Sashe 7
Rabo Ya Rantse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*NA* *AUTAR MANYA* ADABI WRITTER'S ASSOCIATION *007* Washe gari Farha da wuri ta shirya cikin riga da skirt na atamfa ja ta yafa ba in mayafi ta fesa turare ta auki handbag inta ta dubi Umma wadda ta zuba mata ido tana kallon ta. "Umma ni zan tafi ai min addu'a" Umma ta dube ta da kulawa. "Allah ya bada nasara, yau ma baki karya in ba zaki tafi?" Tai murmushi mai ayatarwa. "Umma sai na dawo zan karya Acikin ku in da Salim ya bata jiya umma ta auki dubu aya ta bata tana mata fatan alkairi. Ta fita tsakar gidansu batare data kalli matan gidan dake hada hadar umaman tuwo da dama koko ba. "Manyan ma'aikata sai ina?" Cewar Babarsu Hadiza cikin sigar zolaya. Farha data sa kanta a soro ta aga murya sosai tace mata. "Gidan nasara da sa'a na nufa in Allah Ya yarda" Daga haka tafita daga gidan titi taje ta sami abin hawa sai da ta biya ta auki shema'u sannan suka wuce. Suna tafe suna hira inda shema'u take bata labarin da ya gali ya bata jiya na cewa ashe Gidan rediyon na wannan mutumin ne anan ya galin su ya fara aiki kafin ya bari wai kuma in dai zaka samo wa md rahoto tofa zai ta ara maka albashi. Farha tai zuru kafin tace. "Ya Allah kasa mudai muna da rabo" Haka suka arasa bakin gate in bayan sun sallami mai Adaidata sahun daya auko su, Suka shiga cikin gidan Rediyon zaman jiran Md in sukai har wajan takwas da rabi kafin ya araso. Da far'a ya dube su. "A,a su fatima ne da wuri haka, Ah lallai ba zamu dinga samun matsala daku ba ku biyoni ciki" Suka mi e suka shiga office insa. Zama sukai a saman kujerun office in shima ya zauna sannan suka soma gaishe dashi. Ya dube su Yana aga takardun su. "To Alhamdulillahi duk abin da nake bu ata a tare daku na samu, sai dokar gidan rediyon nan da zan fa a muku, Bana son fashi sannan labarai na hausa da turanci ko wanne ya fa o kanku zaku iyayi" Duk suka bashi nutsuwar su sannan ya ora. "Ni dai fatana duk inda labari yake mai da i wanda zai ja hankalin jama'a ina maraba dashi ku kawo mana Mu watsa tashar mu ta sami kar uwa, Albashin ku dubu ashirin ne a wata, sannan babu taka maiman lokacin tashi ya danganta da yadda duty yazo muku wanda ake kafewa a waje kowa ya duba lokacin shi" Farha a wannan karon ma sai da ta zube asa tai masa godiya ya umarce su dasu tashi ya rakasu su zaga wajan da yakamata haka suka bishi ya nuna musu ko ina hatta akin ya a labarai da sauran su Ma'aitan tashar basu da yawa abin har ya bawa su farha mamaki, Haka suka gaggaisa da sauran ma'aikatan sannan ya baro su anan domin suga yadda ake gudanar da aikin. Ranar su Farha basu tashi ba sai wajan la'asar kuma ba komai sukai ba kawai ganin yadda ake labarai ne da yadda ake auka da yadda ake ya awa Wanda kafin kace me Farha harda da a ganewa sosai. A gajiye li is ta shiga gida wanda tana zuwa akin umma ta zube Fa'iza sai dariya take mata wadda tazo gidan ta wuni Da yar Farha ta mi e tayo wanka taci abinci dama sunyi sallar su acan Da gayya ta fita tsakar gida ta le a ko wani aki ta shaida musu ta sami aiki Sai dariyar ya e suke mata Haka ita dai ta koma aki tana bawa su umma labari. ********** Sadi bayan ya shirya Ya nufi akin Ammi har asa ya tsugunna ya gaishe da ita sannan yace mata zai je ya Dubo Mami sai ya wuce lagos dan jirgin sha biyun rana yake son yabi Ammi tayi masa fatan alkairi sukai sallama ya shiga mota drivern gidan ya kaishi asibitin da aka kwantar da Mami. Da sallama ya shiga akin da mami take Hajiya Tajira maman mami ta saki fuska sosai tana cewa. "Wa nake gani a cikin asibitinnan kamar Abubakar sannu da zuwa" Sadi ya zube har asa yana gaida maman mami kafin ya tashi ya zauna kujerar da take kallon Mami wadda take zaune ta mi afa tana shan tea fuskarta fayau duk ta rame. "Sannu Mami yaya jikin ashe haka Allah ya aiko?" Sadi ya fa a cikin jajantawa. Mami tai asa da kanta tana kallon arfen gado bata ce komai ba. "Kiyi ha uri kada ki sanya tunanin komai aranki In sha Allahu zaki sami wani ingantacce" Maman mami ta kar e zancen cikin kwantar da murya. "Haka ne fa Abubakar nima haka nake ta gaya mata, Amman daga ita har Alin sun aga wa kansu hankali musamman ma shi daya ce ya agu yaga magajin shi" Sadi ya cije le e yana murmushi yasan wannan fa i ne Ba yadda za'ai Aliyu ya fa i haka amman sabida kada ya aryata ta yasa yace. "Dama ai haihuwa ita ce ribar aure Mama muma fatan da muke Allah ya bashi an kanshi" Daga haka ya mi e ya zaro 20k daga aljihun sa ya direwa Mami yayi mata fatan Allah ya bata lafiya ya fita yana arin Fita daga ward in su Sajeeda suka shigo hannun su auke da aton Basket na Kayan Break fast ya dube su. "Ku yanzu dan sakarci kun san zaku zo amman baku bari mun tawo tare ba?" Dariya sukai a tare suka gaishe dashi sannan yayi musu sallama driver ya nufi airport dashi dan yayi jiran jirgin daze bi bai bari maganar Maman mami ta sami gurbi a zuciyar shiba sabida yasan mata basa rabo da kace nace shiyasa ya kawar da maganar bayan yayi wa an uwan shi zato mai kyau. Su Safna sun gaisa da Maman mami sannan sukaiwa mami sannu suka dire mata Basket in sabida sauri suke suna da lecture suka bar akin Mami ta bisu da harara tana jan tsaki. "Wallahi Mama na tsani sadi innan inna ganshi kamar na sha e shi sabida a duniya ba maganar wanda Aliyu yake ji sama data sadi komai nashi ya ora shi akai" Hajiya tajira tace. "Ina sane ai na ya a masa magana kuma nasan ya fahimta kedai sha kurumin ki wallahi ba zamu barsu haka ba dole ma mu raba wannan ala Mami ta kuma jan tsaki. "Suma wa annan an iskan yaran sai iyayi da girman kan tsiya wancan satin fa wayoyi ya sai musu masu uban tsada sannan yace wai ana fara visar umarar azumi zasu tafi Wallahi mama saura ka an na fa i sabida takaici kuma bara na koma nima sai an tafi dasu Hassana" Haka suka lalace a wajan suna ulla sharrin su kafin Likita tazo taga jikin mami jim ka an tazo ta basu sallama da yake da driver nan da nan sukai Gida a maimakon ya wuce da ita gidanta sai Hajiya tajira tace su wuce Fagge inta ara jin wari sai ta koma Basu bi takan Aliyu ba Bare a tambayi izininshi. ****** Ranar Farha ta wuni ta kwana cikin farin ciki kuma washe gari babu sanya ta fita wajan aikin ta Alhamdulillahi ta sami wani daga cikin ma'aikatan yana ara nuna mata komai Taji da in Wajan aikin nata Haka ta cigaba da Fita aikin wanda tuni ta goge har tana arin shiga akin watsa labarai Babban Burin Farha ya cika a sati ayan datai a Garkuwa Radio Duk inda ka zaga Muryarta ce raurau ke fita cikin labaran Yammaci wanda duk wanda ya kunna Radiyo ya kamo tashar garkuwa zaici Karo da Muryar Fatimah andago dan sam batai amfani da Abubakar in ba Dole tasa Salim ya ara aga mata afar kawo ku in sabida da kanta tace yaje ya bawa kawu ha uri ta ro e shi daya bari tai kamar wata guda da fara aikin sai ai maganar auren nasu kuma Salim bai musa ba sabida yana sonta haka yaje wajan kawu da batun wanda kawu yay fa a amman ya ce daga wannan lokacin baze kuma arawa ba damma daga wajan salim inne aka sami tsaikon. Cikin rufin asiri farha take aikin ta sabida bama kowa ne yasan ita ce fatima andago ba sabida yawanci da farha aka santa Wani bin haka zataji kawu na sauraron labaranta taita dariya tana jin farin ciki sam bata da matsala a wajan aikin ta ku in mota kuwa wannan dubu biyar in umma tace ta aje ta dinga auka tana fita aikin Abu aya ne ta kula a wajan aikin shine Md babu ruwan shi da ingancin labari shidai kawai a kawo masa ya ora a kafarshi dan Rediyon shi tai farin jini sam ba ruwan shi sabida Allah ya bashi jarabar son ku in tsiya sabida yasan In dai Radion shi tai suna da talla ma ka ai zai iya biyan ma'aikatan shi. Tana jin an uwanta ma'aikata na orafi da wannan matsala don zata iya jawo wa gidan rediyon barazana Ita dai da yake Allah bai sa taci karo da wata matsala ba yasa ta saki ranta Shema'u tana sashin labaran wasanni na safe ita kuma tana sashen watsa labarai na yamma wannan tasa sam bama sa ha uwa da shema'u sabida lokacin da shema'u zata tashi ita kuma lokacin take zuwa Daga gidansu ma bata da lokacin kowa kullum tana aki tana Rubuce rubucenta na labarin da aka bata wanda zata watsa shiyasa wani bin ma sai kaji Ana cigiyarta acikin gidan. *ABUJA* *09022260850* *RABO YA RANTSE...!!* *NA* *AUTAR MANYA* ADABI WRITTER'S ASSOCIATION *008* Ya lumshe idanunshi yana shafa kwantacciyar sumar da take saman kanshi kwance yake a katafaran gadon dake cikin hotel in IBETO tunda yazo garin Abuja bai sami zama ba zirga zirga yake akan arin ganin Motocin daya yi order daga kwatano sun shigo kamfanin shi. Wayar shi dake gefen shi ce take ringing ya lalubo ta da dogon hannunshi mai cike da gargasa ya ago idanunshi yana duba screen in wayar AMMI sunan dake ta yawo a saman screen in wayar tashi sai da ya bari ta katse sannan ya kirata. "Assalamu alaikum Ammi ya kuke?" Daga angaran Ammi