← Book details Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 110 OF 114

Sashe 110

Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Atare Moddibo da sauran jama'ar dake falon suka juya suka kallesa kusan a tare sukace.
“Me ka gani?”.
Girgiza kai yayi da faɗin.
“Kai tashin hankalin fa ya tsananta, muda muke daji ai munfi ku ganin tashin hankali, ku ai kuna cikin gari ba abinda kuke gani sai dai in an ɗauke muku mutum kuke ganin tashin hankali”.
Lokaci ɗaya zuciyar Moddibo ya tsinke da masifar ƙarfi yana bada sautin dib-dib-dib cikin sauri ya sanya tafin hannunsa na dama ya dafe saitin ƙahon zuciyarsa kana ya runtse Idanunsa yayin da gaba ɗaya ilahirin jikinsa ya hau kyarma wani zufa mai ɗumi ya keto Masa daga tsakiyar kansa cikin raunin murya yace.
“Amma meyafaru meka gani bawan Allah!”.
Girgiza kai Buba yayi da faɗin.
“Abinfa ba daɗin gani, domin ya wuce tunanin mutum”.
Ajiyar zuciya Malam Arɗo ya sauƙe tare da faɗin.
“Toh Allah ya rufa mana asiri amma baki ɗaya zamani ya zama abin tsoro, to amma Ori mai kagani acikin dajin da har ya gigita ka haka, bayan ku Fulani daji kun saba ganin abubuwa!”.
Cikin sauri Ori ya girgiza kai da faɗin.
“Kai gane ganen da muka saba ba irin wannan bane! Duk abinda muke gani na yau da kullum lamuran iska ko halittun dajine”.
Alhj Musa dake fuskantarsane yace.
“To amma meka gani haka?
Ya kamata idan kunga abu irin wannan na tsoro Ku riƙa faɗa acikin gari wurin jami'an tsaro”.

Girgiza kai Ori yayi cikin sanyin murya yace.
“Uhm muna tsoro ai”.
Lamiɗo ne ya sauƙe Ajiyar zuciya da faɗin.
“To amma meka gani?”.
Gyara zama yayi tare da sauƙe ajiyar zuciya kana yace.
“Abinda nagani abin tsoro ne, to amma dai banga amfanin ɓoye muku ba, yau tsawon kwana bakwai kenan ina kiwon shanu na akan Dutsen Membilla”.
Duk ido suka zuba masa tare da maida nutsuwarsu kansa suna saurarensa.
Gyara zama Ori yayi kana ya cigaba da cewa.
“Ina nufar kan dutsen sabida ɗebo kanya, naji wani irin wari mai gigitarwa da fitar da hayyacin ɗan Adam Atake tsoro ya kamani na rasa wani irin wari ne wanan.
Saboda ban taɓa jin wari makamancin wannan ba!”.
Cikin sauri Lamiɗo ya kallesa da faɗin.
“To wannan wani irin wari ne!?”.
Ajiyar zuciya ya sauke da faɗin.
“Hmmm Lamiɗo nima kaina na gigice.
Saboda ban taɓa jin makamancin wari irin wannan ba a duniya!”.
Alhj Ibrahim ya fesar da numfashi kana yace.
“To amma me kagani awajen haka?”.
Girgiza kai yayi da alamun damuwa atare dashi yace.
“Ban taɓa ganin abinda ya tayar min da hankali ya kiɗimani ba irin wannan domin ina jin warin na haura na nufi wajen agindin wata Bishiyar kanya”.
Cikin zaƙuwa da gajiyawa za tsinkewar zuciya Modibbo yace.
“Uhmmm!!”.
Shi kuwa Ori runtse Idanunsa cike da damuwa ya cigaba da cewa.
“Ina haurawa kan dutsen. Naga gawa ɗaure a jikin bishiyar, da igiyoyi tako ina.
Wanda da alamu abin ya kwana biyu domin tuni mutumin ya rasu gawace aɗaure, bisa ga duk kan alamu tunda ransa aka dauresa har ya rasu domin har ya kumbura yayi dam sai wani irin sheƙi fuskarsa duk sauran jinka keyi, fuskara ɗauke da murmushi duk da ya rasu, sai kuma alamun kwaranyar hawaye a kan kumatunsa gemunsa da sajensa sai sheƙi sukeyi tamkar wanda kullum ana shafa masa maine kai in ka ganshi kace balarabene wannan warin ne kaɗai ke nuni da gawane, domin a lokacin bai fasheba jikinsa fes”.
Cikin sauri da wani irin azabebben tsinkewar zuciya Moddibo ya runtse Idanunsa tare da taune lips ɗinsa na ƙasa kana yace.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n Hasbunallahu wani'imal wakil”.
Malam Arɗo kuwa cike da tsoro ya kalli Ori kana yace.
“To amma kai Meyesa baka zo ka faɗa acikin gari ba!?”.
Ajiyar zuciya ya sauƙe kana yace.
“Tsoro nakeji domin Atake awajen na fara sheƙa amai da gudawa saboda warin dana shaka karshe ma agigice na koma gida, domin bana cikin nutsuwa ta kuma tunda na koma saida nayi kwana uku bani da lafiya ko kiwo sai ƙanina ne ya karba, kuma dole muka canza wajen kiwo saboda warin da wannan yankin keyi”.

Cikin sauri da ɓacin rai Lamiɗo yace.
“Haba Ori ya za ayi kuyi haka kuda kuke tare dani ai idan kunga makamancin abu irin wannan, sai ku kirani ku faɗa min idan yaso in tura ƴan sanda su duba ko menene ya za ayi kuyi shiru!?”.

Cikin tsoro da cikekken gaskiya Ori ya sauƙe ajiyan zuciya tare da Girgiza kai kana yace.
“Hmmm ire-iren waɗannan abubuwan gaba ɗaya mu Fulani ma zauna daji ake ɗaurawa alhakin sa, wanda bamusan komai ba banda Bautar Allah da kiwon dabbobin mu, amma baki ɗaya an ɗauki baƙin jini da tsana an ɗaura mana”.
Kallonsa kawai suke zuciyarsu na tsinkewa.
Shi kuwa a hankali ya cigaba da cewa.
“Mutanen gari na cewa Fulani sune ƴan Kidnapping, to idan mun faɗi ire-iren waɗannan abubuwan sai azo ace mu muka aikata ayi ta kamamu, shiyasa mukeyin shiru, kuma nima Aruɗe na koma gida baki ɗaya bana cikin nutsuwa ta shiyasa”.
Cike da damuwa Malam Arɗo yace.
“Allah mai iko kai wannan zamani Allah ya rufa mana asiri”.
Kallonsa ya mayar kan Moddibo da har zuwa lokacin jikinsa ke tsuma kana tun lokacin daya runtse Idanunsa har yanzu bai buɗe ba cikin sanyin murya Malam Arɗo yace.
“Amma Moddibo ka shirya muje wajen mu duba gawan waye!”.
Cikin sauri Moddibo ya buɗe Idanunsa dake rintse ya kallesa kana yace.
“Nikam bazan jeba Malam Arɗo me kake nufi kana nufin J ɗina ne?”.
Girgiza kai Malam Arɗo yayi tare da cewa.
“Ba haka nake nufi ba bakaji bahaushe yace idan raƙumin ka ya ɓataba ko cikin ramin allura ka duba ba to muje mu duba mana”.
Jinjina kai Lamiɗo yayi da faɗin.
“Tabbas kam ya kamata aje aduba yanzu kuje ku faɗawa Mahaifinsa Ni kuma zan kira hukumar ƴan sanda sai muje dasu”.

Girgiza kai Moddibo yayi tare da fesar da numfashi mai zafi kana cikin rawan murya yace.
“Nifa bazan jeba dan nasan in Sha Allah ba J ɗina bane, bakuji yace muku gawa bane kuma tuntuni ya mutu har ya kumbura ni kuma J ɗina bai mutuba inaji Ajikina in Sha Allah yana raye”.

Dafa kafaɗar sa Malam Arɗo yayi tare da cewa.
“Moddibo kada kiɗima yasa ka furta kalmar alamar sanin gaibu”.
Cikin sauri Moddibo ya Girgiza kai kana muryarsa na rawa yace.
“Astagafirullah³ amma dai inaji Ajikina kamar J ɗina yana raye”.
Cikin sanyin murya Malam Arɗo yace.
“Eh duk da haka dai muje”.
Girgiza kai yayi tare da cewa.
“Nifa bazan jeba”.
Cikin lallashi Lamiɗo yace.
“A'a Moddibo ka daure dai kuje Allah yasa ba shiɗin bane amma dai aje aduba ɗin”.
Kai Buba ya gyaɗa kana yace.
“Eh suje su duba kuma alokacin ma na samu an ajiye wayoyi agabansa da kuma goran ruwa fuskarsa ma bata wani kumbura ba dan kyanshi bai ɓaceba”.
Atsorace Moddibo ya kallesa zuciyarsa na bugawa da masifar ƙarfi yace.
“Harda waya kuma shikenan bari Muje mu gani ɗin?”.
Ya faɗa tare da miƙewa suka fita kai tsaye gidan Abba suka nufa kana malam Arɗo ya masa bayani.
Kallon Abba Moddibo yayi cikin raunin murya yace.
“Abba ni dai inaji Ajikina in Sha Allah ba J ɗinmu bane, amma dai tunda sunce muje to muje ɗin”.
Cikin rarrashi Malam Arɗo yace.
“Alhj kayi haƙuri muje mu gani”.
Cikin sanyi da rauni kana da tsinkewar zuciya Abba ya gyaɗa kai dai-dai lokacin da folisawan suka iso tare da Lamiɗo.

Fita sukayi cikin shirin tafiya Abba, Lamiɗo malam Arɗo da Moddibo suka shiga mota ɗaya Ori kuma ya shiga motar Ƴan sanda suka tafi.
Chapter 110 · 0% Book details