← Book details Rabo Ya Rantse Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 94

Sashe 45

Rabo Ya Rantse Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

daban kuma ya bawa safna yace ta mi awa Farha ta amsa tana tura baki ta nufi akin daga bakin ofa ta wurga mata Ita kam farha kwanciya tayi tana kuka shiyasa bata ma ji shigowar Safna ba bare tasan abin da ta aikata matan. Gaba aya tunanin Farha shine yaushe zata sami anci yaushe ze dena oye ita matarshi ce abin da ya ara fusata ta shine halin Ko in kula daya nuna mata bayan ko wace mace idan ta tsinci kanta a waryar manya Mijinta yana tsayawa ya riritata ya kula da ita amman ita jiba yadda ya barta kamar ma ya manta abin da ya aikata mata tabbas maganar daya fa a mata gaskiya ce daya ce mata baya son ta da gasken yake don inda yana son ta baze ta a yi mata haka ba. Ammi ta dubi Aliyu cikin fa "Amman baba me yasa zaka min haka? damu da ita aya ne?" Ya ha e rai sosai ya watsawa su safna Mugun kallon daya sa suka mi e jikinsu na ari suka bar wajan ya dubi Ammi har Lokacin Fuskar shi babu walwala. "Ammi menene abin nuna fifiko ga wanda baka san waye a wajan Allah ba? danna auka mata abinci acikin naku shine matsala to Ammi ki ha uri Da laifin dana yi" Ta hayo masa ka da maganarta mai arfi. "Naga fa abun naka yayi yawa ga Kitchen nan tazo ta girka nata mana dole abin da muka ci shi zata ci salon raini ya shiga tsakanin mu to wallahi ka kiyaye ni Ka shiga taitayin ka ka kama kanka ka fita daga sabgar yarinyar nan tun kafin na sa a maka" Ya rasa me yasa Ammi ta i jinin fatima kuma de yarinyar ba rashin Kunya takewa Ammi ba amman baki aya ammi tabi ta tsaneta ya fuskanci har yaran Ammi su safna ma sun Tsaneta. "Ammi bazan kuma ba ki ha uri" Ya fa a cikin mutuwar Jiki Ammi ta kauda maganar tana cewa. "Niko me akaiwa Mami ne tunda ta dawo bata shigo Min ba nida azu ma zanje naji lafiyarta" Ya ta e baki tare da cewa. "Nima ban san meya hanata zuwa nan in ba duk tabi ne ta damu kanta akan rashin haihuwa azu ma kuka ta gama yi maybe ko wannan matsalar ce data ora damuwarta akai yasa ta i shigowa kin san wani in yana cikin wani yanayi baya shiga cikin mutane" Ammi tace "Haka ne ai ba ita ka ai ba kowa ma burin sa ai ka haihu kaima muga naka an Allah dai ya nuna mana wannan rana in kaje ka turon ita nai mata nasiha" Ya jinjina kai yana cewa. "Da aure da haihuwa da mutuwa duk Lokaci ne Allah ya bamu wa anda zamu iya dasu shi kuma Allah ya iya mana gaba aya Kuka ai bashine ze bata a ba Allah ne mai badawa Ammi ina son haihuwa amman wallahi bana agawa kaina hankali akanta dan nasan daga Lokacin yayi Allah ze bani" Ya fa a yana Lumshe ido. Ammi cike da tausaya mishi tace. "Haka ne baba Nina sanka akwai tawakkali In sha Allah mami zata cika maka gidannan da a masu Kyau irin ka harma da biyayyarka" Yayi Murmushi yana shafa kai bai dai ce Komai ba. ewa Ammi tayi "Bara naje nai wanka naci abinci ka araso daga ciki mana naga kamar yau ba zaka fita Office ba" Ya bita da ido be magana ba sabida yadda ya matsu ta tafi yaje Inda zuciyarsa take muradi........... *RABO YA RANTSE! littafin ku i ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a auka a turo,shaidar biya 09022260850* *A LOVE STORY 53* Sakin ajiyar zuciya yayi mai arfi lokacin daya tabbatar Ammi ta ullewa ganin sa a hankali ya mi e tare da nufar ofar akin yana mur a handle in yaji ta a bu e ya shiga ya sanya key ya rufota yabar key in ajiki a tsaye ya tsaya a kanta hannunsa duka a cikin aljihun trouser inshi kukanta yake sauraro wadda ita sam bata ma san da shigowar shi akin ba, Sannu A hankali ya zauna a gefen gadon yasa hannun shi aya ya tallafe Fuskarshi dashi gaba aya jikinsa yayi sanyi da yadda yaga lamarin nata har Kusan minti ashiri yana zaman jiran ta gama kukan suyi magana ganin bata san yana wajan ba yasa ya matsa Kusa da ita ya janyota jikinsa. Idanunta har lokacin a rufe suke kuma se arin tashi daga jikin nashi take sedai yadda yabi ya kanainaye ta ya kasa bata damar Mi ewa. "Shiii fatima, wai meye haka kukan ya isa haka kada kanki yayi miki ciwo" Ya fa a yana share mata hawayen nata da tafin hannunshi. Juyawa tayi ta dena kallon saitin Fuskarshi yayi Murmushi. "Au wai kukan nawa ne, To naji nayi laifi amin afuwa bazan kuma ba" Ya fa a sanda yake arin Juyo da ita facing inshi ya ta a wuyanta akwai zazza i sosai ajikinta Mi ewa yayi bayan ya sauketa daga jikinshi ya koma toilet in ruwan umin ya kuma ha awa ya dawo ya agata cak shiya taimaka mata wajan rage kayan dake Jikinta duk Kunya ta gama kamata haka ya kuma dannata acikin aton bawon dake sha e da ruwan umi ta jima aciki shikuma yana tsaye a kanta seda ya sauya mata ruwan har sau uku sannan ya aukota suka fito cikin aki saman gado tahau tana rawar arin zazza i ya arasa gaban kayanta ya auko mata Doguwar riga da yar ta yarda ya saka mata. Ya sunkuyo daidai Fuskarta cike da tausaya mata. "Me zaki ci yanzu ina Break fast in da safna ta kawo Miki?" Ta zubo da hawaye. "Ni bazan ci komai ba bakina ma kwata kwata babu da Ta fa a tana jan Bargo ta rufe duk Jikinta. arasa inda takeaway in take yashe ya auka Doya ce aciki da wai ya tabe baki ya aje a saman Madubi ya fita daga akin tare da rufota da Key gudun kada wani ya fa a mata yaga halin da take ciki. Mota ya shiga bayan ya saka face mask ya boye Fuskarshi da kansa yaje ya siyo mata an abinda zata ci marar nauyi ya kar o mata magani a pharmacy bayan yayi wa likita bayanin halin da take ciki Lokacin daya araso ana kiran sallar la'asar seda yayi sallah sannan ya wuce koda ya arasa falon Ammi su safna na dinning suna cin sauran abincin azu dan ba'ai girkin ba Ammi Kuma tana akinta ya zauna a falo ya wayance da danna waya ganin yanayin sa yasa suka Mi e har suna rige rigen barin wajan ya Tashi ya nufi akin farha ya bu e ya shiga ya rufo ofar tana zaune ta idar da sallah a gabanta ya tsugunna bayan ya aje kayan hannun shi ya ta a Goshinta yana cewa. "Yaya yanayin jikin naki?" an kalle shi gaba aya taga ya sauya mata duk Jikinsa a sanyaye har fa awa idanunshi taga yayi. "Da sau i Alhamdulillahi" Ta bashi amsa bayan ta kawar da kanta dan gujewa mayen kallon da yake faman binta dashi. Ya Bu e Ledar hannun shi ya fito mata da robar farfesun Kayan cikin rago da soyayyen dankali se kaza Wadda aka gasa mai romo se shinkafa da miyar hanta gaba aya amshin abincin ya cika akin ya zauna a gabanta ya tan washe afafun sa. "To wanne zaki ci anan Nasan baki ci Komai ba" Ta lumshe idanu sabida yadda yayi mata maganar cikin kulawa yayi mata ita. "Shinkafar nake son ci dan yunwa nake ji sosai" Ta fa a tan ha iyar yawu. Yayi Murmushi. "Farfesun fa?" "Shima zanci duka" auki aramin spoon in cikin abincin ya bu e robar yana iba yana bata a hankali ta No e ta i amsa ya an harareta da sauri ta amsa tana ci tun tana jin kunya harta ware tana cin abincin ganin ta soma oshi ya tura mata farfesun gabanta wannan karon da kanta taci Kuma taji da in bakinta ruwa ya bu e mata tare da magungunan daya amso mata duka na gajiya ne da rage ra i ta amsa tasha zata kwanta ya hana yace ta bari abincin ya narke turo baki tayi ta juya masa baya itafa ya soma isarta haka ya hanata ta kwanta seda yaga ta soma bacci a zaune sannan yace taje ta kwanta aiku nan da nan bacci ya auketa wanda bata samu a daran Jiya ba arfin Fanka ya ara mata sabida Ac'n akin ta lalace ya tattare kayan abincin ya aje a gefe ya Rufe mata rabin Jikinta ya fita daga akin bayan ya rufo shi. Cikin gidansu mahaifin shi ya je Kuma ya sami annen Babansu duka a gida zama yayi suna gaisawa Kuma da alamun sunji da in zuwan nashi nan da nan yara da manya sukai ta fitowa suna Mishi sannu da zuwa matan kawunan shi suka fara jere masa kwanukan abinci agaban shi ruwa ka ai yasha ya fuskanci Hirar da Baba usman keyi masa. Wadda Godiya yake masa akan hidimar da yake yi musu ya an yi murmushi. "Baba kada ka kuma yi min godiya ai in ban yi muku ba wa zan yiwa Kune fa kuka fito ta tsatso aya da mahaifinmu wallahi Ku nakewa kallon Baba a yanzu" Albarka suka ha u suna sanya mashi acikin Gidan sukai sallar magariba wadda Baba Usman yaja su bayan sun idar ganin ba wata matsala a gidan Komai suna da dan hatta sola ya sanya an Musu ko ina haske ga gida yasha gyara. "Baba zan koma ko akwai wani abun?" Baba Usman yayi Murmushi "Haba Aliyu ba komai wallahi dan kayan abincin da ka sa aka cika mana store dashi ko rabi bai are ba Komai akwai shi Alhamdulillah" Sauran ma suka ha a baki wajan yi masa godiya ya fita ya shiga Gidan kawun su Ammi nan in ma ya an jima dan har isha'i yana cikin Gidan yana fitowa yayi sallah ya koma Gida ya shiga Mota ya kuma siyowa farha abinci da fruit, A mota yabar su seda
Chapter 45 · 0% Book details