Sashe 4
Rabo Ya Rantse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kenan wadda sunan ta na Asali shine Fatimah ar gidan Malam Abubakar Mai Bulo dake andago wanda jama'a kewa gidan la ani da gidan Cida kai ko gidan yawa sabida tsabar yawan an babansu Malam Abubakar mai Bulo shine tasa kowa a gidan yake fafutukar abin da zai ci dan tuni Mahaifin nasu ya sallamawa kowa ce mace nauyin kanta ita da anta sabida tsabar yadda nauyi da rashi yayi masa yawa Mata uku ne agidan su Farha Babar su Hadiza Nada a Goma Babar su Ru ayyah nada a Goma babarsu farha nada a Biyar Gaba aya an gidan su ashirin da biyar ne cif. Malam Abubakar mai bulo mutum ne mai son ya kyautatawa iyalinshi ada sanda yana dashi anji da i agidanshi dan wadatar sa ma ita ce ta saka ya tara mata har uku da a batare daya ji wata shakka ba, sai dai yau da gobe ga girma ga nauyi yasa abubuwan suka ca e masa hakan tasa yaja tagumi ya zubawa matan sa ido yanzu haka suke buga buga dan asirinsu ya rufu wani bin inya sa mu yakan arin wajan yaga ya kawo gida mai girki ta sarrafa sai dai akan Shinkafa Rabin kwano ana iya bawa hammata iska acikin gidan Musamman da Farha wadda ita bata i tai dambe da aramin yaro akan shinkafa loma aya ba, in suna fa a akan abinci agidan tamkar basu ta a cin abincin ba haka suke cika gidan da hayaniyar su har ma ota sai sun shigo rabo ga matan ko wacce ba ha uri daga ana fa an kowacce anta take tare wa Malam Abubakar mai bulo ( kawu ) mutum ne mai zafi manyan an sa da ike mata ne suna gama primary ya aurar dasu suma sauran ammatan sabida yadda zamani yazo ne da yar aka shawo kanshi ya barsu suke karatun bokon wa anda suke duk annen farha ne Don ita farha ma ta kammala karatun ta a F.c.e kano inda ta sami diploma a angaran mass communication kuma Cikin ikon Allah ta sami nasarar amsar result inta wanda bata da wata matsala sabida tana da haza a sosai, amman in kaga annen farha sai ka rantse Yayinta ne. akin su farha Yaya sadiya tai aure Yaya Nafisa tai aure Fa'iza tai aure wadda farha take bi yanzu haka daga farha sai aramar anwarta mai suna ikram wadda ita ce autar umman su farha. Suma akin Babarsu Hadiza wadda take itace uwar gida matanta takwas ta aurar da uku saura biyar hadiza ce Babba yanzu a ammatan tana shekarar arshe a secondry sai annanenta mata da suke tawosa sai maza samari guda biyu wa anda suka girmewa Farha sai an babarsu Ru ayya itama ta aurar da biyu yanzu haka akwai shida agabanta Ru ayya ce Babba a ammatan gabanta sai sauran sai maza biyu suma samari aya anin farha aya yayanta Umma mahaifiyar farha bata kai sauran matan gidan jin jiki ba sabida bata da nauyi da yawa sosai tana kuma sana'arta ta wankau sai dai yawanci ku in basa zama daga an samu ake kashewa Musamman Lokacin da Farha na makaranta sabida umma ce ke hidimar taimakon farha akan karatun nata wanda ta wallafa rai akan sai ta karanci aikin jarida, Haka Umma ta tsaya akan karatun farha da taimakon Salim saurayin farha an Abokin kawu wanda tun kafin farha ta taso Salim ke hidima da ita suna son junan su sosai Salim yana kashewa farha ku i sabida an kwari ne anan yake sayar da atamfofi Yayi nacin ya kawo ku i Gidansu farha Lokacin da tagama karatu tace ya bari ta sami aiki sabida taga yadda Iyayenta mata ke shan wahala agidan su akan neman abinda zasu ci ba ason ran kawu farha ke zaune ba aure ba ga zabga zabgan annenta nan duk sun taso sun cika gida yafi son ya soma aurar da ita kafin ya aurar dasu Ru ayya wa anda zasu kammala karatun su na secondry a wannan shekarar Kawu mutum ne mai zafi abu ani in yaji ansa yayi yakan iya kullo ofar gida ya zane shi tas ya huce dukkan ba in cikin talaucin sa akan a bai i ya karya a ya aje uwar sa tai jinya ba shiyasa duk hayaniyar an gidan daga kawu ya shigo zakaji sunyi tsit kamar Ba Wani an adam dake rayuwa acikin gidan. Ta shirya cikin ba ar doguwar riga wadda ta yane kanta da ba in mayafin doguwar rigar ta auki jakarta bayan ta dubi anwarta Ikram wadda bata fi shekaru goma ba tana zaune a saman tabarma tana shan koko. "Ikram jeki akin kawu kiwa ummammu magana ni zan fita" Ikram ta tura baki gaba tana hararar Farha. "Kutss ni kike harara Auta? dan ubanki ni sa'arki ce dan wa nake fafutukar fita neman aikin, idan danni da Umma ne sai mu sha ruwa mu kwanta jiya ina ba haka kikai ta mana kukan yunwa ba" Ikram ta mi e aguje ta fita daga akin sanin halin farha na rashin ha uri yanzu sai ta hau jibgarta. Ummah dake akin kawu taje kai masa kokon karin kumallo ita ta dubi Ikram wadda ta fa akin tana nishi. "Auta meye haka zaki shigo akin Kawunku da gudu?" Ikram data san halin kawu wanda ta ha a ido dashi yana zaune saman darduma da sauri ta koma da baya tana cewa. "Ummah wai yaya ce zata fita shine tace in gaya miki" Ummah ta dube ta. "To kuma sai kin yi gudu daga akin zuwa nan" Ikram ta koma bata bawa umma amsa ba sabida yadda taga kawu na zabga mata harara. "Nifa Hasiya na gaji har ga Allah, lamarin ku keda arki ya isheni haka tace candy na barta tace cigaba da karatu na barta wai mai kuke nufi da Salim ne?" Bai jira amsar ummah ba ya cigaba da cewa. "Maganganu ko ina nata tashi a cikin unguwa ance cin ku in sa muke alhalin ba bashi armu zamuyi ba, To ni Allah ya gani kuma shaida ne ban ta a amsar wandalar yaron nan akan Fatimah ba, Hasalima sanin danai wa mahaifinsa a matsayin sa na aminina yasa naji yaron ya ara shiga raina amman kun kafe sai tai karatu ta gama kunce sai ta kama aiki to nikam na gaji wallahi kuna kaini bango sai dai ta nemi w ani uban bani ba dan nagaji inji dana gabana ma mana haba jama'a" Umma tai asa da murya sabida an la e dan sana'ar matan gidan ne. "Kayi ha uri ka ara mana lokaci in sha Allah daga lokacin da zaka ara ba zamu haura ba" Kawu yace. "To kice mata na bata wata guda salim ya aiko na aurar da ita inta ara haura hakan to ta nemi wani uban ba Habubakar ba" Daga haka yaja rediyon shi ya kunna yabar umma ri e da ha Tashi tai ta fita tsakar gida cin karo tai da Babarsu Hadiza wadda tai saurin Komawa da baya tana sosa kai Umma tasan labe tai musu anjima ka an kawu na fita zata kwaza maganar a tsakar gida yanzu shakkar kawun ce ta hana tai mata habaici. Umma ta arasa akin. "Umma ni fita zanyi sabida na gaya miki wannan awar tawa tace yau yayansu yace zamu ga mutumin nan mai gidan rediyon kin san sabuwa ce tashar ana bu atar sabbin ma'aikata" Ummah ta bita da kallo. "Ke ko an man le e da hoda ba zaki saka ba? gaki ba a kin auki ba en kaya kin lafta babu wani armashi a shigar taki.................. 09022260850 *RABO YA RANTSE...!!* *NA* *AUTAR MANYA* ADABI WRITTER'S ASSOCIATION *005* Farha ta tura baki gaba ta cinno shi sosai nan da nan ta fara sosa ido kamar zatai kuka. Muryarta a sha e ta soma magana. "Haba umma wani irin ba armashi a shigata nida zan je wajan neman aiki kwalliyar me zanyi, nifa umma ba kyakykyawa bace koda nai kwalliyar ma ba kyau zata min ba nafi son fuskata a haka nidai fatana Allah yasa yau na dace dan wallahi har na gaji da zirga zirga" are maganar tana langwa ar da kanta kamar wata aramar yarinya koda yake in ba Sanin shekarunta kai ba tabbas zaka auka irin aramar yarinyar nan ce. Umma takai duba wajan kofin kokon data ajewa farha wanda bata shaba tace mata. "Ga kuma kokon naki baki sha ba, kin san dai ba wani ku in abinci zan baki ba iyakaci na baki Ku in mota daga nan zuwa ofar nasarawa nawa zasu kaikin?" Farha tace. "Ki bani ari biyar inda canji sai na dawo miki dasu, sannan kokon nawa ki rufen inna dawo zan siyo awara wajan Babar su Ru ayya na ha a naci yanzu sauri nake kada na makara" Ta kai maganar tana bu e handbag inta. "Kinga umma bani da canji a jakar tawa ma, bari nai sauri zan duba agogo a akin su Ru ayya tunda ba waya a hannuna yanzu tunda tawa ta fa a rijiya shikenan" Umma ta kunce Ha ar zaninta ta ciro Tsohuwar ari biyar ta mi owa Farha tana ce mata. "Ni gwarama da wayar taki ta fa a rijiyar sarai kin san abin magana bayawa kawun ku ka an, tunda ya saka dokar hana ri e waya gwara kin ha ura in kinyi auren kya ri e ta sannan kuma ki sauri yau karki kai yamma dan jiya baki je Islamiyar dare ba nan yazo kamar zai kawon duka sabida fa a kin san dai halin sa" Farha ta rufe handbag inta, Bayan ta saka Ku in aciki. "Umma duk su Ru ayya da wayoyin su nima Salim yace zai kawon in ya dawo daga lagos nina san zagon asa ake min a wajan kawu ba da ban an kai mai rahoto ba ina yasan ina da wata waya Munafukan banza" Tana fa in haka ta sanya kanta tabar akin Ummah ta bita da addu'ar nasara. aga labulan ofar akin su Ru ayya Tana cewa. "Mutanan akin nan suna kusa a duba min agogo?" Babar su Ru ayya ta ago kai tana wa Farha wani kallo. "A,a manyan ma'aikata yau kuma ina aka cillah?" Sarai farha tasan magana ta gaya