Sashe 35
Rabo Ya Rantse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
baya tayi tabi shi ciki Tsayawa tayi daga nesa tana hangen cikin falon wanda shikuma zuwa lokacin Ya riga da shiga ciki har ya zauna. Jikinta a sanyaye take taka afafunta harta arasa cikin falon kanta a asa batare data kalli mutanan dake zaune a falon ba ta wuce cikin akin ta sum sum. Aliyu ya kalli Ammi wadda ta ora afarta a saman center table Hajjo tana danna mata da ruwan umi. "Ammi meya sami afafun naki kuma?" Ya fa a mata cikin kulawa, Bata kalli inda yake ba ta kauda kanta Hajjo tayi dariya tare da cewa. "Haba hajiya Ammi Uban akina bai cancanci kiyi fushi dashi ba tunda bashi yakar zomon ba" Ammi ta agawa Hajjo hannu tana auke afarta Hajjo ta auki ruwan umin tabar falon, Aliyu ya kuma matsowa gabanta jikin shi duk yayi sanyi murya ya kuma rage wa cikin sanyin jiki yace. "Ammi badai fushi kike yi dani ba Allah ya baki ha uri dan Allah ki yafe min ba danni ba" Ammi dataji zuciyarta tayi sanyi na yadda taga yayi in seta dube shi. "Daga ina kake da alamun wannan yarinyar tare Kuke, Baba kada ka yaudare ni Ko son yarinyar nan kake nasan halin ka kamar yunwar Cikina" Shafa kanshi yayi Batare da nuna wani tsoro Ko furgici a maganar ta Ammi ba yace. "Ammi me kike fa a haka? nikam ko yarinyar ma da kike magana akanta ban gama gano taba" ya fa a lokacin da yake ora hannunshi a afar tata yaja yatsan wanda Ammi ta sanya ara tana rintse Idanu kawar da maganar yayi yana cewa "Ammi wai garin yaya ne kika ji ciwo haka?" Ta yarfe zufar data karyo mata tana kallon shi kafin tace. "Tsautsayi ne wannan yarinyar bata wanke wa su auta toilet ba to ka gama jibgarsu duk ka jigata min yarana shine ni da kaina naje na wanke Musu harfa na gama addara Kumfa ta kwashe ni shine na fa i kaga dai yadda afa ta haye tayi sumtum" Ammi ta fa a a zatonta ze ara ganin laifin farha yace a sanadin ta mahaifiyar shi ta fa i ga mamakin Ammi se jin muryar shi tayi yana cewa. "Sajida safna ku zo nan dan ubanku" Ya fa a da arfi kuma babu wasa acikin idanun shi. Sum sum suka fito daga cikin akin su sabida wunin yau suna a kwance Suna ta wa ammi sangarta kala kala batare dasun tausaya mata akan halin da take ciki ba suka zube a gaban sa suna gaishe dashi. Kawunan su ya ha e waje aya ya gwara ya sanya afa ya ta e su a gabansa suka fa i suna kuka har goshin su ya fashe"Baba meye haka so kake ka kashe min su wai me yarannan sukai maka yau tunda ka tashi kake cin zalin ana kada ka bari na maka baki akan su fa" Ta fa a tana arin tashi amman afarta tai mata nauyi sabida targa an data ji a yatsanta na afa. Ba tare daya bi takan maganar da Ammi take mishi ba ya mi e tsaye ya zaro wata atuwar ba ar waya na e ta yayi ya shiga lafta musu a gadon bayan su ba ji ba gani Ihu suke suna kiran "Yaya ba zamu sake ba yaya kayi mana afuwa mun tuba wayyo ammi zamu mutu" wannan ihu shiya fito da Farha daga akinta tsorata tayi ganin yadda yake Jibgar su kamar Allah ya aiko shi da sauri Bashir dake shigowa falon ya araso wajan Aliyu yana arin ri e wayar hannun nashi Aliyu ya tanka a Bashir ze zuba masa wayar Bashir yayi tsalle yayi gefe yana yarfe hannu dan har ta same shi. Sai da yaga sun kasa tashi sannan ya yarda wayar yana huci. "Dan ubanku daga yau idan kuka sake barin ammi tayi muku wankin ban aki sena karya ku daku saka mata ciwon arin Jiki gwara na karya ku na watsar ai ba ku ka ai ta haifa ba duk kuma abin da kuke a gidannan na sani tara ku nake, bakwa ganin mutuncin kowa har wasu na tunanin duk haka muke daga yau na dakatar da Hajjo kune zaku dinga girki na dakatar da mai gyaran falo kune zaku dinga gyarawa in na kamaku da sa a dukkan sharu ai na wallahi tallahi" Ya matsa yatsun sa suka bada sautin ass da arfi yayi wafa yabar falon fuww kamar kububuwa. Bashir da shigowar shi kenan Garin ya wuce daga wajan shima angaran shi ya nufa wanda yake Kusa da falon Ammi ya aje jakar shi ya shiga wanka batare daya bi takan abin da ya gani ba dan yasan ba mamaki laifi su safna sukai wa Ya Ali, wanda shi kam tsoro ya hanashi magana. Ammi tallafe kumatu tayi tana jin zuciyarta na mata zafi bada ban kukan uwa bala'i bane ga anta yau dase tayi kuka harta godewa Allah da sauri ta isa gabansu tana arin janyo su jikinta "Ni Ammi kada ki ta ani ai kina kallo yana dukan mu amman baki magana ba kamar tsoron shi kike ji" cewar safna babu wata tarbiya acikin maganar tata Ammi jada baya tayi sabida yanayin safna daya bata tsoro se kuka suke kamar ransu ze fita kafin su Mi e suna jan afafu sukai cikin akunansu. Farha da hawayen tsoro ya gama ji a mata fuska taja ofarta zata koma sabida tuni wani tsoron Aliyu ya cika mata cikinta wannan duka ai idan ita yayi wa shi kawai tata ta are Mutuwa zata yi. "Zonan munafukar Allah" Taji yo muryar Ammi wadda take kallonta Jikinta yana rawa ta nufi gaban Ammi ta tsugunna. Ammi ta dube ta. "Da ina cikin kwanciyar hankalina baba baya shiga harkar annen shi amman daga zuwan ki zaki raba min kan ana munafuka bakar kadara wallahi bana aunar ki mai ba ar fuska da muni kamar daran mutuwa idan ba da ban ta dalilin ki ba ta yaya duk haka zata faru Kuma ki bu e Kunne da kyau Kijini ba Musa ne ya kawoki gidannan ba Ni ko uban musa ne ba ruwana akan ana wallahi ko shi Musan zan iya atawa dashi wannan duk wahalar da baba ya lissafa kece zaki Yi ba su ba kuma da kuturin Munafurci inji kin gaya masa wallahi sena karya ki na watsar dake ana ba kalar wahala bane ba abun da zasu yi kece zaki komai munafuka" Farha dai se kuka take ta kasa magana tunda take bata ta a ganin Mutum wanda ya tsaneta ta farar aya kamar Ammi ba. "Tashi ki bani waje Munafuka". Ammi ta fa a tana saka afa ta ture Farha wadda ta hantsila ta Kifa Har hancinta na fashewa Kuka ta saka mai arfi ta Mi e ta Nufi hanyar fita daga falon aguje duk tunanin ta ya gushe tama mance hanyar akinta wanda adaidai nan Kuma Bashir ya turo ofar ya shigo Karaf suka ci karo da Farha wadda tai taga taga ta fa a saman irjin bashir da sauri Shikuma ya tarota Jikinsa ya saka hannun shi ya dam ugunta ya ri e gam........*RABO YA RANTSE! littafin ku i ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a auka a turo,shaidar biya 09022260850* *A LOVE STORY 41* Bashir shagala yayi da kallon Farha tunda yake bai ta a ganin Macen data fusgi hankalin shi irin taba fatar Jikinta laushi ugunta cikakke ya cika masa tafin Hannun shi Bashir wanda idanun shi suke a bu e tar a harkar mata yaga fara yaga ba a mayen mata ne Duk samun sa a gindin mata yake tafiya indai mace zata bashi Jikinta shi kuma ze mora mata komai take so kuma ze mata Gogagge ne akan mata ya ware sosai a fannin neman mata wanda tun yana yi a oye har Maganar tazo kunnen Aliyu da Sadi sedai duk yadda suka so su fahimtar da Ammi abun yaci tura domin ta i yarda da maganar tace arya suke masa Wanda suka fa a ma sharri ne sedai inda Ammi zata saka idanu akan Bashir shine abin da zata fara fahimta ina yake kai Ku in sa Aliyu yace ai masa aure Ammi tace har yanzu Bashir yaro ne ita bazata aurar dashi yanzu ba wannan tasa suka tattara batun sa suka watsar tare da zuba masa ido wanda yake cin karan shi babu babbaka dan har labari aka zowa da Aliyu akan Bashir nada gidan sa inda yake kai matan banza ranar daya gayawa Ammi Seda ta kwanta a gadon asibiti tunda ga nan Aliyu yayi fushi ya zubawa Bashir Idanu. Murza ugunta ya shigayi cikin wani irin salo yana kusanto da fuskarsa daidai tata wanda ita kuma take arin ta waci kanta gaba aya hankalinta idan yayi dubu ya tashi Kokawa ce ta kaure a tsakanin Bashir da Farha shiya gigice da dirin Jikin farha wadda kallo aya yayi mata ya gano karuwar Jiki gareta a haka zaka auka arama ce sedai ga wanda yasan mace yasan Farha aramar asa ce da albarkatun man fetur. A fusace ta ago tana are masa kallo Shima fari ne siriri kamar bafulatani sam basa kama da kowa agidan kamannin sa daban Cizo ta gartsa masa a Hannun daya ri e ta dashi aikuwa ya sake ta yana yarfe hannun aguje ta koma akin ta Lokacin Ammi bata falon key ta murza ajikin ofa ta zube a wajan tana sakin Numfashi idan hankalin farha yayi dubu tofa ya tashi Kukan ma ya i zuwa ita tunda take ba namijin daya ta a ratsa ugunta sai shi Ko Mijinta baya gigin ta a Jikinta ko salim da sukai soyayya Mai tsarki sukai bai ta a kai hannu Jikinta ba gwarama bawan Allah daya an ri e ta Lokacin daya zo wajan ta. yar ta koma saman gado duk a tsorace take Sai da ta an sami Nutsuwa sannan ta shiga Ban aki tayo alwala ta shiga rama sallolin da suka hau kanta ranar Bacci gagarar Farha yayi tabbas Idan har wannan saurayin a gidan yake tofa zaman ta a gidan akwai hatsari tunda ta Lura Mahaifiyar su Se abin da a yaga dama yake