Sashe 24
Rabo Ya Rantse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
fuskanci kowani alubale akan son ki" Farha ta saki baki babba dashi ya dage yana ta zuba mata kalamin soyayya ita har kunya ya bata haka dai ya tafi bai sami amsa a wajan farha ba. Acikin satin salim ya dami farha da naci ga lokacin ta soma F.C.E Inda ta sami departement in da take so wato Mass comminucation a matakin farko na diploma gaba aya farha ta ara mayar da hankalinta akan Karatunta sam bata da lokacin kowa sai na karatu awarta aya shema'u ofar nasarawa Dp insu guda da shema'u farha nada mugun ari yawanci an ajinsu bakwaini suke ce mata sabida tsabar antarta. Soyayyarsu da salim kuma tayi arfi sosai dan salim irin mutanan nan ne masu naci ya nacewa farha, Hidima yake mata yana kashe mata ku i sosai dan yawanci Ku in da take kashewa na makaranta salim ke bata tun umma na fa a harta ha ura kawu mutum ne mai zafi shiyasa ma Farha bata fiye amsar abin salim ba haka Farha ta cigaba da makarantar ta koda yaushe salim idan yace ze turo sai tace ya ara mata lokaci. Farha tana da masifaffan ciwon mara wanda umma ke amsar mata magani dan idan ya tasar mata Har suma take Farha bata da ha uri ga rashin kunya wani bin salim ma inta Botsare masa da yar yake shawo kanshi Umma tayi namijin ari sosai akan farha dan ita ke biya mata ku in makaranta duk wata buga buga umma tayi akan farha ta sami ilimi, Sabida yadda umma take son farha sosai Babban farin cikin farha ta sami aikin jarida idan ta gama makaranta. Zaman gidansu farha ya cigaba da wanzuwa kamar yadda yake sabida Hidimar da kawu ya barwa matansa yasa ake cewa gidan. Gidan cida kai sabida yawan su kuma wasu suce an gidan yawa. a acikinsu kamar me yanzu da an umma suka taso sam matan gidan bamai takata sai dai fa ta ciki na ciki ne kawai gashi kowa yafi son ansa yayi gaba yafi na wani an gidan nada ha in kai a waje dan basa ta uwa amman agida kamar kaji sabida masifa gashi kowa uwarsa ya sani. Cikin wannan adamin farha ta sami aiki a gidan RADIDON GARKUWA bayan ta gama karatun ta, Ta hanyar yayan shema'u Wanda wannan aiki ne dalilin tarwatsa dukkan Burin farha data ci na ta sami aiki dan taga matan gidansu na shan wahala ta sami aiki dan ta dinga taimakon mahaifiyarta sabida wani bin kwana zasu yi basu ciba Ikram taita kuka Sai dai kana taka Allah yana nashi adaidai sanda ta sami aikin addarar Auren Aliyu ta tarwatsa mata dukkan wa annan Burika nata ko yaya rayuwar farha zata kasance? *WANENE ALIYU*......... *RABO YA RANTSE! littafin ku i ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a auka a turo,shaidar biya 09022260850* *RABO YA RANTSE* *25* *A LOVE STORY 25* Marigayi Sale madaki Shine Kakan Aliyu wanda ya haifi Mahaifin shi Allah ya ji an shi da rahma Alhaji Abdu Madaki. Sale madaki haifaffan jahar kano ne anan cikin Galadanci gidan iyayen shi yake mahaifin sale mutum ne mai dukiyar gaske sana'ar saida fata yake shiyasa mutane ke masa la ani da Madakin fata Kuma sale ka ai Allah ya bashi aduniya Bayan Rasuwar Dukkan mahaifan sale sai sale ya gyara aton gidan mahaifan nashi yayi aure ya auro matarshi salamatu ar nan kusa da gidan su Suna zaman su lafiya da salamatu inda ya cigaba da sana'ar saida fata ya gaji mahaifin shi. Shuru shuru tunda sukai aure salamatu bata haihu ba tuni abin ya dameta amman shi sale ya dangana yana bata ha uri koda yaushe akan cewa Haihuwa lokaci ce haka suka shafe shekaru Biyar da aure Amman salamatu ko atan wata bata ta a yi ba Ganin haka yasan ya anin mahaifin sale yazo har gida ya same shi lokacin sale bai fita kasuwa ba. "Nazo ne akan maganar matar ka" Sale ya dubi an uwan mahaifin nashi tare da cewa. "Allah yasa ba wani laifi tayi muku ba kawu" Kawun nashi yace. "Ko aya mu dai mun gaji da ganin ta haka kada kaga ba ran mahaifan ka muma masu tsaya maka ne saboda haka na baka ata Saude kazo ku daidaita mu irin haihuwa ne dan ba zan so yadda iyayen ka suka haife ka kai ka ai ya zamana cewa Ka mutu baka da magaji ba" Sale yayi asa da kanshi yana tunanin ha uri da nagarta irin na salma idan yayi mata kishiya akan rashin haihuwa bai mata adalci ba. "Kawu nagode, amman kai hakuri bani da matsala da matata Ni gaskiya ba zan mata kishiya haka kawai babu wani dalili ba" Kawun sale ya harzu a ya fara cin Mutunci. "To dole ka amshi saude ko ka i koka so dan kaga bani na haifeka ba to bari kaji cikinmu aya da mahaifin ka ko ka i koka so ba'a canzawa tuwo suna sabida haka kazo gida kaga saude ku sasanta a saka ranar aurin aure in kuma ban isa dakai bane ba to" Saleh yayi asa da kanshi sai faman Ha uri yake bawa kawun nashi sannan yayi masa al awarin zai zo yaga saude. Kawun sale yayi tafiyar shi batare daya tsaya amsa ha urin da salen yake bashi ba. Koda ya koma gida ya rasa ta yadda zai gayawa salamatu maganar da sukai da kawun shi sabida kunyar ma gaya mata maganar yake yi. Ta lura sam bai da sukuni har dare ganin haka yasa ta saka shi a gaba da tuhumar meke damun shi? da yar ya aro jarumta ya dube ta. "Salamatu kin san ina son ki, Kuma ina aunar ki" Tayi murmushi tace masa. "Nima in ka cire Allah da ma'aiki da iyayena da suka rasu to sai kai sai kuma anwata Amina da muke shirin auren ta" Yayi dariya sannan yace. "To kawu ne azu yazo min da batun cewar zai bani ar shi saudatu na aura" Bai arasa ba ta katse shi cikin murna tace. "Dama gidannan yayi min girma tsoro nake ji in baka nan Allah ya tabbatar da alkairi kaga na sami anwa" Duk ta yadda Yaso kushe abin ta i sai ma arfin gwiwa da take bashi haka ta shige masa gaba akan auren shi da saudat har yaje ya gano saude aka tsaida maganar aure ba da jimawa ba. Sai dai me Tunda aka saka maganar auren ma salamatu ta soma laulayi wanda ya hanata lafiya gaba aya Sale ya mayar da hankali akan kula da lafiyar matarshi a daddafe ya auri saude wadda tazo gidan da tashin hankali dan saude akwai zafin kishi da zargi haka dai zaman nasu ya cigaba salamatu rabi ha uri take da saude sabida saude akwai saka ido zargi ga zafin kishi abu ka an sai ta kai sale ara an uwansa suzo su zage salamatu ba zata tanka musu ba haka Taita cigaba da zaman gidan cikin ha uri Har Allah yasa ta soma na uda wanda sale Baya nan ranar Tana aki tana ta fama Duk ta fita daga hayyacin ta saude tana tsakar gidan ta ware Rediyo tana wanki ko kallon salamatu batayi ba kwatsam Allah ya jefo Amina anwar salamatu ce wadda akai wa aure a kwanakin Cikin su aya kuma su ka ai ne mata a wajan iyayen su sai yayan su Namiji guda aya da yake zaune anan gidan Da mahaifan nasu suka rasu suka bari. Ganin halin da salamatu take ciki hankalin Amina ya tashi ta ruga gida ta kira matar yayan su aka saka salamatu a mota suka tafi asibiti Amman saude ko kallo basu isheta ba Koda suka je asibitin matar yayan su ta saka yaron ta yaron yace kasuwa ya kira sale sai dai kafin sale yazo har salamatu ta haifo anta ato wanda ko kallon shi batai ba Allah ya amshi ranta iya tashin hankali wannan zuri'a sun shiga sale kuwa kamar zararre haka ya koma yaja yaro ya rungume ya i bawa kowa. Sai da abokai suke ta masa nasiha sannan ya bada yaron Amina da matar yayan salma sunce zasu ri e shi amman Sale ya i har da kukan shi sai mahaifin Saude yace a bawa saude ta Dinga bashi madara sai uban sa ya dinga ganin sa a kusa dashi haka akai bakwai aka watse aka bar saude da jariri wanda Amina tai kuka tai kuka akan aka bata yaron aka Sale kewa Abdullahi wanda suke cewa Audu a wannan lokaci, Shike masa wanka kafin ya fita kasuwa ya bashi madara yasha ya wanke masa kayan shi tas Ba tare daya tsaya bin kan saude ba wadda take jin kamar ta jefa audu a wuta Sosai mahaifin shi ke lura da shi ga audu yaro ne mai hakuri da wiya kaji kukan shi haka yayi ta girma ta silar Kula da mahaifin shi yake bashi A haka har yaro yakai shekara biyu Amina na zuwa ganin shi sosai Dan koda yaushe tana hanya ga uban sa na son shi sai dai fa da zarar Sale baya nan Saude zata saka shi a aki ta kulle ya wuni da yunwa amman in uban ya dawo sai dai audu yayta hawaye dan babu bakin magana A haka ya taso Yakai shekara Biyar saude ta haifi anta itama mai suna Usman. *RABO YA RANTSE! littafin ku i ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a auka a turo,shaidar biya 09022260850* *RABO YA RANTSE* *26* *A LOVE STORY 26* Bayan usman ta haifi Ashiru daga shi ta haifi sa'adu daga shi sai Rabi'u sai salisu sai suwaiba Lokacin Audu ya zama an matashi zai kai shekara Goma sha biyar wahalar Gidan gaba aya ta koma kanshi komai na su Usman shi yake hatta tsarki kashin su Saude ta i bashi abinci sai taga uban ya kusan dawowa kuma dan ha uri irin nasa baze ta a gayawa mahaifin shi ga abin da take masa ba sai dai yayi ta kuka shi ka ai tuni an saka su a makaranta shida usman wazo ne da