← Book details Rabo Ya Rantse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 94

Sashe 92

Rabo Ya Rantse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nikam yaya tsoronki nake sabida wannan layar da Kika amsa ba mamaki In kika rasa gawar da zaki sakawa Ki Zuban guba nasha na Mutu ki sami Gawar da zaki cusa layar aciki dan yadda idanunki ya rufe ason duniya ba abin da ba zaki ba Ni yanzu yaya na nutsu yanzu haka maganar aurena ta taso Ni na yarda dake ashe Ke da wata manufar taki ta daban akaina wato Ke anki da Mijinki ka ai Kika sani wallahi yaya kin bani mamaki" Sakina tasa kuka. "Wallahi Ni kaina ban san ina layar take ba jamila kema tsayin wata hu u ta yaya zan ajeta har sekin zo na saka Miki Ni na san abin da yake damuna wato tunda naje ma abarta kai layar nai gamo se firgita nake Kullum bana iya bacci ar uwata kizo Ki Tayani Kula da ana" Jamila tai dariya. "Yaya sakina an fa kai Ku in aurena tun bayan tawowarki dama ina da wanda yake sona Yadda Kika dage sena auri Ali ne yasa nake ta zabga masa wula anci to Allah ya nunan manufarki sena bawa mai sona dama yanzu haka shirin aure nake Nina hana kowa ya gaya Miki wato Ni na are a bauta Miki keda anki kada nai aure ai Firgita da bala'i yanzu kika fara gani tunda kin kasa gane Cewar Allah aya yake bai da abokin tarayya Nikam In sha Allah na dena zuwa wajan Kowa zanyi aurena na cigaba da istigifari babu ni'imar da Allah bai Miki ba amman ke kin raina wannan Ni'imar taki ta wanin ki kike hange wanda wani Irin takin yake nema bai samu ba lallai kin aura afa da masifa Tunda baki yarda da Allah ba" Jamila tana gama fa a mata hakan ta kashe wayarta tana tsaki domin tun sanda suka je wajan wannan Boka da jamila taji maganarsu lokacin da ta fita waya taji Komai ya sire mata lallai mutum bai da tabbas. Sakina tai Kuka har ta gaji haka ta aje wayar sedai tun bayan tawowar sadi take wasu irin Muggan mafarkai wanda abin har yakai ga tana ganin wata irin halitta mai kama da adangaru manya ba e a zahiri sosai sakina take Firgita ita ka ai taita sosa jikinta daga yaranta sun zo inda take ta rufe su da duka ga ananun zance ita ka ai taita magana tana dariya ka an ka an abun na sakina fa se du'ai. *KANO* Autar manya ce marubuciyar...... OYAYYAR AUNA* *BA SON TA NAKE BA* AN MAJALISSA* *MURADIN ZUCIYA* *ASHE ZUMA* *TAURARO* *KOBA SO* *RABON WANI* *FITAR RABO* *DA IZZATA* ON LAMARI* *AUREN BARE* *H A S K E* *ZUMA A BAKI* AR FATA* *RABO YA RANTSE* *RABO YA RANTSE! littafin ku i ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a auka a turo,shaidar biya 09022260850* *RABO YA RANTSE 105* Duk yadda sadi yake zaton yanayin Jikin Ammi abin ya wuce tunanin sa sabida gaba aya Jikin nata ya rikice bata da magana se ta akira mata Baba kada ta mutu bata nemi yafiyar shiba wannan tasa Likita yace a dena zuwa wajan ta aka barta ita ka ai a akin se Likitan dake zuwa dubata dan koda yaushe Jininta baya sauka ga ciwon kai mai tsanani dan bata yin bacci ganin haka yasa Sadi yaje ya shaidawa an uwanta da kuma dangin mahaifinsu an cikin Gida ranar asibitin ya cika da an uwa Sosai su Baba Usman sukaiwa sadi an mai yasa bai gaya musu abin da yake faruwa ba nan da nan Baba Usman yasa aka fara ro on Allah akan Allah ya juyo da hankalin Aliyu gida a duk inda yake sannan ya sa aka sallami Ammi daga asibitin Gida suka dawo aka fara rubuce mata alkur'ani ana wanke mata da ruwan sama tana sha waraka ne ga dukkan damuwa ko ciwo ko wata matsala Cikin Amincin Allah ta fara dawowa daidai Jikin nata ya soma sau i Ammi kuka ta sanya tana ro on gafarar su Baba Usman suma Kuma haka suka nemi gafararta Suka shirya kamar ba su ta a Yin gaba ba zaman su yay da i dan koda yaushe Ilahirin zuri'ar cikin gida suna wajan Ammi suna Kula da ita Dan tuni baba usman yace wa salma ta koma gidanta Umma suwaiba ce ta dawo Gidan sabida ta dinga ebe wa Ammi kewa ga kuma su Hajja dama ance Shi an adam rana gare shi Kuma Alhamdulillahi a wannan karon dangin mahaifin su Aliyu sun nuna bajintar su domin sunyi zumunci akan matsalar Ammi da kuma tafiyar Aliyu dan har masallatai Baba Usman yakai Barar addu'a akan a taya su da addu'a Allah ya juyo da hankalin ansa Gida. Acikin wannan adamin Iyayen Kamal suka zo wajan Baba usman akan maganar auren safna wanda ada mahaifiyar kamal taso ta dakatar dashi ta hanashi auren safna sabida akwai wadda taso ta bashi Amman yadda yake son safna yasa mahaifiyar shi ta amince masa akan ya aure ta in tare dayi Musu fatan alkairi haka aka kawo ku i da saka ranar safna da kamal watanni Biyar masu zuwa Al'amarin soyayyar Sajeeda da Nura abin Kullum gaba yake daga wajan ta amman ta Rufe ba wanda ta sanarwa addu'a take wanda ita ce ta zama garkuwanta don sosai take Komai kan hankalinta tana jin Nutsuwa na saukar mata tare da neman za in Allah akan lamarin Domin haka mahaifiyarsu ta koyar dasu akan Komai nasu su nemi za in Ubangiji. Kimanin sati Guda da faruwar Komai yau da safe Jikin Ammi ya motsa Wanda gaba aya kowa ma ya karaya da ita dan se Neman gafarar kowa take sadi daya ha a kaya ze Koma lagos se Zama yayi ya sakata a gaba yana Kuka zuwa yanzu Ji yake inda yasan inda Aliyu yake daya Je yazo wa Ammi dashi dan ya shaida wata irin soyayya ce a tsakanin ta da Aliyu Zamzam Baba usman ya auko yana tofa mata addu'a aciki ya bata tasha wanda anan ta samu bacci. ALIYU Gaba aya Aliyu jinsa yake wani iri acikin wa annan Lokuta sanyin Jiki da fa uwar gaba sun sako shi a gaba Tun farha na tambayar shi har Tai masa shuru dan itama ta kanta take yi. Yau tunda ya tashi ya i ma fita Aiki ba wadda yake son gani se Ammin sa kawai seya tashi yahau ha a kayan su Seda ya ha e kaf sannan yace wa farha. Ta tashi su tafi kano ta kalle shi tare da cewa. "Kamar yaya Kano kuma nidai gaskiya ba zan iya doguwar tafiya da wannan cikin ba" A fusace ya kalleta. "In ba zaki tafi ba seki zauna Ni mahaifiyata nasan tana bu atata a wannan Lokacin Jin Garin nan nake kamar wuta" Dama addu'a ai bata fa uwa asa yadda an uwanshi da Mahaifiyar shi suke addu'a Allah ya juyo da hankalin shi gida ne yasa yaji kadunan tai masa zafi. Farha taji takaicin wannan magana daya ya a mata wato ya mayar da ita sakarai. "Nima an uwana da mahaifana suna bu atar ganina dan haka kona koma kano ba zan zauna Kamar da ba wallahi a wannan karon Sedai ai wadda za'ai Koka sake ni Koka Sama min Gidan da zanzauna cikin an cina dan ba zan Kuma Irin zaman danai a baya ba na gaji ni ma ace kamar Kowa kuma mace kamar kowa" Bai kula taba dan ya fuskanci a sama take ya sa i kayan a kafa ar shi Suka fita dan jaraba ko wanka babu wanda yayi acikin su daga Inno har su shafa basu Ji da in wannan tafiya ba dan Inno harda Kukan ta Aliyu yace su kwashe kayan abincin da komai da suka rage Kuma ze waiwaye su komin Bajima komin ba da e haka Suka rabu duk babu da i dama bahaushe yace sabo turken wawa suna zuwa tasha suka sami Motar kano Haka suka shiga ya biya Ku in Mota tafiya sukai har zuwa garin kano gaba aya afafun farha sun Kumbura Duk ciwo suke mata Har suka sauka Da yar take taka afafun Napep ya samu sukai tsada zuwa gida bayan ya zuba musu kayan su acikin napep in farha ta Tsaya ta i shiga napep in a wahalce ya juyo ya kalleta sabida Shima ba aramar gajiya yayi ba. "Fatima muje mana" Ta juya fuskarta wadda ta ha e ta tamau tace. "Ni gidanmu zani danni ma mahaifana suna Bu atar ganina Rabon umma dani Har wata nawa dan haka kowa yayi Gidan su kafin asan abin yi dan ba zan ara zaman rashin an ciba wallahi in ada nayi ha uri yanzu ba zan iya ba" Ta fa a da iyakacin gaskiyarta. "To shikenan Indai ni nake ri e da igiyoyin auren ki ban amince Kije gidan kuba In kuma kika je keda Allah ai seki bari muje Gidan Ammin tukunna kiga wace irin kar a zasu yi Miki kafin ki auki mataki Kuma ke ai sheda ce tunda can ban yarda an taka mutuncin kiba" Kuka tasa tana cewa. "Dan kawai kana aure na seka ha a ni da Allah bayan kasan tsoron sa ze hanani tafiya gidanmu nidai na cuci kaina dana za i auren ka" Murmushin takaici yayi bai iya magana ba Ya shiga napep in haka ta shigo itama tana ta Kuka ya sassauta Muryar shi. "Dan Allah fatima ki shuru kinga a condition in da kike ki rufa mana asiri ki haihu lafiya" Da ire iren maganganun nan yayta kwantar mata da hankalinta har ya samu ta dena Kukan se ajiyar zuciya ya kama hannunta ya ri e tare da cewa. "Inna Cutar dake Allah baze barni ba haka zalika inna juya Miki baya Na zama butulu fatima ba irin wannan zuwan nake so kiyi wa mahaifan kiba Duba duk kin rame Kinyi duhu kowa ya ganki yasan bakya cikin kwanciyar hankali Na fison ki zuwan da kowa ze sha'awarki mahaifan ki suyi alfahari da aurena da kikai dan Allah ki Nutsu mubi komai a sannu" Ko kula shi ma tayi banza tai masa dan zafin Ammi take Ji sosai dan se yanzu ma take ara tuno Cin mutuncin data
Chapter 92 · 0% Book details