Sashe 25
Rabo Ya Rantse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
audu sai dai Yadda Usman yake masa mugunta a littafinsa da zarar an sai masa haka ze yaga in Uban ya dawo yay ta masa fa a yana kammala Firame mahaifin shi ya kaishi kasuwa ya nuna masa harkar fata Ganin haka yasa Saude tace sai an kai usman shima amman uban yace ba yanzu ba sai ya kuma wayo. Zuwan shi kasuwa ne yasa shi yake an jin sau in azabar saude da anta wa anda suka auke halin ta tsaf ga sharri haka Usman zai hau katifar audu ya maka fitsarin kwance da safe saude ta na awa Audu duka. Watarana mahaifin yayi tafiya sai yace audu kada ya fita kasuwa dan bai san hanya ba dama kuma abin da yasa yake tafiya dashi kasuwar ma dan ya fahimci yana cin wahalar zaman gidan ne. Usman da Ashiru sun maka fitsari Saude ta fito da kayan fitsarin ta saka audu a gaba tana duka yana wankin cikin haka Amina ta fa o gidan da tsohon cikin ta yadda taga ana azabtar da an yayarta har kuka tayi bata tafi ba sai da Audu har da kayan shi ta ha a bayan sun gama zage zage da saude. Amina ta saka audu a gaba har gidan ta dake Fagge tana auran miji mai ku i tana zaune lafiya da kishiyarta wadda take goyon a mace itama Mijin Amina yayi murnar ganin Audu kuma yayi takaicin Yadda Amina ta bashi labarin wahalar da audu yake sha . Bayan Sale ya dawo saude ta tare shi da arya da gaskiya haka yazo har gidan Amina yace ta bashi audu fafur ta hana shi abin har yakai su da ba da i haka ya tafi yay fushi yace ya bar mata shi ta cinye. Mijin Amina da ita kanta Aminar sun auki son duniya sun orawa Audu wanda ya murje yayi kyau kuma ya koma makaranta anan faggen Mijin Amina na masifar son Amina wanda soyayyar da yake mata ne yasa ma har take samun sa ani da Kishiyarta wadda take Goyon a mace mai suna tajira. Haka Amina ta haifi arta mace mai kyau kamar ta fara jajir sabida soyayyar da Mijin ta yake mata ne ya sanyawa ar sunan ta itama yarinya taci suna Amina Audu ke renon Amina komai ya samu ita wata irin sha uwa ce a tsakanin Audu da Amina wadda komai na yarinyar shike mata Wanda hakan ya ara jefa tsana mai arfi a tsakanin Kishiyar Amina da arta wadda ta an tasa Suka tsani Audu suka tsani Amina da arta Tuni Audu ya mance da rayuwar Gidan su Har ya kammala secondry insa Lokacin Amina ita kuma tana Primary ta an tasa ta zama budurwa Bayan kammala karatun Amina na firamare sai tafiya ta kama Babanta da Mahaifiyarta sai suka zauna a wajan Babar tajira ita da audu a hanyar su ta dawowa ne sukai hatsarin mota wanda Amina anwar mahaifiyar audu tare da mijinta wa anda sune mahaifan Amina Allah yayi musu rasuwa ta sanadin wannan hatsari. Tashin hankali audu da amina sun shiga ana sadakar bawai yayan salamatu ya auki amina sabida yace baze bawa babar tajira ri on amina ba sabida itama tana fama da kanta wannan ne sanadin da Ri on Amina ya dawo wajan Yayan mahaifiyarta shi kuma audu sai ya koma gidansu wanda ya tarar annen shi dik sun girma ba yadda sale yayi haka ya komar da Audu kasuwa wannan tasa wutar iyayya ta ruru a tsakanin saude da anta wadda suke jin kamar su jefa audu a wuta. Yana fuskantar cin mutunci wajan ta da anta gefe Guda soyayya mai arfi ce ta ullu a tsakanin audu da Amina wanda mahaifin audu ya fahimci haka bai asa a gwiwa ba wajan tunkarar yayan su salamatu da batun yana son Audu ya auri Amina ba'ai wani ja yayyaba aka aurawa audu amina sashe guda sale ya ginawa Audu acikin gidan wanda Amina ta tare aciki. Bata da wata matsala daga farko sabida audu yana samun Ku i fatar ta kar e shi dan a lokacin batai shekara da auran shiba ya biya musu hajji ita da shi da babansa da yayan mahaifiyar su lokacin saude kamar tayi hauka dan ba in ciki ita da anta basu jima da dawowa ba Allah ya auki rayuwar Sale mutuwar data girgiza wannan ahali musamman audu. Haka akai zaman makoki aka watse audu ya koma kasuwa sai dai abu kamar wasa kasuwa ta koma masa baya komai ya ta a narkewa yake hatta jarin sa saida ya rasa Kawun su yayan mahaifiyar su da ansa suke taimakon audu da kayan abinci. Ga lokacin Amina ta sami ciki ya tsufa komai yazo kuma ya tsaya Ga cin mutuncin saude da anta a kullum cewa suke sai audu ya tashi anyi rabon gado watarana Amina ta tashi da na uda ba yadda audu bai da Saude ba akan tazo sukai Amina asibiti sabida cikin dare ne amman ta i daga arshe ya fita ya kira matar kawun su suka tafi asibiti Amina ta haifi anta namiji fari mai kyau dashi ato suka dawo gida da safe. Tashin hankalin da suka tarar yafi gaban kwatance dan su Usman da suke samari a lokacin sun watsowa Amina kayanta sun rushe angaran Wai ai rabon gado basu yarda da zaman Audu agidan ba Amina na kuka Kawun su ya bata aki guda agidansa anan suka cigaba da rainon ansu Abubakar Sadi Sunan yayan mahaifiyar su Audu ya saka. Rayuwar yau da gobe tai musu zafi Audu yana ji yana gani su Usman suka rabe gidan mahaifinsu kowa yaja sashin sa suka gine Sauran gado gona filaye duk basu bashi ba haka ya cigaba da zama agidan kawu Abubakar yayan mahaifiyar shi da taimakon an kawun shi wa anda suke yayye garesu shida Amina suka gina masa aramin gida anan ofar na'isa ya koma lokacin ne Amina wadda sadi ke cewa ( Ammi ) ta haifi anta Aliyu wanda tsiran su da sadik shekara biyu ranar data koma sabon gidan ta haifi Aliyu wanda aka sanya sunan mahaifin ta Marigayi Alhaji Ali Fagge babanta ita da Tajira. *RABO YA RANTSE! littafin ku i ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a auka a turo,shaidar biya 09022260850* *RABO YA RANTSE* *27* *A LOVE STORY 27* Aliyu yafi sadi kyau nesa ba kusa ba kuma yafi sadi Girma tunda Audu ( baba ) da Ammi suka ora ido akan Aliyu suka auki soyayyar duniya suka orawa Aliyu wanda haihuwar shi tazo wa Baba da nasibi domin ya koma kasuwa Lokacin Aliyu na da wata aya a duniya arzi in Baba ya ninka nada tuni ya rushe gidan shi ya sake ginin zamani ya gyarawa yayan mahaifiyarsu gidan shi Lokacin Ammi Ta ara kyau hankalinta ya kwanta ta cigaba da rainon anta da suka taso kamar an biyu ga kyau ga farin jini dan duk inda suka shiga ana son yaran. Duk da yadda su Usman sukai wa Audu ( baba ) hakan bai saka ya i suba haka yaja su ajiki koda zasu yi aure shi yayi komai wanda mahaifi kewa a hatta kayan akin suwaiba shine yayi mata yana kyautata musu sosai tuni an saka su Aliyu a makaranta mai tsada Yanayin arin Aliyu ne ya sanya aka ha e su Aji aya da sadi wanda suka sha u sosai sai dai akwai bambancin hali. Aliyu tun yana yaro miskili ne mai taurin kai marar far'a da son mutane baya da yawan magana sosai Kullum yana jikin mahaifin shi sai dai yadda Baba ke yawan zuwa da Aliyu cikin Gida wajan su Usman yasa Aliyu yake son dangin mahaifin nashi duk da irin abin da sukai wa mahaifin nasu wanda Ammi ta ullata aranta amman ikon Allah duk abin Aliyu bai ta a ri on su ba wani bin har zuwa cikin gidan yake ya kwana abin Allah saude tana mugun son Aliyu sabida lokacin ta tsufa tuni ta nemi yafiyar audu akan abin da tai masa suma su Usman sun nemi yafiyar shi kuma ya tabbatar daya yafe musu matsalar kawai Ammi ce da ko magana bata shiga tsakaninta dasu usman Sabida tace ita dasu har abada akan abin da sukai wa mijinta. Komai da su Usman suka mallaka wanda suka dannewa audu yau da gobe ya are tas gidajen sun ma duk sun lalace ajikin Audu suke ra e a kasuwa shi kuma baya musu Mugunta dan ya tabbata da dama sharri an aike ne Kuma tunda sun tuba sun gane Laifin su shikam ya yafe musu har ranshi dan baka fushi da naka. Allah yayi wa saude rasuwa tsiranta da kawun audu ba nisa haka dama rayuwa take. Sai da Aliyu ya shekara biyar ammi ta haifi salma mai sunan babar Audu daga salma sai bashir daga shi sai Safna daga ita sai sajeeda. Lokacin raino yayi wa Ammi yawa sai aka auko mata mai aiki Hajjo wadda suke zaman lafiya hajjo na taya ammi rainon su safna su Aliyu na Secondry Lokacin Jss 1 bashir da salma kuma na primary dan duka lokacin Sadik na shekara sha biyar Aliyu sha hu u salma tara bashir bakwai Safna hu u sajeeda aya adaidai wannan Lokacin Allah ya auki ran Audu ya rasu yabar Ammi da wa annan ananun yara bida da bi ya rasu yabar tarin an uwa da masoya mutuwar data tarwatsa farin cikin Ammi bata da uwa bata da uba bata da Miji yayan mahaifiyarta mai jin anta shima babu sai ta rungumi anta sune komai nata tasaka su agaba tana hira tana dariya tana kuka Hajjo ce mai bawa ammi baki tana rarrashin ta Yau da gobe kayan Allah komai yazo ya are domin zara bata barin dami Ammi ta cinye komai da audu ya rage sai gidansu da suke cikin sa. Suma su Usman lokacin nauyin a yayi musu yawa ananun a garesu dan aure auren tsiya gare su gashi babu Suma basu samu ba bare su taimaki Ammi. Makarantar su Aliyu suka koro su sabida basa biyan ku in term dan makarantar Ku i ce Lokacin Ammi tai kuka tai kuka kamar ranta zai fita domin abin da