Sashe 62
Rabo Ya Rantse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
u shiyasa Allah ya tsara Muku hakan Kuma naji mati ar da i nai Farin ciki kuma zan bata duk wata kulawa Kuma zan rufe maka sirrin ka in sha Allahu" Salma ta fa a cikin sakin fuska tagumi yayi yana kallon salma yaji ya sami Nutsuwa da maganganun data yi masa. "Sedai salma ina tunanin ranar da Ammi zata san gaskiyar lamarin nan babban tashin hankalina shine na kasa yiwa ammi biyayya akan abin da bata so nayi wannan shine tashin hankalina dan nasan In ta sani ranta ze aci" Salma ta bishi da kallon tausayawa Duk an ammi babu mai biyayyar shi babu mai gudun acin ranta kamar shi wannan tasa Ammi tafi ri e mai wuta fiye da kowa. "Kada ka saka wannan tunanin aranka dama shi ciki an duma ne dole ammi tasan wannan magana komi daran da e wa kuma dama ammi bata da wani dalili na hanaka aure tunda hakan bai sa awa addini ba dan kawai ta Burge ar yayarta ta faranta mata seta i barin ka kai aure fisabilillahi yanzu in a waje akai Cikin nan yaya zata yi sufa Mutane sun kasa gane cewa Rabo kamar ajali yake Allah ya addara matar kace Akwai rabo a tsakanin ku dan haka se kawai a barwa Allah ikon shi, yaya kaje kaita addu'a kada ma kasa ka damuwa aranka In sha Allah akwai nasara acikin lamuranku" Da ire iren wa annan maganganu salma tayi ta kwantar masa da hankali har zuwa sanda taga ya saki ranshi Kuma ya sami Nutsuwa tashi yayi yana ce mata shi ze juya amman Musa ze kawowa fatima kayan sawa Sallama sukai dan yace yana gudun Rigimar fatima ne shiyasa baze je suyi sallama ba Bayan tafiyar shi salma ta rafka tagumi lallai Ammi in batayi wasa ba a kan wannan yarinya zata iya rasa farin cikin anta mai biyayya dan salma ta hango irin umbin soyayyar da yakewa wannan yarinya. ewa salma tayi ta shiga akinta Ko Mijinta bata gayawa gaskiyar abin da ke faruwa ba sabida sirrinta ne ita da an uwanta tana arin fita taji wayarta na ara tana duba taga Ku i ne masu yawa yayo mata transper ta account inta fita tayi da wayar zuwa akin da Farha ke ciki tana zaune su Dady sunyi bacci ita kuma farha ta zuba uban tagumi wanda tausayin ta ya kama salma Sallama salma tayi tare da zama a kusa da ita ta ri e wayar tana Kiran Number insa yayi rejecting kiran salma shiya kira. "Assalamu alaikum,yaya ya zaka min haka naga ka turo mini ku i na menene?" Yayi Murmushi lokacin yana driving ze koma gida. "Ki dinga siya mata abin da take so, Saboda Koni ma tana ce min tana son abu kaza da abu kaza to kada na ora Miki nauyi idan ku in ma bai isa ba Ki min magana sena aro sannan inda hali ina son ki duba min ita ki tabbatar da akwai cikin nan ma kuwa danni ban kaita asibiti ba kawai hasashe nake yi dan naga Shigen irin yadda take yi mami keyi in tana da juna biyu" Tausayi da dariya ya bata tausayin na farko shine harda tura mata Ku i akan ta kula da yarinyar lallai yana son wannan yarinya da yawa dariyar kuma daya bata ashe shi ka ai yake shagalinsa ko asibiti ma bai kaita ba lallai se abar yaya. "Allah ya kiyaye wallahi Ficika ma bazan ta a ba ta yaya zan auki Ku inka kome take so baze fi arfina ba In sha Allah zan mata duk yadda kace" an sauya murya. "A,a nidai ki ri e ban orawa kowa wahala ba Ko ki ri e koki zubar dasu duka aya nidai na tura yanzu tana ina bani ita" Salma tayi dariya tare da bawa farha wayar ta fita dan tabar Musu akin. "Kina jina fatima?" Ya fa a cikin wata irin murya mai kama data wanda yake jin sanyi. "Ummh ina ji" Ta fa a sabida yawun daya cika mata bakin ta. "Menene naji Muryarki ta sauya ko kina cin wani abunne?" Ta mi e tsaye taje ta zubar da yawun ta dawo tare da cewa "A,a bakina ne miyau ya cika shi amman naje na zubar" Ya sauke ajiyar zuciya "To kinci farar taki ko kina son wani abunne?" Ta girgiza kai kamar yana ganinta "A,a wai ka tafi ne?" Da sauri yace "Na tafi sabida in ma nazo nayi miki sallama Kuka zaki Ni kuma bana son yawan koke koken nan naki" Ta langwa ar da Murya tawani shagwa e kamar zata masa kuka. "Shine ka tafi amman koka zo ka min sallama ai shikenan" Yayi dariya ka an "I'm sorry rigimarki nake gudu amman Koda yaushe zannan kiran ki Muna gaisawa harta Vedio call ma, yanzu de ba inda ke maki ciwo ko?" Ta shafa cikinta "Babu ko ina kawai saman Cibiyata ne inda ka ta a naji yayi tudu da marata tayi tauri" Yayi Murmushi mai sauti "Ki dinga cin ayaba sosai ko tsutsar ciki gareki" ya fa a yana dariya daga haka ya kashe wayar Tabi wayar da kallo aikuwa indai tsutsar Ciki gareta zata dage dacin ayaba dan taita yin kashinta. Ta jima a zaune kafin salma ta dawo Ta dube ta da kulawa "Har kun gama wayar?" Tayi asa da kanta tana mi awa salma wayar salma dariya tayi. "Aunty fatima yau kuma kunya ta kike ji" Yadda salma tace mata Aunty se abin ya bata mamaki. "Yanzu me kike so Kici na dafa miki?" Cewar salma Farha ta girgiza kanta. "A,a wallahi Aunty salama na oshi bacci dai kawai nake ji" Salma tace mata. "Taso Muje akin dake kusa dana su Dady seki kwanta acan yafi wannan fa Salma ta aukar mata kayan suka fita zuwa akin babbane sosai da toilet da tv da komai na More rayuwa acikinsa ga aton gado da Manyan barguna salma ce ta jere mata kayan sawarta acikin Wardrobe sannan ta dube ta. "Duk abin da kike so ga kitchen nan ki shiga ciki sannan Kome kike bu ata ki gaya min Ni anwarki ce" Dariya farha tayi kafin tai magana salma ta fice daga akin gadon tahau taja bargo nan da nan wani bacci mai da i yayi gaba da ita dama shi take Ji..... Wani irin missing in fatima yake Ji acikin zuciyar shi da dukkan sassan jikinsa.........*RABO YA RANTSE! littafin ku i ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a auka a turo,shaidar biya 09022260850* *A LOVE STORY 79* Cikin sanyin jiki dana zuci ya shiga gida a harabar adana motocin gidan yayi parking tare da shiga sashin Ammi Lokacin daya shiga dukkan su suna saman dinning suna shan shayin dare wanda a'idar an Ammi ce shan wannan ba in shayi,Ammi ce da bashir da safna da sajeeda. Sallama cikin bakin sa ammi ta amsa ya nemi guri ya zauna Ammi ta tsiyaya masa Kunu cikin cup ta tura masa ya auka ya an kur a ya aje. "Yaya maganar tafiyar tamu ne Banji kace wani abun ba?" Cewar Ammi yace mata "Gobe in sha Allah zanbi Jirgin arfe Ukun yamma Ku kuma se wajan Jibi da safe haka Zaku wuce" ya fa a yana kallon Bashir wanda ya mayar da hankali kan wayar hannun shi yana dannawa sedai sam hankalin shi ba'a kan wayar yake ba yana kan ofar akin waccan yarinyar Burinsa ta fito ya ganta Dan ba lallai Gobe su ha u ba tunda Abuja ze wuce. "ka gama ha a kayan naka kuwa? sabida in sha Allah gobe tare zamu je airport inna tashi kai kuma seka sami ticket in abuja" Bashir ya sosa kai tare da cewa "In sha Allah dama ban zo da wasu kayan kirki ba" Daga haka su safna Tashi sukayi suka bar falon Bashir ma daya wallafa rai akan son ganinta daya ga Boss a wajan mi ewa yayi ya tafi Ammi ta dube shi. "Komai da komai ya kammala azu Matar kawu ta Kirani tana min godiya da irin Hidimar da ka aika Musu, Ni dan dai Lokaci ya ure ne amman da Mun koma da tajira umara, dan rabon ta da saudi tun hajjin Bara da mukai tare" Bece mata komai ba can kuma yace mata"Ai lokaci ya kure dakin magana da wuri,Wanda ma nake son ya koma baba usman" Jin haka yasa ammi ta sauya yanayin ta yayi saurin kauda maganar "Na bawa musa yarinyar nan sun tafi tun azu" da mamaki ammi ta dube shi"Kana nufin har ka kira musan kenan sun tafi amman baka gaya min ba ai da ko an sabulu na bata" Murmushi yayi me ciwo "To Ammi gobe zan tafi ban san abin da ze faru bayan bana nan ba shiyasa na Dam a mai ita shine kawai samun masalaha" Ammi ta ha e rai tamau "Kai baba wani irin masalaha kuma ban gano nufin kaba wai da kake ma wannan Ha ilon uban wa musa ya bawa yarinyar idan bani ba kuma dan Munafurci ai baka gayan zata tafi yau ba ashe bayan kabar akina zuwa kai ka auketa ka bawa Musa to ko na dawo ma kada ta dawo min gida bana bu atarta" yarasa mai yasa ammi take aukar zafi a duk Lokacin daya sako mata maganar fatima"Ammi ai kece kika ce Kin mata alfarmar zama har zuwa bayan sallah" tayo masa kaaa da maganarta mai arfi "To yanzu na fasa kai nifa bana son wannan za ewar da kake akan wannan yarinyar mai kama da igiyar shanya Ni bamma san jarabar data sa Musa ya kawo Min itaba waya sani ma koda wani surkullen nasu na mutan auye tazo min gidana tunda nake dakai baka ta a Min tirjiya ba se akanta duba dukan dakawa su sajeeda akanta kamar ba an uwanka ba wallahi bana aunar yarinyar nan" urawa Ammi ido yayi gabanshi yana tsananin fa uwa Tun yanzu ma ammi tana irin wa annan maganganun inaga tasan Matar shice Muryar shi sanyi alau yace mata "Ammi Dan Allah ki dinga kwantar da hankalin ki ni babu wata manufa a tsakanina da yarinyar in kika cire ta dalilin Musa kuma