← Book details Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 114

Sashe 14

Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ita dai Asma'u hannunta tasa ta rufe bakinta tana murmushi.
Yayinda tun shigowarsu Moddibo ya zuba musu idanu saidai sam su basu lura dashi ba,da gudu Khausar ta juya ta fara taka steps din tana sauƙa ta nufi sashen da Moddibo ke zaune tana faɗin.
“Wowww gaskiya wannan gidan yayi mugun yimin kyau da ace zan rayu a ciki da wanda raina zaiso zan meda mishi gidan tamkar dausayin farin cikin duniya”.
Cikin danne dariya Asmau tace.
“Khausar zomu tafi mana”.
kai Khausar ta girgiza tace.
“A'a ki tafi ni wlh saina cire inabin can da Appel kije kawai”.
Ahankali Asma'u tace.
“Kizo muje mugaida Innayi sai mu gaya mata kafin ki cire”.
dan tasan a irin wannan lokacin tabbas Moddibo na nan shiyasa take mgn a hankali wai dan kar ya jisu.
Kai Asma'u ta dafe tare da cewa.
“Idan masu gidan kuma suka zo suka sameki fa?”.
Taɓe baki Khausar tayi tace.
“Gida kamar wannan masushi bazasuyi rowa ba, kuma ai nan kamar babu kowa babu wanda zaizo”.
ta faɗa tana komawa inda inabi yake tasa hannu ta fara tsinka tana tsalle jin hijabinta zai takurata ne yasa ta zare hijabin tare da ajiyeshi kan kujerar dake ƙasan bishiyar.
Middibo kuwa dafe kunci yayi yana ganin ikon Allah Aransa yace.
“Yarinya kamar ba mace ba dubi yanda take tsalle kamar biri wannan ba budurciba abinda yafi budurcima zata watsar domin yasan illar hawa bishiya yakan buɗa mace duk da cewa ita ba hawan tayi ba.
Tunaninsa ne yakatse asanda ta nufi bishiyar Appel tsalle tayi da niyyar tsinkowa dan bishiyar Appel irin yan masaƙaitan nanne,
tsalle ta kuma yi amman ta kasa ga dai hannunta na taɓawa sede baza ta iya tsinka ba.
tattare gashinta tayi tare da dan mai dashi bayan wuyanta kana ta nannaɗe ƙafar wandonta,
tsalle tayi tare da kamo rashen da yafi kusa,
sai kuma ta hango wasu a can sama haka yasa ta fara taka jikin bishiyar har ta hau bisa rashen duk da ba wani tsowone da shiba,
Cal sai gata akan bishiyar.

Cikin tsananin takaici da sassarfa ya mike tare da nufar wajen, yasan koda yace zeyi mata tsawa muryarsa baze fita ba saboda bashida da amo mai karfi sannan yasan dai baya cikin tarbiyya mai.kyau ƴa mace tai ta hawe-haween bishi yana isa bakin bishiyar ya tsaya tare da harɗe hannayensa aƙirji kafin yayi magana ta juyo da niyyar kai hannu zata tsinki appel sukayi ido huɗu dashi ido cikin ido sukayi kamar yadda damisa kan iya tsare kenwa da ido haka yayi mata.

Cikin tsananin firgici da tsoro da kaduwa tace.
“Hasbunallahu wani'imal wakin,
Aizubillahi Minal shaiɗanirrajim, innahu min sulaimanu wa innahu Bismillahir rahmanir rahim”.
Cikin tsananin tsoro take jera addu'o'in domin gani take shin fatalwane ko kuma aljan yazo mata asuffarsa cikin kiɗima da firgici ta rikito tayi ƙasa ta faɗo gababsa yayin da hannayenta suka sauƙa akan.....!

Kada dai ku shagala wannan duk garaɓasar FREE PAGE. Labarin sashi-sashi gareshi. Ko wacce kusufa da darasin dake ƙunshe a ciki. Al'amarin babbane fa babu abinda babu cikin lbrin

Inada lbri na musamman
Wanda nake son in rubuta in Allah yaso ya yarda ya bani aron rai da lfy da dama.
In na gama TUBALI.
Zafin labarin kan sani inji Tamkar in aje TUBALI na fara wancan ɗin
*SAKAYYAH*

lbri ne mai cike da abubuwa na musamman masu tarin rikitarwa al'ajami matsalar kasarmu kalubale masautu.
Taraddadin rayuwa, tsaka mai wuya, tsubucewar dama da samunta,
Nesanta da kusanta, tausayi, kuka, dariya, barkwamci, iko, isa, mallaka, kasaita, kekkyawan ilimin addini, da aiki dashi, fasadi, zalumci, shirka da sakamonta, kalubalen dalibai ga Malami, matsalar , yadda ya kamata gomnati da jami'an tsaro da masarautun gargajiya su juyo kam lamarin bindiga Dadi Zazzafar soyayya mai kekkyawan tubalin raino a ɓoye!!!.
Ya Salam Labarin ya rusa min tunanin da nake cewa bazan sake wani littafi Mai kamar GARKUWA ba sai gashi in second's Allah ya buda min tunanin na harhaɗo Labarin *SAKAYYAH. FATTANAH kenan.*

Amman sai dai kuwa kusan wani Abu!??!
In kuna son sani ku biya 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276. In kin biya kikuma bibiyeni zakusha al'ajab.

By
*GARKUWAR MARUBUTA*

[19/07, 7:44 PM] Halimatu A/rahman Sadeeya: 📝🍇✨💫⏰🤴🏻👹❤️❤️❤️🍇

*SAKAYYAH*
_Page 4_

*NA*
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*Free page*

*KADA DAI KU MANTA WANNAN FREE PAGE NE, KI KI BIYA KI KARANTA CIKIB AMINCI BA HAƘƘIN WANI GABA GAREKI SAKAYYAH 1k ne kacal ƴar uwa. 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA. Sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276*

*Al'bishirunku Ma'aurata, GA GARKUWAR KU nan tafe muku da tsarabobi na musamman gareku ma'aurata daga cibiyar mgnin mata mai taken GARKUWAR MA'AURATA*

NI DAI AYSHA Ɗiyar ALIYU GARKUWA.
Ina matukar mamakin wani irin lokaci da ya riske mu mai wahalallan fassara. Kullum dai magana daya ce, akan ma’aurata, fada, rashin jituwa, mutuwar aure, akan kuskure kalilan, rashin kula, rashin yi wa juna uziri. Toh wai duk me ya janyo hakan? Na zurfafa a tsananin tunani hakan ya tilasta min bincike mai tarin yawa wanda ya kai ni ga gano inda matsalar take? Shin yar’uwa ke macece amma kin san wacece mace ku? Kin san me ake kira mace kuwa? Mace ita ce matar da take zama iyali a wajan namiji ta zame masa bango, sanyin idaniyarsa, ta zame masa gata da farin cikin rayuwarsa ta zame masa ruwa abar kore ƙishinsa ta zame masa mayafi mai karesa daga gigitar kadaici, ta kuma dorar da mijinta kan turbar gaskiya, ta kashe masa jiki da salonta ta rikita shi da baiwa da ni’imar da Allah ya bata idan har ta san hanyar mayar da kanta sabuwa dal awajanta, wato kullun takasance masa tamkar amarya har ya kasa tantance daren amarcinsu da sauran dararen rakun rayuwar su.

Wannan ita ce mace. Ina da wata saukakkar hanyar da zaki zama abar so da kulawa da soyayya a wajan mijinki ta hanya mafi sauki, 09097853276 hanyar ita ce ki gwada amfani da kayana na gyara ki gani, ina mai tabbatar miki da in sha Allahu sai kin dara da murna sai kuma kin gode min. Kayana kaya ne da aka yi shi da zallan itacanmu na gado marasa illa a cikin jikin dan adam musamman mace, kaya ne da suke taimakawa (sex hormones 😍) dinki.
Misali kina kallon India😘, hollywood, Asian film🥰 kina ganin yanda mazansu ke nunawa matansu tsananin soyayya kamar su ba su kyautar ransu!?
Saboda me hakan? Saboda suna sadaukar da lokacinsu wajan gyara jikinsu da kayan da ke tsattsafo da ni’ima cike da tsukewa, kayan nan kuma ana yinsu ne zallar magungunan gargajiya wanda ba su da illa domin haɗine na ingantattun itatuwa da yayansu.
Ina baiwar Allahn da miji ke daure mata fuska babu hirar arziki?
Zo ki ji yar’uwa zan baki gumbata da zallar gari wanda aka yi su da nagartattun itacen da ke da matukar amfani a jikin mace. Gubar ciko, gumbar tsalle dole, gubar da ba'a baiwa mai kishiya, garin maɗi, garin mallaka, tsumin goron tula, tsumin tsartai, tsumin maratsi, pala-pala butar sirri, kwanon k’asaitacciyar mace, furar mata madararta gareki Hajia takenta sha yanzu mgni yanzu,
Ina mata masu fama da sanyi? Sanyin mara ji zo na hadaki da magani na na sanyi wanda yake wanke mara ya fitar da duk wata cuta da ke samun mazauni a wajan set ɗin 10k ne kacal wlh koda sanyin mahaifane in sha Allah zakiji saukin.
Ina da ciccibi mai kyau. Ina da hadin amare mai kyau wanda zai gyara yarinya ya kankaro mata kimarta akwai hadin mai jego wanda muke yinsa na asali inada kekkyawan Hadi maida tsohuwa yarinya.

Akwai ɗaya bangaren wato *KAMSHI*
Kimarki gyaranki da kamshinki. Matan da suka gane suka san yanda za su kankaro da mutunci su ne masu amfani da kayan gyara da kuma sanyaya jikinsu da kamshi, ina da turaren wanka da na bandaki na daki na jiki da na kaya dana tsuguno kamshin turarena na dabam ne mai sanyaya zuciyar wanda ya shaka ina da kayan kamshi na amarya da na maijego da na uwargida da dukkan macen da take kokarin mayar da kanta mai daraja a idon kowa ta zamo sarauni a idon mijinta, akwai shu'umar humra, kana da kulaccar sirri sayan na gari maida kuɗi gida, banda harkar karanta yayin gyara Hajia.

Zaku iya samun kayyakina a duk garin da kike, zakiyi min mgn ta whatsApp number na 09097853276 domin yin zaɓinki, ko karin bayani, zaki tura kuɗin ta account na 0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU in mun gama mgna zan sa miki kaya a mota yazo duk garin da kike, in baki shirya saya yanzuba Please kada mu wahal da juna ki bari sai kin shirya kafin kiyi min mgn.

🤝🏻🥰😘 Daga taku AYSHA ALIYU GARKUWA
*(GARKUWAR MA'AURATA)*

Tana dirowa hannunta dake dungule da Appel suka sauƙa kan ƙafarsa.
Yayinda yatsun hannunta dake ɗauke da zoban azurfa na kusa da da ƙaramin yatsa da kuma ƙaramin suka sauƙa akan faratun yatsun sa,
atake yatsun hannunta suka bada sautin ƙash! yayin da shi ma Moddibo yatsun ƙafansa suka bada sautin ƙas-ƙas!, Idanshi ya rumtse da sauri, sabida wani irin masifaffen zogi da yaji ya ratsa sa cikin sauri ya tsugunna da niyyan matsasu tuni ɗanƙwalin ta ya zame yalwataccen sumar kanta baƙi daya sauƙa zuwa kafarɗarta ya zubo yana fitar da wani sihirtaccen ƙamshi...

Khausar kuwa jin zafin daya ratsa ƙafarta data malkoɗe ne yasa ta furta.
“Wayyyo Allah ƙafata!”. ta faɗa da ƙarfi tare da ɗago kanta yayin da yalwataccen sumar kanta ya rufe mata fuska da sauri tasa hannu ta janye ta ɗago kanta.
Idanunta ne suka sauƙa akan Moddibo dake durƙushe, cikin ruɗewa da tsanananin tsoronsa ta ɗauki ɗan kwalinta kana ta miƙe da gudu tana cewa.

“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n dan Allah kayi haƙuri wallahi Allah bansani ba”.
Ta faɗa tana ƙoƙarin fita daga gate ɗin.

Asma'u kuwa fitowarta daga gate ɗin da zai sadaka da cikin farfajiyar Innayi kenan ta hango Khausar na shirin fita babu ɗan kwali akanta.
Cikin Sassarfa tabi bayanta tana faɗin.
“Khausar! Khausar!! Khausar!!!”.
ta kira sunanta har sau uku Kafin ta sake cewa.
“Dan Allah kada ki fita ahaka Khausar ki tsaya”.
Chapter 14 · 0% Book details