Sashe 24
Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dariya Haiydar yayi yace.
“Ai dama kin iya ɗale-ɗalen bishiya kina nan kamar Biri”.
Murmushi tayi sai kuma ta ɓata fuska tace.
Ni sa'arkace za kace ina tsalle kamar Biri??”.
Murmushi tare da faɗin.
“Addah Khausar Sarkin son girma kiyi haƙuri to yar uwa”.
sakin murmushi tayi kafin tace.
“Bawa Ramadan”.
Miƙa masa Haiydar yayi.
Ramadan yace.
“Addah Khausi nayi kewarki”.
Cike da ƙaunar ƙannen nata tace.
“Nima nayi kewarka ɗan ƙanina Insha Allah na kusa dawowa”.
Amsar wayar Mommy tayi tace.
“Kin Kusa dawowa haka kukayi da Hajja Nana nan?”.
fuska ta ya mutsa kana tace.
“Sai munyi da ita Mommy yau kwanana biyarfa ana shida nake idan nayi sati biyu zan dawo ai”.
Mommy tayi murmushi tace.
“Tsakaninku de ni yanzu ba ruwana nima ba bari na tayi ba”.
Dariya Khausar tayi tace.
“Ina Raudat? Su Ramadan na zuwa hadda ko?”.
Kai Mommy ta gyaɗa tace.
“Ai Asma'u ma tazo tace malamai nata tambayarki sunce taya zakiyi tafiya baki sanar musu ba kodan ba boko ne sai hadda ne kawai wato?”.
Girarta ta ɗan shafa da yatsarta manuniya kana tace.
“Hmmm ai kuwa na faɗawa Asma'u ta sanar musu wataƙil ta manta ne”
“To ai yanzu kam sai in kin dawo.
Ki dai bi tsohuwar ahankali saboda ki samu tabarki ki dawo akan lokaci”.
Cewar Mommy.
Itako Khausar kai ta gyaɗa kafin tace.
“Toh shikenan Mommy na zanyi duk yanda kika ce. Yawwa Mommy ki turo min Number Ummin Asma'u”.
”Toh”Mommy tace sannan ta katse kiran.
Ita kuwa Khausar juyawa tayi tare da kallon yaya Abba dake tsaye ta langwaɓar da kai kafin tace.
“Ayyah Yaya Abba in ƙara Kiran wata ƙawata?”.
Kai ya gyaɗa kana yace.
“Ki kira ba matsala”.
“Toh”,
tace tare da maida kallonta kan wayar da text ɗin Number ya shigo copy tayi tare da dearling.
Tana kira ringing ɗaya Ummi ta ɗauka.
Khausar tace.
“Ummina”.
Murmushi Ummi tayi tace.
“A'a Khausar kece? Ya mutanen Ruga fatan kun same su lafiya?”.
“Lafiya lau Ummi. Ina Asma'u”. Cewar Khausar
“Gata nan tana tsifa”. Ummi ta faɗa tare da miƙa wa Asma'u wayar.
Asma'u na amsar wayar ta maƙala akunnenta tare da ƙyalƙyalewa da dariya tace.
“Na sani”.
Ita kuwa Khausar hararan wayar tayi jin Dariyar da Asma'u keyi tace.
“Kinsan me?”.
Asma'u tace.
“Na sani tsoron Yah Moddibo kike yasa kika gudu kika tafi Rugar nan inba haka ba keda baki ƙaunar tafiyar nan amma daga arba dashi kika tafi Ruga”.
Ƙwafa Khausar tayi tace.
“Ba dole in tafiba tunda kika kaini kafin in dawo wala Allah ya huce”.
Cike da zolaya Asma'u tace.
“Wai ai Yah Moddibo baya mantuwa duk abinda aka masa".
Wara ido Khausar tayi sai kuma tace.
“Asma'u duk kece kika janyo min da baki kaini gidansu ba da haka bai faru ba wlh”.
Asma'u kuwa murmushi ya subce mata kafin tace.
“Calm down wasa nake Miki shi idan abu ya wuce kwana uku ma wata ƙil mancewa”.
Ita kuwa khausar jin haka yasa ta saki ajiyar zuciya da faɗin.
“Alhamdulillah". Sai kuma ta harari wayar tare da cewa.
“Au wata ƙil nema kenan”.
Dariya Asma'u tayi kana tace.
“Yaushe zaki dawo?”
Taɓe baki Khausar tayi tace.
“Waya sanma wannan tsohuwar wataƙila nan da sati biyu ko kuma sati ɗaya idan nayi sa'a tabarni in dawo anata wuceni ahadda ko?”.
Da sauri Asma'u tace.
“Eh ana wuce ki kam”.
Ita kuwa Khausar ɗan jim taui kafin tace.
“Insha Allah nima dai na kusa dawowa”.
“Toh Allah yasa”. Asma'u ta faɗa kana sukayi Sallama tare da katse kiran.
Kallon Khausar yaya Abba yayi yace.
“Koda kuna hutun ana baku hadda ne?”.
Kai ta gyaɗa da faɗin.
“Eh Yaya Abba muna zuwa hadda”.
“To ai babu matsala inde hadda ne ki riƙa zuwa wajen Babanmu yana ƙara miki ai zai baki hadda ki cigaba kada awuceki”.
Cewar Abba.
Khausar kuwa cike da farin ciki tace.
“Toh shikenan Yaya Abba insha Allah kuwa”.
Daga haka suka miƙe suka taho kai tsaye gidansu Abba suka nufa bakinsu ɗauke da Sallama suka shiga.
Kallon Dije da Ibrahim Yaya Abba yayi yace.
“Bari na rakata wajen Liman”.
Kai suka gyaɗa sannan yayiwa Khausar jagora zuwa ɗakin Mahaifinsa bakinsu ɗauke da Sallama suka shiga ɗakin.
Ɗaki ne irin na bukka mai shatin kwabo baki ɗaya ɗakin kewaye yake da littattafan Addini kana da qura'anai bugu da ban bugun misira da warash.
Cike da ladibi Khausar ta gaishesa Amsawa yayi cikin sakin fuska kafin ya kalleta da murmushi yace.
“Matso mana”.
Kai ta gyaɗa tare da Matsawa kusa dashi ta zauna akan buzunsa.
Yana murmushi yace.
“Lafiya? ko dai ƙaran Addata kika kawo?”.
Murmushi tayi tace.
“Ni Meye ruwana da ita da zan kawo ƙaranta, dama karatune muna hadda Acan toh kuma na tsaya za'a iya wuceni”.
Kai Ya jinjina kana yace.
“Wacce surah kuke?”.
Anutse tace.
“Suratul Taubah muke munyi shafi huɗu zan tashi ashafi na biyar”.
Cikin gamsuwa ya gyaɗa kai tare da faɗin.
“Karanta inda kukayi naji”.
Gyara zamanta tayi tare da gyaɗa kai kana taja sassayan numfashi cikin zazzaƙan Muryanta tayi basmala kana ta fara rerewa karatun cike da jan Tajwidan Tartilan.
Kai Malam Liman ya jinjina da faɗin.
“Masha Allah”.
Yaya Abba kuwa lumshe Idanunsa tun lokacin data fara karatu kana ya buɗe su alokacin da takai ƙarshen ayan yace.
“Masha Allah Allah ya baki zaƙin murya Hafiza”.
Jin abinda yace.
Yasa Khausar sakin sakin ɗan guntun murmushi
Malam Liman ne yace.
“Masha Allah, yanzu dai kullum ki ringa zuwa irin wannan lokacin kina ɗauka darasin saboda maza basu fara zuwa ba, dalibai yara kuma sun tashi. kullum zan dinga baki awa ɗaya sai ki dinga zuwa ina ƙara miki sannan da wasu littattafan ma idan kunayi ki faɗa zan dinga ƙara miki”.
Cikin daɗi tace.
“Toh ba matsala Insha Allah sannan munayin littafin Tajweed, Tauheed, Urasatul Nurul yaƙin, Nahwu, da kuma Mi'atu Hadith da dai sauransu”.
Gyara zaman babbar rigarsa yayi tare da faɗin.
“Insha Allah zaku riƙa zuwa ina ƙara miki keda Dija da Ma'u tunda dama sunyi sauƙa”.
Sannan ya buɗe kur'ani ya miƙa mata shi kuma ya shiga karanta mata akai yayin da yake bin ko wanne harafi yana basa haƙƙinsa saida yakai har ƙarshen shafin kafin ya dubeta yace.
“In mai-maita Miki?”.
Kai ta girgiza alamar a'a tana jinjina baiwar ilimi da zaƙin murya da Allah ya masa.
Anutse yace.
“Ki hadda ce su kafin gobe sannan ki kawo min”.
Khausar kuwa kai ta gyaɗa tace.
“Insha Allah zan dage Malam amman dai goben ma zan biya sai jibi a ƙara min ko?”.
Murmushi yayi tare da cewa.
“La ba'as”.
Miƙewa tayi Sannan tace.
“Zan tafi da Kur'anin”.
“Toh” ya cemata
Sannan suka fice bayan fitansu ta dubi Dije tace.
“Muje gidan garkuwan rugan ki”.
Murmushi Dije tayi tace.
“Gidan Baffa Umaru”.
Kai Khausar ta gyaɗa sannan suka nufi gidan Baffa Umaru.
Aƙofar gida suka samesa yana tare da baƙi,
Juyawa yayi ya kallesu kafin yace.
“Kushiga ciki ina zuwa".
Kai suka gyaɗa sannan suka shiga cikin gidan bakinsu ɗauke da Sallama,kallon cikin gidan Khausar tayi ko ina ashere fes-fes babu alamar datti ko ƙazanta.
Adama kuwa murmushi fuskarta ta faɗaɗa tace.
“Su Khausar ne sannun ku da zuwa”.
Dije tace.
“Yawwa Goggo Adama ya gida”.
Ta amsa da lafiya lau sannan ta miƙe ta kawo musu faten doya da ruwa arandan ƙasa mai sanyi.
Ita kuwa khausar murmushi tayi tana jinjina mutunci da karancin Goggo Adama atare sukaci kana suka gabatar da sallan Azahar sannan sukayi mata har zuwa lokacin Baffa Umaru bai shigo ba.
Bayan fitarsu agidan Baffa Umaru Khausar ta juya ta kalli Dije tace.
“Muje gidan Hajja Nana in ɗauki kayana”.
Dije tace.
“Toh”.
Sannan suka nufi gidan Hajja Nana ba suyi wani tafiya mai tsawo ba suka isa gidan, Atsakar gida suka tarar da Hajja Nana.
Harara Hajja Nana ta watsa mata tace.
“Ke kam Uwar gantali kina nan kina ta yawo bazan ganki ba bare in Zauna dake”.
Fuska Khausar ta ɓata da faɗin.
“Wani irin gantali duk ba gidan ƙannenki da ‘ya‘yanki nake zuwa ba kuma ɗazun nan ina anan na tashi zaki ce amma yanzu zaki ce min gantali na tafi to nide gaskiya ba gantalalliya bace yawwa zaki wani cemin gantali ba gidan ƙannenki na tafi ba kuma saida na faɗa miki zamuje Bishiyar ƙare zancenka in kira Mommy na sannan yanzu ki wani cemin gantalalliya to nide wallahi ba gantalalliya bace”.
Hajja Nana tace.
“Ke kam wace gantalalliya ce ma ta fiki?,In banda gantali me kika iya?".
Ita kuwa khausar juya manyan Idanunta dake lumshe kafin tace.
“Wallahi da abinda na iya”.
Hajja Nana kuwa kai ta gyaɗa tace.
“ƙwarai da abinda kika iya fitsara ba gashi ma yanzu kina yi bayan shi babu wani abu da kika iya”.
Khausar za tayi magana Dije tayi saurin riƙe hannunta cikin ƙasa da murya tace.
“Dan Allah kiyi shiru ki ƙyaleta”.
Kai ta gyaɗawa Dije tare da tsuke bakinta.
Hajja Nana kuwa fuska ta tsuke Idanunta akan Khausar tace.
“Bari in samiki doka gidan Jauro da kike zuwa ki kwana bazan hanaki ba tunda kince kinfi farar kura tsoro.
Amma gobe ana sallar asuba na ganki anan dan zaki riƙa tayani aiki.
Baki Khausar ta taɓe da faɗin.
“Allah ya kaimu sannan bawai ana idar da Sallah bane zanzo saina yi Azkharul sabah da kuma karatuna”.
Harara Hajja Nana ta watsa mata tace.
“Toh Al-huda-huda sarkin karatu”.
Khausar kuwa baki ta taɓe tace.
“Koma de menene”. Sannan ta juya ta shiga ɗaki ta dauko kayanta tana fitowa ne taji Hajja Nana na cewa Dije.
“Kar kice zaki koyi rashin kunyar wannan yarinyar".
Dije kam murmushi tayi ita kuwa khausar batare data tanka taba ta fice Dije tabi bayanta...
GEMBILA
Acan ɓangare Moddibo kuwa kwance yake akan makeken gadonsa daya sha shimfiɗa na Alfarma yayin da hannunsa biyu ke haɗa yana addu'ar bacci ya ɗauki kimanin minti goma kafin yasha fa addu'ar ya gyara kwanciyarsa yana mai lumshe idanunsa da haka bacci ya ɗauke sa can cikin baccinsa yaji wayarsa na ruri ya buɗe idanunsa kasancewar sa ba mutum ne mai nauyin bacci ba yasa hannu ya janyo wayar yana kallon screen ɗin Bahrain shine sunan dake ƙasan screen ɗin.