Sashe 9
Rabo Ya Rantse Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Ya fa a yana girgiza afafun shi Farha ta bishi da ido Duk yadda Allah ya rufa mai asiri Amman bai godewa ba yake hango abin da zai saka shi acikin matsala, Har ta aga kai zata ce ita ma bazata iyaba sai ta tuna da yadda aurenta zai zo ga hidimar Kayan aki wanda da wannan aikin Ita da umma suka laru domin su rufawa kansu asiri dan tasan kawu ba abin da zai Sannan matan gidansu kowa ya sawa aikinta ido idan har ta daina wannan zai basu ofar Yi mata habaici da dariya sannan zata jefa zargi a zuciyar umma na dalilin daya sa aka koreta tasan kota fa i dalili ba lallai a yadda. "Yalla ai zanyi ni zan iya" Ta fa a Muryarta na rawa. Md ya washe baki yana cewa "Yawwa ar gari To shikenan Gobe zamu fitar da tsarin Komai Yau na sallameki da wuri tafi gida ke kuma ga takardun kinan kada ki kuma dawo min Tasha" Yana fa in haka ya mi e ya watsowa shema'u takardunta yabar Office in Shema'u ta ebe su ta zuba a jaka ta Mi e tana bala'i "Dama irin kune kuke atawa an jarida suna kuma in sha Allah wannan labari sai ya wargaza maka farin cikin ka, kawai dan biyan bu atar kanka zaka atawa Bawan Allah suna mutum mai taimako mai tausayi Allah baze baka nasara ba" Tana gama fa in haka ta fice Sauran ma'aikata na mata magana suna tambayarta anwar Gali mai ya faru tai musu banza Ta tari Abin hawa da yar Farha ta cimmata suka shiga adaidaita zuwa gida. "Ke yanzu Farha akan abin da bai taka kara ya karya ba zaki za i abin da zai ja miki matsala dan wallahi arshenta ta rufta dake, Ki zauna ki karatun ta nutsu shi Md mai ku i ne ila ma ya auke iyalinshi subar asar ke kuwa fa? baki da tsuntsu baki da tarko wagairahun Ai a kano" Farha tai murmushi. "Shema'u baza ki gane ba nidai Allah yasa hakan ya zama alkairi Md ya ara min ku in nan dan na kashe matsalolin gabana" Shema'u ta mata wani sakaran kallo kafin tace. "Farha kenan mai yasa mu mutane muke da son kammu ne? kin za i ki atawa wanda nauyin sama da al'umma dubu suke ci a asan shi dan ki kauda matsalar gabanki? kin za untata zuciyar wanda yake taimako domin Allah dan ki kauda taki matsalar lallai kin taro fa an da baki da an wasa Allah ya baki sa'a" Duk wannan Maganganu na Shema'u basu saka farha taji wata karaya akan udirinta ba haka ta rufe ido tana Tunanin yadda zata kaya gobe. Ba yadda shema'u batayi da farha ba akan ta janye amman ta i daga arshe haka suka rabu baram baram Farha a zuciye ta shiga gida Sabida yadda shema'u ta gaggaya mata magana har tana ce mata Shi mai ku i ne zai iya sawa a aure kaf Familyn su Farhan. Tana shiga cikin gidan ta tarar da su Umma a tsakar gida kowa farin ciki yake ta aje Handbag inta ta nufi randa ta ibi ruwa ta kafa kai tana sha. "Farha kinga Allah ya kar i addu'ata Yau dai su Halifa sun sami aiki a kamfanin SA in jiya" Gaban farha ya fa i tai murmushin dole tai Musu fatan alkairi ta wuce aki. Yau gidansu Farha gwanin sha'awa su Halifa an i fita konan da can suna gida ana taya su Murna Shi Halifa yana angaran gyaran motoci Nura kuma sune masu Duba motocin da suka shigo da wa anda suka fita dama an gama karatu ba aikin yi Ga zafin talauci ga Samartaka Wannan samun aikin Nasu Yayi wa kowa na gidan Da i hatta kawu sai da ya shiwa SA in gwamna Albarka Abin da in Kuma shine Kowani aki ya samu aikin Halifa akin su Ru ayya Nura kuma akin su Hadiza ita dama Umman Farha bata da a namiji amman harta fi Iyayen yaran murnar samun aikin nasu. Gaba aya Farha jitai bata da sukuni Ta i sakin Jikinta a gida sai faman Juyi take a saman gado Ko tsakar gida ta i fitowa duk Murnar da ake agidan tana aki a unshe har magariba. "Wai Farha meke damunki kada kija ace kina ba in cikin samun aikin su Halifa kinsan halin Gidannan ba'a raina magana" Farha taja Abin da ta rufe Jikinta dashi. "Umma bana jin da in Jikina ne" Umma ta dube ta da kulawa sosai. "Allah yasa ba ciwon marar ki bane zai tashi ba, ga ba ku i a hannuna" Farha ta dubi umma "A,a lokaci bai yiba kuma ina neman sau i wajan Allah" Ranar Ko makarantar dare ma bata jeba Umma kuwa yau hirar tsakar gida ce ta Ru e a gidan wanda Halifa ya baje yana ta basu labarin Yadda Mai Kamfanin Madaki Motors in ya karramasu Kuma da kanshi ya Duba takardun kowanne acikinsu ya kuma raba musu aiki da albashi mai tsoka Halifa ya ara da cewa. "Ai wallahi sanda naji labaran jiya ko bacci banyi ba Muna tashi Da asubah muka tafi Sai wajan azahar layi yazo kammu Mutum ari da hamsin ya nema amman Mutum yakai Dubu da sukaje lallai ana zaman banza a garin nan" Babarsu Ru ayya tace. "Allah dai yayi masa albarka yadda ya fitar damu daga takaicin rayuwa shima Allah ya yaye masa dukkan matsalolin shi" Babarsu Hadiza tai caraf tace. "Tab su masu ku i ina suka ga matsala zasu sha madara suci kaji Kai dai talaka mai neman na masara kaike da matsala" Halifa yayi dariya sannan yace. "Tab yadda naji fa ance bai ta a haihuwa ba Mama ke kin ganshi kamar shi yayi kanshi dan kyau yadda kika ga Tumatur sabida ja wallahi ban ta a ganin Mutum mai kyau irin nashi ba Kamar ka ta a jini ya fito" are yana kallon Babarsu. Babarsu Ru ayya tace. "Lallai duk wadda Allah yasa ta haihu dashi ta girmi talauci Allah ya bashi an kanshi" Ire iren wa annan hirar sukai tayi har kawu ya shigo shima ya saka baki ranar gidan dai ya wanzu cikin farin ciki ita kam Farha bata san wainar da suke toyawa ba haka tai kwanciyar bacci mai nauyi yayi gaba da ita. *********** Ammi ta dubi Aliyu wanda shigowar shi kenan Falon nata dan tunda yazo bai sami damar zuwa wajanta ba, Yaje gidan gwamna yau kuma ya ebi ananun ma'aikata a kamfanin shi dan ko wajan wasan wallon afar matasan gwale bai jeba sai sa o ya bawa musa yakai musu. "Sannu babana mai za'a kawo maka?" Ammi ta fa a da kulawa. "Ammi ni yanzu bazan iya cin komai ba dare yayi adai ha o min Ba in shayi ka ai ma is ok" Ammi ta kalli Sajeeda da duk ta shiga taitayin ta ganin dodonsu ya shigo falon. "Auta maza ha owa Hammanki shayi a ananun Kofuna" Ya tur une fuska. "Ammi kinsan bani son yarannan na ta a abu kina bani" Ammi ta kama ha a tana dariya. "To sarkin tsafta na manta ne ai, Bara na ha o ma da kaina, Niko nace yaya Kaje ka dubo Mami kuwa? azu na kira yaya tajirar ma bata auka ba ina ga bata kusa da wayar tata ne" Wanni kallo ya watsawa Sajeeda ba shiri ta Mi e har tana ha awa da Gudu tabar falon. Kafin ya an kalli Ammi............ *RABO YA RANTSE! littafin ku i ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a auka a turo,shaidar biya 09022260850* *RABO YA RANTSE...!!*