Sashe 66
Rabo Ya Rantse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sun mata ka an basa shigarta yanzu sabida yadda irjinta ke rinjayarta se kayan da Musa ya kawo mata take sakawa Take harkokinta Daga akinta zuwa falo Tare dasu Dady dasu ka manne mata dan Ko bacci ma tare suke yi. Salma Farha na bata tausayi sosai haka zalika Aliyu gaba aya tausayi suke bata tunda ya gaya mata halin da suke ciki shida yarinyar taji tsananin tausayin su ya kamata ita ka ai take juya abin aranta Ta rasa wa zata gayawa Taji da i Dan shi kansa Mijinta ya lura bata da kuzari yayi nacin ta gaya masa meke damunta tace azumun da take yine ka ai da kuma yanayin aikin ta dama shi mijin ta bamai sa ido bane koda yaga farha sau aya bai tambayi salma wacece ba tunda yasan ba zata kawo masa wadda bata da ala a da ita ba daman ita ma farha ba fita take ba tun da suka ha u sau aya basu sake ha uwa ba. Kimanin kwanaki ashirin da fara azumi rabon farha da Aliyu tun wayar da yayi mata ranar daze tafi abun na damunta sosai na yadda bai ta a kiranta ko a wayar anwar shi yace a bata ba, wani bin inta kwanta haka zatai tayin kuka har bacci ya auke ta a hankali ta shiga tsananin damuwar rashin Mijinta wanda bata san tana son shi da yawa ba seda sukai nisa da juna Komai dai gashi nan a gidan salma amman baya burgeta har taji tafi son zaman gidan Ammi duk da wiyar da take ci amman ai da sau i tunda tana tare da Mijinta Kome tace tana so se salma ta samo mata fara ma da take so Har ta isheta sabida Kullum in salma ta dawo daga aiki seta siyo mata Tsabar yadda ta saka damuwa aranta yasa daga tasha ruwa zazza i yake rufeta haka Zata udundune taita rawar sanyi se cikin dare yake lafa mata sannan ga abin da yake tsorata ta shine Motsin da cikin ta keyi mata Haka zata dafe cikin tana jin yana motsi taita hawaye seta ci ayaba Guda goma arana tana fatan Allah yay gaggawa fitar da tsutsar da take damunta acikinta. Yau azumi kwana ki ashirin da biyar Salma ce ta shigo akin farha kasancewar week end ce ranar babu aiki ta zauna a bakin gado farha kuma tana kwance Cikin bargo yanzun ma kukan ta gama bayan tayi sallar azahar ta kwanta bacci. "Aunty fatima bacci kike yi ne dama zaki bani size in kayan kine sabida zan mi a mana inkin sallah" cewar salma farha ta mi e zaune sabida bata da nauyin bacci. Salma ta kalleta tace mata "Subuhanallahi Aunty fatima kuka! kuma kukan me kika yi haka fuskarki duk ta tashi haka kodai kina Missing an uwana ne?" Salma ta fa a tana Juyawa Kusa da farha suna fuskantar Juna farha cusa kanta tayi a cinyoyinta tana oye fuska sabida maganar salma ta bata kunya "Dan Allah ki sanar dani Ko kina Missing an uwa ne?" ga mamakin salma se taga farha ta girgiza kai se kuma ta fashe da kuka Mai arfi tana yarfe hannunta......... *RABO YA RANTSE! littafin ku i ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a auka a turo,shaidar biya 09022260850* *A LOVE STORY 84* "Subuhanallahi abin har ya kai haka Aunty fatima kuka kike yi meke damun ki me nake yi miki zama dani ne bakya so ko wani ke takura miki agidan nan?" salma ta fa a duk a ru e farha kasa magana tayi kuka take yi sosai wanda hakan ya ara tsorata salma Sabida ko jiya da sukai waya da Aliyu seda ya ara jaddada mata cewa ta dinga kula da fatima sosai sa ani suke dashi duk sanda ya kira salma Ita kuma bacci take idan yace a bata wayar salma seta ce masa ba'a son mace idan tana da ciki ake tashinta daga bacci wannan tasa tun yana cewa ma a bata in ya kira har yama dena sedai kawai ya kira salma su gaisa ya tambayi lafiyar matar sa ya kashe wayar tunda ya yarda da salma ari bisa ari yasan ba zata cutar masa da fatima ba shiyasa Ya saki hankalin shi bai damu ba. Goge hawayen daya wanke fuskar farha salma take da hannunta jikinta duk yayi sanyi muryarta a raunane ta kuma cewa "Kin i min magana fatima dan Allah ki gaya min in da wani abun da yake damun ki, an uwana ya dam a min ke amana in na bari wani abun ya same ki naci amanar zumuncin Allah Ko baki da lafiya ne duk kin min shuru?" salma ta fa a kamar zata yi kuka girgiza kai farha tayi tare da sauka daga saman gadon taje ban aki ta wanko fuska ta dawo ta tarar da salma ta zabga tagumi daga nesa da salma ta zauna muryarta har lokacin bata saki ba tace "Aunty salama wani gagarumin abu ne yake damuna" salma ta ago a sa ule tace mata "To fa wani abu ne Aunty fatima wanda har ya sakaki wannan kuka haka wanda ya aga mini hankalina?" farha ta sunkuyar da kanta asa sabon kuka ne yake tawo mata cikin kukan tace "Nina san arshena ne yazo ila mutuwa zanyi ma" salma tai saurin matsawa kusa da ita tare da cewa "Subuhanallahi Aunty fatima baki da lafiya meke damunki amman baki gaya min ba?" ta fa a tana kama hannayen farha, Farha ta kuma fashewa da kuka! kafin tace "Ni ka ai nasan abin da yake damuna na rasa jin da in bakina kullum yawu yayi ta taruwa naita bacci kuma kome naci bana jin da in sa ban sani ba ko arshe nane yazo shiyasa Allah ya zaren anon komai" salma ta kusan hantsilawa sabida dariyar data zo mata batare data shirya taba da yar salma ta saita kanta tana sauraran Farha wadda take ta faman kuka can kuma ta cigaba da cewa "Aunty salma bazan oye miki ba tabbas akwai abin da yake ajiye acikinnan nawa babban tashin hankalina Allah yasa Ba wata masifar bace Dana gaya masa kwanaki yace min tsutsar ciki ce sabida da farko tauri cikina yake min wajan asan marata shine yace mini na dinga cin ayaba tsutsar ciki ce To yanzu fa abun ya gagara yakai ma ura dan motsi sosai nake ji acikina har dafe wajan nake bari ki gani" da sauri salma ta dafe hannun farha wadda take arin aga mata rigarta duk yadda salma taso danne dariyarta ta kasa tashi tayi ta fita falo ta kwanta a saman Kujera tai dariya ta godewa Allah har cikinta seda ya kusan ullewa wato Yaya Aliyu abin da yace wa ar mutane kenan ya orata a keken era wai tsutsar ciki gareta. Wato shi wayo ga mutum halittace wasu ammatan suna da wayo da ganewa In wata ce da sauri zata fahimci Halin da take ciki, amman ita wannan sam bata gano kome ke damunta ba yadda mijinta ya orata haka ta tafi, to ta yaya bata gane tai Missing mp inta ba cewar salma a zuciyarta Koda yake in kana cin Damuwa bama ka gane kanka wata il tsananin damuwar gidan Ammi da yarinyar ke ciki ce ta hana ta gano Kana lamarin ta salma tashi tayi tare da komawa akin ta tarar da farha zaune ta rafka tagumi. Zama tayi wata dariyar tana ara tawo mata tana danneta "Aunty fatima karki damu babu wata matsala acikin ki ina zaton Kina da ulcer ne kin san ita ulcer Sihiri gareta Yadda takewa Mutum acikin sa seya rantse Ma ciki gare shi" farha ta share hawayenta "Wallahi Aunty salma abin yana damuna sosai, nace to kada naje ko wata gagarumar matsalar ce a tare dani abun yana damuna sosai ban dai gaya miki bane ni naketa fama" salma ta dinga kwantar mata da hankali ta nuna mata wannan motsinfa ba mamaki ulcer ce ke damunta Seda salma ta kar i size in Farha na kayanta sannan ta mi e tsaye "bari naje na kai mana inkin kafin ashara ruwa zan dawo in sha Allah" farha ta an kalleta "Amman Aunty salama sefa an aran rigata dan waccan tai min ka an dama tare muka je aka gwadani kawai dama na jima ban fita ba duk afafuna kumbura suke sabida zaman waje aya" salma ta an zaro ido "Rufa min asirin fa an Mijinki ni na isa na fitar dake waje so kike ya dawo asar yau kenan?" farha tayi dariya "Tab ta yaya dan kawai na fita se ya wani dawo wama ze gaya masa babu wanda ya san na fita ai" salma tayi wata dariyar tana cewa "Nidai rufa mini babu ruwana nafi son mu rabu lafiya da mijinki Dan yadda ya kafan sharu a akanki Ba zan tsallake ba ina fatan Allah yasa yadda ya kawoki lafiya yazo ya aukeki lafiya" farha ta kalli salma "Yawwa dan Allah Aunty salma shine yace Miki ni matar shi ce?" salma ta an fito da ido tana murmushi "Tunda ke wancan karon kin oye mini ai shi ya gaya min be oye mini komai ba" farha tayi asa da kanta "Amman ke ya gaya miki To amman mai yasa be gayawa su Ammi ba? ko lokacin daya kaini gidan cewa yayi kada na bari kowa yasan ni matar sace wannan ne yasa ban gaya Miki ba koda nazo gidannan kwanaki sanda kika auko ni, sabida ya min garga i akan kada na Nuna ko alamar muna da ala a dashi Wannan abun yana aga min hankali dan Allah Aunty salma rayuwar aure zata tabbata a oye ne?" Salma ta girgiza kai cikin damuwa tace "gaskiya maganar oye auren ku ma bazata yuwu ba sabida na tabbata kema ai a wajan mahaifan ki yaje ya amso auren ki to sabida me shi ze Dinga oyewa nasa iyayen ke matar shice bayan auren ku ba haramun bane wannan ba Hujja bace In ma don Kada hankalin Ammi ya tashi yake yin hakan ni a ganina gwara ma tun yanzu ta sani kafin Lokaci ya ure naso na bashi shawara amman kuma Bamu sami lokacin hakan