← Book details Rabo Ya Rantse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 94

Sashe 17

Rabo Ya Rantse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

hannun sai na maido ki gida" Ta zaro ido wanda hakan ya ara fito da kyanta wanda ba kowa ne yake gane hakan ba. "So kake ai gunduwa gunduwa dani agida" Ya wani kashe mata ido aya. "To niba mijin ki bane,Hurry up and let's go back" ewa tsaye yayi kafin ta tashi har yay tafiyar shi bin bayan shi tayi Allah yasa har suka je bakin layin basu ga kowa ba ya bu e mata front seat ta shiga shi kuma ya shiga driver seat Lumshe idanu tai Sabida wani mahaukacin sanyin Ac tare da amshi daya cika motar ita sai tace tunda take a rayuwa bata ta a ganin mota mai kyan wannan mota ba, ( hhh to farha ai masu abu da abun sune da mai kamfanin madaki motors kike tare a rashin sani ) tafiya suke kamar ta kurame shi yana can duniyar tunanin dalar daya aukowa kan shi ba gammo, ita kuma sanyi da amshi da fargabar gida sun sa tai tsuku. Jifa jifa yake aga wayarshi wanda duk maganar da yake bada hausa yake yiba da turanci yake yinta. A daidai ofar an agundi Yayi parking ya kashe motar ya auki face mask ya saka wadda ta lura kamar sakata ya zama a'idar shi. "Muje ko" Daga haka ya sauka daga cikin Motar. Yayi gaba tabi bayan shi gidan sarkin ori Suka shiga kai tsaye akin dake soron gidan ya shiga bayan ya tu e takalman shi Dattijo suka tarar a zaune yana shan shayi Suka gaisa dashi Aliyu yace. "Na kawo ta Baba a duba hannun ta" Dattijon ya aje Kofin shayin. "Allah sarki yarinyar kace kenan? matso mugani jikata" Aliyu yayi murmushi yana ayyana lallai antar Yarinyar tayi yawa. Farha ta arasa gaban Dattijon. "Ki cire hijabin ki fito da hannun" Da sauri Aliyu yace. "A,a zata fito dashi a haka ai yana da hannu, Fatima fito dashi ta cikin hannun shi" Tayi yadda yace Addu'a Dattijon yayi Kafin ya cafki hannun da sauri yana Matsa shi. "Wayyo Ummata Washhh zafi" Ta fa a tana cije bakin ta. Kafin a gama Gyaran ta gama Jigata da gumi da hawaye. Ana gamawa ta sunkuyar da kanta tana Kuka wiwi Aliyu ya cire ku in da bai san adadin yawan suba ya aje wa Dattijon. Godiya dattijon yayi tare da cewa. "Wannan yarinyar taka akwai rigima bari na shiga daga ciki Allah ya bata lafiya. Daga haka ya mi e ya fita daga akin. "Ki shuru dare nayi, Ki tashi na kaiki gida" Kukan take bata kula shi ba. Ya mi e tsaye ya nufi hanyar fita. Da sauri ta mi e agarin saurin ta take Hijabinta aiko ta fa asa tim. Cikin azama ya juyo ya agota. "Kema gaki arama kina sanya wannan abun yayta kayar dake" Hijabin ne ya cukurku e dole ya sanya hannu ya zare mata shi yana warware wa. Farha tai saurin sanya hannu tana kare Jikinta sabida daga ita sai doguwar rigar atamfa wadda ta kama jikinta sosai Daga saman irjinta ya bullutso yayo sama dama duk antar ta Allah ya bata sama da asa ba laifi kuma masu fusgar hankali. Aliyu cikin mamakin Halittar Jikinta wadda ya kalla a rashin sani lokacin daze mi o mata hijabin Ya bata Hijabin Ya fita daga akin Har ya arasa Cikin mota tana la ai la an tafiya Haka ta shigo Cikin motar duk kunya ta gama kamata. "Raguwa sarkin raki" Ya fa a batare daya kalleta ba yaja motar suka bar wajan, a wani ha an restaurant yay parking. Ya juyo ya kalleta. "Wait for me, I'm coming now" Daga haka ya bu e motar ya fita. Minti kusan goma sai gashi nan da Ledoji Manya guda Biyu a hannunshi ya zaga Back Seat ya aje su. Sannan ya dawo ya shiga motar ya zauna ya tayar da motar suka cigaba da tafiya idanunshi akan kwalta. "Are you waiting for me? be patient" Taji muryar shi acikin kunnenta ba tare daya kalle taba. Har suka arasa bakin layin su. Babu wanda yayi magana acikin su. Ya kashe motar ya Fita ya kwaso ledojin Itama ta fito. "Muje na rakaki" Ya fa a, tana gaba yana binta a baya har suka arasa bakin ofar gidan wanda yayi daidai da lokacin da kawu ya fito daga gidan. Farha taja da baya ta koma bayan Aliyu cike da tsoro. "Bawan Allah ga kawu nan na shiga uku" Ga mamakinta sai taga ya tunkari kawu ba tare da wani tsoro ko fargaba ba. Ba tada za in daya wuce tabi bayan shi haka tabi bayan shi kamar kazar da wai ya fashewa aciki. Har asa taga tsugunna yana gaida kawu. Da gudu tayi cikin gida Kai tsaye aki ta nufa ta haye saman gado. Jim ka an kawu ya shigo yana wala mata kira. Jiki na rawa ta fito ta tsugunna a gaban shi. "Allah ya taimake ki, Gobe zasu zo a aura aure amman ki sani duk abin da ya faru dake kada ki nemi gidana" Daga haka ya juya yabar wajan. Tana shiga aki Zuhuriyya ta biyota da ledoji. "Wai gashi inji wani a waje yace wai Allah ya baki lafiya" Umma ko kallonta batai ba jiki a sanyaye ta ebe ledojin ta shige aki. Aliyu daga wajan Farha gidan Kakannin shi inda annen mahaifin shi suke ya nufa Bayan sun gaisa da baba usman Aliyu ya zaro ku i kimanin dubu ari ya zube a gaban anin mahaifin shi. "Baba in Allah ya kaimu Gobe da misalin arfe goma Musa zaizo ya kaiku andago na nemi auren wata yarinya Mahaifinta sadaki ka ai ya bu ata daga wajena, Amman dan Allah baba wannan magana ta zama sirri bana son Kowa yaji inba sauran kawu naina ba" Baba usman ya cika da farin ciki addu'a yahau yiwa wannan aure yana saka mai albarka kuma ya tabbatar wa Aliyu da cewa in ba sauran annen shi da zasu je tare ba ko matansu ba zasu ji ba, Aliyu yayi masa godiya yabar Gidan. Kanshi tsaye gida kuma ya nufa yaje part in Ammi bayan sun gaisa ta kawo masa shayi. "Ammi nifa gaskiya aure zan ara Mami tace sai ta huta zata dawo" Ya fa a yana son ya gwada yanayin ta idan har ta amshi maganar sai ya fito fili ya gaya mata gaskiyar shi. e ranta tayi kamar yadda ta saba duk lokacin daya zo mata da batun aure. "Ban amince ba" Ta fa "Ammi dalilin ki? shin aurena zai sa awa shari'a ne ko kuma arin aure haramun ne?" Ta ha e ranta kamar bata ta a dariya ba. "Ko aya Malam zaka ure ni, auren ne kawai banga damar ka ara ba ka jira har Allah ya bawa Mami rabonta in ma dan shine kake cewa zaka ara aure" Ganin ta au zafi yasa ya sassauta Murya. "Allah ya baki ha uri Ammi ya huci zuciyarki" Daga haka ya mi e ya fita daga parlon, Ammi ta bishi da kallon tausayi sai dai ba zata ta a barin shi yayi aure ba domin tana gudun sharrin matan wannan zamani sannan uwa uba tana taya mami kishi kasancewar ta ar yayarta wadda kuma ita ta ha a auren sabida haka ba zata so ai wa mami kishiya ba. Daran wannan rana Daga Aliyu har farha sun kwana cikin zulumi. Washegari gidansu farha ba'a tashi da shirin komai ba kamar ba auren budurwa ba,kawu yace baze gayawa kowa a dangin shiba kuma yace baze kayan aki ba haka umma ma tace ficikarta bazatai ciwon kai ba wajan arfe Goma Ba in suka araso ofar Gida Halifa ya kira kawu, Musa sarai ya gane Halifa amman shi Halifa bai gane musa ba dalilin kuwa daya sa Musa ya gane Halifa sabida rabon ku in daya yi musu a kamfani, Shi kuma Musa da face mask a fuskar shi wannan tasa Ba kowa zai shaida shiba Iya ma ota kawu ya kira aka shinfi a babbar tabarma a ofar gida bayan addu'oi aka aura auren FATIMA ABUBAKAR MAI BULO DA ALIYU AUDU MADAKI, Akan sadaki naira dubu ari addu'a akai aka shafa gaba aya mamaki ya cika musa wanda dama tunda Aliyu yayi mishi waya ya sanar masa acikin mamakin yake. Buhun goro da alawa Baba Usman daya siyo ya mi awa kawu aka rarraba Musa ya ebi su Baba usman a mota dan ya mayar dasu gida. Bayan ya cewa kawu zai zo ya auki amarya su wuce kamar yadda Aliyu ya bashi umarni. Cikin mamakin sunan wanda aka fa a da angon farha Halifa yake na e tabarman da suka zauna, sai dai tunanin da yayi na suna ai da yawa wanda ake cin karo dashi iri aya yasa ya watsar da mamakin nashi ya shigar da tabarmar gida ya shiga sabgar shi. Kawu yana shiga cikin gida ya watsawa umman farha sadakin farha. Tare da cewa. "Burunku ya cika, Ke kuma maza ki ha e kayan ki yanzu Mijin ki zai zo ya auke ki, kuma koda wasa kada ki zo min gidana da kowace irin matsala" A wannan karon umma tai magana Sabida ta riga ta saduda da lamarin. "In sha Allah wannan aure alkairi zai zame mata, Ni mahaifiyarta ce ya Allah ka kare min ita aduk inda take aduk inda ta tsinci kanta Allah ka sawa mijinta son ta da tausayin ta" Umma ta fa a tana hawaye dan jiya nasihar umman zage yayarta ta ratsa mata Jiki wanda tace mata kada ta yarda taiwa arta Mugun baki ko fata. Bayan musa ya kai su baba usman ya aje su Aliyu yayi masa waya sun jima suna magana kafin Musa ya nufi Gidan su farha cike da mamakin maganganun Ubangidan nashi. Musa ya arasa har ofar gidan yasa yara su masa magana da kawu wanda kawun yace ba inda ze fita farha kawai ta auki kayanta tabi shi Farha kuka Umma kuka da sauran an uwanta wanda kawu yace ba mai binta rakiya itama kuma baya neman tazo masa gida haka Su Ikram suka auki jakar kayan farha wadda suka ha a mata suka fitar mata da ita wajan mota da yar Babarsu Ru ayya ta are farha daga jikin Umma wadda take kuka kamar ranta
Chapter 17 · 0% Book details