Sashe 82
Rabo Ya Rantse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ya tsugunna ya gaishe da Ammi kana ya tashi ya Fita dama shi bamai hayaniya bane ba Kuma ba laifi yana ganin imar Umma sosai. Har Kusan Goman dare Ammi tana Gidan su Farha kafin ta direwa Umma ledar data zo mata da Ita sukai sallama Suka baro Gidan Aikuwa gaba aya Yara da Manya A gidan suka rako Su Ammi har wajan Mota harda kawu wanda yake tayi wa Ammi godiya yana cewa a gaishe da sauran Na gida haka suka rabu Gaba ayan su cike da aukin Juna Kowa na gidan su farha ya yaba da Mutuncin Ammi musamman yadda ta saki Jiki tasha Hirarta sosai ta zama Mutuniyar Kawu. Ko a mota su Ammi labarin karamcin mahaifan Farha suke yi Musa yana Jin su yana ta Murmushi ya sauke Ammi da Sajeeda wadda gaba aya Jikinta ya Mutu tunda taga Ya Nura shikenan taji kaf duniya bata da namijin data ke masifar so in ba shiba soyayyar shi Bugu aya tayi mata Mugun kamu Ita babu ruwanta da Talaka ne shi kawai Nutsuwar shi da kamalar shine yayi mata Hmm anya sajeeda Kin gano Gidan shiga Kuwa Babar su Hadiza mahaifiyar Nura mace ar bala'i bare yadda ta auki so ta orawa Nura sabida shine Babba a an ta Maza! Koda suka shiga gida ma falon Ammi babu kowa Ammi aki ta shige tana Jin kamar ta sauke wani babban nauyi akan ta wannan ziyarar data Je wa surukanta masu Kirki da Mutunta an adam Alwala ta aura Zama tayi tana addu'a seda ta raba dare tana sallah tana wa Aliyu addu'a dan se wajan Asubahi Bacci ya auketa a saman abun sallah Kuma zuciyarta ta an rage damuwar Rashin sa sabida zafin addu'ar da take yi akan lamarin. ***************** Tunda suka shiga mota farha ta Jingina kanta da Jikin kafa ar Aliyu tana tunanin ina ze kaisu Dama yana da an uwa ko gida a kaduna ne Ita kam bata ta a zuwa kaduna ba shiyasa gaba aya tafiyar ta dame ta gaba aya Jinta take a takure ga Fitsarin daya ri e mata mara ga afarta duk ta dame ta sedai yadda take ganin shi a cikin damuwa mai tsanani ba zata iya gaya masa damuwarta ko guda aya ba. Shima a nashi arin nazari yake akan jahar ta kaduna wadda bai da abokan mu'amala acikin ta wannan tasa ya za eta a matsayin jahar dayay balaguro zuwa cikinta wadda yake fatan yayi rayuwa tare da fatima acikin Jahar kafin Allah ya kawo masa mafita sabida tunda ya baro Gida babu Fuskar wadda yake hangowa seta Amminsa Yasan tana cikin tashin hankali ba an ka an ba se Kuma Mami wadda yasan ya tauye mata ha inta tunda har yanzu matar shice akwai nauyin ta akan shi yasan bai kyauta ba ta wannan arin sedai tafiyar tashi kamar Dole ce dan yana tsoron abin da Ammi zata zartar dan uwa ce baze ja da ita ba shiyasa ya za i yayi mata aura Kafin Allah ya kawo musu mafita akan lamarin. Tunda dukkan abin da Ammi ta bu ata a tare dashi babu wanda yayi Kuskure dan ya i Bin umarninta akan su na farko ta nemi ya zubar da Ciki na Biyu saki wanda duka babu dalili bare Hujja mai arfi abin da yasa ma yayi mata auran dan baya son ja in ja da ita ne tana matsayin mahaifiya a gare shi wannan tasa yayi balaguro. Tafiya ta arewa Har zuwa sanda aka kira sallar Isha'i basu ne suka sauka ba se bayan sallar Isha'i a babbar tasha suka sauka Aliyu ya Fito Musu da kayan su ya laluba aljihun jallabiyar shi wadda ya sako Atm card inshi aciki se an Ku in shi wa anda basu da yawa sabida bai fiye aje cash ba shine yasa ya auko Atm inshi na bankin da yake ajiyar Ku Sedai koda ya laluba aljihun nashi wayam ba Atm in Ga wayar da yake transper da ita ya bawa Musa akan cewa ya kashe masa ita ya aje a wajan shi se an Ku in daya cusa cikin aljihun shi marasa yawa. Duk yadda yaso ya dake seda ya ka u sabida babban tashin hankalin shi Fatima yasan mai ciki da tsara be tsara be ga ku in hannun shi ba zasu Ri e Shiba Dama ya taho da Atm in shine dan yasan koda zasu shafe shekaru ba zasu tagayyara ba dan harda Niyar yasai aramin Gida yazo sedai kash Allah baiyi hakan ba dan yafi zaton a akin shi ya manta Atm in garin saurin ha a kaya wa anda Ko rabin kayan nashin ma bai auko ba. "Yalla ai Ku in Mota ka tsayar damu" Kwandastan motar ya fa a a gadarance. Drivern yace. "Haba alha kai masa a hankali wannan bai kama da mutanan banza ba" Aliyu yayi murmushi tare da irgo Ku in motar ya basu yay Musu Godiya tsugunnawa Farha tayi tana Rintse ido da kulawa ya dur usa a gabanta. "Fatima yaya me yake damun ki?" Ya fa a mata Cikin kulawa. "Fitsari nake ji washh bayana afata" an yi Jimm. "Ni har ga Allah ban son Kishiga toilet in tasha sabida toilet Infection" Ta hau Kuka! tana cewa. "To ni a ina zanyi wallahi ya matseni Sosai" Ya kama ugu kafin ya an saka hannu yana matsa mata afar tata wadda ta tasa ta Kumbura Cikin sanyin Murya yace. "Ki bari Mu fita sena sama Miki inda zaki Kinji" Yadda ya furta maganar cikin sanyin Murya ne yasa ta mi e ya auki kayan su suka fita daga Cikin tashar.......... Autar manya ce marubuciyar...... OYAYYAR AUNA* *BA SON TA NAKE BA* AN MAJALISSA* *MURADIN ZUCIYA* *ASHE ZUMA* *TAURARO* *KOBA SO* *RABON WANI* *FITAR RABO* *DA IZZATA* ON LAMARI* *AUREN BARE* *H A S K E* *ZUMA A BAKI* AR FATA* *RABO YA RANTSE* *RABO YA RANTSE! littafin ku i ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a auka a turo,shaidar biya 09022260850* *A LOVE STORY 98* Rabo Ya Rantse Arewabooks autarmanya A bakin titi suka tsaya inda motoci da babura ke ta faman kaiwa da kawowa Farha ta kalli Aliyu wani irin tausayin shi ne ke ratsa mata zuciyarta yana huda mata sassan Jikinta koda bai gaya mata ba tasan yana cikin ru ani da tashin hankali tare da damuwa sedai da ike namijin duniya ne bai ko nuna mata ba. "Ka bani wannan jakar na ri e kayan sun maka yawa a hannun ka" Ta fa a a hankali walla mai zafi tana arin zubo mata. "Nine nace miki kayan sun min yawa a hannuna?" ta girgiza mai kai tare da Kallon fuskar shi se kawai ya juya ya cigaba da kallon titi bai san ko ina a kaduna ba se yace in ba hanyar wucewa zuwa abuja ba bai ta a zuwa wani abu cikin jahar ta kaduna ba taka maimai bai san ina zasu sauka ba zufa ce ta soma karyo masa ya duba agogon hannun shi Goman dare ta kusa dan motoci ma sun soma sau in wuce wa inda Yana da wadataccen Ku i ne daya kama musu Hotel sun kwana sedai yana tunanin in ya kama Musu Hotel yanzu to ze arar da an canjin hannun shi. "Har yanzu kina jin fitsarin fatima ko ya koma kinga yadda Allah yayi damu bama wajan da zaki samu kiyi anan domin titi ne" Ta girgiza kai. "Kada ka damu dani Allah ya duba Mu" Tana rufe bakin ta suka ga wata tsohuwa zata tsallako titi sedai Tsallakowar ta gagara sabida yadda wata babbar mota tayo kan tsohuwar da sauri Aliyu ya yada jakun kunan hannunsa ya tafi wajan tsohuwar a guje ya kamota suka tsallo angaran da farha take. "Jikana nagode Allah yi maka albarka bada ban kaiba da tuni wannan mota ta murjeni" Duk yadda Aliyu ke cikin acin rai seda yayi Murmushi. Mai hali baya fasa halin sa aljihun sa ya duba ya auko naira dubu ya dam a mata. "Baba gashi Kici goro ba yawa" Tsohuwar ta washe Gibi tana dariya tare da cewa. "Kai amman nagode nagode madalla a ina kake jikana na dinga zuwa Muna gaisawa ka ganni tunda nake banta a haihuwa ba dana ganka se naji kamar Nina haifi Mahaifin ka tunda nasan dai na girmi gyatumar ka" Daga farha har Aliyu dariya sukai na dramar tsohuwar kafin farha tace mata. "Mu ba i ne daga kano muke" Tsohuwar tai saurin cewa. "Oh amman kuka tsaya a titi ai da kunyi saurin zuwa inda kuka zo sabida Titin nan akwai manyan Motocin dake yawo akan shi Nima daga Bikin Jikar awata nake Shine na biyo tanan da tuni na zama gawa" Aliyu yace. "Baba zamu bar nan yanzu kema ki daure ki tafi gida dare yayi" Seta kama ha ar zaninta ta aure ku in tana cewa. "To ku gaya min inda kuka sauka sena zo gobe wajan ku mu ara gaisawa" Cikin osawa da maganarta Kasancewar shi mutum marar son magana sosai yace. "Bamu da masauki muna dai duba in da zamu sauka ne dan mu ba i ne a garin" Tsohuwar ta kama baki cikin mamaki. "Baku da masauki fa jikana aikuwa ni ina da shi kaga gidana da Mijina ya rasu ya bari se dangin sa suka tausaya min suka bar mini ni ka ai suka saka min an haya sedai ganin bani da gata tunda ban ta a haihuwa ba ga dangina duk sun are yasa an hayar yake Mini iskanci baya Biyana Ku in hayar Kuma da Ku in nake Cin abinci Jikana alkairin dakai Mini dan Allah nima zan kwatanta zan baka aki guda wanda ke Jikin nawa ka zauna kai da matarka danna san matar kace Amman zance kai an yayana ne kazo Kaga zaka dinga amsar Mini ku in hayata ma da baya bani" Tsananin tausayin ta ya kama zuciyar Aliyu. "Baba idan na zauna kamar na tauye kine sabida Zaki bani aki ne kyauta Kuma Kinga na shiga ha in ki" Da sauri tace. "Ni baka tauye niba kuma kai alkairi ne a gare ni dan Allah jikana in ba raina wa kai ba kazo