← Book details Rabo Ya Rantse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 94

Sashe 70

Rabo Ya Rantse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

guda suke yi bayan sunyi shirin Bacci da ike suma Shirin Komawa gida nageria suke tayi Ammi ta dubi Safna"Ki an ta o yaron nan mana muji ke waya gaya miki haka akewa mazan yanzu in babu kula ai basa zama" daga sajeeda har safna dariya suke Ita ko mami da yake ba da ita aka fita ba tuni ma tayi baccinta dan tunda tazo bata da Lokacin Kowa Kullum addu'arta Allah ya bata ingantaccen rabo mai albarka, sakina kuwa masaukinta daban ita da yaranta Sadi ma ba waje aya suke ba, Safna ta fito da wayarta ta kunna data Tana hawa yana mata sallama da sauri ta shiga mai da masa da replay amai makon ya dawo mata da amsa se ya kira ta voice call, Ta mi e daga wajan su Ammi ta shiga wani an corridor ta tsaya amaimakon tai masa sallama se cewa tayi. "Ina jinka" Kamal ya kama ha a cikin aurewar kai yace mata. anwata kamata yayi ki fara min sallama tare da cewa yaya naje masaukina amman kince kina ji kamar wadda nai wa dole" Sam ita safna bata san ba daidai tayi ba seda ya gaya mata sannan ta kama ha a cike da jin kunya tace. "Au na manta amman kai ha uri" Bai ce komai a wannan ga ar ba se Magana ta gaba data biyo baya "Na ganki kuma kin min a matsayin matata kuma ni da gaske ina son ki da aure ni an kano ne, Mazaunin hotoro nine babba agidanmu ban ta a aure ba ina aiki a Asibitin Malam Aminu kano anne na biyu mata se mahaifiyata dafatan kin gamsu dani nai miki bayanin kaina a ta aice kafin In mun koma nazo har gida" Safna ta washe baki cikin farin ciki tace. "Tom shikenan Allah yasa zamu ga lokacin zuwan naka" Yace. "Ke ba zaki gayan Ta aitaccen tarihin kiba?" Tace. "Sedai kazo In sha Allah!" Bai jada tsayi ba yayi mata sallama cikin farin ciki ta koma take sanarwa da Ammi har abin da ya mata gyara akai. "Kullum dama ina gaya muku ku dinga iya kalami Mazannan da kuke gani se ana lalla asu Sabida haka ki dinga saita harshe in zaki magana Bari Mu koma in Allah ya kawo shima mu ashirye Muke" Har Sukai bacci maganganun suke yi na Saurayin safna in da suka ha u dashi a saudi'a. Gabaki aya al'ummar musulmi yaro da babba kowa murnar tawowar sallah arama yake sabida sallah ce wadda ake sada zumunci ake inka sabbin kaya a saka aje hawan idi a dawo a cigaba da zaga gari. Yau sauran kwana aya sallah har Lokacin Aliyu bai dawo ba kamar yadda farha take Lissafi tuni ta saki ranta domin ta auka baze dawo bama ko se bayan sallah tun safe suka fita wajan gyaran gashi ita da Salma anan akai musu har Kitso sannan aka zana musu ba in lalle da Farha tana mitar ita baze mata kyau ba amman Cikin Ikon Allah ana mata seya fito a saman fatarta yayi mata kyau gwanin sha'awa Daga wajan Saloon in kuma wajan kar inki suka tafi Farha tana mota salma ta shiga ta amso se suka wuce wajan saida takalma da jaka A tare suka fita salma tace ta za i wanda yayi mata ba i ta auka tace bata son jaka dan bata dame taba suka je wajan mayafai nan ma ta za a tare da sar a da an kunne da turare salma ta biya ku in suka wuce Gida a falo suka tarar da mai aikin salma tana ta gyara farar shinkafar wainar da za'ai gobe ga kaji da kayan miya nan Mijin salma ya kawo Ita dai farha kayan Sallar ta bu e zaro idanu tayi sabida ganin ha an Jan lace da yasha buba mai azababban kyau se material da shadda wadda aka mata aiki dan murna Farha kasa magana tayi data gwada inkin kamar an auna yayi mata cif sedai Ko wanne daga sama ya kamata ta rasa wannan cika da irjinta yayi har asa ta zube tana cewa. "Aunty salama nagode da Hidima Allah ya saka miki da alkairi ya raya zuri'a" salma ta kama baki cikin mamaki. "Kai bari kada ki kuma min Godiya ai ya zama dole" Farha kwashe kayan tayi duka takai aki sannan tayi alwala tayi sallar la'asar ta fito waje domin kamawa mai aikin salma aikin Sallar da take yi ita kuma salma ta fito Cikin shiri tace zata je Gidan Ammi ta dawo yanzu suka sauka Jin haka yasa Jikin farha yayi sanyi haka dai suka yiwa Salma adawo lafiya ta fita aikin ya kaisu har dare dan har su in cincin sukai wajan taran dare salma ta dawo Lokacin farha ta bar mai aikin ta ita kuma ta koma aki wanka tayi ta gasa Jikinta dan ta gaji sosai bata kuma fitowa ba bacci yayi gaba da ita. Su Ammi ne suka sauka da wajan magariba shiko se wajan Goman dare Jirginsu ya sauka Musa yaje ya auko shi Mami kamar gawa ya tarar se bacci take shima dai wanka ka ai yayi yasha tea ko wajan Ammi bai iya zuwa ba se Bacci washe gari ta kama sallah Gidan Ammi gaba aya ya cika da Hidima sabida su Hajja tun ana jibi sallah suka dawo kuma da yake komai an tsara kafin su ammi subar asar shiyasa gidan ya cika da Hidimar ora sauke. Wajan arfe takwas Aliyu ya fito cikin Babbar rigar shadda fara takalmi da Hula ba e yayi masifar kyau da dardumar shi a kafa a ya araso falo mami taci gayu cikin shadda turare ta fesa masa ta auko waya tana masa Hoto shi dariya ma ta bashi yadda duk yaga ta ru e da shigar tashi Mayafi ta yafa suka jera zuwa sashin Ammi wanda ya cika da an uwan Ammi wa anda dama duk sallah haka gidan yake cika Suka gaggaisa da juna Lokacin sadi shima ya shigo sabida haka tare suka Mi e da Aliyu domin tafiya masallaci. "Ba zaku ci ko waina bane tunda masallacin da kuke sallah se tara suke tayarwa" cewar Ammi Aliyu murmushi yayi tare da cewa "Haba Ammi ai mukai zaman cin waina makara zamuyi Dan Allah yaya sadi kazo Mu wuce" sadi da yake ta tsokanar Safna wadda taci kwalliya wai saurayin da suka ha u dashi a saudia ne zezo Shine yabi bayan Aliyu wanda tuni ya ace daga falon Musa ne yaja su zuwa babban masallacin Gidan sarki anan sukai sallah Shidai Sadi gida yayo sabida Yadda mutane suka ya e Aliyu tun bayan idar da sallar wanda har seda yaje suka gaisa da mai girma gwamna sannan ya samu ya fito daga cikin Taron mutanan da yar matasa se kirari suke masa Da yar ya shiga Mota kansa har ciwo yake masa dan yawan matasan har yayi yawa Har Motar shi tabar wajan Mutane basu dena bin bayanta ba. "Musa kaini Gidan su fatima na gaishe da mahaifanta kafin mu wuce" Musa ya an juyo tare da cewa. "Ranka ya da e ka manta yau sallah kowa yana gida idan har kaje Gidansu tofa za'a san kaine gwara ma kai shigar dare amman innai ba daidai ba a yafe ni" Aliyu ya lumshe ido. "Haka ne kuma musa to kaini shara a Gidan Salama kokuma kaga kawai Ka bani key in motar zanje da kaina kaikuma zan sauke ka a ofar Gidana se ka auki mota ka wuce harkokin ka" Musa yace. "Mai gida duk yadda kace daidai ne" Musa ya nufi Gidan Aliyu a bakin gate Aliyu ya sauke Musa shikuma yaja motar zuwa gidan salama dan ya matsu yaga ar budurwar sa. "Tsarki ya tabbata ga Ubangijin halitta sarkin daya shinfi a sammai Guda bakwai ya shinfi assai Guda bakwai gaskiya yau inda an uwana ze ganki Aunty fatima daya susuce" Salma ta fa a lokacin data ga farha ta fito daga aki sanye take Cikin Lace in da suka amso jiya daga inki, Yayi mata shegen kyau Sabida fuskarta tai fiyau Dalilin sabon Kitson da akai mata ga Fulawar Datai mata kyau a hannunta ga sar a da an kunne wanda suka cika mata irji da kunnenta. Mayafin ta a kafa a ta saki Murmushi tana oye fuskarta ta zauna a saman kujera dan salma ta hanata zaman asa Waya salma ta auka ta dinga zubawa farha Hotuna tana faman zuzuta kyan datai Farha Tashi tayi taje Kitchen ta zubo waina ta dawo ta zauna tana ci Dady yace zeci shima tace yazo suci tare. Suna cikin cin wainar ne Yayi sallama falon amshin turaren shine ya sanar mata daya araso tsakiyar falon asa tayi da kanta batare data cigaba da cin wainar ba. "Oyoyo Uncle" yaran salma suka ane shi salma cikin murna tace. "Sannu da zuwa yaya jiya har na baro gida baka sauka ba har ya sadi na cewa ko se yau" Zama yayi a kujerar dake kallon farha yana arin ora idanunshi akan fuskarta sedai ta i yarda. "Se wajan 10 na sauka ay Salama yaya gida ya hidima nafa gode" ewa salma tayi tashi ga kitchen ganin haka yasa farha ta an kalle shi akai sa'a shima itan yake kallo. "Sannu da zuwa anyi sallah lafiya" Murmushi yayi batare daya amsa ba. "Kinyi kyau So ma sha Allah" Ya fa a yana lumshe ido tashi tayi daga wajan ta nufi aki ya bita da kallo lallai da gaske tayi iba. Kayan abinci ne salma ta shiga jera masa aga mata hannu yayi. "Salama so kike nai abin Kunya cin abincin gidan suruki a,a turo min fatima da kayanta ina Mota sauran maganar se Munyi waya naji dukkan abin arzi in da kikai mata Na kuma gode Allah yabar zumunci" i ne an naira 500 sabbi ya dire mata yace ta saiwa su Dady Sweet salma sakin baki tayi Lokacin shi har yakai ofar falon Ma. "Yaya to na zuba maka a basket ka tafi dashi amman in baka ci ba ai bazan ji da i ba" Bai ma jita ba Lokacin har ya arasa wajan motar shi ya bu e ya shiga salma tashi tayi ta shiga akin farha a kwance ta tarar da ita "Mai
Chapter 70 · 0% Book details