Sashe 49
Rabo Ya Rantse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
zata kashe Musu kawu Kullum Umma setai kuka damma akwai Ya Sadiya da take yawan zuwa cin Uban kowa take agidan sedai daga ta fita zasu ora shima kawun Wuni kukan a kawo masa Fatima shiyasa Kullum Jinin sa a haye yake baya sauka Kullum cikin shan magani yake. "Umma yau se godiyar Allah, Amman zan fita wajan Abokina se a siyo masa" Umma ta kalli Nura da tausayawa yaran ba aramin ari suke yi da mahaifin suba kunya ta kama Umma tasan duk a sanadin arta Komai yake ta faruwa da Kawu, "A,a Nura ka bari yanzu na aika Ikram Gidan sadiya abin da ta samo se a sarrafa masa" Nura yace "Umma me yasa zaki aika mata Kinsan halin Ya sadiya da Saurin Ki ima Yanzu seta tawo ta auka ko ciwon nasa ne ya tashi kuma ai tana ari kaf an gidannan bamai kula da kawu kamar ita Kusan Kullum fa seta yo masa Girki" Umma tai murmushi "To ai ya zama dole Nura, bada ban naga tana sana'a ba da bazan aika mata ba to sana'ar dana ga tana yi ce yasa nake aika mata ai ya zama dole" Nura ya shafa kai yace "Umma an gyara shi ga Ba o nan yazo wajan shi wai mijin farha ya aiko shi" kawu yana jingine amman se ganin shi akai ya mi e umma ta kama shi tana cewa "Kabi a hankali" Cewa yake "Nura ina ba on shine baka gayan ba yana ina ina fatiman take Tazo ta ganni kafin Allah ya auki rayuwata" walla ce ta kawo Idon Umma bata ta a sanin kawu na son an saba se akan farha ashe duk jarabar Fa an shi ya damu da an sa gashi nan Abin da yayi wa Farha yaja masa ciwo. Abokin musa ya tu e takalmi ya shigo akin ya zauna a tabarma suka gaisa da Umma sannan suka gaisa da kawu Abokin Musa yace. "Dama Alhaji ne yace nazo na duba ku, Sannan ga sa o can A mota yace a baku" kawu yayi saurin cewa "Kai ni babu wani sa o ina fatima take tana wani gari wani hali take ciki?" Abokin Musa yace "Baba kai ha uri wannan Ba'a bani damar na sanar dakai ba iya wannan ka ai aka umarceni shima abin da yasa na fa a maka sabida kasan yadda garin ya koma mutanan duniya sun lalace kada kuga sa o sama taka ku tsorata shiyasa aka ce na bayyana wanda ya aiko ni, Amman garin da take da sauran su wannan ba hurumina bane ni dai nasan arka tana cikin oshin lafiya Kuma ka godewa Allah arka ta sami Miji na nuna sa'a" Daga umma har kawu ba wanda ya iya magana domin su ba wannan bace Bu atar su ba bu atarsu sanin ina arsu take Abokin Musa ya mi e tare da dire damin an dubu dubu har guda biyar a gaban kawu bai saurari me kawun ze fa a ba yabar akin Matan gidan ko wacce tai tsaye cirko cirko suna sauraran abin da Ba on yake fa a ko wacce ta cika da mamakin wannan Aike Da Nura da Halifa ne suka bi Abokin musa mota kamar yadda ya bu ata Kaya ne na abinci buhunan shinkafa taliya makaroni mai komai daya danganci abinci akwai shi haka sukai ta fito dasu suna kawowa Gida wanda har an ma ota seda suka taya su gaba aya tsakar Gidan su Farha ya cika da kayan abinci abokin Musa ya shiga Mota bayan sunyi sallama dasu Halifa Musa dabe Fito ba yaja Motar suka bar bakin layin. Hankalin Umma tashi yayi data ga kayan abincin ta shiga wasi wasin wani irin Mijin farha ta aura kodai an yankan kai ne da sauri ta kawar da tunanin tana ayyana alkairi akin Kusa da kicin aka shigar da kayan abincin Wanda kafin kice kwabo Babarsu Ru ayya ta ha a wuta an ora sanwar safe wadda ba'a ciba kawu kuwa Gaba aya Jikinsa yayi sanyi Nura ya kira ya bawa duka ku in da abokin Musa in ya bayar Matan gidan bakin ko wacce ya Mutu Murus sabida al'ajabi Ma ota kuwa le owa suke zuwa dare Gida ya cika da an barka barka wasu har cewa umma suke dama sun san watarana kawu ze Huta ajikin wani a cikin an nashi Ikon Allah farha data fi kowa Muni agidan itace mai rabon Jin da i yaya Sadiya ma data zo taji kayan arziki Ihu ta saka harda rawa tana cewa Ai alkairi yanzu aka fara gani babarsu Hadiza kuwa ta kasa magana cikin dare ta kama habaici tana ayi dai su gani idan tusa zata hura wuta waya sani ma ko an mafiya ne amman ba yadda za'ai farha ta auri mai kudi irin haka kunjifa Hassada seda kawu ya fito yayi mata cin Mutunci sannan tai shuru Gidan su Farha ya wadata dan Kayan abincin sun haska Gidan an gidan kowa murnar zeyi ci uku ta ishe shi Ku in Da kawu ya bawa Nura kuwa Nura bai ta a su ba zuwa yayi ya zuba a cikin account. Abokin Musa ne ya dubi Musa yana gaya masa duk yadda ya sami mahaifin yarinyar Musa ya jinjina lamarin tare da aukar alwashin sanar da Aliyu duk yadda ake ciki bayan Musa ya sauke abokin sa waya yayi wa Aliyu ya gaya masa duk yadda sukai musa ya ara da cewa. "Kasan yayin ta suna aiki a kamfanin mu shiyasa ni banje sun ganni ba na tura abokina dan nasan baka Bu atar su sanka a yanzu" Aliyu yayi Murmushi daga nasa arin kafin yace. "Haka ne Musa ina son ka gayawa manager a ara musu Ku in albashin wannan watan harma da sauran watannin gaba sannan ka koma akai Baba asibiti mai tsada a duba shi sannan ina son a samu Leburori masu aikin sauri Su fara gyara Musu Gidan su inda hali ma har Bene a ora sannan wannan kayan abincin duk sati Biyu zaku dinga kai Musu amman na cikin azumi yafi ko wanne son samu ma a ara masa mota aya wadda ze rabawa Ma otan shi musa kada ka Bada fuskar da zasu sanni kasan har yau Ammi bata san nai aure ba wannan shine dalilin daya sa ban so su san ni wanene" Musa ya amsa cikin bin umarni kuma beyi mamakin hidimar da Aliyu yace ayi ba dan wanda bai ha a komai dashi bama yayi wa bare surukan sa. Washe gari Abokin Musa ya koma wajan kawu Asibitin Ku i ne mai tsada aka kai kawu aka duba shi aka bashi magani Wani an gida anan kusa dasu Suka koma wanda abokin Musa ya kama musu haya ranar dasu ka kwashe kayan su daga gidan Masu aikin suka fara aiki wanda motar yashi Bulo sumunti ta cika layin su farha Kawu da yar yabar wannan aiki dan seda Su Halifa sukai ta bashi baki da cewa ai ya godewa Allah daya sa ta silar aure farha ta sami wannan cigaba bata silar bariki ba kuma su sun yarda Mijin Farha nagari ne mai gaskiya da ire iren wannan kawu yabari ayi gyaran Gidan ma'aikata suka soma fashe Gida aka fara gyara dakin aka ora a ka fara sabon gini a saman Gidan kafin kace Me cikin kwana biyu abin ka da aikin Kudi an ora bene agidan su farha asa kuma anyi aton falo da akuna da Kitchen aciki saman ne akuna uku daga na kawu sena su Halifa asa ne ya zama akuna Hu akin Umma akin babar su hadiza akin babar su Ru ayya se akin yara guda aya se wani Kuma akin arami a gefen na Umma se Store da kitchen Se aton gate da aka saka cikin kwana Hu u suka gama aikin aka saka sola akai painti aka saka famfuna idan ka kalli Gidan ba zaka gane shiba ma'aikatan suna gama gyaran Ma ota da an uwa akaita zuwa gani kowa na santi wasu na murna wasu na ananun maganganu Sabbin kayan aki aka zuba a falon an saka saitin Kujeru labulaye tv da sauran su haka akunan su saitin sabbin kayan gado an uban su store kuma an cika shi da kayan abinci ga sola haske Kota ina kawu daya ga alatun daka dan ara masa kuka ya saka yana Godiya ga Allah lallai haihuwa mai rana dama akwai ranar daze Huta har haka Ashe rabon arziki ne yasa Farha ta turje seta auri wannan Mutumin Ita ko Umma daran da suka koma gidan kasa bacci tayi alwala tayi ta dinga sallah akan Allah yasa dukiyar Mijin farha ta halak Ce Allah yasa ya kawo farha ta ganta Allah yasa farha tana cikin oshin lafiya. Cikin lokaci ka an rayuwar Gidan su Farha ta sauya daga unci zuwa farin ciki daga matsi zuwa wadata ada ana damben abinci agidan yanzu kuwa sema ayi abincin babu mai ci da ku in wajan Nura aka sauyawa yaran Gidan makaranta aka kaisu Private school, Babar su Ru ayya ta koma Gindin Umma wanda Babar su Hadiza kuwa ta i kwantar da hankalin ta sabida ba in ciki Kullum fatan tsiya take tare da aibata farha wanda Kuma hakan baya hanata Cin abincin da Mijin farhan ya kawo da Kuma zaman gidan da Mijin farhan ya gyara anta fa a suke mata amman ta i Ji ita ko babar su Ru ayya sun ha e da umma har wata biyayya take mata shi kansa kawu yanzu ba wannan fa an idan yana wa Umma magana har asa yake da Murya wani bin idan umma ta damu da wannan Hidima yakan ce yaji ajikinsa mijin farha ba macuci bane ba da wannan yake kwantar wa Umma da hankalinta...........*RABO YA RANTSE! littafin ku i ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a auka a turo,shaidar biya 09022260850* *A LOVE STORY 61* Yau saura kwana ki Biyu azumi gaba aya al'ummar Musulmi sun cika da farin cikin gabatowar wannan wata mai daraja watan da Allah yake Bu ofofin rahmar sa wata mai albarka wata mai daraja yau tun safe su Farha suke ta kwalema a part in