← Book details Rabo Ya Rantse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 94

Sashe 3

Rabo Ya Rantse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*NA* *AUTAR MANYA* ADABI WRITTER'S ASSOCIATION *003* Pillow guda aya ya matse a saman irjinshi bai rufa da komai ajikin shi ba, dama haka tsarin shi yake duk sanyi baya rufa idan yana bacci kuma baya sanya riga iya kacin shi dogon wando ka ai, baccin shi yake cikin nutsuwa sabida yadda gajiya ta zirga zirga ta kashe masa jikin sa damma namijin duniya ne wajan gwagwar mayar rayuwa. Ammi ta arasa bedroom inta bata zauna ba alwala ta auro ta fito daga Toilet Sadi Yayan Aliyu, Aliyu shike bin sa yana zaune a Garin lagos yana kula da kamfanin ALIYU na lagos,Tare yake zaune da matar shi acan Aunty sakinah da yaran shi guda uku mata, yayi sallama cikin akin nata. Fuskarta a sake ta amsa tana cewa. "Kaikuma zuwan dare kayi kano kamar korarre" Sadi ya shafa kai yana dariya. "Hajiya Ammi tamu, to ki fara bani abinci naci sai muyi maganar data kawo ni" Ammi tayi murmushi. "Bari nai sallah tukunna sai na ji dakai" Ta shinfi a darduma a nutse take sallar wadda taja lokaci mai tsayi dama Duk sun san yadda sallar Ammi take aukar Lokaci Sadi har sai da yakai ga yana gyangya i a asan carpet. Muryar Ammi yaji. "To sarkin bacci tashi mu fita daga falo sai kaci abincin" Ta fa a tana fita daga akin Sadi ya bita suka zube nan asan carpet. "Lah Yaya Sadi yaushe ka shigo bamu sani ba?" Cewar sajeeda wadda ta bu ofar akinsu ta fito tana murnar ganin sadi sabida shi mai barkwanci ne da sakewa ba irin Ya Aliyu ba mai tsare gida sam in ya shigo sashin su basa sake wa har sai ya fita. e hannunshi yayi yana dariya yana cewa. "Zo mana autar Ammi ina safnah?" Da sauri sajeeda ta arasa jikin Sadi ya rungumeta suna dariya Muryar Bashir Ce ta kara e Falon shima Dariyar yake shigowarshi kenan gidan. "Babban yaya kaine da tsohon daran nan?" Bashir ya fa a yana dariya. Sadi yace. "Ina naga ta zama mai gida ya kirani azu naji muryar shi babu da i dama kullum abu a cunkushe babu fuskar far'a" Bashir dariya ya saki sabida yasan da wa yake yana nufin Ya Aliyu. Ammi ma dariyar tayi tana cewa. "Ina ruwan ubana nina rasa wannan rashin far'a na wa ya ebo" Sadi yayi dariya yace. "Ammi ke ya gado danni Ammi wani bin in kika aure fuska wallahi har tsoron yi miki magana nake" Gaba aya Falon dariya aka saki Ammi ta auki Pillow ta jefawa Sadi Ya cafe yana dariya Safna ta fito itama Tafiya tai wajan Ya Sadi tana Murnar ganin shi dan shi yake iya aukar duk sangartar su sa anin Aliyu da yake cin Ubansu babu sau Ammi ce ta mi e ta nufi kitchen ta ha owa sadi abinci yana ci ana hira har wajan Sha ayan dare Bashir ne ya fara mi ewa yayi musu sallama sabida Gobe zasu je Abuja shida Aliyu dan duba wasu motoci da aka kawo sabbi kamfanin Aliyun na can. Su safna kuwa anga yaya sadi ai sai ma mi afa da sukai suna ta zuba masa zance kala kala suna bashi labarin makaranta shi kuma sai jansu yake yana ta sakin far'a Ammi wani irin da i take ji aranta gaba aya an nata kansu a ha e yake haka suke in sunga junan su kamar su ha iye kansu Aliyu ne ka ai bai da sakin fuska sai dai shi in yafi dukkan anta son an uwanshi Kawai miskilancin sa ne da zafin zuciyarshi yasa ba'a fahimta. Sai da sadi ya sanya su Safna suka kai Kayan abincin kitchen yasha ruwa sannan yace musu su tafi su kwanta dare yayi. Sallama sukai masa suka nufi akunan kwanan su. Falon yayi shuru daga sadi sai Ammi ya gyara nutsuwar shi ya kalli Ammi sosai cikin sakewa dan Ammi bata alkunyar an fari da Sadi gaba aya ta sake da anta yadda ba'a zato sabida sune sanyin idaniyarta Sune garkuwa a rayuwarta tun suna ananu take gwagwarmaya dasu Sabida suna ananu mahaifinsu ya rasu yabar mata su duka duka lokacin Sadi baifi shekara goma sha biyar ba Aliyu sha Hu u dan tsiransu da sadik shekara aya ne Salma ce suke da an tazara da Aliyu na kusan shekara Biyar ita lokacin tana shekara tara Bashir shekara bakwai Safna shekara hu u sajeeda shekara aya haka Allah ya auki ran mijin nata yabar mata wa annan ananun a wannan tasa ta sha u da an nata taja su ajikinta fiye da ima. "Ammi tun safe Aliyu ya kirani a waya wai Mami ta tashi tana ta zubar da Jini haka yace sunje asibiti a gigice hankalina ne ya i kwanciya shine na biyo jirgin dare nazo akan wannan batu" Sadi ya fa a cike da nutsuwa yana fuskantar Ammi wadda ta bada dukkan nutsuwarta a tare dashi. "Nima bai gaya min ba sai a wajan masu aiki naji, Amman dan shishshigi har an cikin gidanku sun cika asibitin" Sadi ya kawar da abin da Ammi tace dan har ga Allah baya jin da in yadda Ammi take wa an uwan mahaifin nasu. "Ammi ni ina ganin kamata yayi kawai Aliyu ya ara aure, Dan wannn matsalar tayi yawa" Ammi ta watsawa Sadi wani kallo. "Haka ya aiko ka waje na kenan? sa o ya baka?" Sadi ya gigice dan yasan Halin Ammi inta botsare musu. "Wallahi Ammi ko aya kawai dai ni tausayi yake bani ne kinga fa tare akai mana aure dashi yanzu haka Minal shekarun ta goma a duniya kinga shima in da Allah ya bashi da tuni yana da sama da ana" Ammi ta dube shi. "Sadi zaku ga kamar ina takurawa Babana ne akan Lamarin auren shi, Ko aya ni tsorona kada ya auro matar da zata rabamu dashi Na san Baya son Mami ko ka an tsananin biyayya ce ta sa ya aureta Ni kuma na ha a shi da Mami ne sabida Duk tsiya mahaifinmu aya da Mahaifiyarta Kaga Mami tamu ce bamu da matsala da ita Kuma auren su zai ara arfin zumuncin mu da mahaifiyarta" Sadi ya sunkuyar da kanshi a asa Duk wannan fa ba Masalaha bace A zuciyar shi yake fa in haka duba da yadda Ammi take Takura Aliyu akan abubuwa da dama ko lokacin auren su ma shi direct daya kawo sakina Ammi bata musa ba Amman shi Aliyu daya kawo wata Najuwa wadda sukai B.U.K tare da ita yace ita zai aura Fafur Ammi ta rufe ido tace bata yarda ya auri Najuwa ba, Haka yace yana son wata ar nan galadanci itama Ammi ta i daga haka yay fushi yace shi yama fasa auren kwata kwata katsam Ammi taje gidan Yayarta dake fagge ta kawo masa babbar arta Mami tace ala dole sai ya aureta Duk da ba wani sonta yake ba amman haka ya auri yarinyar. "Ammi Wannan fa duk ba Mafita bace, Kowa yana son yayi aure dan ya haihu shima ya sami ansa na kanshi tunda Mami tana da matsala wajan aukar ciki yakamata abar shi ya ara aure wata il Allah ya bashi rabon a jikin wata" Ammi ta sunkuyar da kanta asa kafin tace. "Mami yarinya ce mai ladabi ka duba dukkan Mu babu wanda bata ganin darajar shi, uwa uba mahaifiyarta ma mace ce mai son zumunci, bana son ya auro wadda zata tarwatsa mana gidannan sannan yadda matan nan suke da wankakken ido ba kowacce bace zata aure shi dan Allah wata ma dan dukiyar shi zata aure shi, Muyi addu'a Allah ya bawa mami dan ita ce tamu Kome zata zama agidannan tamu ce ba bare ba" Sadi yabi Ammi da kallo ya kasa fahimtar maganar Ammi kawai yadai fahimci Ammi tana tsoron kada Aliyu ya auro matar da yake sone tazo ta rabasu shiyasa ta aura masa mami sabida tasan baya son mami biyayyace yake mata sannan kuma bayan haka tasan kome mami zata zama ta tace tunda ar yayarta ce. Sallama yayi mata ya nufi masaukin shi ya kwanta Cike da tunani kala kala sai da Asubahi suka ha u da Aliyu a masallaci. Cikin barkwancin da yake jan Ya sadi dashi dan in kana son kaga Aliyu ya sake sosai to Sadi na wajen sabida sha uwar da sukai da Sadi Aliyu baya oye wa Sadi komai nashi kamar yadda Shima sadi in baya oye masa tun asali basu da abokai awaje su biyu ne aminan juna wanda ko Ammi bata san wani sirrin nasu ba. "Ah Babban yaya kaine agidan namu?" Aliyu ya fa a yana murmushi. Sadi yace. "Ba dole ka ganni ba tunda kai min waya hankalina bai kwanta ba wallahi yaya mamin?" Aliyu yayi murmushin gefen baki haka suka jera zuwa sashin Ammi a falo sukai zaman shan ba in shayi har wajan takwas suna tare da sadi Aliyu ya mi e yaje yay wanka ya dawo cikin shirin tafiya Bashir ya fito Musa ne ya kaisu airport Bayan sunyi sallama da Sadi wanda zai je ya dubo mami sai ya wuce lagos shima.......... AUTA 09022260850 *RABO YA RANTSE...!!* *NA* *AUTAR MANYA* ADABI WRITTER'S ASSOCIATION *004* a ce sosai irin ba in nan mai aukar ido dan fuskarta har mai o take yi ga wasu uraje da suka cika fuskar tata ananu Tana da ananun ido marasa girma da gajeran hanci ba zaka sanya ta cikin Mata masu tsananin kyawu ba Bata da tsayi sosai arama ce kamar zaka hureta ta fa i sabida antarta sai dai daga samanta acike take dam haka zalika asanta ma ta wajan hips inta a cike yake dam amman tafarar aya ba zaka hango hakan ba har sai ka ura mata ido Tana da wani irin jiki Wanda ake ce masa karuwan Jiki mai oye halittar jikin mutum, Yanayin jikinta shiya oye mata shekarunta wanda tana cikin shekaru Ashirin da hu u da haihuwa amman in ka dube ta sai kace ar shekaru goma sha shidda zuwa sha bakwai ce, sabida antarta yawanci awayenta basa kiran sunanta sai dai suce mata bakwaini wannan suna In taji sun gaya mata shi fa a ake da ita sosai sabida kowa yasanta bata barin kota kwana ar hayaniya ce FARHA
Chapter 3 · 0% Book details