Sashe 50
Rabo Ya Rantse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ammi an fitar da Kujerun falon an sauke labulayen falon duk an fitar dasu sabon Paint ake tayi a part in zuwa azahar an sake sabbin Kujerun falon tare da labulaye Komai ya sauya Falon sai tashin amshi yake yi. Gaba aya jikin farha ciwo yake mata haka ta shiga aki ta cire kayanta ta shiga wanka tana wanka tana tunanin Bawan Allah matar sa tace kwana takwas zeyi yau gashi har ya kwana Goma sha hu u bai dawo ba, Haka tayi wankan ta fito tana zaune a bakin Gado tana shafa mai Safna ta shigo akin ta an kalleta. "Kizo Ammi tana kiran ki" Daga haka ta juya bata jira cewar Farhan ba, Farha ta gama shafa man sama sama ta je gaban kayan ta Riga da skirt na atamfa ta auka Sedai data zo saka rigar ka an tai mata ta i shiga Musamman daga wajan irjinta Seda ta cire bra sannan ta saka rigar skirt in ma da tsalle ta saka shi aikuwa se Nishi take Numfashin ta har sama yake da yar take janyo shi Hijabi dogo ta saka har asa ta fita daga akin zuwa akin Ammi shima an sauya kayan gadon akin dan bana da bane Ammi ta dubi Farha yau babu wannan aure fuskar tace mata "Fati yanzu me zaki yi?" Farha tana wasa da yatsun hannunta tace. "Babu komai Ammi, wanka dai nayi" Ammi ta an dube ta. "To dan Allah zaku shiga kitchen Keda Hajja, zaku yi girki kamar kala Biyar sabida yau Sadi zezo da iyalan shi, da Bashir da Baba duka yau zasu zo Ina so kuyi girki mai kyau dan Allah" Farha cikin ladabi ta amsa wa Ammi, sannan ta baro akin sallah tayi sannan ta fita har Hajjo tazo Kayan miya farha ta soma gyarawa ita kuma Hajja tana ora sanwa. "Hajja wai waye Baba ne? naji Ammi tana yawan cewa baba?" Cewar farha wadda take Cire hancin attaruhu, Hajja tayi dariya tana cewa. "Nawa zaki biyani na gaya miki waye baba" Itama farha dariyar tayi tana cewa "Hajja zan baki jakaliyan ari" Dukansu dariyar sukai kafin Hajja tace. "To Alhaji Ali shine Baba Kinsan sunan Baban Hajiya Ammi gare shi" Farha ta cika da mamaki domin sam bata auka shi bane Baban dama yau ze dawo wato shiyasa Aunty mami tun safe tace ta fita gyaran Jiki da unshi da Kitso Ah lallai. "To Hajja sadik fa naji tace yau zezo da matar sa shima anan yake?".Hajja ta ora tukunyar akan gas sannan ta juyo "Eh yayan Alhaji Ali ne yana lagos yana aiki a ayan kamfanin Alhaji Ali, Tare akai Musu aure sadik nada mata aya da yara Uku duk zasu zo anjima sabida zasu je umarar azumi ne nan da an kwanaki" Farha bata ce komai ba aikin su suka cigaba dayi Wajan Magariba suka kammala Lokacin Mami ta shigo kitchen in tai kyau ma sha Allah Fuskarta tai fiyau sabida sabon Kitso warmers in abincin ta shiga dubawa tana ta yiwa su Hajja sannu. "Ina abincin Ammi?" Cewar mami tana kallon farha. "Ai gaba aya aka ha a abincin sabida tace anan zasu yi dinner" Cewar Farha, Mami ta yatsina fuska tare da cewa "Da anyi wa Ammi ko tuwon semo ai ina zata iya wa annan ciye ciyen ai se mu" Hajja tayi dariya tana cewa "Hajiya mami ta ammi wannan soyayya taku har tayi yawa to ni dai na tashi sedai Fati tayi mata" Farha jitai kamar tace wayyo Allah dan ba aramar gajiya tayi ba ga ciwon mara ga zafin hannu wanda gyaran attaruhun data yi ne yaja mata shi ga ciwon baya ga wani yawu da yake tarar mata abaki zuciyarta na tashi tun amshin tafashen naman data yi bata sami sukuni ba. "To Farhan an yi mata tuwon Before ai magariba" Mami ta fa a tana fita daga kitchen in farha dan haushi Ko sallamar da hajja ke mata bata amsa ba ta ora ruwan tuwon sannan ta fita daga kitchen in ta koma akinta Da gudu ta shiga Toilet ta ri e Ciki tana she a amai a galabaice ta fito tana Numfashin wahala jagwab ta kwanta a gado hannunta dafe da asan mararta daya aure yana mata ciwo Miyau ne ya tarar mata taje ta tofar ta kuma dawowa Kitchen in ta shiga ta Bu e Fridge ta auki lemon tsami ta yanka tana tsotsa seda tayi sallar magariba sannan ta tu a tuwon ta kwashe sannan ta ora Miyar Kuka wani ha amshin turare taji wanda kafin ta ago mami ta shigo kitchen in taci adon golden lace inkin Bubu wanda yayi mata cif ajikinta ga wasu uban gwala gwalai sar an kunne awarwaro data zuba fuskar nan tata taci kwalliya, Kallo aya Farha tayi mata taji zuciyarta ta motsa wani irin zafin Kishi na taso mata yanzu fa duk wannan kwalliyar Domin Mijinta tayi ta ko, maganar mami ce ta katse wa farha tunanin da take. "Farhan nayi kyau kuwa? Yaya yayi min waya suna airport taimaka ki ora masa ruwan tea mai kayan amshi amman mai an yawa sabida ta lagos ya biya tare suke da su Ya Sadi Ni bara naje wajan Ammi, amman kafin na auko min wancan Ludayin na sama" Farha tayi Murmushin ya "Kin yi kyau mana Aunty sema ya gani ya bada tukwici" Ta fa a tana juyawa wajan Ludayin Mami tana dariyar jin da i da sauri tai wuf ta zuba magani a ruwan Miyar da farha ta ora Farha sam bata lura ba ta mi a wa mami ludayin ta Cigaba da ha a miyar tata Mami ta fita da Ludayin da babu abin da zatai dashi dama dan ta zuba magani a miyar ne tayi wa Farha dubara Farha da ayan Gas in ta orawa Aliyu tea in Ta raba hankalinta Biyu can tana miya nan tana kula da tea bayan ya tafaso ta zuba a flaks ta aje Miyar na tafasa amshin daddawa dasu citta na tasowa Farha taji zuciyarta na tashi sabida bata san amshin ankwali ta saka ta Toshe hancinta haka ta kammala Miyar ta ha a takai Falo ha e da sauran kayan abincin ta gyara dining in tas ta auko turaren wuta ta kunna. Ammi ita kanta a ranar seda ta yaba da yadda Farha tayi arin ha a komai aikuwa se sannu take mata Ammin ma taci gayu Su safna ma haka. Ita dai farha data samu ta shiga aki kwanciya tayi a saman gado nan da nan bacci ya auketa............*RABO YA RANTSE! littafin ku i ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a auka a turo,shaidar biya 09022260850* *A LOVE STORY 62* Yana saukowa daga step in jirgin yana lumshe idanun shi sabida sha ar Iskar Jahar sa Abar alfaharin sa da yake yi kano kenan ta dabo ci gari koda me kazo an fika mai mata mai matasa mai malamai mai masoya Manzon Allah ( s.a.w ) mai dala tushen birni mai gwauron dutse mai masauratar da take da tarin tarihi kano jalla babbar hausa kano tumbin giwa! Da sauri musa ya araso gaban sa bayan ya bar harabar da jirgin ya sauke su Musa ya amshi aramar Jakar dake rataye a kafa un sa Haka suka nufi inda Musa yayi parking in Mota yana jiran shi wata ha iyar Black mercedes benz s class, Musa ya bu e masa Back seat ya shiga ya zauna gaba aya ya gaji tunda yabar lokoja ya tafi lagos bai zauna ba zirga zirga suke shida Bashir wanda jin sadik zezo arewa yasa wa Aliyu kuka akan ko kwana aya ne ya barshi yazo yayi shima tausayin Bashir yaji shiyasa ya bar shi suka tawo tare sedai shi Aliyu ko acikin Jirgi yana Vip section sabida haka jirgin su na landing ya sauko batare daya tsaya jiran su Bashir ba dan su Driver ne yake jiran su. Sadik da Yaran shi da sakina da jamila anwarta da bashir driver ne ya auko su a wata Farar BMW suma Musa yana tafe yana bawa Aliyu labarin yadda Shari'ar Md ta kaya Shidai ya dafe kai bai cewa Musa komai ba suna isa gida part inshi ya shiga Mami ta tare shi tana masa sannu ya hau sama ya shiga wanka ya auro alwalar sallar magariba a aki ma yayi sallar sannan ya sauka asa dan yunwa yake ji Jeans ba i ne a jikinsa se farar Polo shirt se amshin turare yake mai sanyin amshi ya arasa gaban dining ya zauna yana kiran mami. araso tana rankwa o wa jikin shi. "Yaya gani nayi sallah ne" an kalleta ka an tayi kyau ba laifi. "Ina abincina?" Tai murmushi. "Ammi tasa an ha a a part in ta acan zamu yi dinner" Bece komai ba yayi sama da kanshi ya jingina jikin Kujerar da yake kanta yunwa yake ji ba ka an ba can ya kuma cewa. "Ko an ruwan shayi ma babu?" Mami tace "Eh duk suna can" aramin tsaki kurum yaja ya fito da wayar shi ya shiga danne danne seda yayi sallar Isha'i sannan suka jera part in Ammi shida Mami. Su sadi a part in Ammi suka sauka extra room in dake Kusa dana su ammi Sakina ta saka kayanta shi kuma Sadi ya aje nasa a part in Bashir sabida su ba'a gyara musu part insu ba akwai datti sosai Kuma duk aikinne yayi yawa sedai ko zuwa Gobe wanka sukai tare dayin sallah Nan fa suka baje a falo ammi nata tsokanar su Minal an sadik wa anda suke jin yarabanci don maganar suma bata fita sosai saboda zaman Cikin yare, Intisar ce ma mai magana da hausa amman Minal da Hidaya se turanci se yarabanci nan da nan sun koma kamar abilu. Zuwan Aliyu da Mami ne yasa Bashir dasu safna suka an shiga Nutsuwar su da dariyar da suke yi dan Sun san Gogan ba wasa Jamila anwar sakina wadda ita kebin ta wadda sakina keson ta ha a ta da Aliyu shi kuma ya i yarda se kallon Aliyu take kamar ta lashe shi lura da kallon da jamila kewa Aliyu ne yasa Mami ta i sakin fuska tai