← Book details Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 114

Sashe 65

Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Haka yasa ta biyo bayan Mommy da ɗan sauri yayin da ko wanni gaɓa na jikinta ke motsa wa baki ɗaya alamun Budurci sun bayyana ajikinta ta ko wanni fanni ta zama cikakkiyar budurwa ƴar gayu First class.
Bayan motar ta buɗe ta shiga bayan ta ƙarasa wajen gani tayi duk Amina ta wani babbaje.
Kamar ba zata ce komai ba sai kuma tace.
“Ɗan matsamin in zauna”.
Kallon banza Amina ta watsa mata cikin ya mutse Fuska ta kalli Khausar kana tace.
“Keɗin har nawa kike da wannan wajen ba zai ishe ki ba?”.
Cikin juya ido tace.
“Kinsa cikakkiyar sura ta ƙasaitattun mata Allah ya min dole wurin bazai isheni ba tunda ba irin baki bane”.
Cike da fusata Amina tace.
“Eh lallai yarinyar nan wuyanki ya kai yanka, amman dadin ta dai bada ɗuwawunki nake zamaba kuma bada ƙugunki nake ɗaura zabi ba”.
Taɓeki tayi tare da juyawa ta kalleta.
Har kamar zata yi magana sai kuma ta fasa ganin yanda lokaci ke tafiya sannan ya Exam na Geography zasuyi tasan muddin aka fara Moddibo na iya hukuntata baya ga haka ga kuma alamun yau akwai hadari a garin wanda yau kimanin kwana tara kenan ba'ayin musu ruwan saman ba.
Gefen Haiydar ne ya matsa mata ta shiga kana Driver yaja suka tafi.
Suna Isa Khausar tayi saurin ficewa tare da nufar Hall da zasu zana Exam ta nufi Hall ɗin yayin da Iska mai sanyi ya soma kaɗawa gari ya fara duhu suna cikin rubuta Exam ɗin hadari ya fara haɗa gangami sosai a hankali gari ya fara duhu.
Basu wani ja lokaci ba suka kammala rubuta Exam ɗin atare Khausar da Asma'u suka fito.
Asma'u ma ta zama cikakkiyar budurwa komai na Budurci ya bayyana ajikinta.

Juyowa Khausar tayi ta kalleta ƙirjinta rungume da Questions da suka gama rubutawa, murmushi ta ɗan yi kana tace.
“Asmeey ki gaida min Ummi dan Allah, wallahi nayi missing ɗinta, rabo na da ita fa ya kai wata biyu”.

Hararanta Asma'u liƙa mata kana tace.
“Ai baki da kirkine sannan babu saƙon ki da zan fada mata in da gaskene kizo”.
Ta ƙare mgnar tana mai ɗaga kanta ta kalli sama, ganin yadda gaba ɗaya garin ya rufa yayi duhu.
Da sauri Khausar ma ta fara juye-juye tana cewa.
“Yah Salam wannan hadari haka, ina Haiydar suzo mu tafi, kar ruwa nan ya rutsamu a nan.”
Murmushi Asma'u tayi tare da cewa.
“Allah yasa ya rutsa kin dai muga ta tsoro”.
Ta ida mgnar tare da yin murmushin mugunta dan tasan yadda Khausar ke masifar tsoron walƙiya da tsawa.
“Ba Amin ba”.
Khausar ta faɗa tare da tura baki.
Ita kuwa Asma'u dariya tayi tare da jan hannun Bashir sukayi gaba saboda yanda hadarin ke sake gangami ko ina yayi ɗib.
Murmushi Khausar tayi kana tace.
“Bashir dan Allah kagaida Ummi, dan naga yau mutuniyar Black Stomach take ji dashi”.
Asma'u na ƙoƙarin shiga mota tayi murmushi kana tace.
“Oho dai ance zuwa da kai ai yafi saƙo”.
Khausar kuwa murmushi tayi tare da bin bayansu ganin Haiydar yayi gaba.
Da ɗa sassarfa ta tashiga bayan motar ta zauna kusa da Haiydar tana ɗan kallon harabar makarantar da duk aka watse sai mutane ɗaɗɗaya har malamai da alamun sun tattafi da sauri ta juya ta kalli Haiydar kana tace.
“Ina Amina kuma?”.
hannu ya buɗe mata alamar bai sani ba, bata sake cewa komai ba,
ta lumshe idanunta tare da jingina bayanta da jikin Kujeran sassayan iskan hadarin dake bugawa na ratsata.

Acan harabar makarantar kuwa Amina ce da Samira Sani ke tafiya.
Cikin taɓe baki Samira ta kalli Amina kana tace.
“Ni wallahi tunda nake ban taɓa kallon mutum Irin Moddibo ba ace mutum kamar dutse sam baya fahimtar komai”.
Murmushi Amina tayi kana tace.
“Hmmm ke dai Samira bari M Jameel ɗin ma meyene, duk tsawon lokacin da muka ɗauka muna aiki da maganin fa yanda yake wani shan min Ƙamshi”.
Harara Samira ta watsa mata cike da takaici tace.
“Amma Wallahi Amina baki da godiyar Allah ki dubi yanda mutumin nan ya fara sake miki, yana amsa gaisuwar ki da fara'a, yana kula ki da ace nice nasamu wannan damar, awajen Moddibo ai dana godewa Allah”.
Jinjina kai Amina tayi kana tace.
“Haka ne kuma amma gaskiya har yanzu sai mun sake sabon shiri akansu domin har yanzu Malam Jameel yafi ji da wannan shegiyar yarinyar akaina”.
Da wannan hira suka isa jikin motar wani matsiyacin kallo Amina ta watsawa Khausar dake bayan mota Idanunta alumshe cike da gadara da kuma Izzah ta ya mutse fuska kana tace.
“Iyeee ƙarfin hali yau naji Agola da ƙarfin hali, motar na gidan Ubankine da zaki shiga baya kiyi kane-kane aciki, to ni kuma a ina zan zauna ji yanda kika tara ƙannenki kuka lafe abaya ku gaku ramukan kura ko daga ke sai ƙannen ki, wai ma tukunna ni akanki zan zauna ne!? Da kika wani baza masaka-masakan duwaiwaka”.

Ahankali Khausar ta buɗe Idanunta dake lumshe ta zuba mata su tana kallonta cike da mmki, amma ba tace komai ba sai gyara zamanta da tayi tare da buɗa mata inda zata zauna.

Ya mutse fuska Amina tayi cike da jaraba da kuma gadara ta dubi inda Khausar ta matsa mata kana tace.
“Wannan wani irin iskanci ne da raini ne ko kuma ni sa'ar kice ke badan kinyi sa'ar Babanki ya mutu ya bar uwarki tayi zawarci babana ya kwasa ba ai koda hanyar da nabi baki isa ki biba. Agola kawai mara galihu ƴar matsiyata”.

Cike da ɓacin rai Khausar ta ɗago kanta babu walwala afuskarta ta kalli Amina tare da cewa.
“Wai Meyesa kike son zagina ne? Baga shi na gyara niki ba wannan ɗan ɗuwawun da kamar an ɗaurawa kare zani me zai hana filin isarki, baki shigo kin zauna kinga wurin bai ishi tsamurarrun mauzanki da suke kamar an matse lemon tsamiba kawai saboda kin saba da Akuyanci da kuma karnukan ci sai kin tsaya anta masifa dake da raba hali, saboda ke Jaka ce baki san darajar mutane ba, zaki tsaya kina ta goranta min akan wani Akwalar mota! To ki sani ni dai bazan zagi iyayenku ba musamman mahaifinki da yake mumini uwarki kuwa zaginta ma asarane don ko zagi akan mai tsarki yake fatan a aikeshi”.
Harara Amina ta watsa mata kana Afusace tace.
“Eh koda Akwalar ce aiba Ubanki bane ya saya idan kuma Ubankine ya saya sai inji? koda yake nasan har matsiyacin Ubannaki ya mutu bai taɓa mallakar irin wannan na kansa ba!”.
Cike da matsanancin ɓacin rai Khausar ke kallonta idan akwai abinda tafi tsana aduniya kana yake saurin fusata ta shine zagin mahaifinta.
Azuciye ta sauƙa daga motar yayinda Haiydar da su Ramadan ma suka sauƙo,
cikin nuna Amina da yatsa tare da ƙanƙantar da idanunta kana tace.
“Kada ki sake zagin Ubana domin Ubana yafi ki daraja koda Agaban Ubangiji”.

A yatsine Amina ta watsa mata mugun kallo kana tace.
“An zage sa ƴar iskan yarinya mai hana ruwa gudu ƴar matsiyata”.
Cikin wani irin fushi Khausar ta ɗaga hannunta tare da kife Amina da wani irin azabebben mari hagu da dama cikin nunuta da yatsa tace.
“Ki sake zagar min Uba kiga abinda zan gwada miki”.
Dafe kuncin Amina tayi cike da Mamaki take kallon Khausar kana tace.
“Ni kika mara Khausar?”.
Harara Khausar ta watsa mata da manyan Idanunta kana tace.
“An mare ki”.
Ahankali Habu Driver ya leƙo kansa tare da faɗin.
“Khausar kiyi haƙuri".
Sai kuma ya kalli Amina dake huci kana yace.
“Amina kema sam baki kyauta ba taya zaki zagi Ubanta ai duk Abinda zakuyi tsakaninku ne”.
Wani shegen kallo ta watsa masa Afusace tace.
“Habu ka rufe min baki ka fita Idona na zagi Uban nata idan taji haushi tabar mana gidan mu ta tafi gidan Ubanta ƴar matsiyata ƴar jarababbu Angola ta bar nan garin ta koma can dajin nasu mana”.
Ta ida maganar tare da shiga motar taja murfin ta rufe da ƙarfi.
Sai kuma ta sauƙe glass ɗin motar tare da cewa “Haiydar, Ramadan, da Raudat ku shigo motar tunda ku dai ta Ubanmu ne”.
Cikin takaici Haiydar ya girgiza kai alamar a'a su tafi.
Ita kuwa Khausar ciki takaici ta ɗaga Raudat da Ramadan ta sakasu cikin motar tare da nunawa Haiydar ƙofar motar alamun ya shiga.
Murya a cushe yace.
“Toh kefa Adda Khausy”.
Cikin danne fushinta tace.
“Kada ka damu zan shiga Napep”.
Zai yi mgn tayi tayi saurin cewa.
“Dan Allah kada kace komai shiga kuje”.
Ta ƙare mgnar tana turashi ciki, dole ya shiga. Ita kuwa Amina tsaki taja tare da cewa.
“Dole su kam shiga ke kuma sai kije can kishiga naki na Uban”.
Chapter 65 · 0% Book details