cike da mamaki Abba ya kalleta kana cikin ɗaga sautin murya yace.
“Karima to idan ban bada kuɗi akan Jameelu ba akan wa kike so in bayar? Shin Karima anya Karima?”.
Wani irin kallo ta masa kana cikin sauri tace.
“Anya me?”.
Dai-dai lokacin Hajiya Turai ta shigo baki ɗaya ta hargitse babu walwala afuskarta ta kalli Hajiya Karima kana tace.
“Ai dai kam abin nata da mamaki, idan bai ɗauki kuɗi ya bayar akan Jameelu ba akan wa kike so ya bayar?”.
Sai kuma ta maida kallonta kan Abba da idanunsa ke lumshe kana tace.
“Aini Alhj naga ƙoƙarin ku ma da har kuka iya neman ragin da suka rage muku, kuma ai sunyi ƙoƙari ni dai anawa tunanin kada ku kuskura kada ku sake yin batun ragin wasu kuɗin, suje su kashe mana yaro abanza idan aka kashesa mai son sa keda asara wanda bai sonsa kuma bai damu ba”.
Ta ida maganar hawaye na ciko kwarmin Idanunta.

Hajiya Karima kuwa wani kallo ta watsa wa Hajiya Turai tare da cewa.
“To mekike nufi?”.
Taɓe baki Hajiya Turai tayi kana tace.
“To ai gaskiya ne duk mai son Jameelu ba zai so ace za'a sake neman ragi ba”.
Taɓe baki Hajiya Karima tayi tare da watsa mata kallon banza kana tace.
“Kenan kina nufin Ni bana son Jameelu?”.
Hannu Hajiya Turai ta buɗe kana tace.
“A'a wannan ke ki kafaɗa da bakin ki amma dai shawaran da kika kawo ba shawara me kyau bace”.
Hannu Abba ya ɗaga musu tare da kallon Hajiya Karima dake kumfar baki kana yace.
“Bana son hayaniya ya isheku.
Dan Allah kubarni inji da abinda ke damuna”.
Kai Hajiya Turai ta gyaɗa tare da tsuke bakinta alamun itama ba hayaniyar take soba.
Cikin sanyi ta kalli Abba tare da cewa.
“Alhj ga Million biyu a Account ɗina zan bayar ahaɗa”.
Wani shegen kallo Hajiya Karima tabi Hajiya Turai dashi kana cikin taɓe baki tace.
“Hmmm munafurci dai da neman gindin zama haddasu kaza acikin cin danƙo”.
Cikin sanyi Abba yace.
“Nagode Turai Allah ya saka da alkhairi ayanzu kyauta koda na Naira biyar aka bani ita ina buƙatar ta, xansa acikin tumunin kudin da za'a karɓo Jameel”.
Cikin sauri Hajiya Karima tace.
“Nima Allah ya bani in bayar”.
Kai ya gyaɗa kana yace.
“Ameen”.
Juyawa tayi ta fice Hajiya Turai kuma ta zauna gefensa tana sake tausansa.

Acikin kwanaki biyu Moddibo ya saida gwala-gwalan da kuma motocinsa dana M Jameel Yayi total ɗin kuɗin sun kama Million ashirin da biyar ya turawa Abba cikin account ɗin sa Alhamdulillah yanzu akwai Million casa'in da biyar acikin account ɗin Abba Aɓangaren Abban ma yana cigaba da fafutuka ganin ya samu kuɗi.
Acikin kwanakin baki ɗaya abubuwa sun kankama baki ɗaya sun sake maida hankalinsu kan neman kuɗin suga sun samu sun haɗa yau ya kama kwanan M Jameel goma kenan awajen Kidnappers din kana yau kwana biyu rabon Abba da Moddibo suyi waya da M Jameel Misalin huɗu na yamma Moddibo ya bar gidan Abba ya nufi gidansu bayan sun sake tattauna wa.

Acan ɓangaren Boka Kar'uzu kuwa Hajiya Bunayya da Hajiya Lami ce gurfane agabansa cikin wata sandararriyar murya Boka Kar'uzu ya kece da wata mahaukaciyar dariya tare da jujjuya gashin dake wangamemen tafi hannunsa kana ya ɗago kansa tare da Kallon Hajiya Bunayya da jajayen Idanunsa da suka tara kwantsa yace.
“Kin tabbatar gashin yaron ne dai ko?”.
Cike da ƙwarin gwiwa Hajiya Bunayya ta jinjina masa kai tare da faɗin.
“Tabbas na tabbatar Boka Kar'uzu Uban bokaye La'anannen Uban La'anannu Mugu Uban mugaye tsinanne Uban tsinannun wannan gashin kan Ramadan ne domin dana shafa turare na shafa kansa bayan na fita naga gashi ya manne ahannu shine na tattare na kawo maka kamar yadda ka umarceni.
Wata mahaukaciyar dariya. Boka Kar'uzu ya sheƙe dashi wanda yasa bukkan da suke ciki ya hau girgiza cike da jin daɗin kirarin data masa yace.
“Hhhhh magana ta ƙare Ƙaramar la'ananniya me kafirar zuciya aiki ya riga yayi anwuce babinsa saura na Babban”.

Girgiza kai Hajiya Bunayya tayi tare da cewa.
“Agama da batun Ramadan ɗin kafin ayi na Haiydar to babu matsala wannan ba damuwa bace”.
Ajiyar zuciya Hajiya Lami ta sauƙe kana tace.
“Ni kuma Boka yanzu Abban Samira na nan amma nanda sati biyu masu zuwa zai tafi aikin Umrah, shiyasa nayi shiru da batun zuwan Samira nan mu bari sai mahaifinta ya tafi kaga ba kowa agida da banaso daga gidan Hajiya Bunayya arika zuwa ana daukan ta saboda sa idanawa. Amma Alhj na tafiya idan ya kama ma ta dawo gidan ka idan kuma kaine ma zaka rinƙa kwana idan gari ya waye ka dawo to duk daya”.
Wata dariya mai masifar ƙara Boka Kar'uzu ya kece dashi kana buga ƙafarsa na hagu wanda baki daya ƙura ta buke wajen kana yace.
“Hhhhh saishi Boka Kar'uzu Uban bokaye La'anannen Uban La'anannu Mugu Uban mugaye tsinanne Uban tsinannun shaiɗani Uban shaiɗanu babu wata matsala da zaran ya tafi zan zo Ni da kaina dan zamu fi sakewa agidan naku acan ma zan tare in ragargaji sabon budurci”.
Kai Hajiya Lami ta gyaɗa tana murmushi kana tace.
“Yanda kake so haka za'ayi”.
Daga nan suka miƙe suka fita ta baya kamar yanda suka shigo suka nufi gida ransu fari soll musamman Hajiya Bunayya.

Acan ɓangaren Khausar kuwa sanye ta fito cikin hijabi maroon mai facemaks kafadarta rataye da jaka fari sol jikinta na fitar da sanyayyan ƙamshin turaren Oud Ma'aruf cikin yanayin sanyin ta da tun ɓatan M Jameel bata dawo dai-dai ba ta kalli Mommy dake zaune kan 2sitter kana tace.
“Mommy zan tafi”.
Kai Mommy ta gyaɗa kana tace.
“To kice ina gaida Ummi”.
Kai Khausar ta gyaɗa cike da nutsuwa ta fita tare da sanya Platshoe fari Anutse ta nufi coumpund ɗin dai-dai lokacin da Amina da Uncle Naseer suka shigo hannunsu sarƙafe da juna kallo ɗaya Khausar ta musu ta kawar da kanta gefe kana ta lumshe Idanunta.

Ido Uncle Naseer ya zuba mata tare da shafa kansa kana cikin sakin fuska yace.
“A'a Khausi ina zuwa da yamma nan?”.
Batare data sake kallon inda suke ba kana cikin sanyin murya tace.
“Zanje gidan su Asma'u ne”.
Langwaɓar da kai yayi kana yace.
“Ai haka dai maganar bata haɗa muba Khausar, ashe wai Malam Jameel aka sace Agaskiya garin nan ya fara bada tsoro bari muje na kaiki in jajantawa Ummi”.

Girgiza kai Khausar tayi kana tace.
“A'a kabari kawai”.
Cikin sauri Amina ta watsawa Khausar harara kana ta maida kallonta kan Uncle Naseer Shima ta hararesa.
Uncle Naseer kuwa ganin kallon da Amina ke jifansu dashi yasa ya ware idonsa tare da sakar mata da lallausan murmushi kana yace.
“Ohh Baby Colm down mu nayin Auren mu zan ɗauke ki mu gudu mubar ƙasar nan, kafin muma Akinnafemu tunda kinga anfara tsincr ƴaƴan masu kuɗi an ɗauke Malam Jameel next target ɗin su ni za'a ce za'a saɓe ko ke, kafin ma su ankara zamu gudu abinmu.
Dariya Amina ta ƙyalƙyale dashi tare da manna kanta ajikin damtsen hannunsa.
Khausar kuwa cikin sauri ta kawar da kanta gefe tare da lumshe Idanunta.
Ahankali Uncle Naseer ya ɗago kansa tare da tsura wa Khausar Ido tabbas soyayyanta acikin jininsa yake har yau har gobe zuciyarsa na muradin Khausar, itace burinsa Kawai zai Auri Amina ne domin cikar Burinsa amma Khausar itace muradinsa.

fesar da iska mai sanyi yayi yana jin wani irin yanayi agame da ita kana yace.
“Khausi jirani in ɗauko sakon Uwaniyona inzo in kaiki?”.
Da sauri Amina ta janye kanta dake manne adantsensa kana tace.
“Ka kaita kuma?”.
Kai ya gyaɗa tare da yimata raɗa akunne yace.
“Yes My dear wife ai jaje ne".
Ashagwaɓe ta girgiza kai tare da cewa.
“Gaskiya Ni dai Uncle Naseer bana so ka tafi ka barni”.
Shafa fuskarta yayi kana yace.
“Bafa daɗewa zanyi ba”.
Khausar kuwa cike da takaicin abinda sukeyi tace.
“A'a Uncle Naseer ka bari ganan Haiydar ma zai kaini da mashin ɗinsa”.
Kai ya gyaɗa still Idanunsa na kanta yace.
“Ok”.
Dai-dai lokacin Haiydar ya fito daga sashen Abbansu hannunsa riƙe da key mashin dinsa.
Kallon Uncle Naseer da Haiydar yayi da murmushi afuskarsa yace.
“Uncle Naseer yau dai Addah Khausy ta yarda in jata amashin ɗina”.
Cikin alamun so Naseer yace.
“To ayi a hankali dai banda fifita”.
Dariya Haiydar yayi tare da cewa.
“Uhmm aikam zata sha fifita”.
Murmushi Uncle Naseer yayi tare da cewa.
“Dan Allah ka jata ahankali kada kayi mana asara”.
lumshe Idanunta tayi baki ɗaya bata da wani kuzari ɓatan M Jameel yayi masifar ratsata hakan yasa ko magana bata fiye yiba daga Um-sai Um-um.
Haiydar kuwa mashin ya ɗauko tare da ɗaukar ta suka fice kana Amina da Uncle Naseer suka shiga ciki.
Chapter 98 · 0% Book details