← Book details Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 114

Sashe 40

Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin tsananin farin ciki Amina ke kallon Hajiya Bunayya dake mata bayani karɓan maganin tayi tare da rungume Hajiya Bunayya tace.
“Nagode Umma”.
Ƙullin maganin ta karɓa sannan ta shiga ban ɗaki tayi wanka dashi tana fitowa Hajiya Bunayya ta kawo mata wuta akasko ta bata zama Amina tayi tare da kai saitin kaskon bakinta tace.
“Jameel!, Jameel!!, Jameel!!!”.
Ta faɗa da ƙarfi yayin da hayaƙin ke bin ilahirin jikinta kallon Hajiya Bunayya tayi cikin jin daɗi tace.
“Umma M Jameel ya Kusa zama mallakina?”.
Dariya Hajiya Bunayya tayi tace.
“Ƙwarai kuwa?”.
Asiya ce tashigo falon da Sallama da sauri ta toshe hancinta jin wani masifaffen wari da ƙauri tayi saurin kallon ƙofar Bedroom ɗin Hajiya Bunayya inda nan take jin wari da ƙaurin ke fita.
Tana ƙoƙarin shiga Hajiya Bunayya ta fito Kallonta Asiya tayi tace.
“Ummah warin meke fita daga ɗakinki?”.

Harara Hajiya Bunayya ta watsa mata tace.
“Warin lafiya ko kuma ke ki kafi kowa hanci?”.
Girgiza kai Asiya tayi tace.
“Wallahi Ummah da gaske akwai..”.
Tsawa Hajiya Bunayya ta buga mata da faɗin.
“Ki wuce kibani waje sakaryar banza mara tunani”.
Ahankali Asiya tace.
“Allah yabaki haƙuri Ummah”.
Kana ta juya cikin mutuwar jiki ta nufi ɗakinta.

Bayan wata ɗaya:
Amina ta gama amfani da duk maganin da Hajiya Bunayya ta karɓo mata awajen Boka Kar'uzu cike da farin ciki ta dubi Hajiya Bunayya asanda take sanya uniform ɗinta tace.
“Ummah na matsu na isa Makaranta inga irin tarban da Jameel zai min!”.
Murmushi Hajiya Bunayya tayi da faɗin.
“Kede ki kama kanki karki bari ya gane kina sonshi ya rainaki dan yanzu sai yanda mukayi dashi”.
Asiya data fito daga kichen hannunta riƙe da Cup ɗin tea dake tururi ta zauna akan ɗaya daga cikin kujerun falon Idanunta akan Amina tace.
“Amina ki maida hankali akan karatunki kada kice zakiyi wasa da damarki komai da kika gani arayuwa muƙaddari ne daga Ubangiji”.
Cikin tsawa Hajiya Bunayya tace.
“Asiya zanci Ubanki fa idan baki fita sabgar Amina ba shegiyar yarinya me baƙin halin tsiya.
Niko anya ma ba canza min ke akayi ba, dan wallahi badan kamannin dake tsakanin mu ba sai ince sauya min ke akayi”.

Miƙewa Asiya tayi tace.
“Allah ya baki haƙuri Umma amma ita gaskiya ɗaya ce”.
Harara Amina ta watsa mata tace.
“Ke har wani gaskiya ce dake to ki riƙe gaskiyar ki bama bukata”.
tana gama fadar haka ta fice.

Atare suka fito da Khausar dake riƙe da hannun Raudat kallo ɗaya Khausar ta mata ta kawar da kanta gefe,
Ita kuwa Amina murmushi mai cike da ma'anoni ta sakarwa Khausar sannan tashiga motar yayin da Khausar tabi bayan ta suka shiga sannan driver yaja motar suka tafi.

Motar na tsayawa kowa ya nufi ajinsu kamar kullum saida Khausar takai Raudat ajinsu kafin ta wuce ajinsu.
Aɓangaren Amina kuwa kai tsaye ajinsu ta nufa tare da zama tana sakin murmushi duk da Amina da Khausar

Shigansu baa daɗewa M Jameel ya shigo ajin cikin wata farar gezner me kyau yayin da kansa ke sanye da baƙin hula gashinsa ya fito ta ƙeya ƙafarsa sanye da sau ciki baƙi jikinsa na fitar da sanyayyan ƙamshi Amina kuwa ta gumi tayi tare da zu bawa sajensa zuwa gemunsa idanu tana mai furta.
“Wowww”.
Shi kuwa M Jameel hankalinsa ya mayar kan Black Board.
Cikin karya murya tare da lanƙwasa harshe Amina tace.
“Malam Barka da safiya”.
Anutse M Jameel ya juya ya kalleta cikin sauri ya runtse Idanunsa da ƙarfin gaske.
Sai kuma ya sake buɗewa akan fuskarta still da sauri ya sake runtse Idanunsa yana mai furta.
“Hasbunallahu wani'imal wakil.
Astagfirullah wa'atubu ilaik”.
Ita kuwa Amina cike da ƙissa ta sake karya harshe tana juya Idanunta tace.
“Malam ina kwana”.

Shi kuwa M Jameel Batare daya juya ya kalleta ba ya ɗaga mata hannu, domin tun sanda ya kalli fuskarta sau ɗaya yaga kamar an ƙona fuskar Biri, sosai ta masa muni tunda yake kallon fuskar yarinyar bai taɓa ganin tayi masa muni irin na yau ba, baki ɗaya fuskarta babu haske bare annuri Kawar da kansa yayi ya cigaba da koyar wansa batare daya yarda ya sake kollon inda take ba har yagama ya fita.
Ita kuwa Amina bata kawo komai aranta ba domin atunaninta maganin ne ya fara aiki.

Acan ajinsu Khausar kuwa Moddibo ne tsaye jikin Black Board Ya rubuta Geography ajiki,
Da alama shine subject ɗin da zai riƙa ɗaukansu.
Jikinsa sanye da Jallabiya Coffee color yayin da kansa ke naɗe da hirami siririn sajensa zuwa gemunsa yasha gyara sai sheƙi yake jikinsa na fitar da sanyayyan ƙamshi tularen Oud.
Cikin nutsuwa da kuma sanyin Muryansa ya gyara tsayuwar sa tare da harɗe hannayensa aƙirji kana ya ɗan lumshe idanunsa kafin yace.
“Class What is Geogry?”.
ya ƙare tambayar cikin tsananin tsuke fuska da tsare hirar samata ƙasa, sabida yanayin dariasin in yayi garaje yara zasu rainasa, Allah ya sani ba ƙaunar darasin yakeba sabida yanayin abubuwan dake ƙunshe a ciki masu cin karo da addini.
Shiru class din yayi ba wanda yayi magana sabida yadda baya kallon idonsu haka suna kan suke shayin koda motsi bare Kallonsa.
Khausar da Idanunta ke lumshe ta buɗe tare da zaro harshe ta ɗan lashi lips ɗin ta sai kuma ahankali ta ɗaga siririn hannunta dake maƙale da zoben azurfa da kuma Gold.
Shi kuwa Moddibo ahankali ya maida da idanunsa zuwa ta inda take.
Kana tsare sashin da taken yayi da ido amman ba fuskantar yake kalloba, ƙara tsuke fuska yayi tare da sa hannunsa ya shafa yalwataccen sajen dake fuskarsa kana ya mata alamun ta tashi.
Cikin nutsuwa tare da taka tsan-tsan akan gudun lefin da zatayi ta motsa lips ɗin ta da yayi pich saboda man baki data shafa kana ta lumshe Idanunta tace.
“Geography can be defined as the discription of the Earth”.
Jinjina kai Moddibo yayi tare da faɗin.
“Dayyit, sit-down”.
Kai ta gyaɗa tare da zama.

Ahankali ya motsa lips ɗinsa da faɗin.
"Yah Salam". Yayi mgnar yadda ba mai jinshi.
gajeren tsaki, Samira Sani taja dan ji tayi kamar ta haɗiyi zuciya ta mutu saboda baƙin ciki taso ace itace zatayi wannan karatun
Shikuwa Moddibo kallon Khausar yayi tare da yimata alamar tazo cikin sauri ta miƙe ta isa gabansa, ba tare da yace mata komai baya miƙa mata hannunsa.

Kallon tattausan farin tafin hannunsa dake ɗauke da zara-zaran yatsu da ga wasu zoben azurfa fari da baki daya ƙawata yatsun.
Cikin rawan murya tace.
“Malam mai zanyi?”.
Ya mutsa fuska yayi tare da watsa mata harara daya sa ‘ya‘yan hanjinta kaɗawa da ido ya nuna mata zobunan hannunta.
Cikin rawan jiki ta cire ta basa lokaci ɗaya Idanunta suka sauya launi sosai take masifar son zoben ɗaya Mommy tace ta bata ɗaya kuma Hajja Nana ce ta bata ta kuma shaida mata tun na babantane na azurfan.
Saida ta koma ta zauna yace.
“Nasha faɗa muku cewa nan ba wajen ado bane idan kowa yace zaiyi ado yazo ai wasu ma baza agansu ba”.
Ya ida maganar tare da juyawa ya cigaba da koyar musu cike da ƙwarewa tare da kare ƙa'idar musulunci gudun dulmuyar tunanin ɗalibai.

Bayan kwana uku baki daya Amina tashiga damuwa da tashin hankali koda ta gaida M Jameel baya Amsawa sai dai ya ɗaga mata hannu, gwara ma da yana kallonta Sannan wataran yakan mata murmushi amma yanzu koda kallonta baya ƙaunar yi.
Bayan antashi tana komawa gida.

Kai tsaye Bedroom din Hajiya Bunayya ta nufa.
Zaune ta samu Hajiya Bunayya riƙe da kofin tea mai ɗumi ahannunta.
Zama tayi agefen Hajiya Bunayya cikin raunin murya tace.
“Ummah tunda fa nagama aiki da maganin M Jameel Koda kallona ne baya ƙaunaryi, ko gaishesa nayi saidai ya ɗaga min hannun!”.
Da Mamaki Hajiya Bunayya tace.
“Ikon Allah to ya zama dole inshirya na koma gidan Boka Kar'uzu inji me yesa”.
Gyaɗa kai Amina tayi tace.
“Gaskiya ya kamata dai Ummah".

Hajiya Bunayya tace.
“Gashi nima yau nakeso in fara na wannan matsiyaciyar matar dan nafi so dama sai kin gama naki sai in dafa in bata”.
Amina tace.
“Ya kamata dai kam yazo tana ta cika mana gida da yara”.
Ita kuwa Hajiya Bunayya miƙewa tayi da kanta ta shiga kichen ta buɗe fridge ta ɗauko kayan ciki ta haɗa masa kayan ƙamshi da kayan hadi Sosai sai tashin ƙamshi yake.
Warmers ta ɗauka ta juye kana ta dauko ƙullin maganin da boka Kar'uzu ya bata ta barbaɗa akai sannan ta ɗauka ta nufi sashen Hajiya Aysha dashi.
Mommy na zaune afalo ta miƙe ƙafafunta ta jiyo Sallamar Hajiya Bunayya murmushi tayi tare da tace.
“Yaya kece da kanki sannu da zuwa”.

Murmushi Hajiya Bunayya tayi tace.
“Wallahi kuwa kinga Perpesoup nayi na kayan ciki, nasan kuma kina so, shiyasa nace nari na kawo miki, idan kinsha da dan ruwan Tea mai ɗumi zakaji daɗi asanyin da ake”.
Murmushi Mommy tayi tace.
“Aikuwa Nagode yanzu nake tunanin tashi in dafa ko indomie ne naci dan na gagara cin tuwon".
Murmushi Hajiya Bunayya tayi tace.
“Ayyah ƙanwata to ga wannan sai kisha ai zakiji daɗinsa”.

Acan ɗaki kuwa Khausar ce tsaye jikin wodurobe tana gyara kayansu da Raudat ta burkitasu.

Siririn tsaki ta saki tare da kallon tulin kayansu dake burkice kamar basu taɓa ganin ninkiba bare guga stool taja ta zauna tana ninke kayan.
Chapter 40 · 0% Book details