Sashe 32
Rabo Ya Rantse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kuma aini nafi son baba ya haihu fiye da kowa sai dai ki gyara batun wata mace ai daga kan mami babu wata mace da zata shigo gidannan Kina kallon akan waccan Filfiwar yana dukan annen shi ina ga kuma ya samo wadda ya aura yake so take son shi Ina da sake ai kodan haka bama zan bari baba yayo wani aure ba haka nan ze hakuri mami ta zame masa matar addara mutu ka raba takalmin kaza" Salma tabi Ammi da kallo. "Ammi duka maganganun ki se naga kamar kina son kanki ta yaya zaki ce baze yi aure ba bayan da Ku in sa da uruciyar shi Allah ya huci zuciyarki Ammi su kuma su cigaba da rashin Kunya da aukar baki sun manta dukan daya ta a min seda yaji Min targa e akan abin da bai ka ya kawo ba Nikam Ammi na wuce su Dady zan auko a school Allah ya basu lafiya" Salma ta fa a tana aukar handbag inta tabar akin. Ammi bata iya cewa salma komai ba sabida ita indai akan su safna ne to fa a take da kowa Bare kuma ka ta a Mami. Salma na fita falon suka ci karo da Hajjo dake ebe kayan abincin safe wanda basu ta a shiba tana jera na rana. Har asa salma ta zube tana gaishe da hajjo. "A,a uwar masu gida kece a gidan namu bara na ha a abinci" Hajjo ta fa a tana dariya. Salma ma dariyar tayi. "Wallahi Hajjo tafiya zanyi sabida su Dady suna school zan auko su nima kiran ammi ne ya fito dani daga Hospital da ba abin da ze kawo ni nan sabida yara suna makaranta" Hajjo tayi dariya. "Allah sarki su Almustapha sarakan iriniya mutanan su safana amman zasu ara zuwa mana hutu ko? dan naga Alhaji Ali yana son yaran nan suzo hutu yayta aukar su suna fita siyayya shima dai Allah ya bashi nasa" Salma tayi dariya. "In sha Allah hajjo zasu zo ammi ce bata auren dasu fa a suke amman zasu zo se anyi Hutun School, ai yaya Ali akwai son yara yakan je min jifa jifa amman ba danni ba se don su Dady Dan har yazo ya tafi ma baifi yamin magana aya zuwa uku ba yana can tare dasu suna wasa kin san in yaga yara" Hajjo tace. "Haka ne akwai son yara kam Alhaji Ali shima Allah ya bashi" Salma ta amsa da "Amin" kafin ta bu e jakarta ta auko dubu biyar ari biyar ta mi awa hajjo. "Gashi hajjo kisai Goro" Hajjo tai dariya tana cewa. "Ke wai bakya gajiya salamatu Da sallah kimin inki duk da wanda hajiya ammi da Alhaji Ali da sadik ke min kema se kinyi ki sai min ragon layya gashi har wannan shekarar zanje aikin hajji" Sai ta soma arin yin kuka. Salma tace. "Haba Hajjo ai kome mukai miki bamu fa i ba ai shege shike manta alkairi abin da kikai mana dan kawai kin i yarda da zaman sashin nan ne kika ce Kinfi son na an aiki ai ba da ban haka ba hajjo da ba zaki dinga komai agidannan ba makka ba dan kirata bace ai da ba zakije yanzu ba da tuni kin manta da zuwa" Salma ta fa Hajjo tace. "Allah ya saka muku da alkairi yadda kuka ri eni Allah ya duba ku ya ara muku wadata" Salma tace "Amin hajjo ina akin anwar Musa?" Hajjo tace "Muje ciki gashi can" Suka jera zuwa akin da Farha take ciki tare da Hajjo........ *RABO YA RANTSE! littafin ku i ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a auka a turo,shaidar biya 09022260850* *A LOVE STORY 35* Salma ce a gaba sabida haka ita ta soma bu ofar ta shiga kwance ta hango yarinyar sai shashshe ar! kuka! take ta dun ule jikin ta waje aya acan arshen gado. Gyara Murya salma tayi tare da cewa. "Assalamu Alaiki" Farha ta ago da yar tana kallon meyin sallamar wadda sam bata ji shigowarta ba sai sallamarta kallo aya tayi mata ta kauda kai kamar su har tayi yawa dashi daga gani babu tambaya itama anwar shice. Da murmushi a saman fuskar salma ta arasa bakin gadon ta zauna. Hajjo kuma ta tsaya a gaban madubi Fuskarta cike da tausayin farha take ta faman jera mata sannu. "Zaki iya tashi? naga fuskarki duk ta haye ta suntume" Cewar salma cikin kulawa. A hankali Farha ta saka hannunta a saman gadon ta dafa shi tana arin tashi sabida gaba aya jikinta ciwo yake mata. Hajjo tazo da sauri ta taimaka mata suka mi "Hajjo muje Ki samin ita a mota sauri nake so dole zan an dubata idan yaso zan sanya driver ya maido da ita Ki shaidawa Ammi" Hajjo tasan salma dama akwai ta da tausayi. "Allah yayi miki albarka yadda kika taimaki marainiyar Allah kema Allah ya taimake ki" Da taimakon Hajjo ta saka hajib ta ri o ta ajikinta har parking space salma ta sanya ta a mota tana ara jadda dama Hajjo akan ta sanar da Ammi A back seat farha ta kwanta salma ta shiga driver seat ta zauna ta tayar da Motar suka bar Gidan. Hajjo cike da bin umarni ta isa akin Ammi bata ciki sai ta shiga akin ammatan wanda ta tarar da Ammi zaune tayi tagumi ta zuba musu ido duk suna kwance kamar zata Shiga Jikinsu sabida kusanci. "Sannu da hutawa Hajiya Ammi" Hajjo ta fa a tana Zama a saman carpet akin "Yawwa Hajjo salma ta tafi? ga ruwan data sama safna ya are amman tunda ta nuna Min bara na cire" Hajjo ta kama ha a cike da al'ajabin langwan an na Ammi kafin tace. "Wato abin har yakai ga arin ruwa ikon Allah shiyasa yadda na jera abinci haka nazo na kwashe se masu gadi na bawa" Ammi da take Cirewa Safna allurar Ruwan da aka saka mata tace. "Hajjo waya ke ta wani abinci ni ai banda kwanciyar hankali har se naga yarana sun dawo yadda suke Kinsan Allah jiri nake ji da yar idan Jinina bai hau ba Yau Baba ya ata min rai na ba an ka an ba" Hajjo tayi saurin tare ta tare da cewa. "Kuma karki sake ki masa baki akan Abin da bai kai ya komo ba dan ke uwa ce" Ammi dai bata ce komai ba Hajjo ta kuma cewa. "Dama Uwar masu gida ce tace na shaida Miki ta wuce da anwar Musa zata duba ta dan sunji mata rauni itama amman zata sa driver ya maido miki da ita" A hasale Ammi ta juyo tana cewa. "To ina ruwana da ita ni dama daga wannan fitar kada ta dawo Min gidana tsinanniya mai ba ar fuska Tauraruwa mai witsiya ganinta ai baya da alkairi a tare dani" Aran hajjo tace da yake an ta an gwal amman a fili se tace "Hajiya Ammi shifa a na kowa ne da a da dukiya baka musu Mugunta ki sassautawa marainiyar Allah a a'ida daga ita har Safana basu kyau ta ba duk sun zagi iyayen su" Ammi ta aga wa Hajjo Hannu tare da cewa. "Ke kinga sanda akai hakan har da zaki zo kina Fa in yadda akai da Allah tashi Kije kawai maganar nan ata mini raina take" Hajjo ta kama Ha a cikin mamakin halin Ammi akan anta. "To Hajiya Ammi ki ha uri nayi ba daidai ba meza a dafawa Hajiya aramar Naji kince yau zata dawo" Bata ko kalli saitin Hajjo ba tace. "Koma meye ni bata tata nake ba yanzu ta yarana nake" Adaidai nan sajeeda ta farka tana Jan Numfashi da sauri Ammi tace. "Hajjo bani ruwan sanyi da an tsumma har yanzu da zafin zazza in a tare da ita" Hajjo da sauri ta shiga toilet in su Kaca kaca toilet in ba alamar an wanke ita dai taro ruwan tayi ta kawowa Ammi tare da tsumma fari mai kyau. Hajjo ce ta taimaka mata ta tubewa Sajeeda riga ta dinga goga mata ruwan sanyin ita kuma sajeedar ta kwantar da kanta a kafa ar Hajjo tana hawaye. "Jiba fa hajjo kalla shatin waya har wuyanta kai gaskiya Baba ya cuceni" Ammi ta fa a kamar zatayi kuka. Tana gama gogewa sajeeda Jikinta a hankali ta mayar mata da rigar Jikinta Muryar sajeeda a hankali tace "Hajjo zan sha tea" A hankali ta fa a tana komar da kanta saman pillow ta kwantar Hajjo ta mi e ta fita dan ta ha o mata shayin a ranta tana cewa yau fa ba sau i an ta o Kitse a saka ka a rana ka narke a barka a inuwa ka daskare. Hajjo ta ha o shayin mai kauri ta kawo mata kur aya tayi tace bata sha agigice Ammi tace "Me kike so a dafa Miki ko asaka driver ya siyo Miki?" Sajeeda ta girgiza kai alamar bata Bu atar Komai daga Hajjo har Ammi sannu sukai mata ta koma ta kwanta Safna ma Bu e ido tayi wanda Ammi ta mayar da kallo kanta tana cewa "Sannu meke miki ciwo yanzu" are baki tayi kamar wata yarinyar Goye. "Ammi ina ga ya karya min hannuna nauyi yake min wayyo Ammina" Ammi tayi kan safna tana duba hannun ita dai hajjo kama ha a tai yau tana kallon Ikon Allah safna fatan dankali ta bu ata hajjo ta kawo mata a wula ance tasha ka an ta ture. Ammi ta dubi hajjo ido jajir. "Hajjo jeki akina saman madubi na akwai maganin hawan Jinina ki auko Mini jiri nake ji" Hajjo ta dubi ammi. "Haba Hajiya Ammi akan wannan an abu zaki agawa kanki hankali har Jinin ki ya hau Idan Alhaji Ali be dake suba waye ze dake su kada fa ki bada gudunmawa wajan sangarta an ki" Ammi ta ago ido tace wa hajjo "Ai idan ana basu kasheni ba ke kya kasheni da wa annan maganganun naki zaki ebo min kona tashi da kaina" Hajjo ta Mi e ta nufi akin Ammi ta kwaso mata magungunan wanda dama tana da hawan Jinin tun bayan rasuwar Baban su Aliyu ta