← Book details Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 114

Sashe 62

Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin mintunan da baza su gaza biyar ba suka isa ƙofar katafaren gidan Hong M Jameel Yayi mai gadi ya buɗe musu Anutse M Jameel ya cinna hancin motarsa gidan tare da yin parking a inda aka tana da danyi Parking ɗin motoci.
Cike da nutsuwa suka nufi sashen Abban M Jameel, bakinsu ɗauke da Sallama suka shiga tamfatsetsen Falon nasa daya gaji da tsawuwa yana fitar da sanyayyan ƙamshi.
Tsaye suka hangosa yana gyara ɗaurin agogon hannunsa fuskarsa da damshi da alama Al,wala yayi.

Kallonsu yayi tare da sakar musu da murmushi kana yace.
“Ku shiga kuyi al,wala kunga muna shan ruwa sai mutafi masallaci”.
Kai suka gyaɗa sannan M Jameel ya nufi toilet dake Falon kana ya kalli Moddibo da faɗin.
“A.J kashi ga toilet ɗin ciki kayi al,wala”.
Girgiza kai Moddibo yayi kana yace.
“A'a kashiga na ciki ni zan shiga wannan”.
Kallon Moddibo Abba yayi kana yace.
“Wato shi yashiga ɗaki na kai ba zaka shiga ba ko? To ai kaima ɗana ne kashiga babu komai Moddibo”.
Kai Moddibo ya gyaɗa kana yace.
“Toh shikenan Abba”.
Sannan ya wuce Bedroom ɗin Abba ahankali ya saki murmushi ganin komai na Bedroom din tsaf-tsaf akimtse Aransa yace ashe de J gadon tsafta yayi awajen Abba shima komai nashi tsaf-tsaf ajiyar zuciya ya sauƙe tare da shiga toilet ɗin nan ma komai atsaftace Al'wala ya ɗaura kana ya fito atsaye ya samu M Jameel da Abba Kallonsu Abba yayi kana yace.
“Ku ƙaraso mu isa dining”.
Kai suka gyaɗa tare da nufar dindin ɗin da aka ƙawata da kayan ciye-ciye na alfarma wani irin kwando ne na kayan marmari ne kama daga, Inabi, Abarba, Ayaba, Kankana, Lemo, Ruman, Tuffa, Mangoro.
Sai kuma wasu Warmers masu kyau dake ɗauke da pride rice da yaji kayan lambu,sai daga ɗaya gefen kuma wasu jug ne masu kyau ɗaya kindirmo ne mai sanyi adame ɗayan kuma kunun shinkafa ne sai Flaks dake ɗauke da ruwan tea da kuma kofina daga gefensa kuma gongomin madara ne dana Bounvita sai kulan ƙosai sosai dining din ya ƙawatu.
Anutse suka zauna akan kujeran Abba ya zauna daga ɓarin kudu Moddibo ya zauna daga ɓarin yamma yana fuskantar gabar M Jameel kuwa daga ɓarin gabas ya zauna yana fuskantar yamma.
Anutse Moddibo ya ɗauki dabino guda bakwai ahannunsu idan yaci sai ya sanya ƙwallon ahannunsu na hagu bayan yaci sai ya ɗauki inabi yaci M Jameel kuwa dabino uku yaci tare da apple haka ma Abba.
Sai.kuma suka sha kankana da inabi kana suka ɗan ɗaura da ayaba.
Kallon su Abba yayi cike da so da ƙaunarsu kana yace.
“Toh kuci abinci”.
Girgiza masa kai sukayi kana atare suka ce.
“A'a Abba sai mun dawo daga masallaci”.
Kai ya gyaɗa musu kana suka miƙe atare suka tafi masallaci suka idar da sallah bayan sun dawo M Jameek ya ɗebi Pride rice Kaɗan da tsokokin kaza. Modibbo kuwa kindirmon da aka dama ya ɗiba a Cup Abba kuwa chicken peper da pride rice shima ya ɗebi yana ci.
Fara cinsu babu daɗewa aka turo ƙofar aka shigo Idanun Hajiya Karima bai sauƙa ko ina ba sai kan Moddibo dake riƙe da kofin kindirmon kana da plate ɗin da Abba ya sa mishi pepper chicken and vegetables da fork a samansu.

Cike da tsanarsa ta watsa masa wani wulaƙantaccen kallo kana tace.
“Toh acire tsatsan haƙori anan, kaska raɓi mai jini wato ko zuwa shi kaɗai ya samu ya keɓe da mahaifinsa ba za'a bari ya samu damar hakan ba ko?
Oh ni Kareeme tunda nake a duniya ni dai ban taɓa ganin mutum mai shegen nacin tsiya irin kaba, sam baka da godiyar Allah ba zaka tsaya amatsayin ka ba shin kai wani irin Jarabebben mutum ne Aliyu?!”.
Cikin wani irin fushi da ɓacin rai Abba ya mike ahasale ya dubeta kana yace.
“Hajiya Karima mai kikeyi haka ne?
Wai meyasa ne ke baki da hankali ne? kinsan abinda kike faɗa kuwa!”.

Fuska ta ɓata kana tace.
“Toh Alhaji gaskiyane ya barka kaida ɗan ka kuhuta mana kuyi shawara acikin sirri”.
Afusace Abba ya katseta tare da faɗin.
“Me kike nufi shiɗin ba Uwa da Ubane suka haifeshi ba shima ɗana ne”.
Sheƙeƙe Hajiya Karima ke Kallonsa kafin cike da Isgilanci ta kallesa kana tace.
“Yaushe ka haifesa bamu da labari?,yaushe ka auri uwarsa har ka haifesa bamu sani ba?”.
Cikin tsananin fushi Abba yace.
“Kifita anan ki fita Karima bana son ganinki tun da ke kince baki da ɗa'a baki iya Mu'amala da mutane arayuwarki ta duniya ba, bana son haka, Bana son haka kar ki sake yin haka na yi miki kashedi na ƙarshe wannan shine last warning Hajiya Karima!, Kada ki sake yimin haka.
Domin kuwa koda Mahaukaci Jameel ya ɗauko ya kawo wannan gidan wallahi yafi min ke daraja, saboda nasan koda mahaukacine Jameel zai nuna masa cewa ni mahaifinsa ne kuma na tabbata zai mutunta ni”.
Cikin fushi ya sauƙe ajiyar zuciya tare da furzar da Iska kana ya cigaba da cewa.
“Na tabbata ko Mahaukaci Jameel ya kawo gidan nan zai mutuntani, kuma zai ɗauke ni da daraja fiye da yanda ke ki ɗaukeni ban isa da keba, misali ga yadda idan na baki umarni kike fatali dashi, ba zakiyi amfani dashi ba.
Dan haka ko kin san Jameel ya fimin komai.
Jameel da kike gani shine Komai nawa a Duniya akan farin cikin Jameel ina iya yin komai dan haka tun wurima ki kiyayeni!
Kifita idona in rufe Hajiya Karima!!.
Ki kiyayeni kada inci miki mutunci!!!”.
Ya ida mgnar tare da buga jikin kujerar dining ɗin kana yaci gaba da cewa.
“Na tabbata kare idan Jameel zai kawo gidan nan sai yamin biyayya fiye da yanda ke kike min biyayya. Kare dai nasan idan Jameel zai kawo min gidan nan bazai tsaya yamin irin haushin da kike min ba!”.
Sai kuma ya watsa mata Kallon mai cike da fushi kana yace.
“Kare idan Jameel zai kawo gidan nan kare mai ɗa'a da biyayya zai kawo min ba karen da zai kunya ta min baƙi na ba amma ke kullum baki da hankali. idan Jameel ɗan kine da kika haifa acikin ki zaki yi masa haka ne?”.
Kasa cewa komai Hajiya Karima tayi sai huci da take tamkar zakanya.

M Jameel kuwa ƙasa yayi da kansa cike da jin daɗi karo na farko kenan da mahaifinsa ya burgesa a kanta daya buɗewa Hajiya Karima wuta akan abinda ta keyiwa Moddibo domin kullum idan ta wulaƙanta Moddibo sai sunbar gidan kafin yake mata faɗa akan ta daina, amma yau yaji daɗin faɗan da Abba yayi mata agaban Idon Moddibo saboda Moddibo zaiji daɗi sannan zai san cewa yana da daraja da kuma kima awajensu.
Moddibo kuwa kansa ya sunkuyar ƙasa da cike kunya sam baiji daɗin ɓatawan mata da Miji adalilinsa ba, yayi dana sanin zuwa gidan, yasan cewa duk lokacin da yazo gidan sai yayi sanadin da za'a samu hatsaniya, sannan ya riga daya sani tun yana yaro matar nan bata sonshi bata ƙaunar ganinsa da Jameel sai dai ya fahimci ba wai shi ta tsana ba tana fakewa da guzma ne ta harbi karsana.
Cikin sanyi murya ya ɗago kansa tare da furzar da iska mai zafi kana yace.
“Abba kayi haƙuri dan Allah dan darajar Annabi”.
Juyawa Abba yayi ya kallesa kana ya ɗaga masa hannu da faɗin.
“Yi shiru ba maganar ka Aliyu barni da ita haka take yimin, ba kai kaɗai ba, duk baƙon da Jameel zai kawo gidan nan sai taci masa zarafi, duk mutumin da zata gansa da Jameel saita nuna min ba mutumin kirki bane!”.
Sai kuma ya juyo Afusace tare da kallonta har zuwa lokacin tana tsaye cike da ɓacin rai ya tsira mata idanu kana yace.
“Mai Jameel ya tsare miki?, Jameel tun tasowar yana ƙarami biyayya yake miki bai taba Musa Miki ba duk da kinzo kin samu yana da shekara goma sha huɗu na tabbata baki yiwa Jameel wahala ba amma yana karramaki sannan yana mutuntaki kamar yanda yake mutunta mahaifiyarsa”.
Zazzafan iska ya furzar kana still muryarsa cike da ɓacin rai yace.
“Amma ke kullum baki da buri daya wuce kici masa zarafi, Idan kin zauna ki riƙa faɗa mun magana kinyi zaton cewa bana son Jameel ne?.
Shin inada wani ɗa aduniya daya wuce Jameel ne?”.

Cikin tsananin fushi da ɓacin rai Hajiya Karima ta nuna kanta kana tace.
“Ni ka ciwa zarafi akan yaro ɗan maƙota dan yana abokin ɗan ka, sannan dan na faɗa maka gaskiya, kai baka ga yadda yake liƙewa ɗan nakaba duk ya hana sa tattalin arziki sannan ya hanasa ya tara abin kansa”.
Cikin wata fusatacciyar tsawa daya amsa ilahirin falon yace.
“Ki fice min anan Karima bana son ganinki”.
Afusace ta juya kamar zata tashi sama tana wani irin huci tare da jin tsanar Moddibo da M Jameel fiye da komai arayuwarta!.

Anutse Abba ya juya ya kalli Moddibo kana cikin sanyi murya yace.
“Dan Allah Aliyu kayi haƙuri kada ka damu da abinda tayi maka, sannan bance ka ɗauki wannan amatsayin wani mataki da zai hana ka zuwa gidan nan ba, aduk sanda kaga dama zaka zo”.
Murmushi yayi kana yace.
“Babu komai Abba ai ita mahaifiya ce agurin mu dan tayi mana haka ba zai zama wani aibu ba”.
Jinjina kai Abba yayi tare da cewa Ubangiji Allah ya al'barkaci rayuwarku”.
Atare suka amsa da.
“Ameen”.
Juyawa M Jameel yayi tare da kallon Moddibo Cikin sanyin murya mai cike da so da shaƙuwa ya numfasa kana yace.
“Dan Allah A.J kayi haƙuri”.
Murmushi Moddibo yayi kana yace.
“Laa babu Komai J. Yanzu dai tashi muje mu bata haƙuri”.
Chapter 62 · 0% Book details