← Book details Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 114

Sashe 86

Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna isa gida Raudat ta fice da gudu tare da shiga falon Idanunta ya saƙa akan Khausar dake zaune gefen Ramadan tana bashi kazar da already ta gama dafawa shi kuwa yana amsa yana ci Zugin ƙafar yayi sauƙi Sosai sai abinda ba arasa ba da gudu Raudat ta shiga tare da ƙara sawa ta rungume kan Ramadan cikin sauri ya ɗaga mata hannunsa na hagu tare da nuna mata ƙafar sake sa tayi tare da komawa gefensa ta zauna kana tace.
“Ya ƙafan ka?”.
Murmushi yayi tare da cewa.
“Da sauƙi”, Langwaɓar da kai tayi kana tace.
“Allah ya ƙara sauƙi sannu³”.
Haiydar kuwa zama yayi agefensa tare da rintse idanunsa hawaye masu zafi suka zubo masa ahankali ya buɗe Idanunsa tare da sauƙe su akan Mommy kana yace.
“Mommy tamkar gimmawar walƙiya haka naga motar nan tazo ta bugi Ramadan sanda yayi sama kafin ya faɗo Mommy banyi tsammanin kansa ba zai fashe ba”.
Khausar dake cirewa Ramadan ƙasusuwa ajikin kazar ta ɗago kanta tare da miƙawa Ramadan tsokar kana ta mayar da kallon ta kan Haiydar tace.
“Allah ne ya kare Haiydar saboda addu'ar mahaifiyarmu saboda haka Ubangiji zai ci gaba da kare mu yana mana katangar ƙarfe da magauta!”.

Da sauri Mommy dake cirewa Raudat Uniform ta ɗago ta kalleta kana tace.
“Khausar wasu magautan kuma wannan ai ƙaddara ce wacce ta riga fata”.
Murmushi mai ciwo Khausar tayi kana tace.
“Hmmm Mommy kenan”.

Acan ɓangaren Hajiya Bunayya kuwa bayan tashiga ɗaki zaune ta samu Amina hannunta riƙe da Tuffa tana ci,
Amina na kallonta tace.
“Mommy ba abinda ya sameshi ko?”.
Ƙwaffa Hajiya Bunayya tayi tare da zama kana cike da takaici tace.
“Ai shi Haiydar ba abinda ya sameshi ko ƙwarzani bai yiba. Ramadan ne kaɗai ya bugu ba wani na arziƙi ba Karayane kaɗai”.
A kufule ta ajiye Mayafinta tare da kallon Amina data tsareta da ido kana tace.
“Na kirasu munyi magana dasu sannan na nuna musu ɓacin raina sai suka ce wai abinda yasa haka saboda lokacin Malamai sun fara zuwa idan suka tsaya za'a iya kama su”.
Ya mutse fuska Amina tayi kana tace.
“Ai dai kam sai ahankali”.

Hannu tasa tare da ɗaukar Ayaba a Plate dake gaban Amina kana tace.
“Ɗazu bayan kin dawo ina kika tsaya dana shigo ban ganki bane?”.
Murmushi Amina tayi tare da cewa.
“Ina side ɗin Gimbiya Dadu nida Uncle Naseer”.
Wara Ido tayi kana tace.
“Allah ko?,Ni dai Amina da zaki yarda sannan badan Masifar Son da yake yiwa wannan shegiyar Khausar mai kama da sadaka Yallanba yanda yaron nan ya samu cigaba da arziƙi ga kuma arziƙin da Iyayensa suke dashi da kin haƙura da Jameel din Nan duk da kuwa arziƙin da Mahaifin sa yake dashi”.

Ƙwaffa Amina tayi tare da cewa.
“Nifa Mommy Ina son Uncle Naseer kuma Ina son Malam Jameel saboda gaba ɗayan su suna da kuɗi kuma dama Ni ko Malam Jameel saboda kuɗin sa nake son sa”.
Sai kuma tayi saurin cewa.
“Yawwa Ummah ni kuwa Akwai Aure atsakanin mu Uncle Naseer?”.
Jinjina kai Hajiya Bunayya tayi tare da ajiye ɓawon Ayaba kana tace.
“Sosai ma kuwa Akwai Aure atsakanin ku ko a musulunci ya halatta”.
Kai Amina ta gyaɗa tare da faɗin.
“Ummah kiga yanda yake kashewa yarinyar nan kuɗi kinga wayar daya siya mata kuwa wayar kusan dubu ɗari huɗu da hamsin kinga siye-siye tunda kinga Malam Jameel Anyi anyi aka mashi awajen Boka an kasa tunda shi wannan yana da riƙo da Ibada shi kuma wannan shgirigirbaune za'ayi saurin kamashi”.
Jinjina kai Hajiya Bunayya tayi tare da cewa.
“Hakane fa Amina nima na fara wannan tunanin ga abu mai sauƙi sawa zamuyi asa ya tsani Khausar ɗin ya soki shidama in anyi auren bazaku wuce wata uku ba anan zaku tafi india”.

Murmushi Amina tayi kana tace.
“Eh kuma wannan abu mai sauƙi ne duk da masifar son da yake yiwa Khausar tun tana ƙarama amma yau ɗin nan tun da muka zauna tsawon zaman mu ya sake min fuska kamar zai iya maraba da duk abinda naje masa dashi”.
Cikin jin dadi ta saki wani murmushi tare da cewa.
“Tun da muka zauna yau ko yawan kiran sunan Khausar da yake yau be yawaita ba Ummah”.
Ajiyar zuciya Hajiya Bunayya ta sauƙe kana tace.
“Bari zamu duba mu gani sannan zamuyi magana akai ai ɗazun muka rabu da Jameel da wannan ɗan banzan Moddibon ko yaushe ka gansa da Jallabiya kamar ɗan Larabawa”.
Dariya Amina ta fashe dashi kana tace.
“Aini shiyasa Samira Sani ke bani mamaki da take son Moddibo me yake dashi meya mallaka komai fa idan kika ganshi dashi sai dai idan Malam Jameel ne ya bashi kullum yana nan acikin Jallabiya bashi da kayan daya wuce Jallabiya ko motar da yake hawa daga kin gani kinsan mahaifin Malam Jameel ne ya saya mishi”.

Ta gumi Hajiya Bunayya tayi kana tace.
“Ikon Allah shi kuma haka yake ashe se Uban faɗin rai kamar ɗan ƙaruna saboda arziƙi yana abu kamar mai rawani gashi da uban kwarjini”.
Tsaki Amina taja kana tace.
“Ko sutura kika gansa dashi sai dai in Malam Jameel ne yasaya mishi saboda duk yawanci kayansu iri ɗaya ne na rasa Meyesa Samira Sani take son shi koda yake inaga tsabar kyansa da ƙwarjinsa take so”,
Sai kuma ta gyara zamanta tare da taɓe baki kana tace.
“Inba hakaba me abin so ajikin talaka faƙiri komai sai aboki ya masa, arayuwa gashi ba kuɗiba se shegen jijji da kai da taƙamar banza da ɗan karen ƙasaita”.
Dariya Hajiya Bunayya tayi tare da kallon Amina kana tace.
“Nima kaina abin ya ban dariya Amina da Hajiya Lami tazo tana ta haukan bin bokaye akansa yaron da ko wa'azin sa kake kallo yana cikin Jallabiya da Hirami kamar rainon Saudi”.
Dariya Amina tayi kana ta taɓe baki tare da faɗin.
“Ai dai kam ni dai mai ruwana su suka sani mu dai yanzu mun canza shekarar mu daga kan Malam Jameel zuwa Uncle Naseer”,
murmushi ta saki tare da kallon Hajiya Bunayya kana tace.
“Idan kuma za'a tayi akansu su biyun muna raba ƙafa da duk wanda yazo tun da duka Iyayen su nada arziki kuma suma suna dashi duk kansu babu wanda yayi karatu aƙasar nan ko wannensu mijin nunawa sa'a ne da zaran na auri ɗaya daga cikinsu zan zama big Girl acikin garin nan”.

Acan ɓangaren Gimbiya Dadu kuwa Uncle Naseer ne zaune akan 2sitter hannunsa riƙe da wayarsa yana latsawa Gimbiya Dadu na zaune kan Sallaya tunda ta idar da maghariba bata motsa ba suna taɓa hira jefi-jefi.
Cike da nutsuwa Lamiɗo yayi sallama ya shiga, tare da miƙawa Uncle Naseer hannu sukayi Musabaha kana ya gaishe da Gimbiya Dadu.
Cikin sanyin Murya Lamido ya kalli Gimbiya Dadu kana yace.
“Ɗazu fa Ramadan ya gamu da hatsari ya karye”.
Da sauri Uncle Naseer ya ɗago kansa kana yace.
“Subhanallah³ ikon Allah”.
Gimbiya Dadu ma cikin sauri ta ɗago kanta tare da kallon Lamiɗo cikin yana yin damuwa tace.
“Subhanallahi bari idan na idar da Sallar Isha'i zanje in duba sa”.
Miƙewa Uncle Naseer yayi tare da cewa.
“Bari naje na dubasa”.
Ya faɗa tare da ficewa.

Kai tsaye sashen Mommy ya nufa bakinsa ɗauke da Sallama Ahankali Idanunsa suka sauka akan Khausar dake zaune gaban Ramadan kallon falon yayi yaga ba kowa sai su kadai.
Ahankali Khausar data ji Sallamar sa ta juya ta kallesa.

Cike da duniyan ci ya sakar mata da mayaudariyar murmushi kana ya kashe mata ido ya wani langwaɓar da kai tare da Shagwaɓe fuska kana yace.
“Ya dai Matas?”.
Shiru Khausar tayi tare da yin ƙasa da kanta cike da mamakinsa aranta tace Uhmmm Uncle Naseer da tsaurin Ido duk abinda ya aikata ashe zai iya zuwa inda nake.

Cikin rashin damuwa ya matsa kusa da ita idanunsa akan Ramadan yace.
“Ayyah Ramadan sorry Allah ya sawwaƙa³”.
Kai Ramadan ya gyaɗa kana yace.
“Ameen Uncle Naseer”.
Hannun Ramadan ya riƙe tare da cewa.
“Me kakeso in kawo maka”.
Kallonsa Ramadan yayi tare da cewa.
“Komai ma ka siya min ina so Uncle Naseer ”.
Kai ya gyaɗa tare da cewa.
“Toh Autan Mommy”.

Ahankali Naseer ya juya ya kalli Khausar da Idanunta ke kan Ramadan ya narkar da murya tare da faɗin.
“Mommy fa?”.
Kamar ba zata ce komai ba sai kuma tace.
“Ta shiga ciki tana Sallah Isha'i ne”.
Jinjina kai yayi kana yace.
“Ayyah Allah ya bashi lafiya”.
Ta lumshe Idanunta tare da cewa.
“Ameen ya Allah”.
Ahankali ya juya gareta tare da gyara zamansa akan rock ɗin kamar yatsun hannunsa zasu taɓa yatsun Ƙafarta.

Ya karyar da kai tare da sanyaya muryarsa kana yace.
“My dear yau kusan kwana uku kenan koda naki ra wayar ki bata shiga idan wani laifi na miki sai ki faɗa min laifina in baki haƙuri duk da cewa ina da yaƙinin bani nayi miki laifa kece kikayi min laifin, gashi ke kuma baki iya bada haƙuri bako”.
Saurin Kallonsa Khausar tayi tare da maimaita bani nayi miki laifi ba aranta.
Kamar yasan tunanin da take ya jinjina kai tare da narkar da murya kana yace.
“Yes My Khausi Kece kika yi min laifi amma baza kiban haƙuriba to naji na amshi laifina.
Ni zan baki haƙuri duk da cewa kin ɓata mana aiki”.
Sai kuma ahankali ya juya ya kalli ƙofar Bedroom ɗin Mommy kana ya kalleta duk ya koma kalar tausayi kana yace.
“Kin ɓata mana aiki My Khausi baki damu da rayuwata ba ke baki damu da in mutu ko ina rayu ba abinda na faɗa miki ai ba jini kawai ake buƙata ba tunda ba Jinin mutum kawai ba jinin ma na Period ɗin mace magani za'a haɗa min”.
Ta gefen ido ya saci kallonta tare da fesar da numfashi kana yace.
“Amma kika je kikayi min abinda bashi bane, Wallahi kin yimin muguwar fahimta wallahi ba wani abu bane saboda yanda kika ɓata kikasa na dabba shiyasa aka samu akasin da aka samu”.
Chapter 86 · 0% Book details