Sashe 11
Rabo Ya Rantse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*NA* *AUTAR MANYA* ADABI WRITTER'S ASSOCIATION *11* Zagaye aton Parloun shi yake hannun shi Goye a bayan shi Sam ba zaka fahimci inda Halin da yake ciki ya dosa ba Idanun shi ya rintse Har yanzu sautin Muryar yarinyar da take Labaran bai bar amsa kuwa acikin Dodon Kunnen shiba. "Iya sanina bani da abokin fa a a Wajan sana'ata Bani da Abokin Gaba bani da wanda na ta a Musayar Harshe dashi a ko ina Why zaku Min haka mai nayi Muku zaku ata min suna a idanun al'ummah idan wasu sun yarda wasu ba zasu yarda Ba" Da sauri ya Zube a gaban Ammi wadda ta tallafe ha a da hannunta hawaye nabin Idanunta. Ya kamo afafunta ya ora kanshi akansu. "Ammi ki yarda dani wallahi bani da Hannu a zubewar Cikin Mami, Arzi i Allah ne yayi Minshi nima ina mamakin Yadda duk abin da na ta a sai Allah ya saka mai nasibi Ke shaida ce ammi kinsan yadda Muka taso" Yana fara maganar Muryarshi ta sha e ya soma tari da gudu Ammi Ta bu e Frij ta auko ruwa ta alle Gorar ta fara bashi Musa na masa sannu. "Nina haife ka Nina san waye kai Allah ya tsareka daga dukkan wanda ya nufoka da sharri Allah ya kare ka daga dukkan sharri" Ammi ta fa a cikin kuka. Da gudu aya daga cikin masu gadin Gidan ya shigo falon Ammi ta zaro ido tana cewa. "Sun shigo su kashe min shi ko? ku taimaka Ku oye min shi kada a far masa" Mai gadin yayi Murmushi. "Hajiya ku godewa Allah, Ha a baka Alkairi ka ta e kamar yadda baka sharri ka gama lafiya, Dama zaki fito waje da sai Kin mayar da kukan ki Dariya sabida Ilahirin matasan Dake garinnan sunyi dafifi a ofar Gidannan domin bawa mai gida kariya, Yanzu haka mai girma gwamna ya turo da Motocin an sanda kusan Goma suna nan tsaye da Bindigu domin su bawa wannan Bawan Allah kariya Sannan matasan gari sun Je sun ona gidan Radion yanzu haka neman Mai gidan Radion suke ruwa a jallo dan dai basu sami Mutum Ko aya bane daga cikin ma'aikatan sabida kowa ya gudu" Ammi ta sauke ajiyar zuciya tana shafa kan Aliyu wanda ya kwantar dashi akan cinyarta. Ya kasa magana Har Ammi ta sallami su Musa Falon yayi saura daga shi sai ita. "Ka auka hakan wata nasara ce daga Allah in sha Allah hakan ba ze zama sharri gareka ba sai Alkairi kuma bana son kai fushi ka daina taimako wannan ma ya zama ara arfin ka wajan taimakon al'umma domin kaga ranar hakan da idanunka inda baka taimako da bamu san yadda abin zai zama ba, amman albarkacin al'ummar Annabi gashi kana ta samu kariya" Aliyu ya i magana sabida zuciyarshi yadda take a karye ta yaya za'a ce shike salwantar da Cikin Mami dan ya ara arzi i ta yaya za'a dangana dukiyar shi data tsafi shida ya sha wahala kafin ya tarata. Duk yadda ake kiranshi a waya ya kasa agawa Ta ya sadik ka ai ya aga data bashir wa anda suka aga hankalinsu akan Labarin da suka ji ya tabbatar Musu da cewa yana lafiya ya kashe wayar sai ta mai girma gwamna wanda ya bashi ha uri yace kada ya saka abin aranshi hakan ma matakin nasara ce Kuma gwamnati zata auki mataki akan shugaban Gidan radion dan zata binciko shi harma wadda tai labaran. Bayan ya gama jin jawabin gwamna yayi godiya sai dai yace wa gwamna yabar Batun tuhumar mai gidan Radion shida kanshi zai Bibiyi Lamarin dan ya auki matakin daya dace sosai sukai magana da gwamna kafin yayi masa sallama bayan yace ga Jami'an tsaro nan ya Turo masa dan su kare lafiyar shi data iyalin shi yayi Godiya ya katse wayar. Yawan an jaridar dake ofar Gidan ya kai ya kawo dan an jarida kamar su fasa gidan su shiga su auko rahoto haka suka taru ga jama'a kota ina wannan tasa aka rufo gidan ma gaba aya ya zama ba shiga ba fita daga gidan Madaki ma sosai an uwan su Aliyu suka girgiza nan da nan Baba Usman anin Mahaifin Aliyu ya saka malamai aka hau sauke alkur'ani mai girma. Mami kuka take tana kiran layin Aliyu dan hankalinta gaba aya yana kanshi Ko ka an bata yarda da wannan labari ba sabida tasan waye Mijinta har ya fita damuwa akan asarar Cikin da suke yi Suma gidansu Mami sai rufe ofa sukai sabida Yadda jama'a ke dafifin shigowa jaje. Yana rangaji ya mi e da sauri Ammi ta taimaka masa ya haye saman shi ya fa a saman gado yana Lumshe idanunshi Ammi ta rufo masa ofar Ta nufi sashin sa da yar ta rarrashi su sajeeda wa anda suke Kukan abin da aka wa yayan nasu. Wayar shi dake Ringing a karo na ba adadi ya laluba ya aga Muryar mami ke sauka cikin kunnen shi. "Yaya dafatan kana lafiya? wallahi ni na yarda dakai Mijina sabida haka ka kwantar da hankalin ka wannan shiri ne na ma iya" "Umm" Ya amsa mata ya kashe wayar yayi shuru yana sauraran Bugun zuciyar shi. an jarida da sauran jama'a gajiya sukai suka bar ofar gidan har zuwa dare ba aji uriyar shiba amman an tabbatar yana cikin oshin lafiya dama shi haka tsarin sa yake in yana cikin damuwa shuru yake In yana cikin acin rai shuru yake ya killace kanshi wannan tasa Ammi bata sake komawa wajan shi ba tasan yana tunanin mafita ne na wannan matsala data afko masa. *********** Gaban Farha ne ya fa i sanda taji kawu na Allah wadai da Wannan tasha ta garkuwa wadda ta ata sunan Aliyu Matan gidansu kuwa masifa suke suna kumfar bakin cewa ba in ciki ne yasa akai masa sharrin ba wani abu ba ara jan abin rufa tai tana Sakin Hamdala da Allah yasa babu wanda yasan a tashar take aiki kuma ba sunanta a labarin sannan bata can aka ona gidan rediyon kamar yadda taji labarin a tsakar Gida cewa an ona gidan rediyon. Damuwar ta aya wannan sharrin data ja gaba wajan ya awa Ina zata sami wannan bawan Allah ta ro e shi gafara tsananin tsoro da damuwa sune suka ara haddasa mata zazzafan zazza i zuwa dare Jikin Farha ya ara rikice wa wanda hatta an gidansu sun tsorata dan kuka take tana cewa umma ta yafe mata mutuwa zatai Duk zafin kawu sai da ya ru e Salim ne ya kirawo Nurse aka saka mata ruwa aka mata Allura Wanda bacci yayi awon gaba da ita. *********** Daran ranar Aliyu bai bacci ba yadda yaga dare haka yaga rana, Ba abin da yake sai sallah yana ara neman gafarar Allah akan dukkan laifukan sa tare da neman tsari da kariya daga dukkan sharri sai da yayi sallar asubah sannan ya sami bacci arfe goma ya farka ba laifi ya sami nutsuwa sosai harya fito Parlou yana amsa jajen ma'aikata yana kuma aga wayar mutanen sa masu yi masa jaje. arfe sha ayan safe Musa ya araso Parlon nashi bayan sun gaisa ya dubi Musa........*RABO YA RANTSE! littafin ku i ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a auka a turo,shaidar biya 09022260850* *RABO YA RANTSE...!!* *NA* *AUTAR MANYA* ADABI WRITTER'S ASSOCIATION *12* Muryar shi a kausashe wadda ta nuna zallar acin ran daya kwana dashi. "Musa ina son lallai a yau ka gano min inda mai gidan radio innan yake inda hali katafi da jami'an tsaro cikin fararen kaya, su Kama min shi tabbas sai ya gaya min meye nufin shi akaina zan nuna masa ni in wanene in aka shiga gona ta" Ya fa a yana fesar da numafashi mai arfi. "Sannan ita ma yarinyar datai labaran lallai ina son sanin wacece" Ya fa a yana jingina kanshi a jikin kujerar da yake kan ta a zaune. A hankali ya furta. "i will not leave them" ago ya kalli side in da musa yake ya furta. "kuma a yau nake so ka ai watar da komai ba sai gobe ba" Musa daya tsorata da yanayin mai gidan nashi jiki na rawa yace. "I will do my best for that" Daga haka ya aga ma Musa hannu yana cewa. "Thank you very much Musa" Da hannu ya dinga caku a sumar data ke kanshi Duk ranshi a ace yake mai yasa mutane suke haka tabbas inda sun san girman laifin da sukai masa da idan ance su ara ma wani irin sa baza suyi ba. Ya cije baki. ya tashi ya koma bedroom inshi yau ko wajan Ammi bai le a ba yana jin wayar shi na ringing bai bi takanta ba. Musa yana tafe yana tausayawa Mai gidan radion sanin waye Aliyu Sar a ne fa i kirikice Sar a ne mai rikicin gangan Dangin za i ne Layin zuma. Direct police station ya nufa sannan ya bu aci a bashi an sanda Guda biyu Batare da sun saka uniform insu ba Haka suka nufi Gidan Radio in Abin yayi mati ar bawa musa Tsoro na yadda yaga an ona gidan Radio urmus ba wani abu na mora aciki Wajan ba kowa sai Mai gadi wanda su Musa suka arasa wajan sa yana zaune a saman Banchi su musa suka arasa suka mai sallama. Mai gadin Irin Iyamuran nan ne Bayan sun gaisa bai da hausa sosai ya dubi Musa yana tambayar shi. "What do you need here" aya daga cikin Police in ya kalli mai gadin yace masa. "We will ask you a few questions" Mai gadin ya zuba musu ido sabida dama tun jiya a tsorace yake dandai kawai son ku in shi na albashi shine ya zaunar dashi Kowa yasan abila akwai ri o da aiki baya wasa dashi. "I hear you,what is your quesion?" Ya fa a yana kallon an sandan daya masa magana. Musa ya an dube shi. "Gidan mai wannan gidan radion muke son ka nuna mana?" Mai gadi ya zaro idanu cikin hausar da bata ishe shi sosai ba sabida yana jin hausar sosai amman Mayar da amsar ne take basa wiya.