← Book details Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 114

Sashe 92

Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin yanayin gajiyawa da ɗimuwa Abba ya buɗe Murfin motar ya fito kana Moddibo da sauran ma duk suka fito.
Cikin raunin murya me nuni da razani Abba yace.
“Gashi mun biyo har nan ma amma baya nan, to mu gwada zuwa asibiti mu duba ko dai yayi hatsari ne ko yaya”.
Cikin raunin murya Moddibo ya Girgiza kai kana yace.
“Abba hatsari kuma? Ai da hatsari ne da munga mota kuma da ankira mu”.
Kafin Abba yace wani abu Innayi ta kalli Moddibo tare da cewa.
“Eh muje dai asibitin saboda Kore shakku”.
Jinjina kai sukayi tare da shiga motar kana suka nufi Asibitin.
Ahankali Moddibo ya kalli Innayi kana yace.
“Toh wani asibitin zamuje kin san dai bawasu manyan asibiti muke dasu ba”.
Cikin sanyi malam Ahmad yace.
“Mu fara zuwa babban asibitin idan yaso sai mu duba sauran daga baya”.
Kai Moddibo ya gyaɗa tare da nufar babban asibitin Abba na biye dasu.
Suna isa suka tarar da gate din asibitin arufe kasancewar har biyu tayi,sauran asibitin suka shiga zagayawa amma ko wanne arufe in sun buga an buɗe musuma in sun shiga bashi ba lbrinsa.
Cikin han zari Abba ya cewa Moddibo su nufi Private hospital ɗin Abba haka kuwa akayi.
Suna isa Moddibo ya sauƙa tare da nufar cikin Hospital kana ya tambayi Norse dake aiki ko M Jameel yazo suka ce a'a juyawa yayi ya shiga motar kana suka ci-gaba da nemansa.
Wasa gaske fa babu Jameel ba dililinsa ba motarsa, gaba ɗaya sun shiga ruɗu da zulumi gamida tsoro.

Misalin ƙarfe uku hankalin su ya kai ƙololuwa wajen tashi baki ɗaya sun cika da damuwa zuwa wannan lokacin sun tabbatar ba lafiya domin M Jameel baya yawo sannan Gembulan ba wani babban gari ne da keda charking point ba bare su kai report.
Moddibo kuwa banda tasbihi da kiran sunan Allah babu abinda yake Aransa yayin da kasala da mutuwar jikinsa ke ƙaruwa fiye da farko kana ga hadarin da zuwa yanzu yayi gangami asama da alamar ruwa na gab da sakƙowa, dan tuni aka fara yayyafi.

Abba kuwa tunda suka fito a asibiti ya kifa kansa ajikin motar zuciyarsa na bugawa da masifaffen ƙarfi cikin raunin murya yace.
“Acikin wannan daren ga hadari na kira layukan Jameeluna duka basa shiga a wannan yanayin ina Jamilu na ya shiga”.

Cikin raunin murya mai cike da karaya Modibbo ya fesar da numfashi mai zafi kana yace.
“Yanzu acikin daren nan ina J yake?.
Wani hali yake ciki?.
Wani irin yanayi yake cikin a wannan daren da kuma hadarin da yake tasowa ina J ɗina yake!?”.

Cikin ƙarfin hali Malam Ahmad ya numfasa kana yace.
“Insha Allah ba komai mu bari muga zuwa safiya abinda Ubangiji zai yi”.

Cikin tsanananin rauni Ummi ta kife kanta da jikin kujeran Motar kana ta fashe da wani Marayan kuka mai gunji”.

Cikin damuwa da kuma tausayawa Abba ya juya tare da kallon Malam Ahmad kana yace.
“Malam ku tafi gida kaima Moddibo ku koma gida da Innayi kada ruwan nan ya saƙƙo muna nan duk inda ya kamata mu duba mun duba baya nan bari mu gani zuwa safiya”.

Girgiza kai Moddibo yayi Araunane yace.
“Abba ya za ayi mu koma mu shiga cikin gida mu samu mafaka bayan bamu san halin da J yake ciki ba. Abba ina kake tunanin zamu koma mu samu nutsuwa acikin wannan yanayin bayan bamu san ina J yake ba!?”.

Kallonsa Abba yayi cike da rauni yace.
“Toh Aliyu ina zamuje mu duba?, Duk inda ya kamata mu duba mun duba sannan wayoyinsa basa shiga wannan shine babban tashin hankalina mu koma gida muyi alwala mu sanar wa Ubangiji halin da muke ciki Aliyu”.
Jinjina kai sukayi atare cike da gamsuwa da abinda yace sam tashin hankali da ruɗanin da suke ciki yasa sun kasa samun nutsuwar da zasuyi addu'a.
Kai Moddibo ya gyaɗa kana yace.
“Toh Abba”.
Sannan suka shiga mota Abba yaja ya nufi gidansu cikin tashin hankali da ɗimuwa yayin da Hajiya Karima ke kuka Abba kuwa ko da kallonta ya gagara yi bare kuma ya iya lallashin ta.
Ya yinda Moddibo ya nufi gidan Ummi babu abinda ke tashi acikin motar banda sheshsheƙan Kukan Ummi ta rasa shin wani irin tunani zata yi shin ina Jameelunta yake awannan tsohon daren Akuma irin wannan lokacin.
Moddibo kuwa cikin tsananin damuwa da zulumi da macewar jiki ya cigaba da Driving har ya isa kofar gidan yayi Parking.
Fita Malam Ahmad yayi Ummi ma ta sauƙa suka nufi cikin gidan.
Ganin hasken mota yasa Bashir miƙewa da sauri tare da buɗe ƙaramin gate ɗin.
Cikin sauri Asma'u da har zuwa lokacin take zaune ta ɗago kanta tare da miƙewa ta riƙe hannun Ummi kana tace.
“Ummi Ina Yaya Jameel Ummi kunga Yah Jameel?".
Cikin sanyi Ummu ke jujjuya mata kai.
Ita kuwa a ɗimauce tace. “Ummi to ina yashiga awannan daren dubi hadari fa wani hali yake ciki?”.
Girgiza kai Ummi tayi tare da fashewa da kuka kana tace.
“Ban saniba Asma'u Bansan inda Jameelu na yake ba, bansan halin da yake ciki ba Asma'u zuciyata zafi take jinake tamkar kaina zai rabe gida biyu!”.
Aruɗe Asma'u tace.
_“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n Allahumma Ajirni fii musibati wa'ahlifli khairan minha_, nashiga uku Yah Jameel”.
Cikin sauri Malam Ahmad ya riƙe hannun Asma'u ganin kamar bata hayyacinta kana yace.
“Subhanallah Asma'u da iliminki kike kirawa kanki shiga uku kada ki sake haka Addu'a ya kamata mu masa kunji ko?”.
Kallonsa ya mayar kan Bashir kana yace.
“Kuzo mushiga muyi masa addu'a ayanzu ba kuka Jameelu yake da buƙata daga wajen muba face adduoi”.
Kai suka gyaɗa sannan ya sake hannun Asma'u ya riƙe na Ummi Bashir kuma yarike hannun Asma'u suka shiga ciki kai tsaye ko wannensu toilet yashiga ya ɗaura Al'wala kana ya fito suka shimfiɗa Sallaya tare da fara jera nafillah suna roƙon Allah daya fitar da M Jameel aduk halin da yake ciki.

Moddibo kuwa suna isa gida yayi Parking tare da rufe ƙofar kana ya wuce falonsa yayin da Innayi ma tashige sashen ta yana shiga kai tsaye toilet dake falon ya shiga ya ɗaura alwala kana ya fito ya shimfida Sallaya cike da nutsuwa ya fara Sallah kana duk sujjadar da zaiyi sai ya roƙi Ubangiji ya kare J ɗin sa aduk inda yake”.
Baki ɗaya su haka suka raya wannan daren cike da bautar Ubangiji tare kuma da rokon Allah daya bayyanar da M Jameel kana Allah yaraba sa da duk kan sharrin Mutum da Aljan.

Bayan an kira Assalatu Moddibo ya fito ya nufi masallaci ana idar da sallah kai tsaye gidan Abba ya nufa.
Yana isa kiran Ummi na shiga wayarsa ciki. Sanyin jiki ya ɗaga wayar tare da kaiwa kunnensa kana yayi Sallama.
Cikin dashashshiyar murya Ummi ta amsa Sallamar sa kana tace.
“Babana ya labarin Jameelu na?”.
Cikin sanyin murya yace.
“Ummi nima gashi yanzu nazo wajen Abba naji ko ya dawo gida”.
Dai-dai lokacin Abba ya buɗe gate ya fito ganin Moddibo tsaye yasa ya isa wajensa ahankali Moddibo ya zare wayar daga kunnensa bayan yace anjina zai kirata.

“Aliyu dama yanzu zanje wajenka”.
A hankali Modibbo yace.
“Abba to yanzu ya zamuyi”.
Numfashi Abba ya fesar tare da cewa.
“To mu tafi police station Jiya Baki ɗaya ba muyi tunanin zuwa can ba”.
Kai Moddibo ya gyaɗa kana suka shiga motarsa yaja Abba kuwa jingina da jikin kujera yayi baki ɗaya zuciyarsa ta tushe ya rasa wani irin tunani zaiyi yayin da Idanunsa suka tsats-tsafo da ruwan hawaye.
Moddibo kuwa Driving yake amma baki ɗaya baya fahimtar komai ko gilmawar mutum ya gani sai yaga kamar J ɗin sane.
Suna isa yayi Parking atare suka fito daga motar tare da shiga station din Dpo dake ƙoƙarin fita yayi Murmushi tare da cewa.
“Alh Bashiru maidala Barka da zuwa kaine da kan ka?”.
Jinjina kai Abba yayi kana cikin sanyin murya yace.
“Na kawo report ne ɗana Jameelu ne bamu ganiba”.
Cike da mamaki da kuma al'ajabi Dpo da sauran folisawan suka ce.
“Ɗan ka Jameelu kuma?”.
Kai Abba ya gyaɗa kana yace.
“Eh tun jiya ba agansa ba kuma babu motarsa sannan akira layukan sa basa shiga”.
Cike da jimami Dpo yace.
“Subhanallah Alhj mai yasa baku kawo report tun dare ba!?”.
Numfashi Abba ya fesar kana yace.
“Yanayin hadari ne sannan baki daya hankalin mu baya Jikin mu sai mukayi tunanin bari muyi addu'a mu kaiwa Ubangiji kukan mu”.
Daga nan yayi miki bayanin dukkan abinda ke tafiya.
Kai Dpo ya gyaɗa tare da cewa.
“Toh shikenan Alhj insha Allah yanzu zamu kira hedquater mu na cikin Taraba afaɗa musu halin da ake ciki”.
Kai Abba ya gyaɗa kana yace.
“Toh shikenan mun gode”.
Moddibo kuwa tun da suka shiga ya jingina da jikin bango Ya Lumshe Idanunsa yana motsa laɓɓansa alamar tasbihi bai ce komai.

Wunin wannan ranan baki ɗaya haka gidaje uku sukayi sa cikin zullumi,fargaba da kuma tsantsar tashin hankali Moddibo kuwa duk bayan minti biyu sai ya kira Number M Jameel aƙalla daga Jiya da daddare zuwa yau ya kira wayarsa yafi sau ɗari.
Acan ɓangaren Ummi ma haka yakasance bini-bini zata kira layin sa amma amsar ɗaya ake basu shine Switch off.
Haka zalika Abba time to time zaiyi try number M Jameel amma akashe Wunin wannan ranan baki ɗaya sunyi zuru-zuru dasu kallo ɗaya zaka musu kasancewa suna cikin tsananin tashin hankali da ɗimuwa duk inda ya kamata su nema ko su bincika duk sun nema sun bincika amman ba lbri.
Abba kuwa zama yayi afalonsa tare da kira duk wani danginsa ko kuma abokin arziki ko zaiji Jameelu yaje amma kowa amsa ɗaya yake basa baije ba.
Haka zalika Ummi baki ɗaya ta kira danginta ko M Jameel yaje amma suma dai amsar ɗaya ce baije ba.

Wunin wannan ranan har dare babu M Jameel babu labarin sa zuwa wannan lokacin tsananin tashin hankali da ruɗun da suke ciki ba zai misaltuba.
Chapter 92 · 0% Book details