← Book details Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 114

Sashe 80

Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan sun isa bakin gate M Jameel ya nufi jikin motarsa dake fake Kallonsa Moddibo yayi kana yace.
“A'a Baza mushiga muci abinci ba?”.
Cike da kulawa M Jameel yayi murmushi tare da cewa.
“Aini naci tunda zafinsa, kasan tun yaushe muke tare da Innayi kuwa? tun bayan sallar la'asar muna tare fa sai da aka kira maghariba nashigo nan nayi alwala”.
Wara Ido Moddibo yayi kana yace.
“Iyee gulmar me kuka yi?”.
Murmushi M Jameel yayi tare da faɗin.
“Ta faɗa min komai ta faɗa min duk kan abinda baka sani ba”.
Gyara tsayuwa Moddibo yayi tare da harɗe hannunsa aƙirji kana ya juya ya kallesa tare da cewa.
“Kamarya abinda ban sani ba?”.
M Jameel kuwa murmushi yayi tare da cewa.
“Zuwa yanzu nafi ka sanin kan ka ma nafi ka sanin wanene kai duk yanda kasan kan ka to yanzu na fika sanin kan ka”.
Lumshe idanu Moddibo yayi tare da shafa sashensa kana ya buɗe idanun nasan tare da kallon M Jameel yace.
“Iyeeeeh toh zo ka fesa min mana tunda angumtsa maka na hannun damana”.
Tsayuwa M Jameel ya gyara tare da cewa.
“Sirrine sai da nayi al'ƙawari bazan fesa maka ba kafin ake fesa min”.
Moddibo kuwa murmushi yayi tare da shafa sajensa kana yace.
“Toh yanda kayi lallaɓa nima zanje inyi lallaɓan afaɗa min”.
Cikin dariya M Jameel yace.
“Toh kaje ka gwada sa'arka, amma yanzu kam kasani bana cikin duhu”.
Taɓe baki Moddibo yayi kana yace.
“Iyyeeee wato gulmana nema kuka tayi”.
Agogon dake ɗaure atsintsiyar hannunsa ya kalla ganin da ɗan sauran lokacin salla ne ya juyo ya kalli Moddibo tare da faɗin.
“Ba wani gulmarka da muka tayi na dai faɗa mata cewa kana ɓuƙatar aure yanzu”.
Cikin sauri Moddibo ya juya tare da watsa masa Harara Dariya M Jameel yayi tare da buɗe motarsa yashiga mazaunin Driver key yayi wa motar tare da saita hancin motar ya fara tafiya.
Shi kuwa Modibbo da ƙafa ya nufi masallacin.
A hanya ya tsaya yayi salla kana ya ƙarasa cikin gidan.

Parking aharabar gidan cike da nutsuwa ya fito tare da nufar falon bakinsa ɗauke da sallama ya shiga.
Ahankali yake bin cikin falon da kallo batare daya shiga ba cikin hasken fari gloves ɗin da suka haska falon kana da murmushi afuskarsa yace.
“Ina Umminaaaa?”.
Ummi dake zaune kan 3sitter idanu ta zuba masa batare da tace komai ba.
Malam Ahmad dake zaune kan 1sitter ya kalli M Jameel dake tsaye ƙofar falon tare da cewa.
“Ƙara so mana Jamilu”.
Juyawa yayi ya kalli Ummi kana yace.
“Kin tsaresa da ido kuma baki ce masa ya shigo ba”.
Murmushi M Jameel yayi tare da cewa.
“Ummi nayi kyau ko?”.
Jinjina kai Ummi tayi still Idanunta na kansa tace.
“Sosai ma Babana”.
Murmushi yayi tare da Wara ido kana yace.
“Iyyeee naji daɗina yau kuma nine Babanki ko da yake Baban miji ai baba ne?”.
Kai Malam Ahmad ya gyaɗa kana yace.
“Sosai ma”.
Ummi kuwa still Idanunta na kanshi.
Bashir daya fito daga Bedroom ne ya kalli Ummi kana ya kalli M Jameel data tsirawa Idanu matsawa kusa da Ummin yayi tare da cewa.
“Yaya Jameel wallahi Ummi na sonka kamar me”.
Sai asannan Ummi ta ɗauke Idanunta daga kan M Jameel ta mayar kan Bashir tare da yi masa daƙuwa kana tace.
“Haka naka Bashiru”.
Asma'u data fitowarta kenan daga Bedroom tayi murmushi tare da zama gefen M Jameel.
Miƙewa Malam Ahmad yayi tare da nufar ɗakinsa bayan sun gaisa da M Jameel.

Kallon Asma'u M Jameel Yayi tare da cewa.
“Asmeey”.
Cike da ladabi ta ɗago kanta kana tace.
“Na'am Yaya”.
Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da cewa.
“Zuwa yanzu kaso 85% cikin 100% na nauyin ku dake araina nake tunawa 85% sun sauƙa min saura shabiyar nake tunawa 15% ɗin nan kuma sune manya masu wuya”.
Ajiyar zuciya yauƙe tare da cewa.
“Ina so inga kinyi karatu kin gama, sannan na miki zaɓi da miji na gari Mumini, Salihi, Mai tsoron Allah, na Aura masa ke, sannan na danƙa masa Amanar ki.
Hakazalika Ina so inga Bashir ya gama karatunsa ya fara aiki ta yanda ko bana kusa zai kula da Ummin mu ba zata nemi komai ta rasaba”.
Cikin yanayin damuwa Asma'u tayi ƙasa da kanta lokaci ɗaya Idanunta suka ciko da hawaye yayin da taji zuciyarta yana masifar bugawa da ƙarfi Allah ya sani in ta tuna zatayi aure ta rabu da Unminta tanajin ba daɗi.
Cikin raunin murya tace.
“Bare ma Yah Jameel kai zaka yiwa Ummi komai kafin mu”.
M Jameel kuwa murmushi yayi tare da kallon Asma'u kana ya cije labɓansa na ƙasa tare da lumshe idanunsa yana sauraron bugun zuciyarsa ajiyar zuciya ya sauƙe tare da buɗe idanunsa akan Asma'u kana yace.
“To ai ita rayuwar dama ta gaji haka watarana ayi farin ciki watarana ayi baƙin ciki!”.
Girgiza Kai Bashir yayi tare da kallon M Jameel cikin yanayin tsinkewar zuciya ya gyara zamansa tare da cewa.
“Yah Jameel Meyesa kake karyar mana da zuciya ne!?”.
Girgiza kai M Jameel Yayi tare da kallonsu wani irin tausayinsu da kuma ƙaunarsu na ratsa dukkan zuciyarsa, bashi da wani ƙunci a rayuwarsa fiye da yadda ya kasance baya tare da Umminsa da ƙannensa a inuwa ɗaya, ciwon sakin mace ba iya kanta kawai yake tsayuwa ba, har kan ƴaƴan data haifa yake shafa.
Iska mai zafi ya fesar daga bakinsa kana yace.
“Ba karya zuciya bane Bashir burina ne, akan ku inaji kuma har yanzu akwai kason da ban idaba,
sabida ban zaɓawa Asma'u mijin aure a shine babban abinda yafi damuna sannan kai kuma kagama makarantar ƙuruciya ce sai jami'a gidan kazo nazo”.
Numfashi yaja tare da fesarwa Idanunsa nakan Bashir yace.
“Acan ne ake samun tarbiyya daban-daban da halayyar al'ummar matasa kashi-kashi ina tunanin kada ginin da mukayi nida Ummi wani yaje yayi yaɓe akai ya lalata kyakkyawan gini da kyakkyawan tubalin da mukayi maka”.
Da sauri Bashir ya jujjuya kai tare da cewa.
“In sha Allah haka bazai faruba”.
Cikin jin sanyi yace.
“Bashir kayi min al'ƙawarin zaka kasance nagari, kayi min alƙawarin zaka kasancewa Ummi farin cikinta”.
Lokaci ɗaya hawaye suka cika idanun Bashir cike da tsoron kalaman Yayan nasa.
Cikin wata razananniyar murya ya kalli M Jameel da Idanunsa ke lumshe kana yace.
“Nayi maka al'ƙawari Yah Jameel Nayi alƙawari zan kasancewa Ummi ɗa nagari zan kasance me share mata hawaye, zan kasance mai sata farin ciki idan Allah yayi duniya dan Manzo (S.A.W) ”.
A hankali ya ɗaga idanunsa tare da kallon Ummi da ta tsirawa M Jameel idanu cikin wani irin yanayi ko ƙyaftawa bata yi ajiyar zuciya ya sauƙe kana yace.
“Zan kasance mai sata farin ciki, nayi alƙawari Ummi ba zata taɓa shiga ƙunci ko damuwa ba in dai a kai nane in sha Allah”.
Ahankali M Jameel ya maida kansa jikin kushin ɗin ya jingina kana ya miƙe ƙafafunsa tare da riƙe hannun Bashir aciki nasa kana ya cije lips ɗin sa.
Ummi kuwa wani irin sanyi jikinta da zuciyarta keyi cikin wani irin yanayi ta zubawa M Jameel Idanu.
Anutse M Jameel ya buɗe Idanunsa dake lumshe ya sauƙe akan Ummi Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da furzar da iska daga bakinsa kana yace.
“Ummi ya dai kike kallona haka kamar na ƙarshe!?”.
Cikin saurin Ummi ta dafe ƙirjinta daya buga da ƙarfin gaske cikin raunin murya irin na wanda ke gab da zub da hawaye ta kallesa karo na farko arayuwarta data fara kiran sunan sa tace.
“Haba haba Jamilu”.
Cike da mamaki ya ɗago idanunsa da suka sauya launi ya kalleta, Asma'u ma da sauri ta kalli Ummi haka ma Bashir karo na farko kenan arayuwar su da suka ji Ummi ta kira M Jameel da sunan sa.

Ummi kuwa lokaci ɗaya wasu hawaye masu masifar zafi suka fara bin kuncinta Shar-shar.
Cikin yanayin tashin hankali M Jameel ya sauƙa tare da ƙara sawa gabanta ya durƙusa tare da riƙe hannun ta cikin sanyin murya yace.
“Ummi kiya femin Ummina kiya femin kada ki zubar da hawayenki akaina Ummi me nayi miki!”.
Damƙe hannunsa Ummi tayi cikin raunin murya da alamun tashin hankali tace.
“Meyesa kake zuwa kake karya mana zuciya nida ƙannenka, kasani ayanzu kaine Inuwata kaine mafakar da muke samu nida ƙannen ka muke fakewa. Meyesa wasu lokutan idan kazo kake min wasu maganganu masu wuyar fahimta”.
Ta ida maganar hawaye nabin kuncinta.

Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da yin murmushi yayin da Idanunsa ke sheƙi kana yace.
“Toh Ummi inada ikon canza ƙaddarata ce? Idan son samu ne Ummi zan kasance me Kula dake har iya ƙarshen numfashi na, kuma zan kasance me saki acikin farin ciki da walwala har numfashina na ƙarshe”.
Girgiza kai Ummi tayi still Hawaye nabin fuskarta tace.
“Ko yanzu ka sanya ni farin ciki duk kan wani farin ciki da jin daɗi ka bani shi Jamilu”.
M Jameel kuwa cike da mamaki ya ɗago Idanunsa dake jiƙe da ruwan hawaye yace.
“Ummi me kika ce?”.
Cikin Muryan kuka tace.
“Jamilu nace”.
Kallonta yayi cikin rawan murya yace.
“Ummi Meyesa?”.
Hawaye na zuba daga idanunta yayin da jikinta ke tsuma tace.
“Toh me zance maka? Kana tunanin bana jinka araina ne? Kana zaton bana jinka ajikina ne?
Ban taɓa ganin wani ɗa kafin kai bafa Jamilu, kaine ɗana na farko tsatsona, jinina, mallakina, kafin inga Asma'u da Bashir da dai abu ya sameka a ace ina da ikon canza ƙaddara da zan dawo dashi kaina, domin nasan ko bayan raina zaka kula da ƙannen ka fiye da yanda zan kula da su”.
Chapter 80 · 0% Book details