← Book details Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 114

Sashe 8

Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali M Jamil yayi parking a bakin gate ɗin gidansu Moddibo juyowa yayi ya kalli Moddibo dake gefensa yana lallatsa system nasa.
“Toh wazai fita ya buɗe mana gate ne kam?”.
Ba tare da ya ɗago ya kalleshiba ya ɗaga kafaɗarsa ɗaya tare buɗe tafin hannunsa alamun
Oho.
Kai M Jamil ya jujjuya tare da cewa,
“To bari ni buɗe”.
Kai ya kuma gyaɗa masa alamun.
“Toh”.
Murmushin M Jamil yayi tare da fita ya buɗe gate ɗin, kana ya dawo yaja motar suka shiga ciki.

Parking yayi kana suka fito suka nufi cikin gidan,

Kai tsaye sashin Innayin suka wuce.

Wani irin yalwataccen murmushin M Jamil yayi tare dayin saurin ya haura kan barandar zama yayi daɓas bisa tattausan carpert ɗin dake shimfiɗe a barandar.
Innayi na kwance yayinda Ummin Jamil kuwa ke gefenta tana ɓare mata banana.
Itama yalwataccen murmushin tayi tare da miƙawa Moddibo ayaban data ɓaren.
Amsa yayi tare da juyowa ya ɗan kalli M Jamil da ya zame ya kwanta bisa carpet ɗin tare da ɗaura kansa bisa cinyarta, cike da so, ƙauna, shaƙuwa, tausayawa, yace.
“Ummina kin san irin farin cikin da nakeji a raina kuwa in na ganki?”.
Murmushin kawai tayi dan ita bazata iya cewa komaiba a gaban Innayi sabida Jamil shine ɗan ta na fari, kuma su nan Gembila sashine na cikakkun Fulani.

Kawai dai abinda ta sani a baɗini tasan ta fishi farin ciki.
Shi kuwa Moddibo gefen Innayi dake kwance da alamun har yanzu nitsuwarta bai ida dawowa jikintaba, hannunta ya riƙe tare da kallon M Jamil.
“Kai dan Allah ɗagata kada ka karya mana cinyarta da katon kankan nan”.
Ya ƙare mgnar yana gutsuran banana.
Shi kuwa Jamil da sauri ya tashi zaune jin Umminshi na ture kanshi tana cewa.
“Ai kam gskyarka Moddibo”.
Tashin nasa ne, yasa ta miƙe ta nufi kitchen, trayn data shirya kulolin abincinsu ta kawo musu.
Ta ajiye a tsakiyar su,
Shi kuwa Modibbo a hankali ya kamo hannun Innayin tare da tallabota alamun so yake ya ganta a zaune.
Sai kuma duk suka kalli Innayi data buɗe kwayar idanunta jin yana tallabota.
Zaunar da ita yayi cikin kulawa yace.
“Yanzu me yake miki ciwo?”.
Cikin sanyi tace.
“Nima kaina ban saniba, kawai dai zuciyata ke a tsinke tsoro nakeji Moddibo”.
Da sauri Jamil yace.
“Toh Innayi tsoron me kuma kikeji?”.
Cikin sanyi tace.
“Tsoron kada mutuwa tai mini zuwan ba zata”.
Wani irin masifeffen tsinkewan zuciya ne ya riski Moddibo jin Jamil ya ɗan yi yar dariya tare da cewa.
“Kada ki damu Innayi ki dena jin tsoron mutuwa, domin ita wajibinmu ne ita.
Kuma tsufa ba shine hanyar mutuwaba, ba abin mamaki bane ki rayu ni nan Jamilu in mutu in barki, in bar Ummina da rashina, in bar Aminina Moddibo da rashin Aboki kamata, tabbas a al'amarin ubangiji zan mutu in barku a raye da kuma ƙunar rashina”.
Da sauri Moddibo yace.
“Yah Salam wai kai J meyasa ne wasu lokutan kalamanka a baibaisuke? Dan Allah kasan abinda zakana cewa”.
Murmushin mai sauti Jamil yayi tare da cewa.
“Zanfa mutu kam, dole zan mutu to kai dama a gani kake a haka zamu tabbata ne?”.

Da hannu Moddibo ya nuna masa Umminsa da haka kawai taji wasu irin zafafan hawaye sun zubo mata.
Da sauri Jamil yasa tafin hannunsa ya sharce mata hawayen tare da cewa.
“Kada kiyimin kuka kodama na mutu kada ki damu Ummina kinga aminina Aliyu ko to shi zai zame miki madadina”.
Da sauri tayi mishi dakuwa.
Sai kuma yayi dariya mai sauti tare dace.
“Oh su Ummi ana son ɗan fari wato irin bakya son Jamilunki ya mutun nan ko”. Ya ƙare mgnar cikin tsigar wasa kamar dai kakarsa ce,
Hakanne yasasu yin murmushin ganin zata kai mishi duka ya ɗan zille yana cewa.
“Haka kawai wai kunya wai ni ɗan fari bazakice kina sonaba, toh ni kam ina sonki ina sonki ina sonki Ummina”.
Ƙeyarsa ta ɗan buge, kana ta tura musu plate ɗin dake cike da fruits sai kuma ta mimmiƙa musu fork,

Innayi kuma yar wannan hirar da sukayi yasa ta ɗan sake kaɗan, duk da har yanzu in ta rufe idanunta tana ganin abinda Allah ya nuna mata daren jiya.

Jamil ne ya kalli Innayin tare da cewa.
“Dr Jamila tazo ta dubaki ko, dan da safe kafin mu wuce makaranta na kirata tazo”.
Kai Ummi ta gyaɗa alamun eh tazo.

Frutis ɗin kawai suka ci kana suka miƙe suka nufu part ɗin Moddibo.
Suna shiga falon,
Cikin sanyi Jamil ya zauna bisa kujera tare da riƙo yatsar Moddibo manuniya, cikin wata iriyar sassayar muryar yace.
“Moddibo kasan ina jin farin ciki na musamman in naga Ummina ko?”.
Sunkuyar da kai Moddibo yayi tare da zuwa aminin nasa idanu cikin sanyi yace.
“J nasani! Na sani dan farin cikin baya ɓuya a fuskarka”.
Cikin Muryar da tafi ta ɗazu rauni ido na ciko da hawaye yace.
“Amman kuma fa farin cikina raggene, duk daɗin da nakeji in na tuna cewa Ummina ba a gidan Dadyna takeba, inajin ciwo mai yawa a raina, inajin takaicin Kasan cewar mahaifiyata bata gidan mahaifina tana can a wani gidan.
Bayan ita tasha wahalar zama dashi cikin talauci, saida yayi kuɗi dai-dai sanda zataji dadin rayuwa ya saketa, gashi yan uwanta ba masu haliba, mijin da Allah ya ƙaddara ta aura shima rayuwar ba daɗi sabida baida ƙarfi”.
A hankali Moddibo ya zauna kusa dashi cikin ƙarfafa mishi guiwa yace.
“J wanne dadine na kuɗi ya rage wanda bakayiwa Ummi ka tunafa, duk abinda kace kanaso Daddy yana baka, duk kuɗin da zaka nema zai baka, a haka har Makka ka kai Ummi yaranta ka sasu a makaranta mai kyau sanadin su kaƙi kayi aiki a ko ina kace zakayi karantarwa a makarantarsu dan ka tayata basu tarbiyya. Kana kuma yi tunda gashi yanzu sun kusa gamawa, tunda ko Asma'u nanda shekara uku dai zasu gama, secondary School, kace kuma suna gamawa zaka aurar da Asma'u kana ka ɗauki nauyin karatunta, ta na gaba tana gidan mijinta, shi kuwa Bashir na mijine kuma kace in ya gama so kake ya samu jami'atul Madina, in ya tafi can sannan kayi aure kace kuma kana aure zaka ɗauke Ummi da ita da mijinta Malam Ahmad zaka riƙe su, Jamil to meya rage na jin daɗi da baka samawa Ummi ba, ka gyara mata gidan da take, ka gyara mata ɗakinta”.
Wani murmushin mai sanyi yayi tare da cewa.
“To wai Moddibo da kake cewa haka, rainafa mallakin ubangijine a duk sanda yaga dama zai ɗaukeni daga wannan duniyar, ko ban gama cikace burukana ba, in babuni a raye wa zai maiye musu gurbina?”.
Cikin tsuke fuska Moddibo yace.
“To dama wa yake da tabbacin rayuwa, yanzu ni in dai naci zan lizanci irin tunaninka Innayi fa bata da kowa a duniya saini.
J ni zaka gayawa mutuwa? Ni Aliyu zaka gayawa mutuwa?”.
Sai kuma duk sukayi shiru suka zubawa juna ido.
Numfashi mai nauyi Moddibo ya fesar kana a hankali yace.

“J ka kalleni mana! In zame maka madubi, gwara kaifa,
kasan su Ummi kana ganin ta gafa Daddy”.
Da sauri M Jamil ya ri ƙa gyaɗa mishi kai tare da tuno maraicin aminin nasa.
Shi bai san iyayensu ba ranar da mahaifisa ya rasu, firgicin abin ne ya tadawa mahaifiyarsa naƙudansa, ta haifeshi kana itama tabi bayansa kamar yadda Innayi ke basu labari.
Da sauri M Jamil ya kalleshi jin yana mgn a hankali.

“Ba uwa ba uba ba wa ba ƙani ko ƙanwa ba Baffa ba kawu ba goggo ba Yafendo, yanzu ashe bazaka dubi maraicina ba, sai kai ka godewa Allah ba J kaga ni kuwa idan na tuna duk rashin da nayi in naji ƙunci da ciwo sai in tuna.
Allah ya azurtani da rayuwa da lafiya kana yayi min ni'imar kasan cewa Musulmi, ya bani hankali ya ƙara min da haddar izu settin, da littattafai masu tarin yawa wanda masu iyaye da dama basu samuba, ya bani sa'a a dukkan karatuna mukayi digire har master's har zuwa P.H.D a makaranta mafi daraja a duniya Jami'atul Madina, kana muka samu gurɓin aiki kuma a can.
Wanda ko yau muka koma can da aikinmu a hannu, amman kai ga uzurin daya tsareka, nima kuma da uzurin daya tsareni”.
Da sauri M Jamil yace.
“Astagfurullah! Astagfurullah!! Astagfurullah!!! Alhamdulillah aboki na gari rahama ne, ai kam ni ga uzurin daya tsareni to amman kaifa Moddibo uzurin menene ya tsareka duk da bana son mu rabu Amman zaso kaje can kayi aikinka da al'bashinka mai daraja”.
Kai Moddibo ya kauda tare da cewa.
“Uzurina ai a fili yake J Innayi na tana son kulawata”.
Da sauri M Jamil yace.
“Ba gsky bane Moddibo karo na forko kenan a rayuwarmu daka ɓoye min abinda ke ranka kaƙi ka gaya min me dalilin ka na zama a ƙasar nan bayan saudia na buƙatar ka, kuma harda daman zama da iyalanmu fa muke dashi a can”.
Kai ya jujjuya tare da cewa.
“J yaushe na zama makaryacin da har mgnata bazata samu karɓuwa a wurinka ba?”.
Da sauri M Jamil yace.
“No wlh ni mai shaidar ka ne har gaban abadan kai ba makaryaci bane, kawai dai ban gamsu da hujjar bane”.
Kanshi ya jujjuya kana ya nufi bedroom ɗinsa,
Shi kuwa M Jamil ɗayan ya shiga.

A can cikin masarautar Gembila kuwa,
Cike da kaɗuwa Khausar ta...

Ta juyo ta kalli mahaifiyarta sabida jin kalaman da Hajia Bunayya ke faɗi.
“Eh Sulaiman a kawo min mashin ɗin lipan mai kyau wanda zaiyi dai-dai da Haiydar,
A kawo fari dan yafi son komai nasa fari”.
Sai kuma ta ɗan yi jim, alamun tana sauraran abinda ake faɗi a ɗaya sashi,
dariya mai cike da sakewar zuciya tayi tare da cewa.
“Ai kaima kasan shi na musamman ne, Yarima ne fa, mai jiran gado, kuma gashi sunan Babanmu gareshi, in banji dashi ba da waye zanji”.
Chapter 8 · 0% Book details