Sashe 93
Rabo Ya Rantse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sha wajan Ammi a zamanta. Har Bakin gate mai napep in ya dire su Ya sallame shi ya shiga sauko Musu da kayan su Hohoho Masu gadi Ma'aikatan gida Ihu suka sa suna Wa Aliyu barka da zuwa dan basu da labarin Dalilin tafiyar shi sudai sun san sunyi Missing Uban gida nagari mai tausayi da Jin ai Kayan nasu Suka amsa suka Nufi Cikin Gida gaba aya Falon Ammi cike yake sabida yadda Jikin nata yau se a hankali ganin ana shigo da kaya yasa Bashir daya zo Shima daga abuja yake tambayar su na menene kafin ya rufe bakin sa Aliyu ya turo ofar falon hannunshi Ri e dana farha wadda da yar take taka afafunta. Ai Ammi dake kwance kanta yana saman Pillow tana hango Aliyu ta mi e a guje ta Nufesu su dukan ta ha e ta rungume seta fashe da kuka tana cewa. "Baba ina ka shiga baba da tuni na Mutu baka tare dani nayi nadamar abin da nai Muku fatima ki yafe Mini na tuba" Seta hau kuka wanda duk dauriyar Aliyu shima kukan ya saka farha ma Kukan take seda yar aka rarrashe su Suka araso falon Hannun Ammi cikin na Aliyu yau ciwo ya are Su sadi se farin Ciki Shikam Aliyu Yana ta kallon ammi duk ta rame tai duhu Se sannu take wa farha kamar zata mayar da farha cikinta wanda nan da nan tausayin Ammin ya rufe farha nan fa aka shiga mayar da zancen abin da ya faru bayan basa nan Cutar Ammi ta agawa Aliyu hankali se kallonta yake Yafiyar farha Ammi ta nema wadda tace ba Komai ai ita mahaifiyace a wajan ta sabida haka Komai ya wuce Har dare falon yana cike shidai Aliyu zamewa yayi ya tafi yayi wanka bai shigo ba se wajan taran dare Lokacin mutane sun ragu kowa ya kama gabansa farha tana can gadon Ammi tana baccin gajiya bayan tai wanka an bata sabbin kaya ta sanya. Ammi da kanta ta ha awa Aliyu abinci ranar ciwo ya are seda ya gama cin abincin sannan take sheda masa mami bata nan mahaifiyarta tazo ta tafi da ita sedai in ya huta yaje ya dawo da ita. Aliyu yayi Murmushin takaici. "Ammi kawai mami tai zamanta Na sake ta saki Biyu dan na kama mami da tarin laifuka kafin nabar Gidannan kona zauna da ita ma akwai zargi Sabida dumu dumu na kama ta da laifin Yun urin kasheki ta hanyar zuba Miki magani agirki Kuma ban tabbatar ba seda na kamata da manyan Hujjoji wanda ni ban san dalilin udirin hakan gare taba" Ammi ta share hawaye nan take gaya masa Dukkan abun da ya faru wanda tajira tazo tai mata agida Tsaki yaja yana Allah wadai da wasu mutanan to mai wani ya isa yayi maka In ba Allah ba. Ya jima suna hira da Ammi wanda washe gari yacewa Ammi ta shirya suje har gidansu mami ya mi a mata takardar sakin nata tare da bayyana dalilin sa na sakin a gaban mahaifiyarta Sedai koda suka je Gidan su mami yadda suka ga tajira abin babu da i se agawa Ammi hannu take amman ba damar Neman yafiyarta. Mami ta bawa Ammi tausayi dama shi Aliyu tunda ya bata takardar ta ya bayyana mata laifukan ta wanda bata Musa ba ta saka Kuka tana neman yafiyar shi yace ya yafe mata Allah ya yafe masu gaba aya ya fita Ko kallon akin da tajira take beyi ba Ammi da tunanin tajira ta dawo Gida seta ara Jin tsoron Allah lallai Mutum ba abakin Komai yake ba. Kuma a ranar Sadi ya gabatarwa Aliyu riba da ci gaban da kamfanin nikan shi suka samu bayan baya nan Aliyu kuma bai asa a gwiwa ba wajan tara an uwan shi a wannan rana ya sheda cewa ya mallakawa Sadi kamfanin shi na Lagos halak har abada ya mallakawa Bashir kamfanin shi na Abuja har abada shi Kuma ze mayar da hankali ana kano da wanda ze Bu e a garin kaduna dan mutan kaduna sun zame masa dangi Ranar Ammi tai Kukan da i sadi Kuwa yama kasa magana haka Bashir bayan gama Murna Aliyu ya kuma yiwa Bashir albishir da yaje ya Nemi auren Hanan ar Gidan Alhaji hamishi wadda yace se a ha e dana Safna Bashir yayi Godiya sosai haka taron an uwan ya tashi Cikin farin ciki. Wata irin kulawa Ammi take bawa farha tun farha na jin kunyar Ammi har ta ware ta mayarta kamar umma dan shagwa a take zubawa Ammi wadda Komai tace Aliyu ya sauya na angaran shi in farha ta haihu seta tare acan dan haka sabbin gyara aka soma yiwa part in Aliyu Daidai da sutturar farha ammi ta bawa masu aiki sabbin kaya aka inka mata akwati akwati masu kyau da tsada Su safna Sun Ha e kai da farha sun koma an ukun Ammi. Musa daya zo Aliyu ya kar i wayar shi ya kunna tarin sa onni Yayta bi Haka yaje Gidan gwamna ya sheda ya dawo dan sadi ya gaya masa sunje Sun bada Uzirin yayi tafiya har gidan su farha seda yaje anan Su kawu sukai ta masa Godiya da mamaki ya kalli Musa bayan sun fito yake tambayar shi bayan baya nan ana aika masu da sa o ne Musa yace Shiya auki nauyi Aliyu yay wa Musa Godiya sosai Nan fa harkokin Aliyu da tafiye tafiyen sa suka dawo acikin satin Ya aika Musa kaduna dan ya Fara duba in da zasu siya su gina kamfanin su ma acan. Sadi ya koma lagos sedai yadda yaga sakina fa abin babu sau i nan Minal babbar arsa ke gaya masa abin da maman su take lokacin da baya nan Abin ya agawa sadi hankali dan washe gari suka dawo kano Gidan su sakina ya wuce Ya sanarwa da mahaifiyarta dan sosai sakina hauka take da sumbatu jamila ce ta warware wa sadi Komai na abin da Sakina ta aikata sadi yayi Takaicin abin ya kalleta yace. "Mai na rage ki dashi sakina gashi nan kin ata rayuwarki a banza abin da Kike so Gashi na samu dan Aliyu ya mallakamin kamfanin sa cikin sau i bayan Kin fita daga hankalin ki sakina Kin cuci kanki Kuma ni sadi na sake Ki Saki aya kuma ba zan bar Miki yarana ba" Ya kwashe ansa suka bar gidan sakina se dariya take Suna fita Jamila ta samo mota ta saka sakina sukai dawanau gidan mahaukata dan tace ba zata barta agida ba ta kashe su haka kawai Mahaifiyar sakina tai takaici da halin ar tata haka jamila takai sakina gidan mahaukata aka bata aki guda dan A soma duba walwarta dan hauka take Tuburan tana Tone tonen asiri. Sadi duk yadda yaso seda yay Kuka sanda yake shedawa Ammi abin da yake faruwa Ammi ta tafa hannu tana cewa. "Lallai Mutum mugun icce sakina tabani mamaki dama abin da ka shuka shi kake Girba Allah ya za a maka tagari wadda zata ri e maka yaranka yanzu Ka huta zuciyarka tai sanyi kafin ka koma lagos ka bar Min yaran a gabana kafin muga abin da Allah ze mana" Nan take bashi labarin su tajira ma Sadi yaji labarin tajira da Kuma abin da ya gani akan sakina ya aga masa hankali Kuma ya ara Jin tsoron Allah aran shi. Wayyo Allah Kaine mai iko akan kowa zuwa wannan Lokaci abin ya azanta ga tajira dan takai tana oyi tsutsa tana fita daga gabanta kwanan ta Biyu cikin wannan hali rai yayi halin sa an Mutu da Mugun Nufi arai Allah ka rabamu da irin arshen su tajira Babu wani taro da akai haka tsirarun Mutane suka kaita Gidanmu na gaskiya aka gama addu'a aka watse su tajira an gama na duniya sauran nacan. Seda akai kwana bakwai mami ta kira ammi ta sheda mata Ammi batai asa a gwiwa ba wajan saka salma dasu safna a gaba suka Je gaisuwa harda abin arzi inta takai Musu mami se Godiya take. Sadi ya koma lagos. Cikin Farha nata Girma kullum Aliyu na uncin ta i Zuwa inda yake ai tasan yana bu atarta Ita ko dan rashin Kunya taje wajan Miji da wannan aton cikin ta Tsallake mahaifiyar shi Dan haka tai masa banza duk da ba haram bane hakan amman ai da kunya. Bayan wata biyu farha ta tashi da na uda wadda Nan da nan Ammi tasa aka auko Mota suka tafi asibiti basu Jima da zuwa ba Allah ya sauketa lafiya ta haifo yaranta mace da namiji masu kama da Aliyu sak kafin kace me asibitin ya cika da an uwa Aliyu da yaje kaduna dan Bu e kamfanin shi albishir da Salma tai masa ba sanya yayo Gida yabar Komai wajan Dini wanda ya taimaka masa ya sami aiki a tasha to shi Aliyu ya Nema akan Harkokin kamfanin nashi na kaduna kuma ya ora shi a babban matsayi a kamfanin. Zo kaga murna wajan Aliyu duka ya ha e yaran nashi yana Musu addu'a yana farin ciki da yake bata sha wahala ba nan da nan aka sallamo su suka dawo Gida Ammi ta ha a ruwa da kanta taiwa Farha wanka ta gyarata tsaf Aliyu se kallon farha yake yanzu da kanta ta haifa masa wa annan manyan yaran kyawawa. Musa ya aika gidan su farha aka sanar wanda Yaya sadiya da Nafisa da Umman zage yayar umma dasu babarsu Hadiza suka shigo Motar Musa suka tawo Gidan farha Hoho Duniya da duniya se a wannan Rana su Yaya sadiya suka san wa farha ke aure ashe Hasken matasa take aure wanda A kamfanin sa ma su Halifa suke aiki. Sun sami karramawa daga wajan Ammi da su safna Farha kuwa harda Kukan murna ta rungume yaya sadiya wadda ta saki baki tana kallon farha Su yaya sadiya na gidan farha ta Koma sashin ta ashe basu ga komai ba domin sashin farha se ka rantse ba a asar nan aka tsara shiba Umman zage aka bar mata su Kuma suka tafi Gida da labarin mijin da farha ta aura da kuma Duniyar alatun da suka gano. Umman zage kewa farha wanka da yara wanda Koda yaushe se