← Book details Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 114

Sashe 78

Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Wayewar garin Laraba baki ɗaya Jama'ar
Garin Gembu sun tashi da lumshi tun ranan da akayi ruwa tamkar da bakin ƙwarya da kuma rugugi ba asake yin ruwa ba kusan Makonni biyu kenan garin ya zamana har sun fara ɓuƙatar ruwa duk da irin sanyin da ake musu amma garin ya fara ɗumi ga hadari daya haɗu baƙi asama sai dai babu ruwa sai Sanyayyar Iska mai sanyi da ratsa jiki da ake surarawa.
Acan ɓangaren Khausar kuwa cikin shiri ta fito daga Bedroom ɗin ta cikin riga da wando na Pakistan daga saman rigar atsuke take yayin da daga ƙasanta kuwa abuɗe take wando kuwa Pencil ne sosai kayan suka amsheta sai ya fito tamkar Kajol yayin data ɗaura Maroon ɗin hijab har ƙasa jikinta na fitar Sanyayyar ƙamsin turaren Oud Ma'arup bakinta ɗauke da Sallama tashiga Bedroom ɗin Mommy.
Anutse Mommy ta ajiye Carbin dake hannunta kana tace.
“Har kin shirya?”.
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
“Eh Mommy”.
Ajiye Carbin Mommy tayi tare da kallonta kana tace.
“Khausar ki kula koda Ummin Asma'u bana so ku faɗa wa abinda ya faru”.
Kai Khausar ta gyaɗa kana tace.
“Toh Mommy ni dai nasan da ƙyar idan Asma'u ta faɗa wa Ummin ta amma idan ma ta faɗa mata shikenan dan nasan Ummi koda ta faɗa mata babu matsala”.
Jinjina kai Mommy tayi tare da ciro 1k A pose ɗin ta tace.
“Ga Kudin transport”.
Amsa Khausar tayi tare da faɗin.
“Nagode”.
Kana ta fice.

Tana fita ta tari A dai-dai-ta Sahu ta shiga tafiyar minti ashirin da biyar ne ya kaisu gidansu Asma'u.
Anutse ta sauƙa tare da bashi kudin kana ta tura ƙaramin gate ɗin gidan tashiga tare da nufar falon bakinta ɗauke da sallama tashiga Ummi dake zaune a falo ta faɗaɗa Murmushin fuskarta tare da cewa.
“Khausar sannu da zuwa”.
Cike da ladabi Khausar ta tsugunna tare da cewa.
“Ina Yini Ummi?”.
Murmushi Ummi tayi tare da faɗin.
“Lafiya lau Khausar yasu Hajiya Aysha dasu Haiydar?”.
Khausar ta amsa da.
“Lafiya ƙalau suna gaisheki”.
Jin muryan Khausar yasa Asma'u dake Bedroom din Ummi tana gyara fitowa da murmushi afuskarta tace.
“Fattanah”.
Miƙewa Khausar tayi tare da wurga mata Harara kana tace.
“Ai wannan sunan na barwa wanda ya liƙa min shi amakaranta sai dai kuma ya sawa wata amma ba dai niba abi wani sarkin”.
Dariya Asma'u tayi kana tace.
“Ai Suna linzami tunda wasu ma idan za'a kwana ana ce musu Khausar basu sani ba sai ance Fattanah kinga, kuwa Yaya Moddibo ya sanya miki suna ya biki ko ba ragon suna”.
Taɓe baki Khausar tayi kana suka shiga ɗakin Ummi atare suka gyara ko ina tare da jona bona suka sa turare.

Bayan sun gama gyara ko ina suka koma ɗakin Asma'u.
Ajiyar zuciya Khausar ta sauƙe cikin ƙasa da murya tace.
“Asmau'u kin faɗa wa Ummi Maganar?”.
Girgiza kai Asma'u tayi tare da cewa.
“Wallahi ban faɗa mata ba Khausar ai Mommy ta gargaɗe mu”.
Jinjina kai Khausar tayi tare da kallon Asma'u kana tace.
“Asmeey kin kuwa san har yau Naseer bai sake zuwa wajena ba sannan bai sake yi min magana ba.
Kuma wayar daya bani akwai sim card da komai da komai amma har yanzu bai sake kira na ba”.

Girgiza kai Asma'u tayi tare da faɗin.
“In dai bai miki maganar ba kada kiyi masa. waya kuma kima ajiyeta kawai dan kuɗin san nan bama asan na menene ba, kana bamusan me yake nufi dake ba”.
Tagumi Khausar tayi har yanzu abin na mugun bata mamaki koda wasa bata taɓa tsammanin Naseer zai mata haka ba.
Asma'uce ta riƙe Hannunta kana tace.
“Waya sani ma ko Lalata yayi niyyar yi dake yanda ragon nan ya ɓace wataƙil ke ki ɓace tema ma aɗakinsa za'a sameki yayi rapping ɗinki”.
Lumshe idanu Khausar tayi kana ta buɗe su akan Asma'u tare da sauƙe Ajiyar zuciya kana tace.
“Haka ma Mommy na tace kuma kinga ta karɓe wayar ma sannan ta tura asiya min waya acikin Taraba wayar da yafi wacce ya kawo min ma za'a siya Min”.

Muskutawa Asma'u tayi kana tace.
“Yama fi miki nima Ya Jameel yace zai siya min waya”.
Wara Ido Khausar tayi cike da farin ciki tace.
“Kice mun kusa muyi waya mu daina Aron na su Ummi”.
Jinjina kai Asma'u tayi kana tace.
“Ai dai Lallai kam munji daɗin mu”.

Acan ɓangaren Moddibo kuwa a hankali ya fito da motarsa daga gidan Malam Arɗo ya dai-dai-ta hanci motarsa akan titi cikin nutsuwa yake driven yayin da ƙira'ar ke tashi acikin suratul Muminin cikin, Sanyayyar sautin muryarsa yake bin ƙira'ar dai-dai ƙofar gidan su M Jameel yayi parking tare da ciro wayarsa yayi dearling number M Jameel Amma har ya katse ba ayi Picking ba sake kira yayi still ba amsa ajiye wayar yayi tare da buɗe Murfin motar kana ya fita mai gadi naganin sa yayi saurin miƙewa hannu Moddibo ya bashi suka gaisa ahankali Moddibo yace.
“J yana ciki ne”.
Cike da girmamawa mai gadin ya girgiza kai tare da cewa.
“A'a” godiya Moddibo ya masa kana ya shiga motarsa kai tsaye gidan Ummi ya nufa da tunanin ƙila Jameel na can bayan yayi Parking ya fito Anutse ya shiga Falon bakinsa ɗauke da Sallama.
“Ummi dake zaune tana Azkharul masa ta ɗago kai tare da faɗada fara'ar dake fuskarta kana tace.
“Babana sannu da zuwa”.
Cikin yanayin nutsuwarsa da kuma sanyinsa yace.
“Ummi ina yini”.
Ta amsa da.
Lafiya tare da tambayar Innayi
Kansa a ƙasa yace.
“Duk suna lafiya Ummi J fa?”.

Zama Ummi ta gyara tare da cewa.
“Tun shekaran jiya da kuka zo ai be sake zuwa ba amman dai nasan in sha Allah yau zaizo”.
Ajiyar zuciya Moddibo ya sauke kana yace.
“Ayyah ni kuma tun safe da muka rabu bamu haɗu bane shiyasa nazo nan, naje can gidan Abba ma baya nan nayi tsammanin ma yazo nan wataƙil ko suna tare da Innayi”.
Shiru Ummi tayi alamar tunani kana tace.
“Eh to wataƙil ma yana can”.
Jingina kai Moddibo yayi kana yace.
“Ni na kira ma baya ɗagawa”.
Hannu Ummi ta miƙa tare da ɗaukar wayarta kana tace.
“Bari na gwada”.
ta faɗa tare da dearling.
Cikin sa'a yana shiga M Jameel Yayi picking tare da Sallama.
Ajiyar zuciya Ummi ta sauƙe kana tace.
“Ina kake ne?”.
Anutse M Jameel yace.
“Ummi ina wajen Innayi ce muna hira”.
Kallon Moddibo tayi tare da faɗin.
“Aikuwa ga Moddibo yazo neman ka”.
Dariya M Jameel Yayi kana yace.
“Rabu dashi Ummi be nemeni agida ba ya tafi maƙota yana nema na”.

Kallon Moddibo dake sakin ajiyar zuciya Ummi tayi kana tayi murmushi tare da cewa.
“Ai dai kam”.
Moddibo kuwa kallon Ummi yayi bayan ta katse wayar yace.
“Toh Ummi bari na tafi tun da yana gida kam”.
Jinjina kai Ummi tayi kana tace.
“Toh ba matsala Moddibo Nagode bari na kawo maka abin taɓawa”,
Ta faɗa tare da miƙewa kichen tashiga tare da ɗauko masa Alkaki da dambun naman kaza ta ajiye masa acikin wasu roba masu kyau.
Amsa yayi da faɗin.
“Nagode Ummi”.
Sannan ya juya har ya isa ƙofan Falon Ummi tayi saurin cewa.
“Yawwa Babana tsaya dan Allah ka ajiye min yarinyar nan agida”.
Ta faɗa tare da juyawa ta nufi ɗakin Asma'u tare da cewa.
“Khausar ina yanzu zaki tafi ga Maghariba ta kawo kai?”
Daga ciki Khausar ta ɗan daga sautin muryanta tare da cewa.
“Eh Ummi yanzu zan tafi”.
Kai Ummi ta gyaɗa tare da juyawa kana tace.
“Toh ki fito Yayanki ya sauƙe ki tunda dai dole sai yabi ta titin unguwar ku”.
Murmushi Khausar tayi tana ƙoƙarin sanya hijabinta tace.
“Yaya Jameel ko?”.
Cikin sauri ta fito falon Cak ta tsaya ganin Moddibo nanda nan ta nemi fara'ar dake fuskanta ta ta rasa.

Hannunta Ummi ta riƙe kana tace.
“Yawwa Babana ka sauƙe min ita agida kasan ƴaƴa mata bama so suna kaiwa dare awaje”.
Shiru Moddibo yayi tun lokacin da Ummi ta ambaci sunan Khausar ya nemi nutsuwarsa ya rasa sam baya.
Son wata alaƙar da zai haɗa sa da yarinya.
Jin yayi shiru Ummi ta kallesa tare da cewa.
“Ya dai Babana ko dai da matsala ne?”.
Girgiza kai yayi kana cikin sanyin murya yace.
“A'a”.
Still tana riƙe da hannun Khausar tace.
“Toh dan Allah kayi haƙuri ka sauƙeta aƙofar gidansu Lamiɗo”.
Jinjina kai yayi tare da faɗin.
“Toh shikenan Ummi”.
Sannan ya fice.
Har jikin mota Ummi da Asma'u daketa murmushin mugunta suka raka Khausar.
Anutse Moddibo ya buɗe mazaunin Driver ya shiga Khausar kuwa cikin tsinkewar zuciya ta buɗe gaban motar ƙiran Rang Rover tashiga cikin sauri ta lumshe Idanunta jin wani ƙamshi mai daɗi daya ratsa hancinta ne yasata lumshe ido, ahankali ta tukure jikinta waje ɗaya.
Moddibo kuwa motar yaja.
Hannu Ummi ta ɗaga musu tare da cewa.
“Toh Allah ya kare Babana Nagode Allah Yamaka albarka”.
Asma'u kuwa murmushi kawai ta saki ganin yanda Khausar tayi tsuru-tsuru tamkar za'ace ƙyat ta arta da gudu.
Chapter 78 · 0% Book details