← Book details Rabo Ya Rantse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 94

Sashe 73

Rabo Ya Rantse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

matar shi jiyay gwara ya tauna tsakuwa a wannan karon Ko aya zata ji tsoro. Tashin dayay domin ya Nufi wajan Farha Jiri ya ebe shi babu zato suka ji arar fa uwar shi Aliyu ya fa i baya Numfashi kwata kwata kanshi ya bugu a tiles afar shi ta daki Katakon Jikin Kujera wanda yatsan afar ya ce ass wanda ya bada tabbacin Ya sami tsagewar ashi a yatsan nashi ga gefen kanshi da ke zubar da Jini sakamakon fa uwar da yayi daga Ammi har Su Sadi ar Rige rigen zuwa gabanshi Suke yi Ammi kuka kawai take se ta fita a guje tai Compound tana kiran driver agigice suka shigo ammi na cewa "Sadik ku saka min shi a mota in Baba ya mutu nima bin bayan shi zanyi na shiga Uku Baba Me ya same ka Innalillahi wa'innah ilaihirra'jun Allah ka farkar dani daga wannan Mummunan mafarki dana keyi" Da sadi da Bashir da yar suka aga Aliyu zuwa mota Su Safna kuka kawai suke yi ammi kuwa dan Kuka Ko Muryarta bata fita ko mayafi seda aka mi a mata sannan ta shiga motar da ita dasu sadi suka tafi asibiti. Farha juwa ce take ibarta a hankali take dafe bango tana silalewa asa zama tayi da as a asan tiles tana sakin ajiyar zuciya ta saka hannu, ta Shafo hawayen dake Biyo Fuskarta Hankalin ta ya tashi ta kasa Nutsuwa ta kasa tunanin komai akan hakan Lallai akwai matsala kalmar Innalillahi data ke ta fa a ita ta zama makamin bata Nutsuwa ta aga kai ta hango su Safna nata Kuka in ba idanunta Gizo yayi mata ba tabbas matar sadi ba kuka take ba dariya take tana Wa anta wasa sedai daga taga su Safna sun ago zata fara share hawayen arya anwarta bata wajan bare taga a wani hali take itan Bata da Lokacin Tunanin dalilin dariyar sakina sabida haka tashi tayi a hankali ta nufi akin da aka ware ya zama nata ada ta udiri ba zata kuma kwanan Gidan ba amman yadda taga halin daya shiga yasa dole zata zauna domin kota tafi ma bata da sauran Nutsuwa wato kuka ma se da dama ake yin sa hawayen ta ya afe kawai hango yadda ya fa i take tana kuma hango yadda aka fitar dashi kamar gawa take Cikinta ya mur a ta dafe Gefen mararta wanda ke faman juyawa kwanciya tayi a asa bata damu da tarin urar dake akin ba Nishi take tana kiran sunan Allah har Gumi ya soma wanke ta marar ta lafa mata da ciwon Jitai kamar Ihu da kururuwa Hankalin tane ya kuma tashi bayan data tabbata daga falo take Jiyo Ihun! wanda tunaninta ya bata ya rasu Shikenan ta ora hannu aka ta fasa Ihu mai arfi tunanin yanayin su na azu yana mata yawo a idanunta da rarrafe ta fita falon Sedai babu su Ammi Mami ce take kukan daya sa taji kamar Ihu take Su safna na taya mami kukan sakina ce ta fito tana musu magana. "Haba duk kun cika mana gida da Ihu se kace wanda aka ce ya rasu haba da Allah se kace ba Musulmi ba kema mami da Girmanki kinzo kin biyewa ananun yara" Mami ta ago ido tana hararar sakina. "Dole muyi kuka ai kuka muya kama da ma bama su Burin ya mutu suci dukiya ba sakina bari Kiji duk wani iskanci naki a tafin hannuna yake da duk wata gadar zare da kike ha awa" Mami ta fa a tana kallon sakina wata ar iskar dariya sakina ta saki tare da cewa. "Ai duk kanwar jace Ni ma kallon ku nake an gaya miki ana shiga dawa dan arya ne to bari Kiji kifi na ganin ka mai jar koma gwara ma kowa yay takan shi tun kafin ai mutuwar kasko haihuwar guzuma a kwance uwa kwance" Daga farha har su safna hankalin su bai kai kansu mami ba har sukai suka gama ita mami manufar maganarta akan sakina shine Tana sane da yadda take cusa mai anwarta ya aura sannan kuma taga yadda kowa yake kuka amman sakina batai ba shine dalilin daya sa ta fa awa sakina haka wanda ita kuma sakina Jikinta seyay sanyi ta auka ko mami tasan shirin tane Shiyasa itama ta yanko tata ba ar maganar ta ya a wanda tasan dai Aliyu baya son mami ammi ta ha a auren amman bata san komai ba bayan haka Dukkan su Jikinsu yayi sanyi kuma sun shiga ar kamar wani yasan sirrin wani mami Kukan dai ta Cigaba dayi ganin dare nayi yasa farha ta arasa wajanta tana rarrashinta Mami tace wa farha tazo suje part inta su kwanta haka tabi mami Ranar farha dai batai bacci ba daga arshe alwala ta auro tazo tana ta sallah duk hankalinta ya i kwanciya tai kuka ta gode Allah kanta har ciwo yake mata ga ciwon mararta wadda ta aure tai gam. Duk yadda likitoci suka so dawo da Numfashin sa abin yaci tura A ta aice har ya shafe awanni Biyu yana a tsakanin halin rayuwa da Mutuwa ne Likitan ya fito yana yarfe zufa sadi ya Mi e da gudu bawan Allah ko takalmi babu a afar shi ya tari Hanyar da Likitan ze wuce. "Doctor yaya mai jikin da Muka kawo?" Likitan ya an dubi sadi tare da cewa. "Sorry ka kwantar da hankalin ka" Bashir ya taso ido jajir yana cewa. "Kaga malam in kun kasa zamu auke shi a yanzu zamu yanki ticket asar waje wannan wani irin iskanci ne asibitin ku i mai tsada kamar wannan amman Ku kasa aikin ku" Likitan ya dafa kafa un Bashir Lokacin Ammi ta karaso wajan ya an kalli sadi yace masa. "Muje Office" Bashir yace. "Wallahi babu inda zaku seka gayan a wani hali an uwana yake ciki idan ya rasu kawai ku gaya mana mu auki gawar shi" Likitan ya dubi bashir wanda yay kamar baya hayyacin sa. Kafin yayi magana wata Nurse wadda ya bari a akin ta fito da sauri tana cewa. "Doctor yana numfashi yanzu" Da gudu Likitan ya koma dama ya fito ne dan ya aro kayan aiki Taimakon gaggawa suka cigaba da bawa Aliyu har Allah yasa Numfashin sa ya dawo Normal allura sukai masa tare da gyara masa Yatsan sa daya bugu sannan suka manna mai plasta a Kanshi wurin daya fashe Likitan yaja mai ofa bayan yace kada wanda yaje Inda yake. Sadi likitan ya kira Office ai da sauri ammi tabi bayan su. Likitan ya zauna sadik da ammi suka zauna. Likitan ya dubi sadi "Gaskiya yalla ai ku kiyayi abin da ze dinga ata masa rai dan zuciyar shice ta Buga wanda bada ban Allah ya taimaka ba ze iya rasa ranshi sannan Jininsa ya hau lokaci aya tabbas Allah ne yayi akwai sauran kwanan shi akwai abin da akai agaban sa wanda ya aga mai hankali ya kuma ata masa rai se a guda in ba haka ba akwai matsala" Salati ammi tahau yi tana tunanin me yake damun Baba haka Da har wa annan lalurori suka far masa lokaci guda. "Hajiya ai ita addara ba'a mamaki da faruwarta Amman dai a kula dashi sosai dan Allah in ba so kuke ku rasa shiba" shawarwari likitan ya basu tare da Bawa sadi Bill in su yaje ya biya Ammi cewa tai anan zata kwana Bashir yace a,a shima ya sadi ya koma gida shi seya kwana a wajan Aliyu tunda Likita yace sallama se zuwa gobe da yamma kafinnan ya ara warewa. Wajan Sha biyun dare su Ammi da driver suka kamo hanyar gida daga asibitin suka bar Bashir......... *RABO YA RANTSE! littafin ku i ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a auka a turo,shaidar biya 09022260850* *A LOVE STORY 91* Lokacin da su Ammi suka shigo gidan tsit yake sabida kowa yayi bacci Ammi ta wuce aki sadi ma ya tafi masaukin sa Gaba aya hankalin Ammi ya gaza kwanciya don ita ma babu mamaki idan aka duba Jinin nata yahau sedai rashin Lafiyar Aliyu Yafi Komai aga mata hankali har Lokacin kuka take idan ya rasu tasan da wuya itama zata ara Moruwa Duk anta yafi soyuwa azuciyarta yafi mata biyayya to me yake damun sa haka da wannan matsaloli suka taru sukai masa yawa Haka bata kwanta ba alwala taje ta auro ta dinga Sallar nafila se wajan asubahi bacci yayi awon gaba da ita. Sadi yana shiga akin daya sauka mamaki ne ya kama shi ganin sakina a zaune cikin shirin kayan bacci tana ganin shi ta saki Murmushi ta mi e ta shiga ban aki ta ha a masa ruwan umi tazo gabanshi ta shiga cire masa kayan jikin shi bai musa mata ba sabida yadda ya gaji Shima hutu yake bu ata da taimakon ta ya samu yayi wanka ya fito ta kawo mai kayan bacci Catton na maza ya saka yana umartarta akan ta kawo masa ruwan Shayi taje ta kawo mai. "Abbansu yaya naga duk jikin ka yayi sanyi ka shigo babu kuzari?" Sadi ya kur i ruwan zafin tare da aje cup in a center table ya kalli sakina fuska babu sukuni "Jikin Aliyu ne ya bani tsoro wallahi duk hankalina a tashe yake na rasa Nutsuwa ta" an kalle shi cikin za uwa da taji abin da ke damun Aliyu "Mutuwa likitan yace zeyi ko cutar arin jiki ce ta kama shi?" Sadi cikin tsananin mamaki yace. "Ban fahimta ba sakina dama akwai wanda yasan ranar Mutuwar wani ne In ba Allah ba?" an sosa kai tare da cewa "To naga duk ka aga hankali ne In ba haka Likitan yace maka ba to meye zaka wani zo duk ka damu kanka so kake kuyi Mutuwar kasko shi a kwance kai ma a kwance a,a gwara anyi aga shi in dai ya kwanta" Sadi ya zubawa sakina ido cikin Nutsuwa yace "Ban gama gano nufin ki ba Ai ni a tunani na duk abin da ya shafi Aliyu nima ya shafeni kamar duk abin da ya shafe ni shima ya shafe shi" aramar dariya sakina tayi. "Kai dai kake ganin haka Ni
Chapter 73 · 0% Book details