← Book details Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 114

Sashe 28

Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ƙasa da murya Baffa Umaru yayi yace.
“Dan Allah Addah Nana kiyi haƙuri kinsan yarinta ke damunta idan ta girma ba zatayi ba”.
Ya ida maganar tare da jan hannun Khausar suka fice waje.

Bayan sun fita ya juya ya kalleta yace.
“Haba Khausar kidena ki koyi yanda zaki zauna da manya kinga Addah Nana tsufa ya kamata tana buƙatar rarrashi da lallami, kinga duniyar nan ba matabbata bace idan yau kaine gobe ba kai bane ita rayuwar nan bata da tabbas, ki koyi magana mai daɗi ke idan Mahaifinki ina ita fa ɗan ta ne data haifa acikinta kuma ɗan ta mafi soyuwa agareta kada ki sake haka kinji Khausar am”.

Ta gyaɗa masa kai da faɗin.
“Toh shikenan Insha Allah bazan sake ba”.
Ya shafa kanta yana murmushi yace.
“Allah ya miki albarka kizo muje gidana mu kwana zansa ayanka miki Zabbi kici tun da mun gama cin abinci".

Kai ta gyaɗa tare da yin murmushi tace.
“Toh”.
Ya riƙe Hannunta suka tafi suna tafiya suna hira har suka isa gidan bakinsu ɗauke da Sallama suka shiga gidan Adda Adama ta fito daga ɗaki tare da amsa musu sallamar.

Kallon Adama Baffa Umaru yayi yace.
“Akwai nama ne?”
Adama tace.
“Eh akwai Zabbin da aka yanka da yamma yanzu nake ƙarasa dahuwarsu”.

Yace.
“Toh shikenan ki ƙara sa gyarasu ki kawo ma wannan Kuran Birnin taci”.
Dariya Khausar tayi tana zama akan taburman da Adama ta shimfiɗa musu, shi kuma Baffa Umaru ya zauna daga gefenta yayin da Adama taje taci gaba da aikinta kasancewar farin wata ya haska ilahirin garin.

Anutse Baffa Umaru ya kira sunanta da faɗin.
“Khausar”.
Ta ɗago kanta tana kallon fuskarsa acikin farin watan kafin tace.
“Na'am”.
Idanunsa kanta yace.
“Kinsan kamannin Babanki?”.
Kai ta girgiza masa tare da faɗin.
“A'a bansan kamanninsa ba”.
A sanyaye yace.
“Amma kin san akwai Baffanki ai yayan Babanki Hammadu Ɓadamaya ko?”.

Tace.
“Eh amma Ɓadamaya yake ko?”.
Yace da ita.
“Eh yana can Ɓadamaya dashi da Iyalansa da kuma ahalinsa gaba ɗaya.
Insha Allah wataran Zakije shida Babanki Uwa ɗaya Uba ɗaya".
Kai ta jinjina da faɗin.
“Eh Mommy na tafaɗa min cewa inada Baffa yana can Ɓadamaya dashi da matarsa da kuma ‘Ya‘yansa”.

Murmushi yayi yace.
“Toh idan kinje zaki ga mai kamannin Mahaifinki sak da sakin sunan sa Aliyu shine yake kama da Mahaifinki ya gaji Babanki komai da komai kuma shine aka aurawa yayarki Nenne”.
Kai ta gyaɗa tace.
“Toh yaushe zanje in gansa?”
Yace.
“Kinga kamannin Mahaifinki kamar balarabe kinga ba yabon kai ba mutanen Rugar mu duka kyawawa ne amma kyawun mahaifin ki ya fita da ban farin Mutum ne kyakkyawa ga kuma gashin kansa mai tsawo da sheƙi wannan gashin naki ma shi kika ɗauka”.

Idanunta ta lumshe cike da kewar mahaifinta sai kuma ta buɗe su tace.
“Aikam nasan gashin sa na ɗauka ba Mamansa ba da kai agwagwiye".
Murmushinsa ya faɗaɗa da faɗin.
“Ina Addar tawa kike yiwa ba'a itama tsufa ce yasa gashinta kaɗewa”.
Murmushi tayi tace.
“Ai lalle kam”.

Sai kuma ta dai-dai-ta nutsuwarta tace.
“Ku kuma dama nan ne asalin Rugarku?”.
Kai ya gyaɗa mata yace.
“Eh asali nan ne Rugar mu iyaye da kakanni”.
Tace.
“Toh Meyesa ita Hajja Nana ta dawo nan kuma ina ne asalin garinsu Babanmu?”
Murmushi yayi yace.
“Asalin garinsu Babanki yana da nisa lokacin da Addarmu tayi aure ta daɗe kafin tazo ta samu haihuwa to data haifi na farko sai Allah ya sake kawo wasu akan lokaci ta haifi yara uku sai Allah yayiwa kakanki daya haifi Babanki rasuwa,sai ta nemi zata dawo to data nemi zata dawo sai sukace tabarmu su yaran ita kuma tana son yaran sosai sai tace Inde akan dukiya ne tabar musu duka subarta ta taho da ‘Ya‘yanta”.
Zama Khausar ta gyara tana sauransa da kyau.
Shi ko a hankali ya cigaba da cewa.
“Dake dangin Mahaifinki mutane ne masu karamci sai sukace su ba dukiyar su suke buƙatar ba kawai dai suna so suriƙa ganin ɗan uwansu ne sannan ita macece kada subar mata nauyi amma tunda tana son Zama da ‘ya’yanta baza su hanata ba sai suka bata duka gadon Mahaifinki da kuma na Baffanki da ƙannensa mata biyu hadda mai sunanki.

A ranar da tashigo Rugar nan tashigo da aƙalla shanu sun kai ɗari biyu sannan harda raƙuma da tumakai duk gadon sune aka ɗauka aka basu suka dawo”.
Sassayan ajiyar zuciya ta saki tana jinjinawa lamarin.
Baffa Umaru ya cigaba da cewa.
“Toh tun daga lokacin ne zamanta ya dawo nan daga baya Allah yayiwa mahaifan mu rasuwa da gida huɗu ne kacal anan mahaifinmu su suka fara kafata da duk nan dajine mahaifinmu ne ya sare bayan rasuwar mahaifinmu da kuma mahaifiyarmu,
itace ta zame mana Uwa da uba tun muna yara itace ta renemu nida Mahaifinki mun taso tare atare mukayi wasan ƙasa ta raine mu tare ta zame mana kamar uwa Shiyasa mu awajen mu Adda Nana ba ya bace kaɗai uwa ace a garemu”.

Ita kuwa khausar Ajiyar zuciya ta kuma saki tare da faɗin.
“Ikon Allah Allah mai iko Mabuwayi Gagara misali”.
Murmushi Baffa Umaru yayi yace.
“Kin gane ko mu Addah Nana Uwace agaremu ba Ya ba sannan maganarta Umarni ne awajenmu muda ‘Ya’yanmu babu mai saɓa mata har jikokin mu kinga keda kika zo kina wannan abin sai akaga lallai ta samu karan tsaye”.
Murmushi Khausar tayi tace.
“Lallai dai kam,to amma ina ne asalin su Babanmu?”.
Murmushi yayi yace.
Gobe zan faɗa Miki Idan Allah yakaimu rai da Lafiya zan ƙara sa baki labarin insha Allahu”.

“Toh Allah ya kaimu goben lafiya”. Cewar Khausar

Cikin sauƙe numfashi yace.
“Naji ma Addah Nana na cewa kafin ki koma Abbah zai kaiki Ɓadamaya kije kiga Baffanki da ‘Ya‘yansa”.

“Toh ina kuma ance da nisa?”.
Khausar ta tambaya

“Eh danisa amma ai tafiyar wuni ɗaya ce zaku isa”.
Ya bata amsa.

Miƙe sawunta tayi bisa taburmar tare da cewa.
“Toh shikenan ba matsala, Insha Allahu zamuje, nima ingansa sannan kodan inga mai kama da Babana”.
Murmushi yayi tare da cewa.
“Sannan kuma kafin ku tafi zakuje kiga Addarki ‘yar Baffanki da yake Ɓadamaya tana nan Rugar Fulani dake ma ƙobtanmu Adda Ikki aikin santa?”.
Murmushi tayi tare da gyaɗa masa kai tace.
“Eh na santa ai itakam tana zuwa har gidanmu ta dubani duk dangin Babana ma ita nafi sani”.
Yace.
“Toh shikenan Zakije wajenta kiyi kwana biyu”.
Tace.
“Tun kwanaki nake cewa Hajja Nana zanje in dubata, tace min ba yanzu ba, wai in bari ingama sanin mutanen garin nan”.
Adama dake sauraron hiransu ta miƙe hannunta riƙe da kwanan da ta gama gashin Zabbin dake ta tashin ƙamshi sannan ta haɗo musu da madara mai ɗumi.
Akan tabarmu ta ajiye musu su duka ukun atare sukaci.

Gyatsa mai sanyi Khausar kana tace.
“Kai gaskiya naci naji daɗi Nagode”.

Bayan sun kammala ne Khausar tashiga ɗakin Adama ta kwanta Adama kuwa ta nufi ɗakin mijinta suka kwanta tare.

Can cikin dare kamar misalin ƙarfe biyu Baffa Umaru ya miƙe zaune, tare da kasa kunnensa sosai wanda hakan ya kasance ɗabi'arsa ne,
domin shine Garkuwar Rugar tasu, jin motsin tashin sa yasa Adama miƙewa ita ma ta zauna, kusa dashi tana faɗin.
“Lafiya”.

Ajiyar zuciya ya saki da faɗin.
“Naji tsayuwar mota daga can nesa sannan naga haske yashigo har cikin garin nan kamar da akwai wani abu ko dai munyi baƙi ko kuma wani abu!".

Ahankali tace.
“Toh yanzu fita zakayi kenan?”.

“Dole in fita ai Adama idan ban fita ba ‘yan uwana zan bari wani abu yazo ya ritsa da mune ai bazan bari ba dole in fita inga ko menene”.
Ya faɗa a hankali.
Ita kuwa Adama riƙe hannunsa tayi fuskarta na bayyanar da tashin hankali tace.
“Nikam ina tsoro wallahi”.
Da sauri yace.
“Kada ki damu Insha Allah babu abinda zai faru wanda Ubangijin bai sani ba”.

Kai ta girgiza kana tace.
“Kai rashin network ɗin garin nan yana damun mu wallahi, kaga da akwai network tunda yawanci kowa yana da waya zaka kik kira su awaya kowa ya fito kaga idan yaso sai sufito ku haɗu Atsakiyar garin amma Ni ina tsoron fitarka kai kaɗai”.
Suna cikin Maganar ne sukaji antura ƙofar gidansu anshigo Murfin ya fadi ƙasa Kifff kasancewar ba wani Murfin kirki bane gadon kara ne da gwafa aka haɗa.
Cikin han zari ya mike ya tsaya.

Itama miƙewa tayi da saurin ta riƙe hannunsa tace.
“Fita zakayi dan Allah kada ka fita ka tsaya dan Allah kar ka fita”.
Ya juya ya fuskanceta yace.
“Ya kike so inyi idan ban fita ba kina jifa anshigo gidan nan”.
Yana ida maganar ya fin cike hannunta dake cikin nasa ya fita.
Cikin sauri ta shari gabansa ta fito ya zama na itace agaba shi yana bayanta.

Suna fitowa idanunsu ya sauƙa akan mutanen uku dake sanye cikin baƙaƙen kaya hannunsu riƙe da bindigi da kuma toch ligh mai masifar haske.
Arazane Adama tace.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n Hasbunallahu wani'imal wakin”.
Ƙaran buɗe ƙofa da kuma sautin Muryan Adama ne ya fito da Khausar daga ɗaki wacce farkawanta babu daɗewa tana fitowa sukayi saurin kashe mata ido da hasken toch ligh dinsu ita da Adama.

Cikin daga Murya suka ce da Adama
“Ki matsa agabansa kada jini ya taɓa ki ki matsa kada mu illataki!”.
Aruɗe tace.
“In matsa agabansa!?Bazan matsa ba, ku suwaye ne? sannan me kuke nema? me kuka zo yimana acikin daren nan?”.

Ɗaya daga cikin sune yace.
“Kashe sa muka zo yi!”..
Cikin tsananin tashin hankali tace.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n hasbunallahiwani'imanwakil.
dan Allah kada ku kashesa,me yayi muku zaku kashe sa?,Meyesa?”.

Ɗaya daga cikinsu ba wanda yayi magana da farko ba yace.
“Saboda yana hanamu rawan gaban hantsi zamu kashe sa muga takan tsiya bashi yace taurin kai ba”.
Chapter 28 · 0% Book details