← Book details Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 114

Sashe 18

Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin rawan jiki da tsoro daya bayyana amuryanta tace.
“Khausar kidena kar ki sake bata amsa ki bata haƙuri”.
Tana ida maganar ta tsugunna gaban Hajja Nana tace.
“Goggo Hajja Waɗɗu munyal”.

Hajja Nana kuwa kwaffa tayi kana tace.
“Aaaa Dija matsa kusa da ita inzo na same ta ai ke ba ruwanki”.
Ita kuwa khausar batare da tsoro ba tace.
“Toh kizo mana kawai dan mutum ya faɗi gaskiya don dai ba'a son gaskiya da zaman lafiya ai yakata dai akirani muyi sallama da Momyna tunda dai ansa an kawoni wataƙila ma sai nayi sati biyu ko uku bangan taba aida se akirani muyi sallama ince agaida mutanen gida sannan nayi musu fatan isa gida lafiya”.

Ita kuwa Hajja Nana afusace tace.
“To idan kece zaki kaisu gida lafiya kada Allah yasa ki kaisu shegiyar yarinya mara ji Ɓee Usmanu La'ilaha illallahu ohoho gabtarel”.

Tuni Baffa Jauro da Baffa Sadu suka shigo idanun su akan yayar tasu suka ce.
“Lafiya Addah Hajja?”.
Kai ta girgiza tare da nuna Khausar dake cika tana ba tsarewa tace.
“Ɓeee Usmanu,Nikam ban taɓa ganin fitsararriyar yarinya kamar 'yar Usmanu ba”.
Itade Khausar na jingine jikin bango tana tura ƙaramin bakinta dake ƙarawa fuskarta kyau.

Kallon ta Hajja Nana tayi cikin harara tace.
“Nikam Usamanu na Kam ba haka yake ba, haka zalika Mahaifiyarki ko surukata ce bazan mata ƙazafi ba macece mao mutunci amma ke kam waya fitsare miki Ido? Kodan zama tsakiyan Mayun gidan kune yasa kika zama haka!?”.

Khausar dake jingine da bango ta ɗago kanta kana ta wara manyan Idanunta masu kyau da tsari tace.
“Nikam de kar kice min Mayya idan su Mayu ne toni ba Mayya bace idan kince ni Mayyace sede idan awajenki na gada!”.

Baffa Jauro da Baffa Sadu suka dubi juna alokaci ɗaya cikin ƙasa da murya yanda Hajja Nana ba zata jiba Baffa Jauro yace.
“Lalle akwai rigima anan? Addah Hajja ba abata amsa idan tayi magana amma ga 'yar Usmanu daga zuwa tana bata amsa gatse-gatse jika kenan mafi akasari duk zafin mutum jikoki bazasuji tsoronka sosai ba”.
Murmushi Sadu yayi yana jinjina kai.

Baffa Jauro kuwa kan Khausar ya ɗan buga yace.
“Kay Hausajo kidena mu ba'a rashin kunya agarin nan!”.
Ita kuwa khausar inda ya ɗan bugeta tasa hannu ta riƙe tana sosawa duk da cewa bawai zafi ya mata ba ta tura ƙaramin bakinta tace.
“To ai muma ba rashin kunya bane wannan kam”.
Dan ƙolo ya mata yace.
“Dije jata ku tafi”.
Kai Dije ta gyaɗa wacce se alokacin ta samu kuzarin miƙewa tace.
“Khausar kizo mu tafi“, Sannan taja hannunta suka fita.
Suna fita Khausar kuwa hannunta dake cikin na Dije ta janye tace.
“Yanzu ina zamuje?”.

Murmushi Dije ta sakar mata tace.
Rafi zamuje”.
Murmushi mai sanyi Khausar ta sakar mata wanda ke ƙarawa fuskarta kyau tace.
“Toh mu tafi”.
Dan sosai weather garin yake abin burgewa da sha'awa.

Cikin nutsuwa suka nufi Rafin suna hira.
Da sauri Dije ta riƙon hannun Khausar tare da nunawa mata gefen damansu, masu wasa da birine ke tafiya kana yaran rugagen dake gefe dasu na biye dashi, bisa alamun yanzu kuma rugarsu zasu shiga.
wani ƙaton Biri yake ta kolongoiso yara nata ja da baya.
Cike da nishaɗi Khausar tace.
“Muje muma mu gani”.
Kai Dije ta gyaɗa mata , kana suka nufi wajen me wasa da Biri suna ganin yanda Birin ke duk abinda aka sashi.

Cike da farin ciki Khausar ta kalli mai wasa da Birin tana ƙara kusawa cikin yara matan tace.
“Mai Biri yanzu duk abinda na sashi zai min?”.
Kai mai wasa da Birin ya jinjina yace.
“Idan kuma baki yarda ba ki gwada ki gani”.
Kusa da Birin Khausar ta matsa tana murmushi tace.
“Yauwa yaya salon mugun Malami yake idan zai daki ɗalibansa?”.
Da sauri ta ware idanunta ganin.
Birin ya wani ja baya tare da harɗe hannunsa aƙirji kana ya ɓata fuska tare da harɗe sawunsa sai kuma ya ɗauki wani sanda ya riƙe yana nuna Khausar da Dije.

Hannu Khausar tasa ta dafa kafaɗar Dije tare da tintsirewa da dariya mai cike da sautin shauƙi yayin da ɗaya hannun kuma ta ɗaura saman shafefen cikinta tana mai cigaba da dariyar.
Domin kuwa babu wanda ya faɗo mata arai lokacin da Birin ke gwadawa face Moddibo duk da kasancewarsa ba mutum ne mai Fara'a ba amma duk sanda zaisa a zaneta a makarantar Islamiyya seya sake tamke fuskarsa..
Dariya sosai takeyi wanda da yawa cikin yaran tayata sukeyi.

Ganin bata da niyyar daina dariyar ne yasa Dije jan hannunta cikin dariya tace.
“Khausar Mu tafi,Dariyar me kuma kike haka!?”.

Tsagaita Dariyar Khausar tayi sai kuma lokaci ɗaya jikinta yayi sanyi tuna wa da tayi Moddibo zai iya jira duk lokacin da tawo ya yanke mata hukunci ahankali tace.
“Kawai na tuna da wani Malamin mune”.
Murmushi Dije tayi tace.
“Allah sarki shike zaneki kena”.
Kai ta jujjuya tare da cewa.
“Wancan da shegen madarar ƙasaita sawa yake a zaneni dai yana nan jiki kamar auduga ai shi dukan ma aikine a wurinsa”.
Murmushi Dija tayi tare da cewa.
“Da Goggo Hajja zataji haka sai ta sa mishi al'barka”.
Baki ta tura ba tare da tace komai ba sukaci gaba da tafiya.

Suna shiga Rafin idanun Khausar ya sauƙa akan Bishiyoyin Piya, Caɓɓulle, Mangoro, Ayaba, Gwanda, Gwaba, Lemo, da sauran kayan itatuwa duk sun yiwa wajen ƙawanya.
Sake wara Ido Khausar tayi ganin bishiyoyin Inabi guda uku a jere,
Cikin farin ciki ta dubi Dije tace.
“Harda Inabi Laha'Ila Ha'illalhu Masha Allah zan kuwa ci”.
Ta ida maganar tare da nufar jikin Bishiyar zata hau.

Saurin riƙe hannunta Dije tayi tace.
“Kada ki hau Khausar Baffa Liman ya hanamu yace ba shida amfani 'ya'ya mata su riƙa hawa bishiya ba tarbiyya bace mai kyau”.
Ita kuwa khausar janye hannunta dake cikin na Dije tayi tace.
“Ke rabu dashi da ƙa'idojinsa hawa za muyi mu cire abinmu, ai kuma ba har can sama zamu hauba”.
Langwaɓar da kai Dije tayi kafin tayi magana suka hango wani farin saurayi kyakkyawa daga ɗaya gefen.
Hannu Dije ta ɗaga masa da faɗim.
“Yawwa Sadik dan Allah zoka cire mana Inabi wai zata ci”.

Ƙara sowa Sadik yayi idanunsa akan Khausar yace.
“Dije wannan yarinyar wa kika samo?”.
Murmushi Dije tayi tace.
“Yarinyar Marigayi Baffa Usmanu cefa yaron Goggo Hajja”.

Murmushin fuskarsa ya faɗaɗa yace.
“Allah sarki itace wacce take Birni ko?”.
Kai Dije ta gyaɗa tace.
“Eh itace”.
Ita dai Khausar ba tace komai ba.
Raɓar bishiyar yayi ya ciro musu Inabi kana ya koma bishiyar Ayaba shima ya ciro yasa musu aƙaramin kwandon dake hannunsa irin na saƙar kaba na gargajiya miƙawa Dije yayi.
Sai asannan Khausar tace.
“Mungode”.
Murmushi kawai yayi ba tare da yace komai ba,
suka fara tafiya cikin rafin akai-akai Khausar ke lumshe idanunta tana wasa da yatsun hannunta sosai weather garin ya mata daɗi.
Juyowa tayi ta kalli Dije tare da cewa.
“Garinku yayi min daɗi”.
Cikin sauri Sadik yace.
“Garinmu de kin cire kanki ne a ciki? Ko kin manta nanne tushenki kuma asalinki nanfa cibiyarki take abinne”.
Dariya tayi kafin tace.
“Hmmm Shiyasa ma naji daɗin garin inba haka bama masifar wannan tsohuwar yasa bana sha'awar zuwa garin nan”.
Zare ido Sadik yayi yace.
“Wacece masifaffiyar!?”.

Asanyaye Dije za tace.
“Wai Goggo Hajja take cewa masifaffiya”.
Sake zare ido Sadik yayi se kuma yace.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n”,Ya dubi Dije yace.
“Meye sunanta ma kika ce?”.
“Khausar”
Dija tace.
Ya maida kallonsa kan Khausar da hankalinta yabi shuke-shuken da kallo yace.
“Khausar kiyi Istigfari”.

Khausar kuwa kallon mamaki tayi masa kafin tace.
“Saɓon Allah nayi da zanyi Istigfari?”.

Habarsa ya riƙe still Fuskarsa ɗauke da Mamaki yace.
“Goggo Hajjan kike cewa Masifaffiya”.
Baki ta taɓe tace.
“Yo ba masifaffiyar bace daga zuwa na fa kawai takama yimin bala'i”.

Kai ya jinjina kafin yace.
“Toh kar ki sake wallahi in Goggo Hajja taji abinfa baze miki daɗi ba”.
Cikin sanyin murya Dije tace.
“Allah de ya kyauta anma wannan baƙunta ai akwai kallo aciki”.
Ba wanda ya sake magana har suka fito daga cikin Rafin.
Gani tayi Sadik ya ɗauki wani babban kwando da sunyi ta fiya kaɗan sai ratsa cikin ciyawa ya buɗe ya ɗibi ƙwan Zabbi ya saka acikin kwando.

“Me kakeyi haka?”.
Khausar ta tambayesa tana kallon wajen da ciyayi masu kyau da tsari suka lulluɓe wajen.
Murmushi yayi yace.
“Ƙwan Zabbi nake tattarawa”.
Cikin lumshe ido tace.
“Ohhhh lalle kam Masha Allah abamu naci”.
Murmushi yayi tare da faɗin.
“Toh babu damuwa”.
Haka suka riƙa tafiya suna hira jefi-jefi sun kusa fita daga cikin Rafin ne Khausar ta jiyo hayaniya na tashi kamar kasuwa anata surutu da dariya jujjuya wa tashiga yi amma bata ga inda sautin surutun ke tashi ba.Ta dubi Sadik da Dije tace.
“mene nake tajin hayaniya da surutun nan kam a cikin daji?”.
Sadik ne yace.
“Mutanen Bishiyar ƙare zancen kane”.
Da sauri ta sake duban sa tare da cewa.
“Bishiyar ƙare zancen ka?,Wai mene ma'anar Bishiyar ƙare zan cenka?”.

Dije ce tace.
“Ai mu garin nan bamu da service, Service ɗinmu waje ɗaya ne inde mutum yana so yaje yayi waya seya je ya hau bishiyar ƙare zencen ka anan ne ake samun network idan kina wajen zaki iya kira sannan za'a iya kiranki kina sauƙa daga bishiyar ko kuma kina Matsawa daga wajen bishiyar toh shikenan Service ya yanke ba zaki samu kiyi magana ba kuma shima sai in layin MTN ne ko Zain”.

Cike da Mamaki Khausar tace.
“Ikon Allah wannan wani irin ruga ne?. Dama ashe har yanzu akwai irin wuraren nan daya rage aduniya?”.
Murmushi Dije tayi tace.
“Sosai ma”.
Ahankali Khausar ta ɗaga kanta nan ta hango manyan tsaunika da bishiyoyi Kallonta ta mayar kan Dije tace.
“Haba ko wannan manyan tsaunuka da bishiyoyin ai sa tare muku service da network”.
Chapter 18 · 0% Book details