← Book details Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 114

Sashe 25

Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Picking Yayi tare da kai wayar kunnensa tare da sallama.
Amsawa Jalaludeen yayi da faɗin.
“Ya yatsun ƙafar naka sun warke ne!?”.
Moddibo kuwa gyara kwanciyarsa yayi da faɗin.
“Jameel ya faɗa maka kenan?".
Jalaludeen yace.
“Kamar dai baka sanni ba sai Jameel ya faɗa min zan sani?”.

Moddibo kuwa kwanciyar sa ya gyara kana yace.
“Eh ainaga kunyi waya ne bayan abin ya faru”.
Jalaludeen yace.
“Wallahi Jameel bai faɗa min ba lokacin da abin yafaru ma ai ina nan”.

Shi kuwa Moddibo kwanciyarsa ya gyada tare da faɗin.
“Hmmm yayi kyau ka kawo mana ziyara kenan”.

“Eh nakawo muku ziyara Barka da jumma'a ai tare mukayi jam'in sallan jumma'a ma”.

Sassayan numfashi Moddibo ya fesar kana yace.
“Mungode amma aiba mu gaisa ba".

Murmushi Jalaludeen yayi yace.
“Ai zamu gaisa sai kuma na samu abin kallo ana dramer Shiyasa ba mugaisa ba, na tafi shi Kam Jameel baima San nazo ba Dan ban faɗa masa ba”.
Kai Moddibo ya jinjina kafin yace.
“Toh yayi kyau ya labarin mutanen England”.
Jalaludeen yace.
“Duk suna nan lafiya”.
Kana sukayi Sallama.
Kallon screen ɗin wayar Moddibo yayi Aransa yace Allah mai kyauta shi Jalaludeen jinsinsa da ban amma haka yake jin daɗin Mu'amala damu sannan babu cutarwa atsakaninmu da wannan tunani bacci ya ɗauke sa.

Acan Rugar Jauro yaya kuwa Washe gari da Asubah bayan Khausar ta idar da Sallah tayi Azkharul sabah da tagama ta juya tare da kollon Dije tace.
“Muje gidan Hajja Nana”.
Dije tace.
“A'a kije Ni zan dafa mana abinda zamu ci kinga Goggo Nanne bata jin daɗi”.
Kai Khausar ta gyaɗa sannan ta miƙe ta fita atsakar gida ta samu Hajja Nana ta jiƙa wankekkdn wakenta ya jiƙa,
Zama Khausar tayi tace.
“Ina kwana Hajja Nana”.
Ba yabo ba falassa Hajja Nana tace.
“Lafiya".
Sannan ta ɗaura da cewa.
“Ga can wake ki ɗauka ki markaɗamin acan”.
Ta ida maganar tana nunawa Khausar inda ta kafa dutse irin na mutan da saboda basu da inji agarin".

Ita kuwa khausar inda Hajja Nana ta nuna mata da faɗin zatayi markaɗe ta riƙa bi da kallo kafin ta mayar da kallonta kan Hajja Nana tace.
“Wai in markaɗa Miki me?”.

Hajja Nana tace.
“Waken ƙosai kinga kwana biyu banyi ba tunda kika zo Mai nane ya ƙare sai jiya na samu da Sadik ya shiga Gembila ya sayo min”.

Ita kuwa khausar da Mamaki tace.
“Kamar ya in miki markaɗe?”.
Kallonta Hajja Nana tayi tace.
“Kiyi min markaɗe nace”.
Ita kuwa Khausar ƙugu ta riƙe tace.
“Ni wallahi ban taɓa ganin yanda akeyi ba ban sani ba kuma ban iya ba”.

Hajja Nana kuwa sheƙeƙe ta dubi Khausar tace.
“Insaki aiki kice baki iya ba?”.
Baki Khausar ta tura tare da riƙe ƙugu tace.
“To ban iya ba ya za'ayi na iya ni Wallahi ba zanyi ba taya ma nasan zan iya riƙe dutsen nan nace zanyi markaɗe kije ki kirɓasa aturmi mana kawai”.

Haɓa Hajja Nana ta riƙe cike da mamaki tace.
“Ni kike cewa Inje in kirɓa aturmi Meye amfaninki Kai Allah wadaran naka ya lalace ke kam ba irin Addarki ba sam”.

Ita kuwa khausar hannunta ta harɗe aƙirji Idanunta tsaye akan Hajja Nana tace.
“Toh yanzu tunda kinsan Ni ba irin Addah bace sai kiyi min hakuri Addah na agabanki ta girma duk wani horonki ta iya Ni Kuma ba agaban ki na girma ba, kuma ban iya ba ya za'ayi kice min haka wata ƙil ma bakya tuna ta kiyi mata addu'a sai in magana irin haka aya tashi kike tunata”.

Dafe ƙirji Hajja Nana tayi da faɗin.
“La'ilah ha ilallahu Muhammadu Rasulullah (S.A.W) Khausar ni zaki nunawa son Nanne?”.
Ita dai Khausar na riƙe da ƙugu sannan tace baza tayi markaɗe akan dutse ba.

Suna nan atsaye haka Baffa Umaru ya shigo ganinsu tsaye ahaka yasa yace da Khausar.
“Lafiya kuwa”.
Fuskarta babu walwala tace.
“Wai Hajja Nana ce saina yi mata markaɗe akan dutse Ni kuma ban iya ba”.
Baffa Umaru kuwa juyawa yayi ya sake kallon Hajja Nana yaga sai wurgawa Khausar Harara take Kallonsa ya mayar kan Khausar yace.
“Ayyah Khausar ki gwada mana ba aikin mata bane”.
Da sauri tace.
“Toh ban iya ba Baffa Umaru taya zan gwada”.

Hannunta ya riƙe tare da faɗin.
“Zo in koya miki”.
Ba musu ta matsa kusa dashi ɗan dutsen ya ɗauka ya kafa sannan ya matso da roban waken ya ɗibi wake cikin hannunsa yace.
“Ki markaɗa”.
Ta gyaɗa masa kai sannan ta fara Markaɗawa ga mamakinta sai taga yana markakaɗuwa har tayi niyyan zagewa ta markaɗa sai ta fasa ta fara jefar da ɗaɗɗaya tasan muddin tayi mai kyau Hajja Nana zata mayar dashi aikinta baya ga haka kuma daga riƙe dutsen yatsun hannunta sun sage tun lokacin data faɗo daga bishiya agidansu Moddibo hannunta bai dawo dai-dai ba.

Ganin tana jefer da waken da guda-guda yasa Hajja Nana cewa.
“Hegiya gantalelliya kibar min abuna”.
Ta ƙarashe maganar tare da amsar dutsen tashiga markaɗawa.
Miƙewa Khausar tayi tare da kaɗe hannunta tace.
“Yafi Nono fari”.
Shi dai Baffa Umaru murmushi yayi tare da yiwa Hajja Nana sallama ya tafi,
Ita kuwa Khausar saurin bin bayansa tayi suka tafi adai-dai ƙofar gidan Malam Liman suka tsaya tagaishesa cike da ladabi.
Sannan suka cigaba da tafiya suna taɓa hira har suka isa gidansa.
Adda Adama na ganinta ta sakar mata murmushi tare da faɗin.
“Khausar sannu da zuwa ya gida ya gajiyarku na jiya?”.

Murmushi tayi da faɗin.
“Ba gajiya Adda Adama ya Aiki”.
Ta amsa da.
“Alhamdulillah.
Kana tace.
“Ke kam tunda kika zo baki taɓa zuwa kin kwana mana ba”.

Khausar na gyara zama tace.
“Insha Allah yau zan zo mukwana”.
Murmushi Adda Adam tayi da faɗin.
“Aikam Nagode”.
Khausar ta juya tare da kallon Baffa Umaru dake sakin murmushi tace.
“Amma fa ki faɗawa jarumin mijinki ya kawo min abu mai daɗi”.
Murmushi kana tace.
“Inde wannan ne baki da matsala”.
Bayan sun gama hira tayi musu sallama ta tafi.

Da daddare bayan sun idar da Sallah Isha'i Khausar tace da Dije.
“Muje gidan Garkuwan Rugarku mu kwana”.
Dije tace.
“Toh muje”.
Sannan ta miƙe suka shiga ɗaki sukayi wa Goggo Nanne sallama.
Adda Amada dake ɗaki tana jin Sallamar su ta fito fuskarta ɗauke da murmushi tana cewa.
“Ai yanzu nake cewa zanbi sawunku”.

Khausar tayi murmushi tace.
“To aigamu ina Jarumin mijin naki?”.

“Yana nan mai zaki bashi?”.

“Babu abinda zan bashi abin daɗi da yace zai ajiye min zai bani idan kuma babu in tattara in tafi”.
Ta Ida maganar tana murmushi.

Miƙewa Adda Adama tayi tace.
“Toh ki kwantar da hankali ga abin daɗi”.
Tayi maganar tana ajiye musu karamin kwandon kaba dake ɗauke da Inabi, Tuffa, Mangoro, Ruman, da sauran kayan itatuwa sai kuma kwanon farfesun kifi yana tururi.

Murmushi mai sauti Khausar tayi tace.
“Lallai yana yina ashe wannan gara haka”.
Ita dai Dije murmushi kawai take musu.
Duka suka haɗu suka ci sannan suka kwanta ɗaki ɗaya da Adama.

Shiko Baffa Umaru yana can aɗakinsa ya kwana.

Misalin ƙarfe biyu na dare Khausar ta farka aɗan firgice sakamakon hayaniya da take jiyowa.

Dije ta gani itama zaune tana zazzare idanu ganin sukayi Adda Adama ta fice aɗakin da mugun sauri suma cikin sauri suka bi bayanta.
Da gudu Adam ta nufi ɗakin mijinta dai-dai lokacin daya fito.

Hannunsa ta riƙe cikin raunin murya tace.
“Dan Allah kada ka fita da alama suna da yawa kaji hayaniyar su”.

Da sauri ya juya ya kalleta tare da faɗin.
“Idan ban fita ba wa zai dakatar da su wannan daga ji mutanen Ƙauyen Garinga ne bamusan mai suka zo dashi ba dare dare zasu zo mana haka babu yanda za'ayi dole in fita”.

Ta girgiza kai tare da riƙe sa kana tace.
“Dan Allah kada ka fita".
Tureta yayi daga jikinsa ya fita yana fita ya hango Arnan mutanen Garinga ne wanda yawansu zai kai kimanin mutum ɗari da sauri ya nufi hanyar jejin yayin da bayansa ke rataye da kwari da baka hannunsa na riƙe da touch light mai masifar haske.
Cikin fushi da tsawa ya haskasu da touch light ɗin hannunsa mai masifar kashe ido yace.
“Menene wai ma tukun ina kuka nufa!?”.

Ɗaya daga cikinsu wanda ya kasance babban su yace.
“Ƴar mu muke nema ta ɓata”.
Duk da acikin duhu ne hakan bai hana shi watsa musu kallon banza ba yace.
“Ƴarku ta ɓata shine dare-dare haka zaku zo wajenmu nemanta?”.
Biyu Daga cikin su suka ce.
“Ai kidnapping ɗinta akayi”.

Afusace yace.
“Kuma in kidnapping ɗinta akayi sai akace muku tana nan Rugarnu?”.
Babban cikinsu yace.
“Tana nan Rugarku dama Fulanin ku ai sune suka sace ta suka kawota dan haka an saceta tana nan mu nan muke zargi”.

Cikin tsananin fushi da zuciya Baffa Umaru yace.
“Baku isa ba babu yanda za'ayi haka ya faru!”.
Babban cikinsu yace.
“Dole sai mun shiga garinku gida-gida ɗaki-ɗaki mun bincika”.

Cikin tsananin fusata Baffa Umaru yace.
“Wallahi in dai ina raye baku isa ba babu wanda ya isa yashiga garinmu yace yayi bin cike indai haka kuke so kuje kuzo da rana muyi magana”.

Babban su yace.
“Mu adaren nan muke so muyi magana”.
Baffa Umaru yace.
“Toh baku isa ba”.
Dumfaro sa sukayi da niyyar shiga Rugar gadan-gadan.
Shi kuwa baya yaja tare da jan kwari da baka yace.
“Duk wanda yake jin shi Jarumi ne kuma ya kai to ya kuskura ya shiga mana cikin Ruga yaga abinda zai faru”.
Tsayawa su kayi akuma dai-dai lokacin ne sauran mazan cikin Rugar suka fiffito mafi yawa ma sautin Baffa Umaru ne ya tashe su dan shi mutum ne mai zafin gaske musamman ma idan ransa ya ɓaci.
Acan bakin ƙofar gida kuwa sosai Khausar ta shiga mamaki sai asannan ta tabbatar da maganar Adama da tace mijinta Jarumi ne kuma Garkuwan Rugar.

Malam Liman ne yayi gyaran murya bayan isan su wajen yace.
“Tun da kunce haka yanzu ku koma da safe sai kuzo aje wajen Mai gari sai ayi magana”.

“Toh”, Babban su yace sannan suka juya suka tafi badan ransu ya soba.
Chapter 25 · 0% Book details