← Book details Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 114

Sashe 34

Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin nitsuwa yake tafiya, tare da taka steps ɗin a hankali, yana sauƙa ƙasa, yayinda hankalishi baki ɗaya ke bisa system nashi dayake kan hannunsa na dama yana daddanashi da hannun hagunsa, bisa dukkan alamu.
Abu mai mahimmanci ne yakeyi.

A dai-dai lokacin kuma Khausar ta iso bakin steps ɗin, cikin sauri take tafiya, da alamun tsoron kada malami ya rigata shiga aji ne.
Da sauri take tattaka steps ɗin tanayi sama.
Steps biyu ta taka ana uku, taji juyo da kanta da sauri dan jiyo muryar M Jameel na ce mata.
“Khausar sai yanzu?”.
Ba tare da ta tsaya ba, kana bata kuma juyo kanta ba taci gaba da tafiya a haka, hannunta na kan da ƙarfe dake gefen steps ɗin cikin yanayin sakewarta da M Jameel ɗin tace.
“Wallahi tun ɗazu muka iso fa Malam”.
Yana mai binta da ido yace.
“To kuma meya hanaki shiga class?”.
Still bata janye kanta daga kallonsa ba, kana bata tsaya daga haurawa saman da takeyi ba tace.
“Raudat ce ta tsaidani a side ɗin su”.
Da sauri yace.
“Da me ta tsaida ki?”.
Ɗan guntun murmushi tayi tare da cewa.
“Wai ƙwarone ya shiga idonta, shinefa tai ta ihu taƙi sakina dole saida aka cire matashi Allah sai kaga yadda idonta yayi jazir”.
Kanshi ya sunkuyar yana ɗan murza zaɓen azurfan dake yatsar yace.
“Ayya kwaro bai kyauta ba ya shiga idon Gimbiya Raudat”.
“Ai dai kam fa”.
Ta faɗina tana mai ƙoƙarin juyo kanta.
Cikin tsokana yace.
“Gashi kuwa har Malam Moddibo ya shiga ajinku”.
Cikin sauri ta kuma juyo kanta da dama bata gama juyashi ba cike da kaɗuwa tace.
“Da gaske?”.
Kai ya gyaɗa mata tare da cewa.
“Tun ɗazuma kuwa”
Cikin yanayin tsoro ta ɗan zaro manyan udanunta tare da cewa.
“Na shiga ukuna”.
Murmushi M Jameel yayi tare da cewa.
“Ato kiyi sauri ki hau, in kinyi sa'a ya barki ki shiga”.
Jin haka yasa ta juyo da sauri tare da taka step ɗin gaba kana tayi kwanan haurawa kam steps ɗin da zai sadata da sama.
Wanda kuma dai-dai lokacin Moddibo ma ya taka step na ƙarshen kwanan.
Unexpected taji tayi karo da mutu.
Shi ma Moddibo ba zato ba tsammani yaji kanta ya bugi ƙirjinsa yayinda hannunta ya bugi System ɗin dake hannunsa ya subce ya tafi ƙasa da sauri ya sunkuyo ya cafe system ɗin da kana ya miƙe tsaye,

Ita kuwa Khausar cikin sauri ta ɗago kanta dai dai lokacin kuwa ya ɗago kansa shima ido cikon ido suka kalli juna kamar a fuzge ya furta.
“Again?”. a lokacin guda kuma, cikin tsananin takaici da zafin rai ya ɗaga tafin hannunsa na hagu ya yarfa mata wani irin gigitaccen mari mai masifar zafi gami da raɗaɗi.

M Jameel kuwa jin sautin sauƙan marin ne yashi ɗago kansa da sauri.

Ita kuwa Khausar wani irin gigitaccen ihu mai cike da rauni tare raɗaɗi ta saki, tare da dafe kuncinta kana ta rumtse idonta wanda duhu mai tarin yawa ya mamaye mata gani, kana tayi taga-taga ta koma baya zata faɗi, jin ta tafi suuuuu ƙafarta ta sule yasa takuma sakin wani ƙaran tare da buɗe idanunta, sai kuma tayi sauri ta medasu ta rufe sabida ganin wasu irin taurarin masu wutsiya da tartsatsi suna gilmawa ganinta sabida zafin marin da yasa suka mamayewa ganinta.

Gaba ɗaya ta sadakar domin tasan muddin ta faɗo nan to ita da karaya sun zama aminan juna.

M Jameel kuwa kanshi ya riƙe da hannu bibbiyu tare da faɗin.
“Innalillahi!!”.
Wanda faɗin hakane ya jawo hankalin Malam isa da yazo wucewa ta gefensa.
Shima ma Malam isa idonsa ya rumtse da ƙarfi tare da cewa.
“Yah Salam”.

Shi kuwa Moddibo cikin takaici yayi sauri miƙa hannunsa da nufin kamo hannunta amman ina tuni tayi nisa.
Sai yatsunta biyu ya samu ya riƙe da masifan ƙarfi.
Wanda saida suka bada sautin ƙas-ƙas.
Cikin zafin nama ya fincikota da ƙarfi wanda hakan yasa ta afka jikinsa.

Ita kuwa Khausar jinta a jikin mutum ne yasa tayi masa wani irin sahihin rugguma mai cike da razani dan gani take kamar dai har yanzu bata tsira ba.
Kanta ta cusa cikin ƙirjinsa tana mai shaƙan turarensa mai masifar ƙamshi.
Wanda a take nitsuwarta ta fara dawowa.

Shi kuwa Moddibo cikin tsoro da wani irin masifeffen abu da yaji ya soƙi tsakiyar kansa har zuwa cikin ƙahon zuciyarsa kana ya harba masa wasu irin masifaffun baƙin al'amuran a cikin jijiyoyin jikinsa da suka sa jikinsa sakin wani irin masifeffen karkarwa da sabauta aniyarsa, ya ware hannunsa tare da rumtse idanunsa da masifan ƙarfi.

M Jameel kuwa ajiyan zuciya mai ƙarfi ya sake tare da jingina bayansa da jikin ƙarfen.
a hankali ya kuma sakin numfashi tare da kallon yadda Moddibo ya buɗa hannayensa duka biyu kana ita kuma Khausar tana kwance bisa ƙirjinsa tayi lip tana ruggume dashi da masifan ƙarfi.

Wani irin shu'umin dariya mai sauti M Jameel ya sake.
Wanda hakan yasa Moddibo buɗe idanunsa kana dai-dai lokacin yaji gaba ɗaya tsikar jikinsa na tashi.

Malam isa kuwa sunkuyar da kansa yayi yana murmushi.

M Jameel kuwa dariya yake tare da nuna Modibbo da Khausar ɗin wacce tuni fuskarta tayi jazir shatin yatsun hannunsa sunyi ruɗu-ruɗu a farar fatarta.
Cikin sauri Moddibo ya ɓalle hannunta daga jikinsa tare da matsawa gefe da sauri.
Wani irin tsuke fuskarsa yayi tare da watsa mata kallon da yasa hantar cikinta kaɗawa.
Wanda cikin rawan jiki da rawan murya cike da rauni tace.
“Ana Aspet ya Mu'allim Allah mi larai ma on! Please! Kayi haƙuri”.
Ta ƙare mgnar cikin tsoro tare da gwamusa yaruka hudu duk a wuri ɗaya dan neman afuwa.
Shi kuwa Moddibo juyawa yayi tare da ratsa gefenta ya wuce kana cikin wata fusatacciyar murya mai matuƙar firgitarwa yace.
“Biyoni!”.
Cikin ɓarin jiki tace.
“Toh”.
Sannan ta miƙe tabi bayansa.

M Jameel dake riƙe da System ɗin yana juyawa yayi saurin bin bayansa da faɗin.
“Alhamdulillah kamar babu abinda ya samu System ɗin”.
Shi dai Moddibo ko juyawa baiyi ba bare kuma ya tankawa M Jameel.

Malam Isa kuwa dake ƙasa ido ya zirawa Khausar dake sauƙwa dafe kuncinta da kunne ya da tun da tasha marin ya bada sautin kauwww har yanzu ƙaran takeji, kana ga idanunta da suka kaɗa sukayi jawur asanda ta saƙƙo yace.
Fattanah sam bakya yin abinda ya dace a rayuwarki”.

Cikin zafin raɗaɗin marin da fuskarta keyi ta ɗago Idanunta da suke sake girma da ja ta kalli Malam Isa sai kuma tace.
“Wallahi bansa niba ne na juya ina kallon Malam Jameel ne dake yimin magana ne mukayi karo”.
Bata jira jin abinda zai ce ba tabi bayan M Jameel dake biye da Moddibo.

Cak Khausar ta tsaya daga bakin Office ɗin, karo na farko kenan arayuwarta da zata fara shiga Office ɗinsa, duk da cewa da basu da office da yawa, amma yanzu gyaran da akayi an haɗa Malamai biyu akan Office ɗaya Office din ba wasu masu girma bane, haka zalika ba ƙanana bane, sannan duk kusan ajere suke.
Ahankali Khausar ta maida Idanunta bakin office ɗin da akasa wasu irin flowes masu launi mai kyau da ɗaukar hankali aka jera suna fitar da wani irin sanyayyan ƙamshi.
Cikin Office ɗin kuwa Madaidaitan deks ne da kujeru ɗaya na fuskantar gabar ɗaya na fuskantar yamma daga gaban ko wanne kuma akwai kujeru guda biyu daga kan deks ɗin daga gefen damar sa akwai wani Cubet kamar kanta dake ɗauke da tarin littattafai na addini da kuma na boko cikin wajen kamar dai Library haka wurin yake.
Daga gefen hagunsa kuma flowes ne masu kyau da tsari daga jikin bangon kuma Room hitane ne maƙale abango yana fitar da ɗumi mai daɗi a jiki,
Sai kuma labulayen window da suka kasance farare sol Sanyayyan iska na kaɗawa daga bangon kudu dake kallon yamma TV ne maƙale abango daga tsakiya kuwa wani irin dakekken turkey carpet mai yawan gashi fari sai ratsin maroon kaɗan. sosai Office ɗin yayi kyau.

Shi kuwa Moddibo cikin nutsuwa da kuma zafin da zuciyarsa keyi masa ya zauna akan kujeran dake gabar yana fuskantar yamma yayin da M Jameel ya zauna akan kujeran dake yamma yana fuskantar gabar kana da sunan ko wannensu ajiki kujerarsa.

Ita kuwa khausar cikin tsananin tsoro ta ƙarasa shiga office ɗin tare da tsugunnawa agaban table ɗin da Moddibo ke zaune.
Ta riƙe kunnenta Muryanta Araunane wanda ke nuni da tsantsar tsoro da tashin hankali tace.
“Malam kayi haƙuri bansan kana tahowa ba”.
Shi kuwa Moddibo ko kallonta baiyi ba saboda yanda zuciyarsa ke tsananin ta farfasa ya tabbata idan yace zai daketa to zai iya karyata ko kuma ya sumar da ita hakan yasa ya janyo kujeran dake kusa dashi ya ɗaura ƙafafunsa akai kana ya lumshe idanunsa tare dasa hannu ya janyo Hiramin dake kansa ya rufe saman Idanunsa.

Cikin tsantsar nutsuwa da kuma sanyayyan sautin muryarsa mai zaƙi ya fara rara Ƙira'a acikin suratul Rahman yasan hakan shine kaɗai zai sanyaya masa ransa da zuciyarsa yasan muddin yace zai daketa ayanzu zai iya sumar da ita ko kuma karyata.
Saboda abubuwan da yarinyar ke masa yayi yawa.
Sabida tsabar raini da rashin kunya fa har gidansu ta bisa tayi masa rashin kunya sannan ta jima sa ciwo ayatsun ƙafansa wanda ya ɗauki tsawon kwanaki yana fama da ciwo.
Kana yaje ƙauyen su nan ma bata barshi ba saida ta bisa tayi masa rashin kunya ta nemi jefa shi acikin ruwa da wannan masifeffen sanyin garin nasu,
kana amakaranta ma bata barsa ba shin tsaranta ta mayar dashi kome?.

Ita kuwa khausar cikin Sanyayyar Muryanta me cike da tsoro tace.
“Ayyah malam na tuba kayi haƙuri wallahi bansani bane”.
Ƙin tanka mata Moddibo yayi ya cigaba da rera karatunsa cikin zazzaƙan muryansa.
Shi kuwa M Jameel Gyaran murya yayi hakan yasa Khausar tayi saurin Kallonsa da manyan Idanunta da suka kaɗa sukayi jawur.
Da ido yanuna mata Moddibo alamar ta cigaba da basa haƙuri.
Kai ta gyaɗa sannan ta cigaba da cewa.
“Ayyah Malam na roƙeka kayi haƙuri bazan sake ba”.
Chapter 34 · 0% Book details