← Book details Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 106 OF 114

Sashe 106

Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kai tsaye hanyar gida ya nufa ba abinda ke yawo acikin kunnensa face sautin Muryar J ɗinsa yana isa gida yayi Parking tare da rufe musu gate.
Kai tsaye sashen Innayi ya nufa yana isa ya zauna abakin baranda tare da riƙe kansa da hannu duka biyu,
Kana ya fashe da wani irin kuka mai masifar ciwo a zuciya.
Wani irin azaban zogi yaji zuciyarsa na masa hadi da zafi da raɗaɗi yayin da wani masifaffen rauni ya lulluɓesa.
Innayi da bacci ya fara fisgarta ne, ta miƙe da sauri jin kamar sheshsheƙan Kukan Moddibo kana ta fito tare da Kallonsa yayin da gaba ɗaya ilahirin jikinta ya ɗauki rawa cikin sanyin murya tace.
“Ya dai Moddibo lafiya kuwa mai ya faru da Jameelu?”.
Cikin matsanancin kuka yace.
“Innayi ya zamuyi taya zanyi in.
Samu in taimaki J duk kan tattalina ya ƙare babu abinda zan samu in saida cikin gaggawa.
Zan saida tsohuwar motar da kika siya min da wannan sabuwar da kuma na J duka za'a siyar sannan Innayi nasan koda an siyar dasu duka, kuɗin ba zasu ciki Million ɗari ba”.
Sai kuma ya kife kansa bisa guiwowinsa ya sake fashewa da sabon kuka kana yace.
“Innayi sunce idan muka sake neman ragi akan kuɗin kamar mun nemi akashe J ne”,.
Jingina kansa yayi jikin fillan dake gefenta tare da fashewa da matsanancin kuka hadda sheshsheƙa.

Cikin Sanyin jiki Innayi ta zauna kusa dashi batare da tace yayi shiri ko kuma ya daina kukan ba, domin ta tabbata duk abinda yasa Moddibo kuka ba ƙaramin abu bane, kana idan har bai yiwa wannan abin kuka ba to mai zai yiwa kuka arayuwarsa.
Moddibo kuwa kuka ya cigaba da yi tamkar ransa zai fita har shidewa yake.
A ƙalla ya ɗauki Mintuna masu tsawo yana kuka kafin ahankali ya ɗago kansa tare da kallon Innayi kana yace.
“Innayi”.
Cikin sanyin murya tace.
“Na'am Moddibo”.

Cikin Muryansa daya dishe da kuka yace.
“Innayi ta wace hanya ce wace damace wane daliline kike samu kike mana duk kan buƙatun rayuwarmu?
Innayi in dai har adana kuɗi kikayi in dai har basu ƙare ba Innayi ki fito mana dasu ki taimakeni aceci J dashi”.
Jinjina kai tayi kana tace.
“Moddibo gaba ɗaya tattalin da mukayi na zaman rayuwar mu awannan yanki awannan gari a wannan ƙasar anje matakin da gaba ɗaya tattalin namu yazo ƙarshe sabida lokacin komawa muhalli ya kusan cimmmana”.
Sai kuma ta kalli Moddibo da har zuwa lokacin hawaye ke bin Fuskarsa kana tace.
“Na tanadi komai ne domin sanin cewa muna da bukatar su kama daga karuntaka, ci, sha, Jinya, sutura.
Da dai sauransu to yanzu kuma lokaci ya tafi rayuwa ta juya abubuwa sun tafi baki ɗaya tattalin namu yayi ƙasa tsadan rayuwa ya cinye kaso mafi tsoka”.
Numfashi Moddibo ya fesar kana yace.
“Innayi koma wani irin tattaline shin babu ragowa ne ko kaɗan ne?”.
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
“Akwai ragowa”.
Cikin kuka yace.
“Menene amfanin ragowan duk tattalin arzikin da kike dashi matukar dai ba zai fito atemaki J ɗina da shiba Jamelunki fa ya fito daga inda yake fa”.
Ya ƙare mgnar cikin ƙunan rai, domin gani yake kamar ma duk duniya ba'a damu da J ɗinsa ba.
Ita kuwa Innayi cikin tafiya wani sashi nazarin Jinjina kai tayi tare da cewa.
“Bashi da amfani Indai bazan fito dashi ba, amma bari na fito dashi amma yanzu ka fara yin shiru tukunna kana kayi min al'ƙawarin cewa bazaka tambayeni komaiba akan duk abinda zaka gani”.
Kai ya gyaɗa mata kana yace.
“Innayi muga abinda zan fara samu awajenki tu kunna zanfi jin sanyi, ni yanzu a duniya babu tambayar da ke bakina daya wuce ina J yake , wanne hali yake ciki”.
Sai kuma ya fesar da zazzafan numfashi tare da cewa.
“Wallahi Allah ji nakeyi tamkar naje na zauna abakin masallacai inyita bara asamu ahaɗa kudi in cikata in karɓo J Innayi ya zanyi”.
Cike da rauni Innayi tace.
“Ba zakayi bara ba Moddibo Bari muga abinda Allah zai mana”.
Kai ta gyaɗa tare da jan hannunsa suka nufi bayan ɗakinta inda randunan ƙasa ke ajiye.
Kallon Moddibo da har zuwa lokacin hawaye ke zuba a idanunsa tayi kana tace ɗaga min randan nan”.
Sauri kallonta yayi kana ya Kalli randan ƙasan tare da cewa.
“In ɗaga miki randa kuma?”.
Ba tare data kallesa ba tace.
“Kada kayi min musu idan na baka Umarni kabi”.
Kai ya gyaɗa cikin sanyin yace.
“Toh”.
Tare da ɗaga randan ya matsar gefe.
Ajiyar zuciya ta sauƙe kana tace.
“Toh ɗaga fantekar”.
Kai ya ɗaga tare da matsar da fantekar dake cike da ƙasa gefe.
Yana janye fantekar yaga ƙasan wajen alailaye.
Ahankali Innayi ta zauna agaban wajen Moddibo kuwa cikin sanyi jiki ya durƙusa agefenta.
Itako Innayi hannunta ta sanya ta fara tono ƙasan dake wajen ganin duhu agarin yasa Moddibo sanya hannunsa acikin aljihu ya ciro wayarsa tare da kunna tochligt ya haska mata inda take tonawan.
Innayi kuwa ahankali ta cigaba da tono ƙasan bayan ta gama kwashe ƙasan ya rage sauran wasu manyan duwatsu ahankali ta ciresu duka.
Cike da mmki Moddibo ya tsaida idanunsa akan fafakekken rami an lailayeshi da siminti yana rufe da murfin tukunya kamar na lamba uku, da ɗan ƙarfi ta ɗago Murfin tukunya.
Cikin sauri Moddibo yayi saurin rintse idanunsa da karfu sakamakon wani haskene mai masifar sheƙi daya ɗauke masa idanu daya kashe masa idanu,
A hankali ya kuma saƙe buɗe inadunsa, da sauri ya mitso ganin yadda cikin ramin ke sheƙi da ƙelƙeli mai ɗauke ido yake fitowa daga cikin ramin, acan ƙasan ramin kuwa cike yake da ƴan ƙananan sulallan gwala-gwalai wanda basu fiye yawa ba sosai hasken ya ɗauke masa idanu saboda hasken wayarsa daya haske cike da tsanananin mamakin ya sunkuyo tare haska cikin ramin da kyau kana ya sanya tafin hannunsa acikin ramin ya ɗebo guda huɗu tabbas sulallan Gwalne...!

Littafin SAKAYYAH na kuɗine ko kin ganshi a wani wurin na satane. Ki biya ki karanta cikin Aminci 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA.

By
*GARKUWAR MARUBUTA*
[30/07, 1:42 PM] Halimatu A/rahman Sadeeya: *Littafin nan dai ba free book bane, na kuɗine ko kin gashi a wasu wuraren da ba Group na da ake biya insa mutum, littafin 1k ne kacal in sha Allah zaki karanta shi daga forko har ƙarshe akan 1k kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276 ki biya ki karanta cikin Aminci da salama babu haƙƙin kowa a kanki yar uwa*

Sbpndegoo. Lamiɗo kuwa cikin yanayin, tausayi da jinƙai da ƙauna mai haɗe da taraddadi da tsoro, ya sanya tafin hannunsa na dama ya tallafo, fuskar Ramadan ya juya gefe da gefe ga mmkinsa gaba ɗaya uwayan yaron ya koma lagob-lagob cikin yanayi da kiya da son aro Jarumtaka ya runtse Idanunsa tare da maimaita kalmar Hasbunallahu wani'imal wakil. Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n.
Cikin sauri Hajiya Bunayya dake zaune ta buga hannunta aƙirji tare da kallon Lamiɗo daya zubawa Ramadan ido tace.
“Mai Martaba ya rasu ko?”.
Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da ɗago ido ya kalleta kai ya girgiza mata batare da yace komai ba.
Da sauri Mommy dake tsaye tayi baya tare da zama da ɓas akan kujeran dake bayanta, baki ɗaya jikinta ya saki Atake ta fara Maimaita kalmar.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n Hasbunallahu wani'imal wakin”,ta faɗa hawaye na bin kuncinta Shar-shar.

Khausar kuwa juyawa tayi ta kalli Hajiya Bunayya kana ta mayar da kanta kan Mommy da hawaye ke bin kuncinta ahankali ta sake maida kallonta kan Lamiɗo da yayi shiru yana jan yatsun Ramadan alamar yana dai-dai-tasu.
Cikin wani irin yanayi tace.
“Abba mu tafi dashi asibiti,Abba mu kaisa asibiti”.
Jujjuya kai Lamiɗo yayi kana yace.
“Khausar ki nutsu”.
Kallon Hajiya Bunayya da Idanunta ke kan Ramadan yayi yace.
“Hajiya Bunayya kama khausar ki zaunar da ita”.
Mommy kam tana zaune akan kushin babu abinda take maimaitawa face kalmar Innalillahi still hawaye na bin kuncinta.

Ganin haka yasa Lamiɗo fesar da numfashi kana ya miƙe tare da ɗaukar Ramadan awuyansa ya fice.
Da sauri Khausar ta miƙe tare da bin bayansa tana cewa.
“Abba inzo mu tafi Asibitin ne!?”.
Tsintsiyar hannunta Hajiya Bunayya ta riƙe tare da gyara zamanta tace.
“Khausar ki nutsu mana ki dawo ki zauna?”.
Kai khausar ta girgiza cikin rawan murya tace.
“Ki sake ni zamu tafi asibiti ne kiga Ramadan fa”.
Jinjina kai Hajiya Bunayya tayi tare da faɗin.
“Ki zauna mana ba kiji Abbanku yace ki zauna ba.
Kai ta gyaɗa cikin wani irin yanayi ta koma ta zauna.

Lamiɗo kuwa yana fita kai tsaye sashen Gimbiya Dadu ya shiga bakinsa ɗauke da Sallama zaune ya samu Gimbiya Dadu afalon.
Ganinsa Rungume da Ramadan yasa cikin sauri tace.
“Ya dai lafiya Lamiɗo meke faruwa?”.
Cikin sanyin murya yace.
“Ramadan ne fa ki duba min shi”.
Kai ta gyaɗa tare da Matsawa gaban Ramadan dake kwance ƙasan ɗakin yatsunta biyu ta kai saitin hancinsa sannan ta riƙe jijiya hannunsa kallon Lamiɗo tayi cike da mamaki tace.
“Ha'a bashi da rai ai ajikinsa?”.
Araunane Lamiɗo ya ɗago idanunsa da suka kaɗa sukayi jawur jijiyoyin kansa ya tashi cikin raunin murya yace.
“Nima dai kamar haka na gani ahannuna na ya cika kamar babu rai atare da shi.
Jinjina kai Gimbiya Dadu tayi cikin rawan murya tace.
“Tabbas ba Rai atare dashi Ramadan ya rasu fa”.
Ta ida maganar tare da ɗago hannunsa ta juya sangalam duk ta inda ta juya sai ya tafi luuuu zai fadi kana ga bakinsa dake aɗan buɗe idanua kafe.
Chapter 106 · 0% Book details