← Book details Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 105 OF 114

Sashe 105

Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ƙara sawa Moddibo yayi tare da zama gefensa kana yace.
“Abba ina yini ya kuma haƙurin rayuwa?”.
Ajiyar zuciya Abba ya sauƙe tare da cewa.
“Alhamdulillah Aliyu ya wajen su Innayi?”.
Kansa a ƙasa yace.
“Lafiya lau Abba basu sake kira ba ko?”.
Girgiza kai Abba yayi tare da fesar da numfashi kana ya runtse Idanunsa cikin sanyin murya yace.
“Basu sake kira ba Aliyu”.
Jinjina kai Moddibo yayi tare da cewa.
“Toh yanzu Abba kuɗi kimanin nawa aka samu awajenka?”.
Abba kuwa ahankali ya zame daga kan kushin ɗin ya zauna akan capet tare da fuskantar Moddibo kana yace.
“Aliyu na tattara duk abinda yake wajena kana duk wanda nake binsu bashi na tattarasu sannan na nemi temakon bashi duk wanda zan nemi temakonsu sunban bashi baki ɗaya kuɗin dana samu awajena Million hamsin da shida ne, iya adadin kudin dake hannu na kenan, duk ta inda zan buga na buga Aminaina ƴan uwana duk na nemi temako awajen su wasu sun bani kyauta wasu kuma aro na buga shine Million hamsin da shida”.

Jinjina kai Moddibo yayi tare da cewa.
“Toh Abba kuɗi dai sun ɗanyi gwaɓi gashi awurin Ummi an samu Million Sha uku yanzu kenan muna da Million Saba'in dai-dai a ƙasa.
Ajiyar zuciya Abba ya sauƙe tare da fesar da numfashi kana yace.
“Alhamdulilah kuɗi sun fara taruwa Amma ɗari biyu fa suka ce gashi ko ɗari cikekke bamu samu ba”.
Cikin raunin murya Moddibo yace.
“Abba bari mugani idan sun sake kira sai mu rokesu su rage mana idan sun tallafa sun tausaya mana ko bashin banki ne zamu ci sai mu ƙara akai kuɗin ya cikata”.
Kallon sa Abba yayi tare da jinjina kai kana yace.
“Toh shikenan ba laifi Allah yasa mu dace”.
Ameen Moddibo ya amsa kana suka cigaba da hira har Misalin ƙarfe goma.
Abba najin ringing din wayarsa Yayi saurin zabura tare da picking kana yayi Sallama.
Daga ɗaya ɓangaren cikin bauɗaɗɗiyar murya mutumin yace.
“Alhj Bashiru ka haɗa kuɗin?”.
Cikin raunin Murya Abba ya gyaɗa kansa kana yace.
“Kuyi haƙuri bawan Allah dan Allah kuyi haƙuri wallahi kuɗin nan da kuka faɗa babu su awajena kwata kwata babu”.
Daga ɗaya ɓangaren mutumin ya juya tare da kallon M Jameel dake zaune a ƙasa kana cikin wata dakakkiyar murya mutumin yace.
“Da alama dai mahaifinka baya sonka”.
Jin muryan mutumin agefe yasa Abba saurin cewa.
“Don Allah ku bani inji muryarsa”.
Cikin wannan bauɗaɗɗiyar murya Mutumin ya wurga wa M Jameel wayar kana yace.
“Gashi kaji muryan sa”.
Cikin sauri M Jameel ya cafke wayar tare da kaiwa Kunnensa kana cikin sanyin mai cike da rauni mai tada hankalin ɗan Adam cikin murya mai cike da galabaita yace.
“Abbana”.

Cikin sauri Moddibo ya karɓi wayar a hannun Abba kana yasa a handsfree tare da danna record.
Cikin raunin Murya M Jameel yace.
“Abba kabasu kuɗin Abba dan Allah ka basu abinda suke so ka fitar dani awannan wajen mana Abbana”.
Runtse Idanu Abba yayi kana yace.
“Babana zan fitar da kai ina nan ina har haɗawa kuɗin insha Allah zan fitar da kai amma Jameelu duka-duka kuɗin da muka haɗa anan Million Saba'in ne su kuma sunce Million ɗari biyu suke so”.
Cikin wata raunan'niyar murya mai cike da masifaffiyar galabaita da neman jin ƙai M Jameel yace.
“Abba a saida motocina duka sannan aduba ɗakina akwai kuɗi amma bai cika Million biyu bama dan Allah ahaɗa Abba abasu azo a karɓe ni”.
Cikin rauni ya runtse Idanunsa da hawaye suka cika kana yace.
“Abba bana son zaman nan babu daɗi ba Ummina ba A.J sannan kaima ba kai wuri ba daɗi dan Allah Abba ka basu duk abinda suke so kazo ka karɓe ni ku saida komai nawa a haɗo kuɗin”.
Kai Abba ya gyaɗa tare da ƙoƙarin hana hawayen sa zubowa kana yace.
“Babana Insha Allah zan zo in karɓe ka koda raina suke so zan basu amadadin ranka”.
Modibbo kuwa tuni wasu irin hawaye masu masifar zafi ke kwaranyo mishi tamkar mace.

Fisge wayar sukayi daga hannun M Jameel kana cikin wannan bauɗaɗɗiyar murya Mutumin yace.
“Toh kaji dai abinda ɗan ka ya faɗa zamu baka dama ta karshe”.
Cikin sauri Moddibo da idanunsa ke rintse ya buɗe tare da cewa.
“Dan Allah! Dan Allah!! Dan girman Allah!!! dan darajar Annabi Muhammad (S.A.W) badan muba kamar yanda kuka ce J nada mutunci da kamala toh dan Allah saboda wannan kamalar tasa ku rage mana kuɗin zamu yi muku duk kan biyayya amma ku faɗa mana abinda zamu iya kawo wa”.
Daga ɗaya ɓangaren shiru mutumin yayi ba tare da yace komai ba kana bai katse kiran ba.
Cikin raunin murya Moddibo yace.
“Dan Allah kuyi haƙuri ku rage mana Insha Allah ba zamuyi gardama ba, amma kuɗin hannun mu munyi munyi sun kasa kai adadin da kuke buƙata mu samu su kai adadin da kuke buƙata wannan shine matsalar mu ku temaka ku ragar mana”.
Ajiyar zuciya mutumin ya sauƙe tare da cewa.
“Wannan Moddibo ne ke magana ko?”.
Kai Moddibo ya gyaɗa kana cikin sanyin murya yace.
“Eh”
Cike da gadara Mutumin yace.
“Toh shikenan ku bada Million ɗari da hamsin”.
Cikin raunin murya Moddibo yace.
“Mungode amma dan Allah ba zaku ƙara rage mana ba?”.
Cikin wata razananniyar tsawa Mutumin yace.
“Dan ubanka dan ka samu na zabge Million hamshin.
Atake to wallahi acikin Million ɗari da hamsin Naira biyar ba zamu rage ba kuma wallahi idan ku ka yarda kuka sake yi mana batun ragi kuɗi to wallahi akan ran Jameel domin kuɗi ne dai mu ki ya rayu ko ya mutu zamu samesu”.
Cikin tsanananin tsoro da kaɗuwa Moddibo ya dafe ƙirjinsa yayin da kansa ya sara da masifan ƙarfi.
Cikin tsawa Mutumin ya cigaba da cewa.
“Yanzu Moddibo gashi kayi magana dashi na ƙarshe wanda ko bacci yake yana kiran sunan ka gashi kayi magana dashi dan wataƙil shine maganarka na ƙarshe kenan dashi matukar dai baku haɗa kuɗin nan ba ku kasake yi mana batun ragin kuɗin to kayi magana dashi na ƙarshe kenan”.
ya faɗa tare da wurgawa M Jameel wayar.

Cikin sauri M Jameel ya cafke wayar tare da maƙalawa akunnensa kana cikin raunin murya yace.
“A.J”.
Cikin sauri da zaƙuwa Moddibo yace.
“J ina kake?”.
Girgiza kai M Jameel Yayi tare da cewa.
“A.J ban san inda nake ba ina Ummina!?”.
Runtse Idanu Moddibo yayi tare da taune lips ɗinsa kana yace.
“Tana lafiya J?”.
Cikin sanyin Murya M Jameel yace.
“J ka tabbata?”.
Cikin raunatacciyar murya yace.
“Na'am”.
jin haka yasa yaci gaba da cewa.
“Kace mata kada tayi kuka tayi ta min. Addu'a A.J ina sonka Ina son Ummina Ina son Abbana Ina Son Asma'u Ina son Bashir”.
Da sauri Moddibo ya dafe ƙirjinsa dake harbawa da masifan ƙarfi cikin raunin murya M Jameel ya cigaba da cewa.
“A.J Ina son Khausar tashigo rayuwar mu”.
Cikin tsanananin rauni Moddibo yace.
“Na sani J nasan kana son mu muma muna sonka, kuma in sha Allah duk zamu kasance a tare, zata shiga rayuwarka J zan mutunta abinda kakeso J”.

Girgiza kai M Jameel Yayi still cikin raunin murya yace.
“Ngd A.J in kayi haka kayi min komai, kayiwa Ummina magana idan akwai wani abu a hannunta ta bayar ahaɗa azo a karɓeni awajen nan dan Allah katemaka min”.
Araunane Moddibo yace.
“Insha Allah J zan taimaka da duk kan iyawa ta da kuma duk kan damata J koda ace da raina ne zan fanshi ranka da rayuwarka Insha Allah zamu fito da kai”.
Jinjina kai M Jameel yayi tare da faɗin.
“Nagode Nagode A.J ina maka fatan al'khairi acikin rayuwarka ga Amanar Ummina, Asma'u, Bashir,Abba da.... ka kula dasu kafin in dawo sannan kada ka mance batun Kh”...
Fisge wayar akayi daga kunnensa tare da katsewa.

Dafe kai Moddibo yayi cikin wani irin azabebben rauni ya fashe da matsanancin kuka tare da miƙewa batare da yace komai da Abba ba ya fice yana fita ya shiga motarsa tare dayi mata key.
Kana ya ciro wayarsa tare da dearling number Ummi tana ɗagawa murya a raunace yace.
“Ummi”.
Cikin sanyin murya tace.
“Na'am”.
Cikin ƙoƙarin hana kansa kuka yace.
“Ummi munyi waya da J yanzu”.
Ajiyar zuciya Ummi ta sauƙe kana tace.
“Dagaske Babana?”.
Kai ya gyaɗa kamar tana gabansa.
Cike da tsoro Ummi tace.
“Babana to Meyesa kake kuka?”.

Fashewa yayi da kuka kana cikin sheshsheƙa yace.
“Ummi ina kukan rashin J akusa dani ne Ummi wanda suka sai motarki Alhj Abdallah kice ya tura Azo aɗauki motocina da na J duka azo asiya ahaɗa kudin duka”.
Numfashi Ummi ta fesar tare da rintse idanunta kana tace.
“Sunƙi ragewa ko?”.
Girgiza kai yayi tare da cewa.
“A'a Ummi sun rage mana Million hamsin akai yanzu ya zama Million ɗari da hamsin suke buƙata”.
Ajiyar zuciya Ummi ta sauƙe tare da cewa.
“Toh Alhamdulillah wataƙila zamu iya cin nasara".
Cike da rauni Moddibo yace.
“Insha Allah Ummi da izinin Ubangiji”.
Ya faɗa tare da katse kiran jin wani kuka na neman kufce masa.
Chapter 105 · 0% Book details