← Book details Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 114

Sashe 89

Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Acan ɓangaren Ummi kuwa zaune take a falonta kan kujera 3sitter tayi ta tagumi da duka hannunta biyu, kana ta tsirawa waje ɗaya Idanu yayin da ƙirjinta ke bugawa da masifar ƙarfi zuciyarta na tsinkewa yana bada sautin dif-dif-dif lokaci ɗaya taji wata muguwar kasala na rufe mata jiki haka nan take jin zuciyarta na tsinkewa.
Jiki a mace Asma'u ta fito daga kichen hannunta riƙe da Plate ƙara sawa falon tayi Idanunta akan Ummi data zabga tagumi ta zauna akan 1sitter tare da cewa.
“Ummi har yanzu baki kwanta ba?”.
Ajiyar zuciya Ummi ta sauƙe tare da fesar da numfashi kana ta gyaɗa mata kai tare da cewa.
“Eh Asma'u ban kwanta ba”.
Cike da kulawa Asma'u ta ɗaga kanta tare da kalli agogo, tare da cewa.
“Ummi kalli fa har sha ɗaya ta wuce me kikeyi afalo ke kaɗai shiru ga Abban mu yashiga tun ɗazu”.
Lumshe Idanu Ummi tayi still zuciyarta na tsinkewa kana tace.
“Babu”.
Numfashi Asma'u ta fesar tare da ajiye cokalin dake hannunta tace.
“Toh Ummi ko dai baki da lafiya ne?”.
Kallonta Ummi tayi tare da girgiza kai.
“Lafiyata ƙalau Asma'u”.

“Ayyah Ummi am to mai yasa baki kwanta ba kin zauna shiru ke kaɗai dubi yanda kika yi tagumi da hannu duka bibbiyu”.
Cewar Asma'u.

“Ban sani ba Asma'u ba wai bani da lafiya ba amma ina jin jikina wani iri bai min daɗi ba ina jin zuciyata na tsinkewa sannan ga wata kasala data rufe ni”.
Ido Asma'u ta zuba mata kamar mai son gane wani abu sai kuma tace.
“Toh Ummi ki riƙa maimaita Hasbunallahu wani'imal wakin mana kuma may be rashin bacci ne kinga jiya kwana mukayi muna hira ba kisamu kinyi wadataccen bacci ba, sannan yau da safe ma baki samu kinyi wani ishesshen bacci ba”.
Gyara riƙon da taiwa plate ɗin tayi kana taci gaba da cewa.
“Har yanzu ma baki samu kinyi Ummi, kiyi ƙoƙari kije ki kwanta Insha Allah zakiji dama dama”.
Kai Ummi ta jinjina tare da cewa.
“Toh ki maida Plate ɗin kichen idan kin gama sannan ki rufe ƙofar kichen ɗin kana kizo ki rufe mana ƙofan falon”.
Kai Asma'u ta gyaɗa tare da cewa.
“Toh”.
Ta mike tare da ajiye Plate din ta kife Sauran abincin sannan ta rufe ƙofar tare da murza mukulli ta dawo.
Still zaune ta samu Ummi tayi tagumi.
Cike da kulawa tace.
“Ummi kije ki kwanta dan Allah kiyi baccin”.
Ahankali Ummi ta ɗago ta kalleta tare da sauƙe ajiyar zuciya kana tace.
“Toh kije Insha Allah yanzu zan kwanta”.
Kai Asma'u ta gyaɗa kana ta wuce Bedroom ɗin ta Ummi kuwa kasa tashi tayi ahankali ta lumshe Idanunta tare da komawa ta kwanta akan kujeran still zuciyarta na cigaba da tsinkewa tana mai maimaita kalmar Hasbunallahu wani'imal wakin aƙasan ranta.

Acan ɓangaren Moddibo kuwa yana Picking call ɗin yakai kunnensa tare da cewa.
“Assalamu Alaikum”. cikin sanyin murya M Arɗo ya gyara zaman wayar akunnensa tare da cewa.
“Wai yanzu yaran nan tsakanin ku da Allah kun bar batun karantarwa Amakarantar nan kenan?”.
Anutse Moddibo ya lumshe Idanunsa kana ya buɗe su cikin yanayin kasala da tsinkewar zuciyar da yake ji ya gyara zamansa tare da cije lips ɗinsa na ƙasa yace.
“Toh ka asamsa Sallamar da nayi maka mana Before ka fara ƙorafi da zakayi”.
Girgiza kai Malam Arɗo yayi tare da cewa.
“Toh Wa'ailaikum salam kune ai baki ɗaya kuke son caza min kai, baki ɗaya satin nan yashiga har ya fita amma baku zoba toh gashi yau jumma'a gobe Asabar za akoma shiyasa nace bari na kira ku kada ace baku zoba”.
Iska mai zafi Moddibo ya fesar daga bakinsa tare da shafa sajensa kana ya lumshe idanunsa tare da cewa.
“Gaskiya baza mu zoba”.
Asanyaye Malam Arɗo yace.
“Toh meyesa”.
Muskutawa Moddibo yayi tare da gyara zaman wayar akunnensa kana yace.
“Ai mun riga da mun gama yi maka magana kayi haƙuri kawai ”.

“Amma kunsan ina son koyar wanku Amakarantar nan ina jin dadin zama daku sannan ɗaliban ma suna jin daɗin koyarwanku, makaranta na ya cigaba adalilin kune kada kuyi min haka”.

“Malam kayi haƙuri da akwai Uzurin da yake gaban mu, wanda yafi wannan na tabbata badan wannan Uzurin ba babu dalilin da zaisa mubar koyar wa Amakarantar”.
Cikin sanyi murya Malam Arɗo ya sauƙe Ajiyar zuciya kana yace.
“Toh shikenan tunda abin ya zama haka dole in sawa zuciyata haƙuri amma kusa marmin wasu Malamai masu Hazaƙa, duk da nasan da wuya asamu kamar ku tabbas nasan nayi rashin zaƙaƙuran Malamai kamar ku”.
Kai Moddibo ya gyaɗa kana cikin sanyin murya yace.
“Toh ba matsala zamu yi kokarin hakan”.
Cikin sanyi Malam Arɗo yace.
“Toh Nagode saida safe”.
kana ya katse wayar.
Moddibo kuwa cikin sauri zuciyarsa ya cigaba da bugawa yana bada sautin dif-dab-dif-daf ahankali ya ɗago wayar da niyyar kiran M Jameel cikin wani Irin yanayi ya dafe saitin ƙahon zuciyarsa jin yanda yake bugawa da azabebben ƙarfi yana cigaba da bada sautin dif-dif-dif rintse idanunsa yayi still hannunsa na dafe da saitin ƙahon zuciyarsa.

Acan ɓangaren Gimbiya Bunayya kuwa har Misalin ƙarfe sha biyu da minti biyu na dare Uncle Naseer da Amina na zaune akan 2sitter suna hira.
Yayin da ita kuma ke kwance a Bedroom ɗin ta kunneta maƙale da waya tana Magana da Hajiya Lami.
Murmushi Hajiya Bunayya tayi tare da cewa.
“Hajiya Lami ni dai yanzu Alhamdulillah buƙata ta biya hankalina ya kwanta, yanzu batun soyayyar Amina da Naseer ya kankama yayi zurfi”.
Atake fara'ar dake fuskanta ya gushe ta mike ta zauna tare da cewa.
“Yanzu kuma hankalina ya koma kan ƴaƴan wannan shegiyar matar mai kama da Mayyar wannan yaro mai ƙwala-ƙwalan ido daya karye nake son kawar dashi tun da shi wancan mai kama da Brolas ɗin Uwarsa ta shayar dashi saɓani, tunda kinga wannan hatsarin ma shi na shiryawa abi takansa amma, ba'a samu babban ba akabi takan ƙaramin”.
Sai kuma ta sauƙe numfashi tare da jan dogon tsaki kana tace.
“Dole saina koma na samu boka Kar'uzu da maganar ayi duk abinda za ayi nikam Haiydar shine babban matsala ta tunda shi Ramadan shine ƙarami akan Aminu, babu yanda za ayi Aminu na raye aɗauki Sarauta abawa Ramadan dole dai sai ɗana ɗin dai”.
Cikin sauri Hajiya Lami ta katseta tare da cewa.
“Kul-Kul Hajiya Bunayya kada kiyi la'akari da wannan ƙaramin tunanin naki, ba kiji Malam Bahaushe na cewa ɗan hakin daka raina shike tsole maka Ido ba?.
To ki rufa wa kanki asiri ki kawar dasu duka biyun hankalinki ya kwanta ki samu nutsuwa da salama aranki”.
Kana ta saki wani murmushi tare da cewa.
“Kinga idan kika gama dasu ɗaya ce zaki samu nutsuwa akanta itace Raudat da kuma Khausar.
Kinga Khausar kuwa ba ƴar gidan bace babu yanda za ayi agola tavi gadon Sarauta koda na mijine bare kuma mace. Raudat kuwa ƙarama ce kuma mace.
Amman Haiydar da Ramadan dai kaudasu, da kike batun Ramadan shine ƙarami a kan sulaiman, sau nawa manyan Yayu ke zaune ake bawa ƙannen su Sarautar, ni dai shawarar da zan baki yanda zaki gama da Haiydar haka zaki gama da Ramadan”.
Jinjina kai Hajiya Bunayya tayi tare da gyara zaman wayar akunnenta kana tace.
“Haka ne fa kuma aini duk wannan tunanin bai zo min ba, atunanina idan na kawar da Haiydar shikenan”.
Girgiza kai Hajiya Lami tayi tare da faɗin.
“A'a tsaya kallon ruwa kwaɗo ya miki ƙafa, har kina wani batun shine ƙaramin akan Aminu ai ba'a wannan zancen kima rufawa kanki asiri, kigama dasu gaba ɗaya to asannan hankalin zai kwanta, ki samu nutsuwa anan ne zaki tabbatar sarauta ahannun Aminu take, ke kuma kin zama Gimbiyar Gembulan Matar sarki Uwar sarki amma muddin ƴaƴan wancan koɗaɗɗiyar matar na nan keda Saurauta saidai hange daga naisa”.
Jinjina kai Hajiya Bunayya tayi cike da gamsuwa kana tace.
“Aikuwa hakane Nifa duk wannan tunanin bai zomin ba shiyasa nake alfahari dake ƙawata.
Insha Allah zanje muyi magana da boka Kar'uzu asan yanda za'a ɓullowa lamarin”.
Kai Hajiya Lami ta gyaɗa tare da cewa.
“Eh nima Insha Allah gobe idan muka je zan faɗa masa ya tsaida rana da Samira zata fara zuwa wajensa suyi satin, tunda dai yace idan ya kusance tama zai mayar mata da budurcinta ai shikenan”.
Atare suka sheƙe da dariyamai cike da farin ciki da annushawa kana Hajiya Bunayya tace.
“Ai dai haka yafi shiyasa na yarda da aikin Boka Kar'uzu kamar yankan wuƙa dan sha yanzu magani yanzu ne tun yaushe muke bin boka bursunu tsawon shekaru ba biyan buƙata sai asaran kuɗi”.
Jinjina kai Hajiya Lami tayi kana tayi mata Sallama suka katse wayar.
Chapter 89 · 0% Book details