← Book details Rabo Ya Rantse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 94

Sashe 81

Rabo Ya Rantse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sallar isha'i dan har Lokacin bai tafi ba Yazo dan yayi wa Ammi sallama. Ammi ta dubi Musa. "Musa in ban takura maka ba dan Allah ka kaini Gidan surukan Baba nida salama Tunda bata zo da Mota ba In mun dawo ka ajeni seka wuce da ita Gidan ta" Musa yace. "To babu damuwa" A ladabce. Ammi ta shirya bayan ta Zuzzuba kayan arzi i acikin atuwar Leda Salama ta auka suka Fita sajeeda ta yafa mayafin abaya akan ta tabi bayan su safna wayar da suke da Kamal sam bata san fitar su Ammi ba. Harabar Gidan suka Nufa suka shiga Cikin mota Musa yaja Motar suka fita kai tsaye Gidan su farha suka Tafi a bakin layin Musa yayi parking shine yayi wa su Ammi jagora har ofar Gidan sannan ya koma Mota ya zauna Jiran su Fito su Koma gida. Gate in suka tura suka shiga gidan ko ina hasken farin wan sola ya haske Gidan, Suka shiga ofar Babban falo wanda ilahirin Mutan gidan ke zaune wasu na kallo wasu na cin abinci Salma tai sallama Babar su Hadiza ta amsa tana cewa. "Maraba lale Ku shigo mana Ku zauna" Duk su Ru ayya suka zubowa su Ammi ido suna kallon an gayu akan Kujera su Ammi suka zauna suna gaisawa da Babar su Ru ayya da Babarsu Hadiza. Shuru ne ya biyo baya kafin salma tace. "Yawwa dan Allah Munzo wajan Maman Farhan ne Ko tana nan?" Da sauri Babar su Hadiza tace. "Eh tana ciki Bata fiya fitowa waje bane" Su Ammi basu saurare taba suka Mi e Babar su Ru ayya tai Musu jagoranci har zuwa akin Umma. aramin falon Umma wanda yasha an madaidai tan Kujeru daidai shi tare da aramar TV'n jikin Bango su Ammi suka zauna Ikram dake zaune tana Cin Tuwo jin sallama da zaman Mutane a falon Yasa ta ago tana kallon su. Kafin tace musu. "Sannun ku da zuwa ina yinin ku" Ammi ta zubawa Ikram idanu. "Lafiya lau ammata Ina mamanki?" Cewar Ammi har Lokacin tana kallon Ikram Kyan yarinyar yana fusgarta wato ita matar Baba Ita ce ba a a gidan tunda ta lura duk an matan falon farko farare ne masu Jiki kyawawa ma sha Allah. Ashe ba Ammi ce ka ai ta shiga mamakin ba har su salma da suka saki baki Tun farkon Shigowar su suna kallon kyan an Gidan So Ma sha Allah! Ikram ta mi e ta shiga aki domin Kiran Umma dan Babar su Ru ayya tun da ta rako su Ammi ta fita daga akin don ta basu Guri. Ikram ta shiga cikin akin Umma wadda take zaune a saman darduma hannun ta auke da carbi mai Dubu tana jan shi...........Autar manya ce marubuciyar...... OYAYYAR AUNA* *BA SON TA NAKE BA* AN MAJALISSA* *MURADIN ZUCIYA* *ASHE ZUMA* *TAURARO* *KOBA SO* *RABON WANI* *FITAR RABO* *DA IZZATA* ON LAMARI* *AUREN BARE* *H A S K E* *ZUMA A BAKI* AR FATA* *RABO YA RANTSE* *RABO YA RANTSE! littafin ku i ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a auka a turo,shaidar biya 09022260850* AUTAR MANYA Arewabooks autarmanya *A LOVE STORY 97* Rabo ya rantse A gefen gado ta zauna tana jiran Umma ta shafa zaman Kusan Minti Goma tayi kafin Umma ta arasa lazumin ta shafa tana kallon Ikram. "Har kin gama cin tuwon kenan amman dai ba bacci zaki ba Ko kin san akwai Guga a gaban ki gaba aya kayan ki babu guga" Ikram tace. "Ehh umma ba kwanciya zanyi ba ba i Kikai suna falo suna Jiran ki" Umma tahau salati tare da cewa. "Amman anyi sakaran yarinya salon suce na wula anta su shine baki gaya Mini ba su waye?" Ikram tai dariya tare da cewa. "Wallahi ban san suba Nima Umma kina lazumi se kawai na katse Miki Kefa kika hanamu Yi miki surutu In kina lazumin Ki" Umma ta na e abin sallah tare da kama hanyar Fita tana ara yiwa Ikram fa a akan mai yasa bata gaya mata ba Har ta arasa fita falon da far'arta da komai. "Ah maraban ku lale marhaba sannun ku Da zuwa dan Allah Kuyi ha uri Wai Ikram data tarar ina lazumi shine bata gaya Mini nai ba i ba" Ammi da far'arta itama tace. "Ai ta kyauta sosai Koni bana bari sumin magana In Ina lazumi sabida ata nake yi" Umma tai dariya tana fita daga falon Babban falo taje ta Bu e Fridge ta auko Ruwa da lemo ta zubo a tray ta Nufo aramin falon sabida yanzu Alhamdulillahi Tunda Aliyu ya Bu ewa kawu aton shago wanda yake sayar da kayan masarufi Shikenan Suka ara wadata dan babu abin da kawu baya dire Musu gana Aliyu duk arshen wata gana su Halifa duka shiyasa gidan sedai Godiyar Allah. Umma da sallama ta shigo falon ta aje Musu ruwa da Lemon sannan ta Kuma fita ta ebo Cincin a plate ta kawo Musu. Zama tayi a asan carpet tare da cewa. "Ikram zoki kawo Musu tuwo Ki duba sama akin su Halifa Ki auko Babban Fulas in tuwon yana can azu aka kai Musu" da yake ranar Girkin Umma ne. Ammi data saki baki tana kallon karamcin matar tun kafin tasan daga ina suke su waye su Ammi take haba haba dasu Se wata Kunya ta kama Ammi yanzu wannan mata mai Kirki da mutunta an adam ita ce ta haifi ar da anta ya aura Amman ta kasa Ri ar da daraja Lallai Aliyu ya auro ar Mutunci dan ba tarin Dukiya ake bi a aure ba ka auro ar Daraja ar Gidan Girma da tarbiya shine kayi aure. Kafin kace me Ikram ta fita se gata da kwanukan tuwo da Miya ta aje Musu Umma tace. "To dan Allah Kuci mana Duk da ban sheda kuba Amman ai ba o daraja gare shi" Saboda Umma ba wayewa tai da Aliyu ba shiyasa bata gane suba Amman in da tasan shi sosai data kalli salma taga Aliyu don suna kama sosai Haka zalika Ammi to da yake bawai kallon shi Umma tai ba shiyasa sam bata gane su Ammi ba. Sajeeda ta auki ruwa salama ta auki Lemo Ammi kam bata auki Komai ba se Murmushi take kawai tana Hamdala a zuciyarta. "To Nidai sunana Hajiya Amina amman ana ce Min Ammi mahaifiyar Aliyu Mijin fatima dama Mun zone domin Mu sada zumunci wa annan Duka annen shine su basa nan sun anyi ar tafiya" Ammi ta fa a Cikin Nutsuwa Se Umma ta Kuma washe baki Cikin farin ciki tana cewa. "Kai Ma sha Allah abu yayi da i sannunku sannunku mungode Mungode Allah yasa ka muku da alkairi Muna ta ganin hidima daga wajan Aliyu Amman Farha ce har yau bata zoba" Umma ta arasa fa a Cikin rauni. "Kallo aya ammi tai mata tasan Tabbas rashin iyarta yana susar ranta" Ammi ta dafa kafa ar Umma. "Ki ha uri Maman fatima arki tayi dacen Miji ba danni na haifi abuna ba a,a wannan magana ce ta gaskiya nake Yi Miki ita Ki Godewa Allah Surukin ki an albarkana ne Kinji Ki kwantar da hankalin naji duk yadda auren su ya kasance wanda Ma asudin auren nasu zazzafan rabo Ne don yanzu haka fatiman ki nada ciki har na wata Uku" Umma setai asa da kanta sega hawaye nan Ammi bata hanata Kukan ba dan daga Umma har Ikram Kuka suka saka wiwi Umma har tana ajiyar zuciya kafin Salma ta soma rarrashin Umma. Cikin haka kawu ya aga labule yana cewa. "Asiya zo mana ga kaji nan na kawo ki gyara su Gobe Musha dabge a gidannan Asiya kina ina......"maganar kawu ta tsaya sanda yaga ba i a zaune a falon Ga kuma Umma tana share hawaye a ru e yake magana. "Asiya Ke Ikram Kukan me kuke wani abun akai Muku?" Duk ya fa a a ru e Su Ammi ne suka katse masa tambayar wajan gaishe dashi A mutunce suka gaisa da kawu kafin Umma tace Muryarta a sha "Surukar mu ce tazo Babar Mijin Farha" Se kawu ya zauna ana sabunta gaisuwa. Ammi na dariya tace. "Wai fa daga Munce mata Fatima nada Ciki shine take wannan Kukan" Kawu ya fara tafa hannu yana cewa. "Ai halin Asiya se ita wallahi Koda yaushe haka nake fama da ita ta i kwantar da hankalin ta akan auren nan na fatima Kuma na gaya mata dama wani alkairin baya samuwa seda alubale ni kaina na shiga damuwar data kaini ga kwanciyar asibiti bayan dana bawa Ali fatima batare dana san ko shi waye bane sabida zuciyar danai na bijire Min datai akan umarnina na wanda na bata tace Ita Ali take so to daga arshe daya zo nan Ya gaishe ni wallahi se naji na yarda dashi Amman Asiya ita ta i sakin hankalinta Kullum tunani Kullum Kuka sabida jarabar son da ta auka ta orawa Fatima kamar ita ka ai ta haifa a duniya" Ammi dariya ta saki Sajeeda da Salma asa sukai da kansu Suna dariyar Dramar Kawu lallai mahaifan fatima ba aramin Son ta suke Yi ba. Ammi ce tace. "Lallai dole na bawa Fatima kyauta wato akan Babana tai ya i ba an ka an ba lallai fatima ar soce yadda Mamanta ke son ta Nima haka nake Son Baba kaf yarana yafi damuwa dani baya son damuwa ta Allah de yayi Musu albarka bai ayan su" Se kuma aka shiga hira yadda Kawu yake hira da Ammi kai kace sun jima da sanin Junan su, Dan Ammi batai wata alkunya ba sosai ta sake suna hirar su da kawu kafin Umma tasa Ikram ta Kira matan gidan ta gabatar Musu Da Ammi a matsayin uwar Mijin farha wadda nan suma suka zauna suka gaisa dasu Ammi kafin su tashi subar wajan. Ya Nura ne ya shigo akin Umma yana kiran Ikram ta zuba mai Miya tunda ya shigo sajeeda ta zuba masa ido gabanta yana fa uwa ta Lumshe ido har wata iska ke ka ata sabida ganin Nura matashin saurayi fari an dumurmur mai Jini a jika. "Nura ga Mahaifiyar Mijin farha Ku gaisa" cewar Umma Ya Nura
Chapter 81 · 0% Book details