Sashe 26
Rabo Ya Rantse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
zata ci ma ya gagare ta cikin haka ta fara sana'ar sayar da abinci da goyon Sajeeda Hajjo na ri e da Safna haka zata fita kasuwa ta siyo kayan girki agidanta take sayar da abincin da wannan ribar suke ci suke sha har ta biya musu Ku in makaranta ita dai Burinta anta su rayu cikin farin ciki. Sannu sannu jarin ma yazo ya are tas Lokacin su Aliyu na Jss 3 Ammi dole tasa tace wa hajjo ta koma gida ta nemi sana'a dan itama ta kanta take yi amman hajjo ta i tace ita kam ba zata rabu da Ammi ba haka suke zaune Cikin girmama juna dan hajjo nawa Ammi biyayya kamar lokacin da suna da shi bata ta a sauya wa ba. Ganin halin da suke ciki yasa Aliyu Kullum in sun tafi makaranta baya zuwa sai yayi tafiyar shi kasuwa dako yake duka lokacin ba wani girma yayi ba zai samo ari ari biyu sai ya sami banki ya oye Haka yay tayi lokacin jarrabawa yazo Malamin su yazo har gida ya shaidawa Ammi Aliyu baya zuwa makaranta. Hankalin Ammi ya tashi Aliyu yana dawowa ta rufe shi a aki tana tuhumar sa tana kuka sabida tana tsoron kada yabi abokan banza dan yafi sadi wayo, Bu ar bakin Aliyu sai yace mata dako yake zuwa kasuwa yayi har ya fito mata da tarin da yake yace zai biyawa salma da Bashir ne Ku in makaranta ku in Sun kama dubu Uku ammi tai kukan tausayin yaron Haka ta mayar dashi makaranta sai ta sami aikin sharar titi ta dalilin yayanta an wajan kawun ta da sassafe take fita tayo sharar ta ta dawo a wata ana biyanta dubu sha biyar bata cin ko kwabo a wannan Ku i haka take biyawa su Aliyu ku in makaranta da sauran Hidimar rayuwa. Ganin wahalar da ammi take yasa Aliyu da safen kafin ya fita sai yaje yayi mata sharar tun tana hana shi harta barshi da wannan an ku in da kuma wanda an uwanta an kawunta suka ha a mata taja jarin Sayar da manja da man uli a daddafe su Aliyu sukai candy daga nan yace bai san zancen komawa makaranta ba. Ammin sa na cikin wahala gwara ya tashi ya nemi na kan shi haka Aliyu yake fita kasuwar ofar Ruwa ta an gwangwan wadda wani abokin sa yayi masa tayi a kasuwar an gwangwan ta ofar ruwa awon arafan mota ake a fitar dasu lagos. Ranar da Aliyu ya fara zuwa kasuwar yana bakin wani shago a zaune. *RABO YA RANTSE! littafin ku i ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a auka a turo,shaidar biya 09022260850* *RABO YA RANTSE* *28* *A LOVE STORY 28* Wani Babban Mutum yazo zai wuce Sai ya yar da aramar wata jaka adaidai afafun Aliyu wanda yake gyangya i sabida wanda abokin nashi ya ha a shi dashi har Lokacin bai zo kasuwar ba Shi Kuma Aliyu tun safe ya dako sammako ya Zo kasuwar dan Burin shi Ko jari Bola ce yayi muddin zai sami Hala in shi. Da sauri Aliyu ya bu e idanun shi ya ga jakar sai ya auka yabi bayan Mutumin Da sauri ya tare shi yana ce masa bawan Allah ka yada jakar ka Mutumin yayi farin ciki har ya bawa Aliyu kyauta wanda Aliyu ya i kar a ya koma wajan zaman shi aranar ma dai Aliyu bai sami komai a kasuwar ba haka ya koma gida yana unci dan ko ammi da tana masa magana banza yayi mata kuma ya i cin abincin dare haka da sassafe ya koma kasuwar still wannan Mutumin ya kuma zuwa kasuwar yazo ta gaban Aliyu ya wuce har ya yi nisa ya dawo ya dubi Aliyu. "Jiya na ganka anan yau na ganka lafiya an saurayi?" Aliyu shuru yayi wa mutumin can kuma sai yace. "Nazo neman aiki ne" Mutumin yayi dariya. "To ban da abin ka matashi ta ina ake samun aiki ana zaune ai sai ka motsa taso Muje Shagona" Aliyu yabi Mutumin wani shago wanda ake sayar da kayan gyaran Motoci suka zauna mutumin ya kalli Aliyu. "Ni sunana Alhaji Hamishi, Ni sana'a ta sayar da Motoci da kawo kayan gyaran su daga lagos da kwatano tunda na ganka ka bani tausayi ina zaune anan ofar ruwa matata aya da a na mata Biyu Hasina da Hanan" Aliyu yayi shuru. "Baka ce komai ba" Atakai ce Aliyu yace. "Sunana Aliyu Ni kuma maraya ne da yayana da babata da annena dansu ma na fito neman Aiki dan ina taimakon Ammi nauyi ya mata yawa" Wannan shine mafarin Bu ewar idon Aliyu akan harkar motoci dan kunsan Komai akwai sila Alhaji Hamishi shine silar Komai na arzi in Aliyu dan bai wa Aliyu Mugunta ba ya fara ajeshi anan shagon siyar da kayan gyaran motoci na ofar ruwa kafin daga baya daya ga amanar Aliyu ya auke shi ya kaishi kamfanin sa dake Kan titin malam ato square Aliyu shine ya biya wa sadi in makaranta a tare suka koma B.U.K Shida sadi inda suka ha a degree insu dama tun suna primary sunyi saukar su ta alkur'ani mai girma Suma su Bashir tuni Aliyu ya tsaya musu akan karatun su yana kammala service inshi ya fara fita kwatano yana shigo da motocin hannu yana siyarwa Ta dalilin Uban gidan shi Alhaji Hamishi wanda Aliyu ya mayar dashi uba a gare shi kullum arzi in Aliyu bun asa yake lokaci Guda ya auke nauyin annen shi idanun shi ya bude sosai a harkar wadda harta kai ga ya soma zuwa yana siyo sabbi da kanshi ya ora riba ya siyar da kayan shi sabida yadda idanun shi ya bu e a harkar. Sannu a hankali arzi in Aliyu ya bun asa tuni yabar kamfanin Alhaji hamishi ya Tsaya da afar shi Haka ya siye aton filin Kusa da gidan su shine ya gina wannan aton gidan da suke ciki a yanzu ya dawo da ammi ciki kuma ya zuba mata ma'aikata Sannu a hankali har gidan su baba usman sai da Aliyu ya gyara shi tsaf lokacin kuma ya mayar da hankalin shi kan ginin kamfanin shi dake titin lawan danbazau wanda ya bawa sadi manager Kuma rabi ma'aikatan shi an su baba usman ya iba amman ba a san ran ammi ba. Aliyu sun ha u da musa kamar irin ha uwar da sukai da Alhaji Hamishi shiyasa Aliyu yake ji da Musa sosai Kuma ya yarda dashi Kamfanin Aliyu mai suna Madaki Motors an services ya bun asa wajan kawo sabbi motoci na zamani dana hannu tare da kayan gyaran su Wanda kamfanin yayi suna a garin kano har ma da kewayan ta Aliyu na lagos da kwatano sadik na kano yana lura da wannan kamfani na Aliyu tare da Musa cikin haka Allah yayi wa Alhaji hamishi rasuwa Amman duk da haka Aliyu bai yada zuri'ar Alhaji Hamishi ba yana zuwa sosai matar shi mai Kirki an sane ka ai sai a hankali Musamman aramar hanan da sam bata da kamun kai wannan kenan. Cikin haka Aliyu ya bu e kamfanin sa a lagos wanda sadik ya koma can Taimakon Al'umma Aliyu yake da dukiyar shi musamman mabu ata dan ya ana rayuwar talauci yaji shiyasa bai ta a wula anta wani dan yana da shiba shiyasa idan yana kano kofar Gidan shi tam da jama'a Haka zalika a dangin su Kowa ya lalubo matsala wajan Aliyu zai tawo Kuma bai ta a juyawa dangin mahaifin shi baya ba. Taimakon su yake da su da gidan Kawun Ammi Dan duk matasan gidan daga sun taso Aliyu ke aukar su aiki a kamfanin shi. Salma tai aure wadda take Bin Aliyu zuwa wannan Lokacin Ammi tace wa su Aliyu su kawo matan aure Sadi ya kawo sakina ar nan iso wadda ammi ta yaba Aliyu ya kawo najuwa course mate in shi a B.u.k ammi ta i amince wa sabida taga Najuwa wayayyace tace tana tsoron wadda zata raba su da Aliyu still dai bayan najuwa ya kawo wata ar nan galadanci nan ma ammi ta i yarda sai yayi fushi yace ya fasa auren. Cikin haka tajira yayar Ammi ta kawowa Ammi ziyara wadda rabon ta da ammi tun barin Ammi gidan su Lokacin da mahaifan ammi suka rasu Ammi taje fagge har ba adadi neman tajira amman bata same taba ita ko tajira tana sane da dukkan labarin halin da Ammi ta shiga amman ta i zuwa sai da mahaifiyarta da mijinta suka rasu Taji labarin arzi in da Aliyun Ammi yayi shine tazo dasu mami cikin wahala tana kuka Ammi ta tausaya mata suka jajanta rashin juna kafin ammi ta ha awa tajira sha tara ta arzi i tasa aka kaita gidanta wanda take ciki da an ta marayu a fagge. Kusan koda yaushe tajira tana wajan ammi biyayya takewa Ammi kamar itace anwa Aliyu yaji bai yarda da matar ba sabida biyayyarta da Kirkinta yayi yawa Amman yadda Ammi ta aukake ta tana yayarta ce uban su aya su ka ai suka ragewa juna shiyasa Aliyu ya zuba musu Ido dan bama cika zama yayi ba dama. Kamar wasa Tajira tazo wa Ammi da batun ha in auren an su abin kamar aikin asiri ammi bata musa ba dole tasa Aliyu ya auri Mami ar wajan tajira sadik ya auri sakina suka wuce lagos Shikuma Aliyu anan yabar mami a part insa ba dan yana son mami ya aure taba sai dan Bin Umarnin Ammi amman yadda mami ke masa biyayya yasa ta sami Gurbi a zuciyar shi Ta sami ciki har sau Uku yana arewa yanzu haka shekarar su ta goma da aure sadi an sa uku duk mata salma an ta biyu shiko Aliyu shuru kake ji dan daga Mami ta sami ciki arewa yake. Matar Alhaji Hamishi Momcy tana ganin mutuncin Aliyu dan duk wata matsala tata data anta shi take Kira ta gayawa Babbar ar Alhaji Hamishi Hasina tayi aure aramar ce ka ai take bawa Momcy ciwon kai dan hanan bata ji kule kulen maza ga shaye shaye sabida kawai uban su ya rasu yabar