← Book details Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 114

Sashe 47

Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Moddibo kuwa jinjina kai yayi kana yace.
“Toh yaushene tafiyar?”.
Kai M Jameel ya Girgiza tare da faɗin.
“Toh dai ban sani ba tukun”.
Moddibo dake ƙoƙarin shan kwana yace.
“Yawwa zanyi ƙoƙari inga na gama rubutunan idan zaka tafi sai ka tafi min dashi”.

Shi kuwa M Jameel Kai ya gyaɗa cike da gamsuwa da maganarsa yace.
“Toh shikenan hakan ma yayi Allah yatemaka”.
Moddibo ya amsa da.
“Ameen”,tare da parking motar bayan ya isa ƙofar gidan su M Jameel.
Sauƙa M Jameel yayi tare da yi masa sai anjima, kai Moddibo ya gyaɗa kana yaja motar ya tafi.

Yana isa gida bayan yayi Parking motarsa ya wuce Bedroom ɗinsa kasancewar yana da alwala yasa ya ɗauko abubuwan buƙatar sa na rubun Alkur'ani da yakeyu kana yaciigaba da rubutu, saida aka kira sallar La'asar sannan ya tashi yaje masallaci ya gabatar da sallan la'asar, bayan ya dawo kuma, yazo ya cigaba da rubutun, yana yi yana karantar Suratul Kahfi kasancewar yammacin jumma'a ne, sai misalin ƙarfe biyar kafin ya ajiye Kur'ani.

Acan ɓangaren Innayi kuwa zaune take akan kujera ’yar tsugunno acikin kichen tana juya miyar zogala wanda yaji namar Rago da kuma wadataccen man Shanu da wake yana tashin ƙamshi bayan ta sauƙe miyar ta ɗaura Ruwan shayi daya ji na'ana, kaninfari da kuma ɗanyan citta yana tafasowa yana ƙamashi mai daɗin shaka.
Flaks guda biyu ta ɗauka ta juye sannan ta ɗauki ɗaya ta nufi sashen Moddibo dashi.

Acan gidansu Asma'u kuwa bayan tafiyar Moddibo da M Jameel Khausar ta miƙe tare da fitowa falon Idanunta akan Ummi tace.
“Toh Ummi mu tafi ba dama kince gidan mu zaki jeba”.
Jinjina kai Ummi tayi tace.
“Eh Khausar inaso naje na duba jikin Mommyn ki”.
Ba tare data zauna ba tace.
“Toh Ummi mu tafi”.
Kai Ummi ta jinjina kana ta miƙe suka fita su ukun Bashir ƙanin Asma'u ne kaɗai suka bari agida Ummi da kanta take Driving Khausar da Asma'u na baya suna hira.

Acan ɓangaren su Hajiya Bunayya kuwa Kallonsu Boka Kar'uzu yayi cikin wata razananniyar tsawa yace.
“Wannan maganin ya riga daya ɓaci, ta lalata komai yanzu sai anyi aikin dai-dai-ta fuskarta ma tukunna kafin azo ayi aikin jawo hankalinsa, yaran nan biyu da kuka gani kuke magana akansu yarane dasu na tsaye da sunan Allah da riƙo da Ibada, musamman ma Moddibo da kuke magana akansa kwata-kwata baya rabuwa da alwala ajikinsa ka masa zaiyi wuya”.
Cikin tashin hankali Hajiya Bunayya ta juya ta kalli Hajiya Lami da duk tagama shiga ruɗu.

Boka Kar'uzu kuwa cigaba yayi da cewa.
“Yanzu sai munyi aikin wata uku kafin fuskarta ya dawo dai-dai sannan sai tabar Sallah na tsawon watanni shida kafin mu samu mu fara aiki shiko aikin za'ayi na tsawon watanni shida kafin ta fara nuna masa muradanta”.
Kana ya maida kallonsa ga Hajiya Lami data zabga uban tagumin tana kallon sa cikin Muryansa Mara daɗin Amo yace.
“Kema naki hakanne sai tayi wannan watannin”.
Dafe ƙirji Hajiya Lami tayi tare da zare Ido kana tace.
“Har Watanni shida shida Boka kafin wannan lokacin fa har sun kusa gama Ss 2 ma zasu tafi 3 awannan lokacin daka ɗiba mana”.
Cikin tsawa da hargagi yace.
“Dole sai anbi wannan ƙa'ida idan ba haka ba babu abinda zaku samu ya tafi dai-dai!”.

Ta gumi Hajiya Lami ta rafka kana tace.
“Shikenan Babu damuwa Indai burinmu zai cika tunda ai makarantar basu gama ba zamu bi ahankali”.
Ya yamutse fuska tare da watsa musu wani kallo da jajayen Idanunsa cikin wata murya mara daɗin Amo yace.
“Ƙa'idah ne yanzu zata je tayi ta aiki da wannan maganin na tsawon watanni ukku fuskarta zai koma dai-dai a Idanunsa sannan bayan wannan kuma tsawon watanni kar kuyi sallah daga nan kuma zan fara haɗa magani na tsawon watanni shida kafin su tun kare su daga magana”.

Murmushin Hajiya Bunayya tayi tare da gyara zamanta tana fuskantar Boka Kar'uzu da kyau tace.
“Toh shikenan ba matsala.
Amma fa ciki ya zube aiki yayi kyau!”.
Wani irin mahaukaciyar dariya mai matuƙar razanarwa Boka Kar'uzu ya saki da faɗin.
“Ai dama dole aiki zaiyi kyau idan kun bishi da ƙa'ida wannan ma ku kuka je kuka ɓatashi!”.

Jinjina kai Hajiya Bunayya tayi tare da cewa.
“Godiya muke Boka ana gaba zamu kiyaye”.
Kai ta gyaɗa kana yace.
“Toh ya batun aikin toshe mahaifar!?”.
Kai Hajiya Bunayya ta Girgiza tare da faɗin.
“Boka muga ma da batun aikin Amina tukunna, kaga ga yayar ta ma tana zaune ba tayi aure ba, sannan ga itama Aminan ta girma shiru, amma ita kace rabonta ne yayi nisa abin ya ɗaure mana kai mun rasa yanda zamuyi har wajen ƙan wata na tura ta Aƙasar Khautal ko zata samu rabonta acan amma acan ɗin ma shiru kuma kaga ta dade da gama karatu amma har yau Auren bai samu ba zamu jona mata wani makarantar ta fara zuwa jami'a kawai, tunda itama kanta Amina dan wasa da karatun take da tayi shekaru biyu da gamawa amman sai aikin maimaita aji gashi har shegiyar yarinyar nan ta kusan cimmata”.

Kai Boka Kar'uzu ya ɗago daga bugun ƙasar da yake tare da cewa.
“Babu matsala ita Aseeya rabonta yana nan tafe”.
Cike da jin daɗi Hajiya Bunayya tace.
“Godiya muke Boka Uban bokaye La'anannen Uban La'anannu Mugu Uban mugaye Hatsabibi Uban Hatsabibai!”.

Wata mahaukaciyar dariya Boka Kar'uzu ya kece dashi cikin jin daɗin kirarin da ta masa yace.
“Aikin ki zai tabbata ƙaramar la'ananniya Aljani ɗan ƙundalu mai ido Atsakiyar kai zai cika miki burinki ku fita da ƙafar hagu ta baya!”.
Miƙewa sukayi suka fice kamar yanda ya faɗa ransu fesss suna tsalle da kafar hagu kamar kutaren agwagi...

Acan ɓangaren su Ummi kuwa bayan sun isa gidan su Khausar sun gama gaisawa da Mommy da kuma Hajiya Ruƙayya da har zuwa lokacin suke tare.
Mommy tana murmushin tace.
“Ummi ya fama rigimar Khausar, ɗazun nan tace zata je ta duba ki ashe kina hanya”.
Dariya Ummi tayi tace.
“Ai lalle dai kam Hajiya Aysha babu ruwan Khausar ai”.
Murmushi Mommy tayi tace.
“Kina dai karate ta Amma Khausar ba dai rigima ba?".
Aunty Ruƙayya tayi Dariya kana tace.
“Ai Khausar bata da rigima ita dai baza'ayi gulma agaban Idanunta bane, sannan ba za'a cakake ta ta haƙura ba, kunga kuwa ai da gaskiyar ta”.
Dariya Ummi tayi tace.
“Aikam de lalle da gaskiyar ta”.
Ita kuwa Mommy Dariya tayi kana suka cigaba da hira.

Washe gari Asabar suka koma makaranta Khausar kuwa cikin tsoro da fargaban abinda Moddibo zai mata ta zuciyarta ya riƙa bugawa da ƙarfi lokacin da yashigo raba musu questions pepar tayi zaton zai mata hukunci sai taga baima kalli inda take ba.
Shikuwa Moddibo kawai ya fita sabgarta ne ganin alamar bata da cikikakkiyar nutsuwa in ya biyata zata zarar dashi.

Akwana atashi haka al'amura suka cigaba da tafiya komai yana wakana Moddibo ya kammala rubutun Kur'aninsa ya bawa M Jameel ya tafi wa da Sheykh Jabeer Habibullah Nuruddeen Joɗa na Adamawa.
Satin M Jameel biyu ya dawo tare da shedawa Moddibo ya karɓa harma ya fara dubuwa Insha Allah nan kusa zai turo masa.
Karatun su Khausar na tafiya komai na tafiya dai-dai yanda ake buƙata Anyi gasar musabaƙa jihar Taraba Makarantarsu Khausar Al'ansar Academic school_ shine yazo na farko Khausar ce tazo na ɗaya a haddar Izu arba'in yayin da Asma'u tazo na biyu Aishatu Abdullahi tazo na uku ,A haddar Izu biyar Raudat ce tazo na ɗaya kyaututtuka masu yawa suka samu kana suka dawo cike da nasarori.

Yanzu karatu na tafiya akwana atashi babu wuya wasa gaske yanzu Khausar suna Ss2
thirth term suna shirye shiryen fara Exam gashi kuma Ramadan ya kawo kai yayin da ake ta shirye shiryen shiga Ramadan tuni Gwamnatin Jaha ta rarraba malamai zuwa inda ko wanne zaiyi Tafseer kamar yanda aka saba Moddibo da M Jameel antura su Babban Masallacin juma'a dake ƙofar sarki Gembu anan zasuyi Tafseer ɗin su na Ramadan.
Lokaci natafiya karatun su Khausar na sake tafiya yanda ake buƙata tsakanin Amina da Khausar babu wani jituwa hasalima gaba ce domin har gobe M Jameel na sake nuna kulawa ta musamman akan Khausar yayinda Moddibo kuwa kwata-kwata baya lura da al'amuran Khausar hasalima idan tayi laifi zai yanke mata hukunci fiye dana kowa wannan dalili yasa basa shiri kana babu wata jituwa atsakaninsu.

Alhamdulillah ayaune Khausar suka rubuta exam na ƙarshe kuma da Geography suka rufe.
Taro Moddibo yasa aka haɗa kamar yanda aka saba a kowani ƙarshen hutu ko baki ɗaya Malaman sun haɗu awajen zamansu haka ma ɗalibai Khausar da Asma'u na zaune awaje ɗaya.

Shi kuwa Moddibo cikin nutsuwarsa da kuma kamala ya nufo wajen as usual cikin shigar sa kaman ko yaushe sanye yake cikin Jallabiya fari kansa naɗe da hirami idanunsa sanye da ɗan siririn farin glass daya ƙawata kyawun fuskarsa yalwataccen sajensa zuwa gemunsa ya kwanta luf-luf yana sheƙi.
Cikin tsantsar nutsuwa da sanin darajar kansa ya gyara zaman microphone ɗin tare da hura iska kaɗan kana yayi gyaran murya yace.
_“Bismillahir Rahmanir Rahim, Innalhamdulillah nahmaduhu wanasta'inuhu wanastaghfiru wa'nazubillahi min shururi anfusna wamin sayyi ati a'amalina, man yahdillahu fala mudillahlah waman yudlil fala hadiyala, Wa'ash hadu Allah ilahalillahu, Wa'ash hadu anna Muhammadu Abduhu wa Rasulullah (S.A.W)”._

Sai kuma ya ɗan lumshe idanunsa tare da sauƙe Ajiyar zuciya kana ya cigaba da cewa.
“Duk kan yabo da godiya su tabbata ga Allah subhanahu wata'ala mai kowa mai komai, da yakawo mu wannan lokaci da muke shirin karɓan hutu saboda gabatowan wannan wata mai falala, haƙiƙa watan Ramadan wata ne mai falala da rahma wanda duk kan musulmi yake da burin ganinsa.

Baki ɗaya wajen shiru yayi kowa ya maida nutsuwarsa zuwa garesa yayin da Samira kejin aduk lokacin data mallakesa babu macen da takaita sa'a a faɗin wannan duniya tamu ta bani adam.
Malam Arɗo kuwa Aransa yake jin Moddibo ne Garkuwa kuma ginshiƙin makarantarsa.
Moddibo kuwa cikin yanayin sanyin Muryar sa mai cike da nutsuwa ya cigaba da cewa.
“An abu Huraira ta radiyallahu anhu,
_Manƙama Ramada Imanan Wahtisaban gufra lahu mata ƙaddama min zambi muttafaƙun Alaik”_
Chapter 47 · 0% Book details