← Book details Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 112 OF 114

Sashe 112

Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Acan Asibiti kuwa ana kai Moddibo likitoci suka shiga bashi temakon Gaggawa saidai koda wasa bai farfaɗo ba ganin haka yasa suka dauƙo wani na'ura mai kama da Iron akafara danna masa aƙirji.
Amman ina babu alamun zai motsa, sosai likitocin suka dugufa wurin ganin sun cetoshi, a karo na biyu suka kuma danna mishi a ƙirjunshi, amman ina, Dr Lukman ne ya karɓi aikin tare da goggoga jikin na'urar ya manna masa a kirjinsa da ƙarfi.
Cikin ikon Allah yaja wani dogon numfashin sake dannawa yayi da karfi wani irin maraitaccen numfashi ya sake ja amma still bai farfaɗo ba sake dannawa sukayi akaro na biyar ne yaja wani dogon numfashi tare da buɗe idanunsa kana yace.
“Jyyyyyyy”.
Malam Arɗo da bai daɗe da dawowa daga gidan Abba bane, yayi saurin riƙe hannunsa tare da cewa.
“Moddibo kayi addu'a”.
Duk da cewa baya Cikin nutsuwarsa hakan bai hanashi maimaita duk wata addu'a da tazo bakinsa ba ahankali ya ɗago kansa tare da kallon Malam Arɗo yace.
“Malam J ɗina nefa!”.
Jinjina kai Malam Arɗo yayi cike da tausayawa yace.
“Eh shine Moddibo Allah ya karɓi Jameelu muyi masa addu'a Allah ya karɓi shahadarsa”.
Girgiza kai Moddibo yayi tare da cije lips ɗin sa duka biyu, kana ya runtse Idanunsa cikin wani irin yanayi mai wuya yace.
“Malam Arɗo mutuwar azaba suka masafa, ɗaure sa sukayi suka ajiye masa goran ruwan agabansa ta yanda yana ji yana gani bashi da damar sha sun barshi da azabar ƙishi”.
Kallonsa Malam Arɗo keyi cike da tausayawa yana ganin yanda zuciyarsa ke bugawa da ƙarfi.
Cikin wata raunan'niyar murya Moddibo ya cigaba da cewa.
“Malam ɗaure sa sukayi suka ajiye masa wayoyinsa agabansa ta yanda yana kallon muna kiransa bashi da damar ɗauka bare yace mukawo masa ɗauki”.
Sai kuma ya rintse idanunsa da masifan ƙarfi zuciyarsa na cigaba da buguwa da masifaffen ƙarfi kana yace.
“Ɗaure sa sukayi ta yanda yana ganin ga hanyar tsira sai dai bashi da damar kiran wani ya kawo masa ɗauki ɗaure sa fa sukayi ta yanda yana ganin kiran mu amma bashi da damar ɗauka”.
Jujjuya kansa ya farayi kamar zautacce hawaye na bin gefe da gefen idanunsa har suna shiga kunnensa cikin Muryan kuka yace.
“Ɗauresa fa sukayi ta yanda yana ganin kiran Abbansa bashi da damar ɗauka,Mutuwar azaba da raɗaɗi suka masa da ƙishi fa suka kasheshi”.
Kasa ƙarasa maganar yayi kawai ya fashe da matsanancin kuka mai tafiya da numfashi Atake numfashinsa ya ɗauke ya sake sumewa!.

Cikin sauri Malam Arɗo ya miƙe tare da kiran likitoci kana ya sanar dasu ya sake suma taruwa likitocin sukayi akansa kana suka shiga bashi temakon Gaggawa da kyar da temakon Allah suka samu ya farfaɗo ganin ya farfaɗo yasa Dr ya masa Alluran bacci Atake baccin wahala ya ɗauke sa.
Ajiyar zuciya Malam Arɗo ya sauƙe tare da miƙewa ya fita kana yayi dearling number Lamiɗo yana ɗauka yace.
“Ranka shi daɗe yaron nan fa gashi agigice yake baki ɗaya da zaran ya farfaɗo sunan Marigayi Jameelu yake kira, yana kiran sunan kuma zai sake suma!”.

Acan gidan Abba kuwa zaune yake afalonsa hannunsa riƙe da waya tunda suka dawo yake zaune awajen ya kasa koda motsawa se kwalin Gawar Jameelu daya zubawa Ido yana jujjuya wayar hannunsa ajiyar zuciya ya sauƙe tare da kiran number Ummi Yana Jin tayi picking ya fesar da numfashi kana yace.
“Fatima”.
Cike da mamaki Ummi tace.
“Abban Jameel”. Jin muryansa.
Cikin raunin murya ya sake cewa.
“Fatima”.
Anutse Ummi ta amsa da.
“Na'am”.
Runtse Idanunsa yayi kana yasake cewa.
“Fatima”.
Cikin dakiya Ummi da taji zuciyarta ya tsinke da Masifar ƙarfi tace.
“Na'am Abban Jameel ka faɗa min me yasamu Jameelu na sun kira ne ko kuma yaya!?”.
Cikin rauni yace.
“Hmmm”.
ya faɗa tare da katse kiran kana ya fito da Number Malam Ahmad.

Malam Ahmad na ɗagawa Abba yace.
“Malam kazo da Fatima da yaranta!?”.
Cikin tsinkewar zuciya Malam Ahmad dake Bedroom ɗinsa ya miƙe tare da cewa.
“Meya faru Alhj Bashir ka faɗa min”.
Girgiza kai Abba yayi tare da taune lips ɗinsa kana yace.
“Ga gawar Jameelu na agabana”.
Cikin tsanananin tashin hankali Malam Ahmad ya dafe bango tare da faɗin.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n Allahumma Ajirni fii musibati wa'ahlifli khairan minha”.
Katse kiran Abba yayi cikin sauri ya fito falon tsaye ya samu Ummi riƙe da waya a hannunta cikin ƙoƙarin ɓoye tashin hankalin sa yace.
“Fatima Lafiya!?”.
Ahankali Ummi ta juya ta kallesa tare da cewa.
“Yan zun nan Abban Jameel ya kirani, to kuma ya yanke gashi kuma ina ta sake kira naji line Busy”.
Da ƙyar ya haɗiye wani abu mai masifar ɗaci kana cikin ƙoƙarin ɓoye damuwarsa yace.
“Toh kada ki damu kizo muje muji meke faruwa”.
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
“Toh”.
Sannan ta nufi hanyar fita.
Kallon Bashir da Asma'u dake tsaye yayi kana yace.
“Kuma kuzo mu tafi”.
Kai suka gyaɗa kana suka bi bayansa suka fita.

Suna isa falon suka samu Hajiya Turai da Hajiya Karima da ƴaƴan Hajiya Karima na kuka cikin sauri Ummi ta ƙara sa shiga falon tare da tsayawa agaban Abba kana tace.
“Abban Jameel meye faru?”.
Ahankali ya ɗago ido ya kalleta, sai alokacin yaji kuka ya kufce masa ganin Ummi agabansa baki ɗaya ta gigice jikinta na rawa.
Cikin rawan murya tace.
“Abban Jameel meyafaru!?”.
Kasa cewa komai Abba yayi sai kuka da yake tamkar ƙaramin yaro.
Da sauri Ummi ta juya tare da kallon yanda su Hajiya Turai ke kuka cikin rawan murya da yanayin tashin hankali tace.
“Ku faɗa min mana meke faruwa!?”.
Tayi tambayar baki ɗaya ilahirin jikinta na rawa.
Asma'u da Bashir dake tsaye Atare suka fashe da matsanancin kuka ganin yanda ƙannen M Jameel ke kuka.
Ahankali Malam Ahmad ya matso kusa da Ummi tare da cewa.
“Fatima ki zauna”.
Girgiza kai tayi kana tace.
“Ni bazan zauna ba kafaɗa min abinda ke faruwa”.
Cikin sanyin murya Lamiɗo yace.
“Maman Jameel kiyi haƙuri ki zauna”.
Kallon sa tayi tare da cewa.
“In zauna?”.
Kai ya gyaɗa mata kana yace.
“Eh”.
Cike da tausayawa Malam Ahmad ya janyo hannunta tare da zaunar da ita.

Abba kuwa kallonta yayi cikin tsanananin fargaba da tashin hankali yace.
“Fatima”.
Cikin rawan murya da raunin zuciya tace.
“Na'am Alhj Bashir”.
Cikin sauri Abba ya kalleta wannan shine karo na farko arayuwar sa da yaji ta kira sunan shi kai tsaye.
Jinjina kai tayi Idanunta tsaye akansa tace.
“Eh Alhj Bashir ka faɗa min menene? kafaɗa meke faruwa”.
Rintse idanunsa yayi yana jin kansa na sarawa Araunane yace.
“Fatima Jameelun mu”.
Kai ta gyaɗa kana tace.
“Eh nasani akan Jameelu ne to Menene ya faru?”.

Kasa cewa komai Abba yayi kawai sai ya fashe da matsanancin kuka yayin da hawaye ke bin kuncinsa Shar-shar-shar.
Cikin raunin murya yace.
“Fatima ga Gawar Jameelun mu”.
Atake maganar ya daki dodon kunnenta kana ya ratsa ƙwaƙwalwar ta zuwa zuciyarta saurin kallon Abba tayi tare da sakin Murmushi kana ta juya tare da kallon su Hajiya Karima dake kuka cikin wata dakakkiyar murya mai cike da ƙuna tace.
“Toh kukan me kukeyi!?,
Juyawa tayi tare da kallon Abban M Jameel kana tace.
“Har kaima kuka kakeyi!?Haba Alhj Bashir Addu'a ya kamata ka masa amma ba kuka ba!, Su mata suyi kuka kaina kayi Yanzu ina yake?”.
Cikin sheshsheƙan Kuka Abba ya nuna mata kwalin da ya tsarsa kana yace.
“Gashi can”.
Saurin Kallon wajen tayi Zuciyarta na bugawa da masifar ƙarfi still Muryanta adake da wani irin bushewa da hurawar zuciya tace.
“Gawar ne kuma acikin kwali”.
Cikin wata raunan'niyar murya ya Girgiza kai kana yace.
“Kiyi haƙuri kiyi ta maimaita Addu'a”.

Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da rintse Idanunta kana tace.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n Hasbunallahu wani'imal wakin La'ilaha Illah anta subhanaka inni kuntu Minal Zhalimin Allahumma Ajirni fii musibati wa'ahlifli khairan minha³”.
Ahankali ta gyara zamanta tare da naɗe ƙafafunta tare da sakin murmushi kana ta fuskanci gabas yayin da Idanunta suka kaɗa sukayi jawur jikinta na wani irin tsuma na tsananin tashin hankali cikin raunin murya tace.
“Ya Allah kaine ka bani Jameelu, kai kasa ya zamemini Garkuwa, ya Allah kajiƙan sa da rahma, ya Allah kasa ya huta Alfarman Annabi da Alkur'ani, Allah kayi mana SAKAYYAH akan dukkan waɗanda suka cutar damu ya Allah kayi mana SAKAYYAH”.
Kusan a haɗe baki daya mutanen falon suka amsa da Ameen.
Wani irin kuka mai tsuma zuciya ne ya kufcewa Asma'u da Bashir musamman Asma'u numfashinta har fisga yake baki ɗaya Falon kaurewa yayi da koke cikin rawan murya Ummi tace.
“Ina gawar yanzu Jameelu na ne haka acikin kwali?”.
Jinjina mata kai Abba yayi tare da cewa.
“Eh shine”.
Still Muryanta adake tace.
“Wani irin mutuwa yayi da har gawarsa zata ƙankace ya zauma acikin kwali”.

Asp dake tsaye ya kalli Ummi cike da tausayawa yace.
“Hajiya kiyi haƙuri ya riga daya bushe, shiyasa ana taɓa shi ya kakkarye!”.
Ahankali ta juya ta kalli Asp kana tace.
“Toh ya akayi kuka tabbatar Jameelu na ne?”.
Cike da tausayawa Asp ya ƙara sa gaban Kwalin kana ya buɗe mata ahankali Ummi ta tsirawa jerarrun gabɓan gawar dake cikin kwalin ido ahankali ta sauƙe Idanunta akan zara-zaran yatsun, hannunsa da suka bushe kana ta tsirawa zoben hannunsa ido.
Cikin wani irin yanayi na ƙunan zuciya da sadaukarwa tace.
“Hmmm!”.

Ahankali Asp ya sake nuna mata takalmin M Jameel dake cikin leda da kuma wayoyinsa cikin sanyin murya yace.
“Ga takalmansa da kuma wayoyinsa duk agabansa muka samu sun ajiye masa da goran ruwa.

Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da fesar da numfashi kana tace.
“Tabbas Jameelu na ne”.
Ahankali ta matsa jikin kwalin sosai tare da sanya tafin hannunta ta rufe kana ta sunkuyar da kanta akan kwalin cikin Muryan ta daya fara karaya tace.
“Babana bazan yi maka kuka ba, sannan baza zubar maka da hawaye ba, kana bazan yi maka Ihu da kururuwa ba, amma zan ƙarashe baki ɗaya sauran rayuwata ina maka addu'a, zan ƙare rayuwata da ƙunan rashinka zan ƙare rayuwata babban giɓin rashinka”.
Chapter 112 · 0% Book details