Sashe 5
Rabo Ya Rantse Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
mata sabida haka sai tace. "Alkairi muka nufa kuma dashi zamu dawo arfe nawa?" Babarsu Ru ayya ta Cije baki tana cewa. "Ki shigo ki duba mana sai kace akin ba on kine" Farha ta araso cikin akin ta kalli agogon dake bangon akin sannan ta arasa gaban madubin Su Ru ayya ta auki Hoda ta shafa ta fesa turare, dan su Ru ayya an kwalliya ne sa anin ita da ko hodar ma sai dai ta bi akunan su ta shafa tasu dan bata da ita sabida kwalliya sam bata dame taba. "Keko farha ko an caro white innan na zamani ba zaki siya ki goga ba wannan ba i naki har yayi yawa ki duba kaf an gidannan Kamannin kawun ku suka auko farare tas kyawawa amman ke wallahi kamar ar gudun hijira nina rasa mai salim ya gani a tare dake keba Tsaho ba keba wata cikar a mace ba" Babar su Ru ayya kenan mai ga a ga a ita kai tsaye take Nuna yashinta akan farha kuma duk maganar data fito daga bakinta haka zata fa e ta babu batun ta tauna ta sa anin Babar su Hadiza mace ar bariki sam aryane ka gane inda ta dosa sai dai farha tana lura da kowacce kawai sai dai ka zauna da mutum ne da halin shi kuma ba komai bane ya tsone musu ido ba illah son da Salim yake mata suna ganin duk yafi mazan an su rufin asiri sai kuma karatun datai musamman wannan aiki da take nema ya tsone musu ido shiyasa ko wacce ta dage sai arta tai karatu sabida suma su sami aiki in sun gama ba in cikin su iri iri baya uya Wanda suka ha ewa Umma kai su biyun ba'ajin kansu Gwarama an babu ruwansu ta wani bin amman wataran in iyayen suka zugo su haka za'aita bala'i agidan har sai kawu ya tsawatar in kuma aka shirya shikenan. "To babar su Ru ayya in dai kawu ne ya haife ni ai shikenan kyau kuma tunda su rukayya nada shi na bar musu suje suyi gasar shi" Daga haka ta aga labulan tabar akin tana gab da kaiwa soro taci karo dasu humaira annenta an su babarsu rukayya suna dambe akan kwa an kwaki tsaki farha taja aranta tana takaicin wannan abi'a ta yaran gidansu a kullum tana addu'ar Allah ya bata abin da zata wadata gidansu da Abinci. Har takai bakin titi wannan takaici bai bar ranta ba Suke nan kullum cikin dambe akan abinci kamar wasu mayunwata har an layi sun shaida su tana nan tsaye a bakin titi Allah ya bata adaidaita sukai ciniki dashi akan zai kai ta ofar nasarawa akan naira ari biyu tafiyar ba wahala sabida babu cunkoso a titi bayan ta sauka ta bashi ku in sa ya ciro canji ya bata layin gidan su awarta shema'u ta shiga tana tafe tana sauri haka ta shiga gidansu shema'u ta tarar da ita Itama tana shiri tana ganinta ta washe baki. ar halak yanzun nan ya gali yake maganarki dafatan dai kinzo da komai naki?" Farha tai dariya. "Da takarduna nake kwana fa a jaka sabida kiran kota kwana, ina mamanku?" Shema'u tace "Tana wajan aiki bara na masa magana sai mu tafi" Shema'u ta fa i tana aukar mayafinta Jim ka an suka fito tare da Ya gali Farha ta rissuna ta gaishe dashi ya amsa yana sakin murmushi suka jera zuwa bakin titi ya samar musu adaidai ta zuwa Inda Gidan rediyon yake a titin audu ba o way ne A bakin gate mai an sahun ya sauke su suka bashi ku in shi, Farha ta kalli saman gate in inda aka rubuta GARKUWA RADIO da manyan harufa ya gali ne agaba su kuma a bayan shi. Haka suka shiga cikin gidan radion sun jima a zaune kafin suga Md in wanda yace su shigo office in shi bayan sun gaisa ya fara duban shema'u yana cewa yaga takardun nata ta mi a mai sannan ya kar i na Farha. Ya jima yana duba takardun nasu kafin ya dubi Ya Gali. "Gali kasan fa wannan tashar tamu sabuwa ce gaskiya muna bu atar gogaggun ma'aikata wa anda suka san kan aiki su wa an nan yaran da alamu ma basu ta a yin harkar ba" Caraf farha tace. "A,a wallahi lokacin da muke school an ta a tura mu gidan radio kuma ba laifi mun sami gogewa a wani angaran" Md yayi murmushi kafin yace. "To shikenan babu matsala In sha Allah gobe da safe ku dawo domin muyi muku screening, In mun sami abin da muke nema a tare daku shikenan" Farha harda zamowa daga saman Kujerar da take zaune. "Dan Allah ka taimaka mu sami aikin nan musammam ma ni dana ke ta zarya kaga yau zuwa na kusan uku kenan Ban sami ganin kaba, sai yau da Ya Gali yace mu tawo tare dashi" Daga Md Har Ya Gali da shema'u dariya suka sanya mata sabida yadda tai kamar zatai kuka. "Karki damu Fatimah Ko?" Da sauri ta aga kanta. Sannan Managern director in ya cigaba da cewa. "Mudai fatan mu wannan tasha tamu ta sami kar uwa ta aukaka tai suna wannan shine burina" Da sauri farha tace. "Wallahi zamu yi iya yinmu ko kasuwa ka turani nikam zuwa zanyi" Sosai aka ci dariyarta a wajan haka sukai sallama suka baro Office insa A bakin gate suka rabu Ya Gali ya basu ku in adaidaita shikuma ya tafi Inda zashi har suka rabu da shema'u dariya shema'u kewa farha sabida yadda tai in kowa ya gani sai yaci dariya. Bata damu ba ita dai burin ta Allah yasa ta sami wannan aiki haka ta wuce gida a bakin titi ta sauka ta arasa Cikin layin su da afa ga uwar ranar data walle sosai. *09022260850* *RABO YA RANTSE...!!*