← Book details Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 114

Sashe 71

Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin damuwa M Jameel yace.
“Toh meke damunka?,Ka faɗa min abinda ke damunka mana”.
Sai asannan Moddibo ya buɗe Idanunsa cikin raunin murya tamkar mai shirin fashewa da kuka yace.
“I don't know J I really don't know what's wrong with me WLH BAN SANIBA, BANSAN MEKE DAMUNA BA J”.
Da Mamaki M Jameel ya kallesa kana yace.
“How A.J kamar ya bakasan meke da munka ba”.
Langwaɓar da kai Moddibo yayi cikin yanayin damuwa da tashin hankali ya kalli M Jameel daya tsaresa da ido ya sauƙe Idanunsa ƙasa kana yace.
“Bansani ba J bansan meke damuna ba Na dai san bana jina dai-dai ina cikin ɗimuwa”.
Ya ida maganar yana mai lumshe idanunsa sam ya rasa taya zai fara faɗawa M Jameel yanayin da yake ji ajikinsa.

Ajiyar zuciya M Jameel ya sauƙe kana yace.
“To ko dai zazzaɓi ne?”.
Girgiza kai Moddibo yayi still cikin raunin murya yace.
“A'a”.
Ahankali M Jameel ya sake cewa.
“Toh ko Kanka ke ciwo?”.
Still Kai Moddibo ya sake Girgiza masa alamar a'a.
Numfashi M Jameel ya fesar kana yace.
“Toh ko dai cikin kane?”.
Nan ma kai Moddibo ya Girgiza kamar zai fashe da kuka.
Tagumin M Jameel Yayi kana yace.
“Toh meke damunka?”.
Lumshe idanu Moddibo yayi cikin sanyin murya mai rauni ya buɗe idanunsa tare da kallon M Jameel daya tsaresa da Ido kana yace.
“J bana jina dai-dai ina jin kamar akwai wani abu da nake buƙata amma bansan menene ba”.
Murmushi M Jameel yayi kana yace.
“Toh me kake buƙata?”.
Girgiza kai Moddibo yayi tare da buɗe hannunsa kana cikin sanyin murya yace.
“Idont know J nima ban sani ba bansan me nake so ba amma inaji kamar akwai wani abu da ɗan Adam yake buƙata acikin rayuwarsa wanda nima nake buƙatarsa kusa sani, daga jiya zuwa yau amma bansan menene bane”.

Kallonsa M Jameel Yayi tare da kallon yanda idanunsa suka sauya launi zuwa Ja tun safe da suka zo ya lura da hakan tamkar mai mayen bacci kana ya lura da yanda lips ɗin sa ke rawa sannan ya lura da yanda bini-bini yake matse ƙafafunsa.
M Jameel na cikin Kallonsa. Moddibo yayi miƙa tare da matse ƙafafunsa kana lips ɗin sa suka shiga rawa sai kuma ya runtse Idanunsa.
Murmushi M Jameel yayi kana yace.
“J kodai kana jin kana ɓuƙatar mace akusa da kai ne?”.
Lokaci ɗaya Moddibo yaji zuciyarsa ya tsinke da masifar ƙarfi ajiyar zuciya ya saki tare da kallon M Jameel ji yake tamkar ya fashe da kuka ko zaiji sauƙin abinda ke damunsa sunkuyar da kai ƙasa yayi cikin wata raunan'niyar murya mai sanyi yace.
“Ban sani ba J”.
M Jameel yace.
“Toh mutafi gida mana tunda na gama abinda nake kai kuma naga kamar baka da komai”.
Kai Moddibo ya gyaɗa kana ya miƙe tare da yin miƙa da ayau ya zame masa jiki domin baya minti goma mai kyau sai yayi miƙa.
Kallonsa M Jameel yayi dan yanda yaga Modibbonsa ya tashi ta saman rigar duk da kuwa boxes biyu ya saka duk dan ya suturta jikinsa ɗagowa M Jameel yayi tare da kallon fuskarsa yayi Murmushi.
Fita Moddibo yayi M Jameel yabi bayansa dai-dai lokacin da aka kira sallar Azahar acikin masallacin dake makarantar.
bayan sun Idar suka fito suka shiga mota M Jameel ke driving yayin da Moddibo ke gefen mai zaman banza idanunsa alumshe duk abin duniya ya Ishesa.

Suna isa gida M Jameel yayi Parking ya fita kai tsaye sashen Innayi ya wuce ya karɓa musu abinci Moddibo kuwa cikin mutuwar jiki ya wuce sashen sa ya kwanta.
Ba jimawa M Jameel ya dawo hannunsa riƙe da Warmers da kuma Plate kwance ya samu Moddibo akan 3sitter yayi rub da ciki idanunsa akan ƙofar falon.
Ƙarasa shiga falon M Jameel Yayi tare da zama aƙasa kana ya kalli Moddibo da faɗin.
“Saƙƙo muci abinci idan muka gama sai muje kaga Dr”.
Girgiza kai Moddibo yayi cikin sanyayyar Murya yace.
“Bana jin yunwa bana son cin komai”.
Buɗe Warmer M Jameel Yayi tare da cewa.
“Toh Meyesa haka J?”.
Cike da raunin murya tamkar wanda ke shirin fashewa da kuka yace.
“Ban saniba nima”.
Dariya mara sauti M Jameel Yayi kana yace.
“A.J Na fahimceka fa kamar *Mace* kake buƙata acikin rayuwarka!”.
Cikin sauri Moddibo ya lumshe idanunsa jin suna tsats-tsafo wa da hawaye, miƙewa yayi tare da wucewa Bedroom ɗin sa yana shiga yasa key ya rufe.

M Jameel kuwa jingina bayansa da jikin kujera yayi tare da fashewa da dariya harda riƙe ciki.
Moddibo kuwa yana kulle ƙofar ya juya ya kwanta ruf da ciki tare da lumshe idanunsa yayin da ƙwaƙwalwar sa ta shiga tariyo masa moment da suka kasance acikin mota lokaci ɗaya Muhalinsa ya shiga harbawa da ƙarfi tamkar zai fisge ya fito, yayin da lips ɗin sa suka shiga rawa har haƙoransa na haɗuwa kar-kar-kar.
Batare daya shirya ba yaji hawaye suna bin kuncinsa shi kansa baisan meyake so ba bai san meke faruwa dashi ba yakasa sanin yana yin da yake ciki ji yayi kawai yana kuka hawaye na bin kuncinsa yana sheshsheƙa.
Miƙewa yayi cikin rashin sanin madafa shin ya zaiyi da wannan jarabar tun jiya yake fama da zaran ya rufe Idanunsa yanayin da suka kasance da yarinyar ne yake gani.

M Jameel kuwa dambun shin kafa dayaji vegetables da soyayyen naman kaza dake tashin ƙamahi ya zuba a Plate ya fara ci yana cikin ci ne wayarsa dake gefensa ya hau ruri.
Ahankali ya sanya hannunsa ya ɗauka Turkey Kawai ya gani babu Number.
Picking yayi tare da kaiwa kunnensa yana dariya yace.
“Yaushe kaje Turkey?”.
Murmushi Jalaludeen yayi kana yace.
“Na kusa kwana biyar acan ai”.
Kai M Jameel ya gyaɗa kana yace.
“Lallai dai kam yayi kyau ya gida”.
Gyaran murya Jalaludeen yayi tare da cewa.
“Lafiya wai meyasamu Aliyu ne”.
M Jameel na ajiye cokalin hannunsa yace.
“Nima kaina ban sani ba”.
Dariya Jalaludeen yayi kana yace.
“Mace ta fara shiga rayuwarsa kenan.
Aure fa yake da buƙata yana da ƙaƙƙarfan sha'awar da tuntuni na kwantar masa da shi”.
Zare Ido M Jameel Yayi kana yace.
“Auuu Jalaludeen kenan kaine ka maida mu waliyan dole?”.
Cikin sauri Jalaludeen yace.
“A'a Ni ban mayar daku mata ba, amma dai kawai nasan Aliyu nada ƙarfin sha'awa na masifa idan har aka bar shi da wannan sha'awar zai iya zame masa masifa kana zai iya jefashi acikin damuwa gashi naga burinsa a lokacin yayi ilimi mai zurfi, kuma in ka tuna a lokacin yana yawan fama da ciwon ciki”.
Dafe kunci M Jameel Yayi yana saurarensa.
Murmushi Jalaludeen Yayi kana ya cigaba da cewa.
“Tun haɗuwar mu na farko kafin ku fahimci wanene ni kafin ku fahimci komai akaina, kana tun kafin afahimci wanene ni asan komai akaina na bashi abinda yasha wanda ya karyar masa da ƙarfin sha'awarsa har yake ji kamar baya buƙatar mace acikin rayuwarsa”.
M Jameel ya gyara zamansa tare da cewa.
“Ikon Allah”.

Jalaludeen kuwa cikin yanayin su na can yaci gaba da cewa.
“Toh ajiya akwai abinda yafaru ko dai mace tashiga rayuwarsa ko dai akwai macen data kama jikinsa wannan dalili yasa gaba ɗaya takarya alƙadarin abinda ke jikinsa!”.
Ajiyar zuciya M Jameel ya saki kana yace.
“Toh fa”.
Murmushi Jalaludeen yayi tare da faɗin.
“Kai kuma kwaɗayin ka ne ya kaika dana bashi maganin yana cikin sha kawai ka amshi kofin kasha shiyasa kuka kasance atare haka amman ai kai naka ba kamar nashi bane ”.

Murmushi M Jameel Yayi kana yace.
“Amma dai gaskiya Jalaludeen baka da mutunci”.
Dariya Jalaludeen yayi kana yace.
“Nifa bance komai ba gaba ɗaya abinku lafiya lau yake kawai dai sha'awar ce na kwantar”.
Girgiza kai M Jameel Yayi kana yace.
“Toh yanzu shi kuma wannan ya za'ayi dashi dan yanzu wallahi ya tashi ya tafi ɗaki kamar zaiyi kuka”.
Murmushi Jalaludeen yayi kana yace.
“Kukan ma yakeyi yanzu”.
Ware ido M Jameel Yayi kana yace.
“Lallai dai kam maza sun gamu da aiki kenan”.
Jinjina kai Jalaludeen yayi tare da cewa.
“Gaskiya yanayin daya ke ciki ne awahale yake haka ya wuni jiya still haka ya kwana gashi kuma yau ma ya wuni haka”.
Cike da tausayawa M Jameel yace.
“Toh yanzu ya za'ayi ?”.
Girgiza kai Jalaludeen yayi tare da cewa.
“Gaskiya ban sani ba dan bani da yanda zan mishi kawai abune daya zo masa babu yanda za'ayi haka zaita rayuwa mafita ɗaya ne kawai yayi ƙoƙari yayi aure”.

Ajiyar zuciya M Jameel ya sauƙe tare da cewa.
“Ok zamu yi ƙoƙari muga mai ya dace tunda gashi dama duk abinda ya dace mun gama”.
Jinjina kai Jalaludeen yayi kana yace.
“Masha Allah amma yanzu ka samu ruwan ɗumi kasa masa laimun tsami yaji kana ka sanya zuma yaji sai ka bashi yasha zai ɗan ji sauƙi”.
Kai M Jameel ya gyaɗa kana yace.
“Toh shikenan ba matsala mun gode”.
Sallama sukayi tare da katse kira.
Miƙewa M Jameel Yayi yashiga cikin kichen dake falon ya buɗe Flaks dake ɗauke da ruwan tea ya zuba a Cup lemun tsami ya duba yaga babu rufe Cup ɗin yayi ya nufi cikin gadin ɗin gidan ya tsunko guda biyar sannan ya dawo ya wanke tare da matse su duka acikin shayin kana ya buɗe kofin roban zuma yasa.
Fita yayi a kichen ɗin ya nufi Bedroom din Moddibo yayi Knowking ƙofar.

Dai-dai lokacin da Moddibo ya cire kayan jikinsa ka ya zura Jallabiya kasancewar boxers ya takure masa jiki har yana jin mallakinsa na yimasa ciwo saboda yanda ya takuresa ya hanasa miƙewa cikin gajiyawa ya mike ya cire boxes ɗin tare da cewa.
“Bari naga iya inda zaka tsaya uban ƴan zalamammu”.
Yayi maganar yana kallon jikin nasa daya miƙe ya tsaya acikin Jallabiyar.
Muryar M Jameel yaji yana cewa.
“A.J ka buɗe min ƙofar mana in baka magani”.
Daga ciki Moddibo ya buɗe masa ƙofar.
Kallonsa M Jameel Yayi sai kuma ya kalli yanda ya ɗaga rigar kawar da kai gefe yayi yana jin dariya na neman kufce masa.
Kofin dake riƙe ahannunsu ya miƙa masa.
Cikin Sanyayyar muryarsa yace.
“J Me wannan?”.
M Jameel ya Kalli kofin kana yace.
“Kasha mana zaka ji sauƙin abinda ke damunka na fahimci meke damunka A.J”.
Chapter 71 · 0% Book details