Sashe 51
Rabo Ya Rantse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kicin kicin da ranta ta koma bayan Mijinta ta zauna ya an kalli sadik da ke bawa Ammi labari. "Oga nifa nazo yin dinner ne sabida yunwa nake ji" batare daya jira amsar sadik ba ya gaishe da Ammi wadda ta mi e tana cewa su sakina. "Ku taso muje muci abinci seku yi sallar isha'i" Duk suka tashi ban da Jamila data zauna tana sunne kai ammi ta kalleta da kulawa. "Jamila taso mana kema ai kin zama ar gida" sakina tayi dariya tana cewa. "Ai Ammi ita haka take, yau fa kwanan ta biyu a lagos taje min hutu shine na tawo nan da ita" Ammi tayi dariya tana cewa. "Aiko ta kyauta" Shikam Aliyu har ya arasa dining ya shiga bu e warmers in da aka jere duk ba abin da yayi masa se tuwon daya gani marar yawa ya zuba a plate ya auki spoon da sauri Mami ta ri e Cokalin da Aliyu ze kai cikin bakin sa jikinta har rawa yake wajan ce masa "Yaya kada kaci dan Allah" Ya aje cokalin ya tsareta da ido Lokacin kowa ya zauna a saman dining kuma kowa ya shiga zuba abin da ze kai cikin sa. "Sabida me kar naci? idan naci mutuwa zanyi kome?" Gaban mami ya fa i ta shiga sosa kanta. "A,a yaya dama Ammi nasa Farhan taiwa kasan ita bata son girke girken mu na zamani" Aliyu yayi wani Basaraken Murmushi ya auki cokalin ya cigaba dacin tuwon hankalin sa kwance Ammi kam dariya tayi tana cewa "Ai kema da se kisa ai da yawa Kin san yadda Mijin ki yake son tuwo" Mami sam bata ji mai ammi take fa a ba ta shiga tashin hankali ko abincin ma ta kasa zubawa taci. Falon ya auki shuru kowa yana faman cin abinci se arar cokula da Plate ke tashi. Aliyu ya an kalli mami ya cigaba da cin tuwon shi. "Ina tea in?" Sosa kai tayi tare da aga Murya sosai. "Farhan kawo tea" Aliyu yabi ta kallo yana tuna wace Farhan in da take ta faman fa i dan shi ya manta sunan farha farhan dan shi Fatima yake ce mata. Lokacin Farha ta mi e daga baccin tana sallah seda ta idar ta fito waje sabida jin Yadda Aunty mami keta wala mata kira. Gaba aya se ta shiga damuwa sabida yadda taga mutane da yawa a falon kowa kuma ya zuba mata ido sum sum ta wuce Kitchen ta ha o kayan tea in a tray ta kawo gaban mami ta aje ta Lura da yadda wannan matashin ya tsaida Cin abincin sa tun bayan data fito se kallonta yake kamar maye, Sannan wannan ba ar Budurwar ma kallon ta take, a arare ta shiga gaishe dasu sakina. Sakina ba sakin fuska ta amsa jamila ma haka Bashir kuwa bai amsa ba se jarababban kallon da yake bin ta dashi Sadik ne ya amsa yana cewa. "Hajiya Ammi tamu ina kika samo ar budurwa haka?" Ammi murmushi tayi bata ce komai ba sabida abinci take bawa hidaya aramar ar sadik. Sakina ce ta ago a gadarance. "Ke da Allah auki yarinyar can Ki mata wanka" ta nuna intisar Farha ta juya zata auki yarinyar Aliyu daya daskare a zaune yana binta da kallo na mamakin yadda ta kalli kowa ta gaishe dashi amman shi ta kasa koda kallon shine bare ya sami arzi in gaisuwar ma. Da sauri yace. "A,a Sakina Ita wannan anwar taki taiwa Intisar wanka mana, bakya ganin ita aiki take" batare daya kalli sakinar ba yayi maganar da sauri kuma ya cigaba da cin tuwon shi...............*RABO YA RANTSE! littafin ku i ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a auka a turo,shaidar biya 09022260850* *A LOVE STORY 63* Cikin son ta cusa masa haushi tace. "Lah bari nayi mata wankan, meye aikina in ba yiwa kowa na gidannan Hidima ba ai bani da wani hutu se Hidimta Muku" daga haka ta auki Intisar cak tayi hanyar akin ta da ita Bashir da yaji ta burge shi data gwale Aliyu dama cike yake da haushin yadda Aliyu ke hana yarinyar tai wani abun sannan kuma yana nuna kamar shike iko da ita. an nisha i Bashir ya aga Murya bayan ya kora ruwa. "Hy baby zo mana ki zuba min Lemo a cup" cak ta tsaya tana nanata sunan daya gaya mata Anya ta je kuwa murmushi ta saki ta aje Intisar ta juya gaban Bashir se kallonta yake ta tsiyaya masa Lemon ta mi a masa tana wani Irin murmushi ta koma ta auki Inti ta shigar da ita akinta ta cire mata kaya ta ha a ruwa tayi mata wanka sam ta mance yaushe rabon ta da sabulun wanka se yau sabida ita idan zata yi wanka sedai ta auko omo tayi dashi sabida bata son amshin sabulun tana toshe hanci tana wa Inti wankan tana kwa gamawa ta soma she a amai wanda yarinyar ta gudu daga toilet in ta fita falo ko kaya babu ajikinta. Lokacin sun kammala cin abincin Shi ka ai ke dining yana shan bakin shayi. "Ke Intisar ina kayan naki?" cewar Jamila wadda ta Mi e zata shiga akin da suka sauka yarinyar tai kalar kuka tana cewa. "Nanny in amai take tayi a bathroom in shine na fito" Jamila ta kamata suka wuce aki Mami zama tayi a falo duk jikinta a sanyaye har lokacin a tsure take sabida Aliyu yaci wannan tuwo da sauri kuma ta mi e ta nufi sashin su don ta kira maman ta a waya su san matakin auka. Bashir wata irin tafiya yake yana aga lemon data zuba mai yana sha ji yake kamar bakin ta yake tsotsa dan jaraba Aliyu ya fuskanci Abin da tai masa yayi wa Bashir da i Se kawai ya raka Bashir da idanu har yabar falon domin Aliyu ya gama gano Bashir me yake nufi da yarinyar wannan tasa ya nesan tashi da gida amman yanzun ma ze auki mataki akan Bashir in daga cikin falo sakina ma aki ta wuce dan ta gaji sosai hutu take bu ata Falon daga sadik se Ammi dasu safna suna ta faman Hira shiko Aliyu be shiga cikin suba kuma bai tafi ba waya yake tayi da mutane daban daban duk da yaji zafin yadda ta yarfa shi ta gwasale shi a gaban annen shi da matar shi amman sabida tsabar Muskilanci bai ko nuna a Fuskar shiba. Sadi hamma yayi tare dayi wa su Ammi sallama ya araso wajan Aliyu sukai sallama ya wuce makwancin sa su safna ma wuce wa sukai bedroom insu ganin haka Ammi ta dube shi. "Wai kai me kake jira anan ne kowa ya kwanta kai ba hira ba kai ba tafiya ba?" Ya shafa kanshi bai ce mata komai ba ta mi e ta kama hanyar Bedroom inta tabar shi a wajan. Ya sauke ajiyar zuciya ya mi e ya nufi akin marar kunyar can, kamar yadda ya ra a mata yaja handle ofar ta bu e ya shiga ya zira key a jikin ofar ya kunna hasken akin sabida ta kashe hasken tun sanda ta fito daga toilet bayan ta gama aman ta kashe wan ta kwanta duk da tana tsananin jin yunwa ga yawun ta se tsinkewa yake, amman bata sha'awar shinkafa ko taliya yau innan wainar fulawa take son taci mai man gya a da albasa da tumatur da yajin tafarnuwa har amshin wainar take ji a hancin ta wannan dalilin ne yasa ta ora hannu a saman cikinta tana kuka wiwi dan sosai take muradin cin wainar kuma bata son amshin suyar tafi son kawai ta ganta a gabanta tana ci cikin haka hasken daya kunna ya gauraye akin ta ago ta zauna tana kallon shi ya wani ha e fuska kamar bai ta a yin dariya ba. "Ke baki da kunya ko? baki da mutunci baki san darajar aure na da yake kanki ba har Bashir yana ce Miki Baby kina amsawa kin mayar da kanki kamar baki san me kike ba me sakina ta fiki dashi da zata wani daka Miki tsawa! ki mata abu har Kiyi, sannan ince ba zaki ba ki gwale ni bayan rashin gaisuwa dana kasa samu a wajan ki, so kada ki ga na ha irji dake wallahi I will surprise you if you refuse to follow what I told you" Har ya gama masifar bata ko kalli inda yake ba ita ta kanta take se faman sakin Numfashi take yi Shurun data yi masa ne ya ara fusata shi idan da abin da yafi tsana a duniya bai wuce Yayi magana ai masa banza ba bai wuce yayi fa a a i bashi ha uri ba aiko yayi mata kaa cikin hargowa yana daka mata tsawa! "I talked to you but you kept quiet, you made me crazy or something?" Ya fa a yana zuba mata girman idanunshi wa anda sukai jajir Se tace tunda take bata ta a ganin Yanayin nan a tare dashi ba rintse idanu tayi Jikinta yahau rawa Bakinta mai cike da yawu ta aga tana cewa "To ni me kake so nace maka, nayi magana kace nayi maka rashin kunya kome?" Seta saka kuka ta cigaba da cewa "Ni ka rabu dani ka barni haka nina san me yake damuna zaka wani zo kana min Ihu akaina dame zanji da gajiyar aikin gidanku koda Abin da yake damuna kashe kaina zanyi idan ban musu aikin ba, ba jaka ka kawo ba? ai ni jaka ce mai muku hidima kaine kace nida fita sedai naje gidan zoo wajan dabbobi an uwana to meye danna yiwa matar yayan ka Biyayya nayi wa anin ka duk fa acikin aikin dana zo yi muku ne ni baiwa ce daka siyo duk inda kuka ka ani nan zanyi sabida haka ni kada ka kuma zuwa kana Min wannan ihun idan ba haka zan fa i tsakanina dakai kowa ma ya sani idan yaso ka sake ni na huta da wannan addararran auren naka wanda bashi da anci" Da gudu ta arasa maganar sabida Aman daya tawo mata tun kafin takai ga shiga ban akin ma