← Book details Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 114

Sashe 17

Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Ina magana kina magana!?”.
Hajja Nana ta fadi a faɗace.
Cikin tura baki tace.
“Ai gaskiyane”.
Danƙolo Momy ta yiwa Khausar hakan yasa ta tsuke bakinta.
Ɗaya daga cikin ƙannen Hajja Nana wanda ya kasance shine ƙaramin su (Autah)ya miƙe da faɗin.
“To bari na kawo musu”.
Sannan ya shige uwar ɗakan Hajja Nana ba daɗewa ya fito hannunsa riƙe da Akwashi ya ajiye agabansu sannan ya koma ya ɗauko goran zuma kana ya koma ya sake ɗauko wani Akwashin.

Hajja Nana ta dubi Momy tare da cewa.
“Ayyah wallahi ban san da zuwanku ba”.
Kai Momy ta gyaɗa tare da cewa.
“Ai inata gwada kiran layin ki baya shiga”.
Murmushi Hajja Nana tayi kana tace.
“Kinsan Rugar tamu bamu da network se kaje bishiyar ƙare zancenka in kaje bishiyar ma seka hau sama ni kuma ban cika son zuwa ba da girmana Inje in hau bishiya na faɗo”.

Khausar kuwa taɓe baki tayi tace.
“Hmmm ba network kuma har sai anje wani bishiya?”.
Harara Hajja Nana ta watsa mata ta cigaba da cewa.
“Wallahi bansan da zuwan kuba dana shirya muku abin taɓa wa”.
Murmushi Momy tayi batace Komai ba.
Akwashin da aka shigo dashi ne Autansu Hajja Nana ta buɗe Nono ne me zafi yana tururi ga kuma goran zuma dake gefe ɗayan kuma daya buɗe ɗumamen danɗerun zabbi ne suna tururi.
Sauran mazan dake kewaye da Hajja Nana ce suka shiga Gaisawa dasu Lamiɗo.

Muskutawa Hajja Nana tayi tare da gyara zamanta ta kalli Lamiɗo dake zaune ya tanƙwashe ƙafafunsa tace.
Wa'annan daka ke kallo duka ƙannena ne mu goma ne acikin mahaifiyarmu gaba ɗayansu Mazane ni Kaɗai ce mace kuma nice 'yar Fari.

Jinjina kai Lamiɗo yayi yana sauraronta da duka nutsuwarsa duk da yasa abinda take faɗa kishin. tunda ba yaune zuwansa na firkoba.
Ita ko Hajja Nana nuna wanda ke gefenta tayi tare da cewa.
“Ga mai bina Jauro, Sannan kuma sai Sadu, Sannan se Abubakar, Sai kuma Garga, sannan sai Aliyu liman, Sannan kuma sai Dumau ,Sai Salmanu, Sannan kuma Isa sai kuma Umaru”.
Lamiɗo kuwa kallon su yake yana sake tabbatar da abinda ta faɗa saboda kamannin dake tsakanin su.

Hajja Nana tayi murmushi tace.
“Duk ƙanne nane sannan kuma duk da matansu”.
Ta nuna Jauro tace.
“Matan sa biyu,Garga ma Matansa biyu, Sannan Sadu ma matansa biyu, sai kuma Liman shima Matansa biyu”.
Ta sake nuna Jauro, Sadu, Garga, da kuma Liman tace.
Jauro da Sadu 'ya'yansu maza biyu sunyi aure kuma 'ya'yan Liman da Garga suka Aura ma'ana Auran dangi sukayi”.
Lamiɗo kuwa murmushi yayi alamar yana fahimtar abinda take faɗa masa.

Ita kuwa Hajja Nana cigaba tayi da cewa.
“Duk garinmu babu bare mu ya mune, sannan kuma babu maye mu garinmu atsarkake yake kushigo hankalin ku kwance ku fita lafiya,
Salamun Ƙaulan Min rabbil Raheem”.

Momy kuwa sunkuyar da kai ƙasa tayi Saboda tasan ana zargin Mahaifiyar Lamiɗo da Maita.
Shima Lamiɗo sun kuyar da kansa ƙasa yayi dan yasan zargin da ake yiwa Mahaifiyar sa kenan kasancewar sa mutum me haƙuri da kuma dattako saiya ɗago kansa fuskarsa ɗauke da murmushi yace.
“Masha Allah yayi kyau zuri'a tayi albarka Allah yaƙara rufa asiri”.
Murmushi Hajja Nana tayi tace.
“Ameen ya Allah”.

Domin Hajja Nana 'yar takife ce bata tsoro inma tsoron wani abu ake itace ke isar dashi.
Miƙewa Sauran sukayi suna kallon Lamiɗo suka ce bari mu barku kuci abinci sannan suka fice.

Itama Hajja Nana miƙewa tayi tace.
“Khausar zo mu shiga ciki kici naki”.
Girgizi kai Khausar tayi tace.
“A'a zanci anan”.
Ta juyi ta dubi Khausar da kyau tace.
“Kizo mu tafi nace”.

Shi kuwa Lamiɗo cike da ladabi yace.
“Da kin barta munci anan ɗin babu matsala”.
Juyawa Hajja Nana tayi kafin tace.
“Toh shikenan”.

Miƙewa Khausar tayi tabi bayanta ta karɓo ƙananan akwashi aka zuba mata sannan suma suka zuba,Yanayin sanyin da ake tsugawa agarin yasa mazauna garin ke bukatar abu me ɗumi,Suna cin zabbin suna ɗaurawa da Nono me ɗumi bayan sun gama Khausar ta miƙe ta tattara akushin ta mayar.
Ganin ta mayar ne yasa Hajja Nana fitowa suka zauna.
Atake sega yara suna ta shigowa a jere a jere angama abincin rana suna kawowa duk gida Jen garin Hajja Nana tana da kwanonta acan suna kawo mata abinci domin ita bata girki abinci safe ne kawai bata Yarda akawo mata ita take dafa wanda zata ci,Duk ƙannenta taran nan sai ankawo kwanuka tara an ajiye mata ga kuma na 'ya'yansu da sukayi Aure tana da ƙore goma sha uku.
Ga yaran garin ƙanana kyawawa dasu farare soll kamar irin yaran ƙauyen larabawa.
Lamiɗo da kansa da yaga yaran na shigowa sun basa sha'awa,Ko wacce idan tashigo zata ce.
“Goggo Hajja! Goggo Hajja!! Aɗonna”.
Ƙannenta da Addah Nana suke kiranta 'Ya'yan ƙannenta kuma Goggo Goggo Hajja idan kuma jikoki zasuce mata Hajja Nana.
Duk Wacce ta kawo mata abinci zata ce nice,daga gidan Sadu,Nice daga gidan Garga,saboda yawansu kowa ke gabatar da kansa.
Duk wanda yazo ya ajiye zata ce.
“Angode masu nomawa Allah ya basu ƙarfi da lafiyar nomawa masu girkawa ma Allah yabasu ƙarfin girkawa”.

Sannan ga yanayin tsarin yaran garin babu alamar ƙazanta ajikinsu ko wanne tsaf dashi ga kuma tarbiyya duk wanda suka zo sai sun tsugunna sun gaida Lamiɗo da Momy da fulatanci kasancewar basu iya Hausa Sosai ba.

Ɗaya daga ciki data zone ta ajiye kwanon Idanunta akan Khausar tace.
“Goggo Hajja Khausar naa” .
Murmushi Hajja Nana tayi tace.
“Eh”.
Murmushi yarinyar tayi ta matso kusa da Khausar tace.
“Sunana Dija”.
Murmushi Khausar tayi tace.
“Yayi kyau Dija”.
Dija ta kuma murmushi tace.
“Kullum Goggo Hajja na bamu labarin ki rabonki da nan tun kina ƙarama yanzu ya kai shekara shidafa ake cewa”.
Kai Khausar ta jinjina da faɗin.
“Eh”.
Hannunta Dija ta riƙe tace.
“Kizo muje gidanmu ku gaisa da Mamana”.
Ta ƙare mgnar tare da jan hannu Khausar suka fice...

Kiran sallan Azahar yasa Lamiɗo ya miƙe ya tafi masallaci tare da Ƙannen Hajja Nana ita kuma Momy tayi alwala tare da gabatar da sallah bayan sun idar da Sallah Hajiya Aysha ta ɓude jakan da tazo dashi ta fito da turaman zannuwa da Sabulai ta miƙawa Hajja Nana.
Murmushi Hajja Nana tayi tace.
“Hadda ɗawainiya haka?,To angode Allah yayi albarka”.

“Ameen”, Momy ta amsa kafin tace.
“Hajja ga Khausar nan na kawo tayi hutu amma mako uku ne hutun nasu”.
Murmushi Hajja Nana tayi tace.
“Toh Nagode”.
Ita ko Momy tana gyara mayafinta tace.
“Sati uku ne hutun nasu”.

Faska Hajja Nana ta tsuke tare da cewa.
“Sai kin sake Jaddada min ne?”.
Da sauri Momy ta girgiza mata kai.
Cikin isa tace.
“Toh sai sanda naga dama zata dawo kinyi naki saura nawa”.
Ƙasa da kai Momy tayi tare da faɗin.
“Shikenan Hajja duk yanda kikace yayi mukan zamu tafi”.

Miƙewa Hajja Nana tayi tace.
“Bari akira muku Khausar kuyi sallama”.
Cike da ladabi Momy tace.
“A'a Hajja base ankira taba”.
Dan tasan muddin aka kirata sai tayi kuka kafin su rabu.
Sallama suka sake yi musu kafin suka fice suka tafi...

Acan Gembila kuwa Washe gari.
Asabar Moddibo ya shirya kamar ko yaushe cikin Jallabiya Sky blue Kansa sanye da hula da kuma hirami cikin nutsuwarsa kamar ko yaushe ya shiga cikin makarantar yana motsa laɓɓansa alamar tasbihi da hannu kawai yake amsa gaisuwar da ɗaliban haddar ke masa kai tsaye Ajin haddarsu Khausar ya nufa yayin da Aransa yayi ƙudurin sawa Malam Bello ya casa masa ita saboda gaba ta kiyaye domin ya lura ganganci da sakalci ke damunta.
Cikin rashin sa'a yana shiga ajin ya samu bata nan.
Asma'u ya kira.
Cike da ladabi ta fito tare da tsugunnawa agabansa tace.
“Gani Yah Moddibo”.

Tsayuwar sa ya gyara cikin yanayin sanyin Muryansa yace.
“Ina wannan Birin?”.
Asma'u kuwa kanta aƙasa tace.
“Nima yau da nazo ban ganta ba sai nake tambayar Amina ina take shine tace wai taje garin Kakanninta”.
Ƙwafa yayi yace.
“Shikenan yayi kyau”.
Kana ya juya ya bar waje....

Acan mota kuwa Momy ta dubi mijinta tace.
“Kayi hakuri da Hajja Nana yanayin tsufa ne”.
Murmushi yayi still Idanunsa ahanya yace.
“Ai bakomai ba gamu da Gimbiya Dadu ba ai haka take”.

Acan Rugar Jauro yaya kuwa bayan Khausar ta dawo gida ta tar da Momy ta sun tafi ta tsare Hajja Nana da ido tace.
“Meyesa ba ki kirani ba kafin su tafi?”.

Salati Hajja Nana ta sanya tace.
“Tuhuma ta kikeyi? Ko kuma me?”.
baki ta cinna sama tare da cewa.
“Ai gaskiyane abinda ya dace na faɗa”.
Salati Hajja Nana ta sanya tare da faɗin.
“Ohhh ni Shatu Allah ya nuna min 'yar Usmanu yarinya kamar ruwan aski sai rashin ta ido”.
Ta ƙare mgnar tana kallon Khausar dake tsaye fuska akumbure cikin tsawa tace.
“Bari kiji in faɗa miki ni agarin nan idan nayi magana kamar yankan wuƙa yake babu me bani Amsa ko musu ko jayayya dani!”.
Ita kuwa Khausar wani irin juya Ido sama tayi tare kana tace.
“Uhummm to gwara ma ki sani.
Idan maganarki yankan wuƙa ne to kin samu me yankan rez”......!

Littafin SAKAYYAH na kuɗine biya ki karanta 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA

By
*GARKUWAR MARUBUTA*
[19/07, 7:44 PM] Halimatu A/rahman Sadeeya: 📝🍇✨💫⏰🤴🏻👹❤️❤️❤️🍇

*SAKAYYAH*
_Page 5_

*NA*
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*FREE PAGE*

*LITTAFIN SAKAYYAH NA KUDINE, 1K NE KACAL ki biya ki karanta cikin Aminci ba haƙƙin wani a kanki. 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA, sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276.*

Zare Ido Hajja Nana tayi cikin faɗa da fushi tace.
“Ke! Ke!! Ke!!!.Faɗimatu ki kiyayi kanki dani fa zan tsige Miki fuka-fukinki!”.

Ita kuwa khausar fuska ta haɗe Idanunta tsaye akan Hajja Nana tace.
“Nifa ba tsuntsuwa bace da zaki tsige min fuka-fuki, ai gaskiyane tsakani da Allah da Annabi mahaifiyata zata tafi kinsa ankawo ni aise ki kirani muyi sallama na musu Allah ya tsare”.
Ta ƙare mgnar tare da juyawa ta kalli Dija tace.
“Fisabillilhi ba haka ya kamata ba Dija?”.

Dija kuwa tuni ta sunkuyar da kanta yayin da jikinta ya shiga ɓari tsananin tsoro ya bayyana afuskarta sanin halin Hajja Nana babu wanda ya isa tana magana yana mayar mata da martani!.
Chapter 17 · 0% Book details