← Book details Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 114

Sashe 58

Sakayyah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Juyiwa Mommy tayi jin motsi abayan ta ganin Khausar yasa ta maida hankalinta kan aikinta kana tace.
“Kin dawo?”.
Kai Khausar ta gyaɗa tana kallon tuƙeƙken tuwon shinkafa da Mommy ke kwashe maran ƙarshe.
Ahankali Khausar ta matsa kusa da Mommy kana tace.
“Mommy ki bari zanyi miyar”.
Kai Mommy ta gyaɗa kana tace.
“Ok to Miyar zogala za kiyi”.
Kai Khausar ta gyaɗa tare da ɗaukar.
Da fara aikin haɗa miyar zogalen.
Cikin abinda bai gaza awa ɗaya da rabi ba, duk ta haɗa ta sanya komai na buƙata kana.
Ta rufe nan danan kichen ɗin ya kaure da ƙamshin miyar sauran kayan da Mommy tayi amfani dasu ta haɗa ta wanke tare da sauƙe Miyar ganin tayi tik gwanin kyau.

Bayan ta gama ta buɗe miyar da yayi mugun kyau a ido ta ɗauki kular wani sashe ta zuba miya kasancewar babban gidana yasa kowa kaina nasa akeyi, na buɗa baki kuwa ki wacce a side ɗinta takeyi, mai girki zata sawa Lamiɗo, da Dadu, haka tsarin nasu yake.
Shigo wa Mommy tayi fuskarta ɗauke da murmushi ta kalli yanda kichen ɗin yayi fess ga ƙamshin miyar zogalan da yaki kifi da naman dariko, kallonta ta mayar kan Khausar kana tace.
“Sannu da ƙoƙari ki ɗauki na sashen Hajiya Bunayya ki kai mata”.
Kai Khausar ta gyaɗa sannan ta ɗauka kular Hajiya Bunayya ta wuce Haidar Mommy ta ƙwalawa kira bayan yazo tace ya ɗauki kular sashen Gimbiya Dadu ya kaimata dan Mommy tunda ta lura da Khausar batason zuwa yasa ta rage aikanta sashen shi kuwa Haiydar daga sashen Gimbiya Dadu ya wuce sashen Hajiya Bunayya.

Hajiya Bunayya dake zaune akan kujera ta faɗaɗa fara'ar fuskarta ganin Haiydar ta tsira masa idanu kana tace.
“Babana kaine dama yanzu nake niyyan zuwa in yi maka albishir”.
Murmushi Haidar yayi tare da zama kana yace.
“Daga sashen Gimbiya Dadu nake nace bari nazo na gaishe ki”.
Murmushi tayi masu cike da Ma'anoni tayi kana tace.
“Insha Allah bayan sallah mashin ɗinka zai zo kaga dama tun shekara biyu baya naso saya maka Abbanka yace saika ƙara girma kuma kaga yanzu aika girma”.
Jinjina kai Haidar yayi cike da tsananin farin ciki mara mistuwa ya gyara zamansa kana yace.
“Nagode Ummah Allah yarabaki da sharrin maƙiya”.
Murmushin gefen baki tayi kana tace.
“Bana son godiyar nan Babana”.

Cike da farin ciki ya miƙe ya nufi sashen su fuskarsa ɗauke da murmushi ya shiga falon zaune ya samu Mommy da Khausar.
Kallonsa Mommy tayi kana tace.
“Ina ka tsaya?”.
Zama yayi daga gefen Khausar still.
Fuskarsa da murmushi da yakasa ɓoyewa ya numfasa tare da cewa.
“Mommy Machine ɗina ya Kusa isowa fa, kinga tun shekara biyu baya Umma taso siya min shine Abba ya hanata yace saina ƙara girma ai yanzu kam dai na sake girma bazai hana ba ta saya min Machine sabo mai kyau bayan sallah zai iso”.

Khausar kuwa tunda ya fara magana ta tsira masa idanu saida ya kai aya ta sauƙe ajiyar zuciya mai zafi tare da furzar da iska daga bakinta kana babu walwala afuskarta ta kawar da kanta gefe tare da cewa.
“Kai kuma farin ciki kake ko?”.
Juyawa Haiydar yayi tare da kallon ta kana yace.
“Sosai ma kuwa kema kamata yayi kije kiyi mata godiya”.
Harara Khausar ta ɓalla masa.
Murmushi Mommy tayi kana tace.
“Rabu da ita ai ni zanje.
A yanzu kam aika girma yanda kake da tsawon ƙafan nan”.

Murmushi yayi tare da kallon Khausar kana yace.
“Sosai ma Mommy ai yanzu na girma yanzu fa shekara kusan sha shida nake nema gashi mai shekara sha takwas ɗinma na fita koda yake sha bakwai ne da yan watanni ne ko gareta”.

Jinjina kai Mommy tayi kana tace.
“Ai lallai dai kam kama cika sha shida kam Allah yasa kafara hawa asa'a.
Ubangiji ya tsareka da sharrin ƙarfe.
Allah yatsare gabanka da bayanka!.
Ubangiji ya makantar da idanun makiyan ka akanka!.
Allah ya tsare ku ga duk kan abinda zai cutar da rayuwar ku! Allah ya muku katangan ƙarfe da dukkan abin da zai zama sharri acikin rayuwarku!”.
Cike da jin daɗin Addu'ar ta Haiydar yayi Murmushi tare da cewa.
“Ameen ya hayyu ya ƙayyum Mommy na”.
Ajiyar zuciya Khausar ta sauƙe tare da kallon Mommy kana tace.
“Ameen ya Allah Mommy tunda kinyi addu'a magana ta ƙare baza'a ji tsoron komai ba babu bakin uwa akansu duk kan mai sharri zaiyi ya gama babu abinda zai sameshi da izinin Ubangiji”.

Murmushi Haiydar yayi tare da kallon Khausar kana yace.
“Aikam Addah Khausy babu bakin uwa akaina duk kan wani mai mugun nufi zai ƙare akansa”.
Murmushi Mommy tayi cike da ƙaunar ƴaƴan nata,
kallon ta ta mayar kansu tare da cewa.
“Ku tashi kuje kuyi bacci dan mu samu mu farka da wuri mu kaiwa Ubangiji bukatun mu”.
Miƙewa sukayi tare da yiwa juyawa sai da safe kana kowa ya wuce ɗakinsa ya kwantar.

Misalin ƙarfe ɗaya na dare Mommy ta farka kallon Lamiɗo daya miƙe yashiga toilet tayi sai kuma ta miƙe ahankali ta tafi side ɗinta.
ɗakin Khausar tashiga tare da kunna haske.
Idanunta suka sauƙa akan Khausar dake sharan bacci ƙara sawa tayi tare da bubbuga ƙafarta kana tace.
“Khausar ki tashi kiyi nafilla”.
Ahankali Khausar ta buɗe Idanunta cikin Muryan bacci ta kalli Mommy kana ta yunƙura ta zaune bakinta ɗauke da addu'a tace.
“Toh Mommy”,Sannan ta Sauƙa ta shiga toilet.

Juyawa Mommy tayi ta koma ɗakin Lamiɗo lokacin data shiga har ya fara Sallah kai tsaye toilet ta shiga ta ɗaura Al'wala bayan tayi ta fito tare da shimfiɗa Sallaya ta tada Sallah cikin nutsuwa ta keyi bayan tayi sujja tayi Subhana Rabbiyal a'ala³ kana ɗaura da du'inta.
“Ya Allah kayuwa ƴata zaɓin alkhairi,Ya Allah kashirya Khausar kasata ahanya madaidaiciya Ya hayyu ya ƙayyum ka tsare mata imaninta, Ya Allah ka kare min Haiydar ɗina ya Allah katsaresa daga sharrin mai sharri ya Allah ka kare min ita ya Allah kabawa Ramadan da Raudat ilimi mai albarka da yayunsu dama dukkan ƴaƴan musulmai. Ya Allah katsare min ƴaƴana daga sharrin,Mutum, aljan da kuma ƙarfe, ya Allah katse min imanina Allah ka tsaremin zuciyoyinsu, ka tsaresu da sharrin hassada, ƙeta, munafurci, da ƙyashi ya Allah ka kare min mijina kabiya masa buƙatunsa na Alkhairi dama ɗauka cin al'ummar musulmai.
Bayan ta idar da nafillah ta ɗauki Alkur'ani ta shiga Muraja'a.

Khausar kuwa ƙarfe biyu da rabi bacci ya riƙa fisgarta akan Sallaya ta kwanta nan da nan bacci mai nauyi yayi nasarar ɗauke ta.
Can cikin baccinta ta fara wani mafarki mai cike da al'ajabi ganinta tayi.
Gata nan tsaye a wani ƙaton fili.
Baki ɗaya ilahirin filin ashare yake kuma , yashine malale a wurin iya ganinka sai wani irin haske mai masifar ƙyalli da ɗauke idon da ya cika wajen baki ɗaya, ahankali ta ɗaga kanta ta fuskanci gabas, da sauri ta rumtse idanunta gani wata ya fito ta gabar juyawa tayi taga yamma da sauri Still nan ya fito ta yamman sake juyawa kudu tayi still ta nan ma ya fito ahankali ta sake juyawa arewa, wani irin masifeffen karkarwa jikinta ya farayi, ganin tanan ma watan yafito duk kusurwa huɗu wata ya fito sai asannan ta lura da haskensa ne yake ɗauke mata ido.
Ahankali taga wani kyakkyawan.
Yaro fari ƙal agabanta yayinda gashin kansa ke kwance lib-lib, daga bayansa ta hango wani kyakkyawan mutum sai dai fuskarsa na kallon gefe hannunsa na kan yaron yana shafawa cikin wata.
Sanyayyar murya yake kallon yaron kana yace da ita.
“Wannan shine jininmu mahaɗinmu, wannan shine sanadin haɗayyarmu bugun zuƙatanmuuuhh”.
Ya ƙarasa jan kalmar cikin wata iriyar ƙasalalliyar murya mai cike da shauƙi.
Ita kuwa ƙoƙari take taga fuskar mutumin sai dai ta kasa sai iya fuskan kyankyawan yaron take iya kallo.
Dai-dai lokacin kuma ta buɗe Idanunta jin Muryan Mommy nacewa.
“Khausar, Khausar ki tashi zaki makara fa ƙarfe huɗu tayi bakiyi Sahur ba anjima kaɗan zaki fara ce mana kin fara jin wahalar azumi”, Ta faɗa tana buga ƙafarta da saurin Khausar ta tashi zaune tare da sakin ajiyar zuciya kana tace.
“Innslillahi wa'inna ilahi rajiu'n Hasbunallahu wani'imal wakin Astagfirullah wa'atubu ilaik”.
Sai kuma tayi addu'a ta shafa.
Mommy dake tsaye har yanzu kuwa sake taɓata tayu tare da cewa.
“Khausar kada ki koma bacci fa kitaso”.
Kai ta gyaɗa kana tace.
“Mommy na tashi bazan koma ba”.
Juyawa Mommy tayi ta fice ita kuma Khausar toilet ta shiga.
Brush tayi kana ta fito kai tsaye falon ta nufa.

Samu tayi Mommy ta haɗa mata ɗumamen tuwon jiya da Tea mai kauri ahankali ta zauna tare da kai tuwon bakinta da ƙyar ta haɗiye baki ɗaya jikinta yayi mugun sanyi da mafarkin da tayi.
Mommy dake zaune a kujeran falon ta juya ta kalleta ganin bata cin tuwon yasa ta girgiza kai tare da cewa.
“Kici abinci fa Khausar kin sanki sarai da cin abinci anjima kaɗan zaki fara cewa yunwa kike ji”.
Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da fesar da iskar bakinta kallon Mommy tayi kana cikin sanyin murya ta lumshe Idanunta tare da cewa.
“Mommy wallahi tuwon ne nakeji kamar ba zai shiga ba babu wani abu ne?”.
Kai Mommy data tsira mata Idanu ta gyaɗa kana tace.
“Kije kichen akwai indomie dana ɗaura wa Haiydar shima yace ba zai ci tuwo ba to amma ke kam nasan indomie ba wani riƙe Miki ciki yake yi ba”.

Lumshe Idanunta tayi kana ta buɗe su akan Mommy ahankali ta motsa laɓɓanta tare da cewa.
“Bari in cisa yau ɗin kam amma Mommy da kifi ne koda nama”.
Tayi tambayar ne domin bata fiye son kifi ba.
Chapter 58 · 0% Book details