← Book details Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 114

Sashe 63

Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri Abba ya kalli Moddibo kana yace.
“Baza ku bata haƙuri ba ku zauna kuci abinci”.
Kai suka gyaɗa sannan suka zauna baki ɗayansu, basu wani ci abincin kirki ba, domin ko kowa da irin damuwar dake ransa, bayan sun kammala suka miƙe tare da yiwa Abba Sallama haƙuri Abba ya sake bawa Moddibo.
Murmushi Moddibo yayi kansa aƙasa yace.
“Ayyah Abba Allah babu komai”.
Sannan suka juya har sun kai ƙofa Abba ya ɗan ɗaga sautin muryansa tare da cewa.
“Yau kam ba zamu kwana anan bane?”.
Girgiza kai Moddibo yayi kana yace.
“A'a Abba idan mun kwana anan Innayi ita kaɗai zamu bari acan”.
Jinjina kai Abba yayi kana yace.
“Eh kam ya kamata gida babu namiji ba gida bane kuje”.
Godiya suka masa kana suka fice.
Suna cikin mota aka kira Isha'i kai tsaye masallacin da suke limancin suka nufa kamar ko yaushe Moddibo ne yaja Sallar bayan sun idar sukayi Asham kana suka wuce gida.

Suna shiga gida kai tsaye sashen Innayi suka nufa zaune suka sameta riƙe da carbi ahannun Asma'u kuma tana riƙe da Alkur'ani mai girma tana karatu.
Batare da sun ƙarasa shiga ba Moddibo yace.
“Innayi Barka da shan ruwa”.
Anutse ta kallesa kana tace.
“Yawwa yau ina kuka tsaya ne baku dawo da wuri ba, nace Asma'u ta kira min ku inji kuma ashe wayar ba kati”.
Murmushi M Jameel Yayi kana yace.
“Ayya Innayi Abba ne ya kiramu wai muje mu sha ruwa acan shiyasa kika jimu shiru”.
Kai ta jinjina tare da kallon Moddibo tace.
“Fatan duk suna lafiya?”.
Kai Moddibo ya gyaɗa mata kana ya sake labulen tare da faɗin.
“Innayi akawo mana abinci”.
Ya ida mgnar tare da zama akan shimfiɗar dake barandar Asma'u Innayi ta ƙalla kana tace.
“Ɗauki abincin ki kai musu”.
Kai Asma'u ta gyaɗa sannan ta ɗauki lemun tsani ta yanka ta matsa kaɗan akai kana tayi slinzing ɗin ƙwoyi kana ta zuba musu wadataccen man gyaɗa da kuma dakekken yajin barkono sai Cucumber da Cabbage ta Kai musu.
Sosai suka Moddibo da M Jameel suka ci ɗan waken tare da 5alive, bayan sun kammala kai tsaye ɗakinsu suka wuce tare da watsa ruwa, kana suka sake shiryawa tare da feshe jikinsu da turaraku masu daɗin ƙamshi.
Cikin nutsuwa suka fito aharabar gidan suka samu Innayi da Asma'u sun fito buɗe bayan motor sukayi suka shiga sannan Moddibo ya shiga mazaunin Driver yayin da M Jameel yashiga gefen mai zaman banza, kai tsaye masallacin suka nufa har suka isa ƙira'a na tashi amotar suna parking Innayi da Asma'u suka shiga sashen mata suka ma suka ƙara sa sashen su.

Yau ma kamar kullum gaba ɗaya cikin masallacin da harabar sa cike yake da ɗumbin jama'a cikin tsantsar nutsuwar daya zame musu jiki suka nufi wajen zamansu cikin sanyi mai cike da kamala da kuma kamun kai Moddibo ya ajiye System ɗin sa kana ya zauna tare da ɗan jingina bayansa da jikin kujeran ya lumshe Idanunsa tare da motsa laɓɓansa alamar tasbihi Shikuwa M Jameel zaman microphone da aka dasa masa ya gyara tare da buɗe System ɗin sa Lokaci ɗaya cikin masallacin ya gauraye da ƙamshin sanyayyan turaren su yayin da hasken Fararen glob ɗin ya haskaka hasken farin fuskarsu na fitar da sheƙin annuri yayin da baƙin sajensu ya kwanta luf-luf komai nasu kusan ɗaya yake tamkar tagwaye.

Cikin nutsuwa M Jameel ya lumshe Idanunsa tare da gyara zaman Microphone kana Yayi gyaran murya cikin Sanyayyar muryarsa mai cike da kamala yayi gyaran murya kana yace.
_“Innalhamdulillah Nahmaduhu Wanastainuhu wanastaghfiru wa'nazubillahi billahi min shuriri anfusna wamin sayyi ati a'amalina manyah dillahu fala hadiyala waman yudil fala mudillalah Wa'ash hadu Allah ilahalillahu wahdahu lasharika Wa'ash hadu anna Muhammadu Abduhu warasulu Ya Ayyuhal lazina amanut taƙullaha haƙƙu tuƙatihi wala tamu tunna illah wa'antum muslimun Ya ayyuhan nasu taƙu rabbakummalazi halaƙakum min nafsi wahida wahalaƙa minha zaujuha wabassa min huma rijalan kasiran wa Nisa'a wattaƙullahal lazi tasa aluna bihi wal arhama innalaha kana bikum raƙiba, Amma ba'ad faya Ikhwatul musulmi Assalamu alaikum warahmatullah wabarkatuhu”_.

A tare jama'ar dake cikin masallacin suka amsa da.
“Wa'alaikum Salam warahmatullah wabarkatuhu”.
A hankali M Jameel ya fesar da sassayan numfashi tare da lumshe idanunsa kana a hankali yace.
“A yau muna sha huɗu ga watan Ramadan a cigaba da tafsirin Alkur'ani mai girma da muke acikin masallacin mai Martaba sarki Bashiru acikin Suratu An-Nisa'i ayau zamu tashi akan aya ta Cassa'in da huɗu wala Allah kuma bazai wuce da biyar zamu tsaya ba, sai kuma shekara mai zuwa idan Allah ya bamu aron rai da lfyar”.
Sai kuma ya sauƙe numfashi kana ya cigaba da cewa.
“Tun daga kan aya na cassa'in da biyu muka shiga babi akan kashe ran mumini, da kuma hakkin ran Muminai, ayau Insha Allah zamu cigaba, amman kafin nan zamuyi duba i zuwa kan dukkan ayoyin Alkur'ani dake mgna kan ran muminai”.
A hankali ya buɗe kwayar idanunsa, sabida jin yadda masallacin ya cika da kabbara.
Gyara system ɗinshi yayi kana yace.
“Insha Allah ayau Aramma zai zaƙulo mana Ayoyin da Ubangiji yayi magana akan hakkin kashe ran mumini, domin tunatar wa da kuma jan hankali da kuma fito da darajar ran ɗan Adam Dan kiyaye lalacewar zamani da kuma tunatar da hakkin ran musulmi amatsayin ba komai ba”.
Cikin yanayin kamala ya juya tare da maida kallonsa kan Modibbo da idanunsa ke lumshe ajiyar zuciya sauƙe kana yace.
“Aramma bamu ayoyin da Ubangiji yayi magana akan kashe ran mumini”.
Anutse Moddibo ya gyara zamansa tare da ɗan ture system ɗin sa gefe kana yayi gyaran murya cikin sanyayyar sautin muryarsa ya fara kamar haka.
Surah Al-ma'idah Aya 32
مِنْ أَجْلِ ذَٰلِكَ كَتَبْنَا عَلَىٰ بَنِي إِسْرَائِيلَ أَنَّهُ مَن قَتَلَ نَفْسًا بِغَيْرِ نَفْسٍ أَوْ فَسَادٍ فِي الْأَرْضِ فَكَأَنَّمَا قَتَلَ النَّاسَ جَمِيعًا
Ya ƙare jan karshen ayar da fesar numfashinsa da ya riƙe domin fidda cikekken haƙin ko wanne harafi,
Yayin da Al'ummar Annabi dake cike a masallacin kuwa, sukayi sit suna masu samun cikekkiyar nitsuwa ta mu'ijizan jin karatun Alqur'ani mai girma kenan.
M Jameel kuwa cike da raunin murya ya fara fassara ayar Allah madaukakin sarki nacewa-:
“Sakamakon haka ne muka wajabta akan 'ya'yan Isara'ila cewa, duk wanda ya kashe wata Rai ba tare da ita Rai ɗin ta kashe wata ba, ko kuma yayi ɓarna a kan ƙasa (ta'addanci, Fashi da makami etc) toh kamar ya kashe mutane ne gaba ɗaya na Duniya kuma ubangiji zai hukunta shi dai-dai da laifinsa”.
Shiru masallacin yayi baki ɗaya, kowa jiki nai a mace, yayinda manyan dottaɓai dake ciki kuwa, suka zuba M Jameel da Modibbo ido suna nazartan yadda akayi akalar tasirin ya sauya daga kan Suratu An-Nisa'i ya koma kan duk ayar da ke mgn kan kisan kai.
Shi kuwa M Jameel juyowa yayi ya kalli Modibbo tare cewa.
Aramma koma cikin suratul Al-ma'idah akwai ayar da Allah ke mgn kan rayuka”.
Cike da ƙwarewa da cikekkiyar hadda mai ɗauke da kaifin basira, Modibbo ya lumshe idanunsa da yakeji suna cika da rauni cike da zaƙin murya ƙira'a mai sa nitsuwa ya kawo ayar
Surah Al-ma'idah Aya 33 إِنَّمَا جَزَاءُ الَّذِينَ يُحَارِبُونَ اللَّهَ وَرَسُولَهُ وَيَسْعَوْنَ فِي الْأَرْضِ فَسَادًا أَن يُقَتَّلُوا أَوْ يُصَلَّبُوا أَوْ تُقَطَّعَ أَيْدِيهِمْ وَأَرْجُلُهُم مِّنْ خِلَافٍ أَوْ يُنفَوْا مِنَ الْأَرْضِ.
Cike da nitsuwa ya dire ƙarshen ayar,
M Jameel kuwa gyara zamansa yayi tare da fara fashin baƙin.
“Allah madaukakin sarki nacewa-:
Lallai sakamakon waɗanda suke yaƙar Allah da Manzo nai, kuma suke yaɗa ɓarna a doron ƙasa (ta'addanci, Fashi, ƙwamushe Garkuwa Da mutane etc), shine a kashe su, ko a giciye su”.
Sai kuma ya fesar da sassayan numfashi tare da lumshe idanunsa wanda tuni suke sheƙin ruwan hawaye, murya cike da rauni yaci gaba da cewa.
“Ko a yanke Hannayen su da Ƙafafuwan su a saɓani (hannun hagu da ƙafar dama, ko kuma Hannun dama da ƙafar Hagu), ko kuma a kore su daga Garin.”.
Zuwa yanzu shar-shar hawayensa ke kwaranya yayinda tuni muryarsa ke rawa, haka yasa da yawa mutanen suke zubda hawaye.
Haka dai Modibbo ya rinƙa zaƙulo dukkan ayoyin Alkur'ani dake mgna kan ran mumini, M Jameel na fassarawa, yayinda gaba ɗaya zuƙata jama'ar masallacin ya cika da rauni.
Kasan cewar gobe ne, Modibbo da M Jameel ɗin zasu wuce ƙasa mai tsarki, damin yin Umrah Ramadan, yasa dole a ranar aka rufe tafsir ɗin. Bayan jero Addu'o'in wa al'ummar musulmi dama kasa baki ɗaya.

Washe gari ranar 15 ga watan Ramadan misalin ƙarfe tara na dara dai jirgi su Modibbo ya tashi daga cikin Taraba zuwa ƙasa mai tsarki...!

Daga yauwa ɗin nan Laraba mun gama free page, in kina son ci gaban littafin SAKAYYAH to ki biya ki karanta cikin aminci. Littafin SAKAYYAH 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA, sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276. Ki biya ki karanta ba haƙƙin kowa a kanki.

By
*GARKUWAR MARUBUTA*
[19/07, 8:57 PM] Halimatu A/rahman Sadeeya: 📝✨💫⏰🤴🏻👹❤️❤️❤️🍇

*SAKAYYAH*
_Page 17_
*LAST FREE PAGE*
_NA_
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*DAGA WANNAN PAGE ƊIN FREE PAGES SUN ƘARE, IN MA KIN SAKE GANIN LITTAFIN SAKAYYAH A WAJE TO. NA SATANE NA ALLAH YA ISA ne, littafin SAKAYYAH 1k ne kacal yar ki biya ki karanta cikin Aminci da salama babu haƙƙin kowa kanki 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276 kiyiwa da Annabi in dai kin san kin sayane don ki fitarmin da littafin na kiyi min mgn in mayar miki da kuɗinki. In kuma kin san zaki sayane dan ki fidda min littafina, wasu Groups ɗin, kiyiwa Allah da Manzonsa ki bar kuɗinki na yafe cinikin bana buƙatar sa*
Chapter 63 · 0% Book details